Sashe 13
Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wucewa tayi wajen driver zuwa dauko Aabid saboda 1:30pm ake tashinsu,Amana yan gayu har takama takeyi tana kamewa a bayan mota,
Tana zuwa schl din har an tashi Aabid da gudu ya shigo motar yana rungume Amana,schl bag dinsa ta karba suka karaso gida,
A palon sama suka iske Alim zaune cikin 3qtr brown da Riga coffee color,sai kamshi yakeyi part din dama yan aiki sun gyarashi neat ko ina kyalli yakeyi, Suna shigowa suka rafkawa Alim sallama tare da cewa Daddy mun dawo cewar Amana kaji shishigi wajen Amana,
Daya room din opposite Na Alim ta kai Aabid ta cire masa uniform tare da jefa kayan a washing machine,ta hau yiwa Aabid wanka,a towel ta nadoshi ta fito dashi Palo yana bayanta ta zaunar dashi a kujera,komawa tayi ta shanya kayan da ta cire masa,sannan ta fito da sauri tana ta fiyarta zata dakkowa Aabid kaya ji kake timmm skert ya harde ta fadi,wannan karan sai da taji ciwo a kafarta,Alim ko a bai ce ba Aabid ne kadai yayi mata sannu,
Abinci ta dauko musu suka ci abinsu a Palo,Alim sai satar kallonsu yakeyi yanda suke wasa da cokula,
Bayan ta shirya Aabid cikin uniform din islamiyya nan kuwa ba nisa a kusa da gidan Alim Islamiyyar take,a kafa ta kai Aabid ta dawo ta gyara wajen da suka bata kana ta wuce room dinta.
Mum Alim zaune a bakin makeken bed dinta da Alama nazari takeyi a ranta tana ta tunanin yanda zata bullowa Abban Alim domin so takeyi tayiwa Alim aure tana jin tsoron karfa Alim ya hadu da wacce yake so,
Bari zanje gidan Alim da kaina next Wk zamuyi magana dashi dole ya karbi zabina haka ta gama sake sakenta sannan ta fita kitchen wajen masu girki tana zunduma musu ashar basu gama girki a kan lokaci ba,
Gidan baki kuwa yana nan inda yake sai abinda ya karu domin lalacewar tayi yawa,yayyen Amana mata guda biyu an sako su daga gidan miji suna nan an hadu ana sheka tsiya,Baba kuwa wato sulemanu Harka ya shagala wajen wata bakuwar bazawara da ta zo wajen matarsa wato umma Babar Amana kenan sun bude harka a boye suke fasikancinsu a gidan liman abokinsa,wani dakinsa da yake harkar bokanci anan suke kwashewa tare da wannan bazawara me suna Salamatu, har yau matan gidan basu gano ba,har Babar Amana bata sani ba sabo da Salamatu ta kware wajen rike sirri,bata wasa da sirri.
5pm Aabid ya dawo daga islamiyya, 8pm Amana ta dauko abincin Aabid ta zo sama part din Alim,Aabid yana can yana wasansa Alim yana cike wasu takaddu Amana tayi sallama ta shigo dauke da tire,ta kalli Alim Wanda ya ke cikin jallabiya fitted fara tas sai sheki yakeyi,yayi kyau matuka kamar aljani cewar Amana,sai kuma tace barka master asha aiki Lfy master,
Ko kallonta Alim baiyi ba yana jinta,TV Amana ta kalla taga ana nuna wasan Barcelona da Chelsea, da sauri ta ajiye abincin gefe,wata uwar sufa tayi a kasan center carpet kamar zata fada cikin TV din,ta tsura ido tana kallo,
Can Messi ya fara yanke yan wasan Chelsea Ya wuce zai kaita raga Amana da karfi ta fara uhum....uhummm...yawwa....yanke shege....sai Messi.....a....goal.......sai tafi ta fara raf raf tana murna kamar an mata bushara da gidan Aljanna,Alim dake aiki cak ya tsaya yana kallon abinda Amana takeyi,
Can kuma Iniester ya dakko ball Amana tace ehem..good idea mikawa Suares mana ai kuwa Iniester kamar yaji ya mikawa Suares,
Amana ta fara ihu cikin siririyar muryarta tana tafi Suares ya buga sai ta daki pose ta dawo ai Amana tace Oh.....God..tayi kararrawa...shege yayi kararrawa, dakiki Suares ya zakayimana haka dabba shashasha dolo,common ka buga ta ka wani makata sama,
Ana ta ball tayi zafi Chelsea suka farke 1-1 Amana tayi lakwas tana zage zage,Alim kuwa tsayawa yayi yana kallon abinda Amana takeyi kamar tv, ana ball fa can wani lokaci Suares yaci daya,minti kadan messi ya karawa Chelsea,sai ga Amana ta mike tsaye tana ta tafi da tsallen murna,kuma gashi an tashi 3-1 Barcelona sun cinye Chelsea.
Juyowa tayi taga Alim ya kafe ta da ido a tunaninta shima ball din yake kallo shi kuwa Alim tunaninsa anya Amana kalau take kuwa.
Abinci ta jawo tare da cewa Aabid my Boy zo maza muci abincinmu sai wasa kakeyi kana gani munci ball ko murna baza ka taya ni ba,shi dai Aabid dariyarsa yayi ya zauna,
Abincin ta bude wata hadaddiyarr jallop din taliya da doya tasha kifi,ga wani lemon dabino da kwakwa da ta hada me sanyi da dadi,ga wani flask dan karami ta hada coffee lafiyayye,wani plate kuma kankana ce da yawa ta yanka da pork ciki,gefe guda kuma wani farfesun kazane sai kamshin dadi,
Kallon Aabid tayi tace boy da wanne zamu fara?Alim tun a ido yasan girkin zaiyi dadi da ace zasu bashi to da ba shakka zai ci,amma yaga Amana kwatakwata bata iya tayi ba a rayuwarta,idan zata ci mene a gaban mutum baza tace gashi ba,kuji Alim din nan da kwadayi,to Amana a gidansu basawa juna tayi haka suka taso,
Yau kamar Amana tasan Alim me yake sakawa a ransa,taga yanda yake kallonsu,kawai sai tace uhm mutum da yake siyo kayan abinci a cinye a dinga hanashi,ban taba yi masa tayi ba,yau dai bari Na gwada ko zaici,
A plate ta zuba girki ruwa ruwa malam yana tiriri da kamshi ta je har gabansa ta ajiye masa gashi ko zaka iya ci,dawowa tayi ta zauna,a ransa yace to iya taliyar zata bani jibi fa abubuwa,bai gama tunani ba yaganta taje kasa ta dawo dauke da wani glass jug da karamin glass cup,lemon kwakwa ne ciki ta ajiye masa,ta ebo farfesu nan ma ta ajiye,kankana ma ta zuba masa tasa ta ajiye masa,sannan suka cin nasu da Aabid,kafin kace me Amana da Aabid sun cinye girkin su tas komai coffee kawai basu sha ba,
Alim yana gani yagansu sun fara exercise suna motsa jiki sai tsalle sukeyi,suna faman sheka dariya kamar tababbu,can Aabid ya kwanta yayi flat Amana ta danne masa kafafu yana tasowa a hankali yana komawa,sosai sukeyin gym dinsu,shi Alim mamaki yakeyi har yaushe Aabid dinsa ya koyi irin abubuwan nan?lallai in hakane yarinyar nan ta cika shedaniya,su kuwa kala kala suke gym dinsu idan ta kwanta tayi Sai ayiwa Aabid ma,wurin 30mnt sunayi sannan suka gama,bayan sun huta suka fara shan coffee dinsu,
Alim kuwa sai abincin Amana yakeci yana lumshe ido bai taba cin abinci me dadin Na Amana ba a duniya,saida ya cinye komai ya shanye komai,
Aikinsa yaci gaba da yi sai da ya kwashe 1hr lokacin Amana harta kwashe komai ta gyara wajen,coffee ta hado masa shima a cup ta ajiye masa sannan ta fara koyawa Aabid assignment suna gamawa suka tafi dakinsu tare da cewa Alim Good night Daddy Amana ita a dole Aabid take koyawa tarbiya.
Satin Amana Biyu da fara aiki a gidan Alim yanzu sun shaku da Aabid sosai,shi kanshi Alim ya saba da hayaniyarsu a part dinsa,dama Alim indai ya dauki me kula da Aabid yafi so su dinga yawan zama a part dinsa ta yanda zai dinga ganin meke faruwa da dan nasa,shi yasa baya hana me kula da Aabid zama a part dinsa,ganin yanda yan aikin Alim ma Kansu yan gayu ne yasa Amana ta kara wayewa,amma harkar jagaliyancinta yana nan,bata ragawa kowa sai Alim,uniform dinma sai taga dama take sawa,kayanta take sawa,bata mutunci da matan masu aiki,amma duk ma'aikatan Alim maza natane mutunci sukeyi sosai,tafi yin muamula dasu,mata kuwa tsakaninta dasu sai harara,har girki take shiryawa me dadi ta rabawa mazan,watarana har kaji take soya wa ta basu kowanne me yawa,
Shi yasa idan ka dauke Alim to Amana ce ta biyu da suke girmamawa,
Amana kuma duk kula mazanta ko yatsa bata bari ko da wasa wani ya ce zai rike mata,ita duk harkar iakancin nan bata sanshi ba,ba ruwanta da shi,dan yanzu ko american film da finanan soyayya bata kaunarsu,tafi son film din yaki ko Na sojoji,tafi so taga film din tashin hankali,bata son taga film ana zaman lafiya,tafiso taga Wanda ake kashe kashe ana harbe harbe ana Sara suka,ana harba bum.to fa ka gama birge Amana
Yau Aabid tazo dauka a bangaren Alim sai taga ana film din yaki american film wani Na sojoji me taron mutane,kawai wuta ake ba daga kafa,
Kawai sai ta samu waje ta zauna,Alim kuwa da Aabid suna bedroom har 11pm tayi har Aabid yayi bacci a wajen Alim ba Susan Amana tana Palo tana kallon ba,11-30pm aka gama film din akasa 2 dinsa,duk Amana tana zaune a wajen,har bacci ya saceta ta bingire a wajen,ta wani baje skeet din uniform din nata ya tartare ya dawo Rabin cinyarta Allah yasa tana da wando tight gajere shima Rabin cinya amma da ansha kallo,
Alim yaji karar tv ya fito zai kashe sai yaga Amana ta baje a kasa tana ta bacci skert ya kara tattarewa ya kusa komawa kugu,dankwali ya kwance gashi yayi yalala a kasa,juyi ta karayi tana Sosa cinyarta tare da sa hannu ta zuge zip din skert dinta ta zareshi ta jefar,Alim ya saki baki yana kallon inda zallar baiwar kyau da kyan sura yake,cikin jikinta har yafi fuskarta fari ma kal dashi luwai luwai ko gashin jiki bata dasu,
Can ta kara juyowa ta zuge zip din rigarta ta jefar da ita daga ita sai vest da tight dinta,tana ta baccinta,Alim duk ya diririce,maimakon ya kashe tv sai ya kashe ac ya juya dakinsa kamar munafuki ya kwanta yayi lakwas yana ta nazari,tare da tunanin surar Amana,
Da kyar ya samu yayi bacci,Amana kuwa bata farka ba sai da asuba,ganin inda take yasa ta kwashe kayanta ta arce da gudu dakinta tare da banko kofa tana mamakin yaushe ta cire kayanta,
Sallah tayi ta koma baccinta kasancewar yau Saturday ba kai Aabid schl,ba ita ta farka ba sai 11am,da sauri ta fada kitchen ta hadu da Saude ,Saude tace aikin banza dama zuwa nayi Na fada miki Alhaji ya canja min wajen aiki ya mai dani bangaren gyaran swimming pool yace daga yau ke zaki dinga yi masa abinci,munafuka abinda kike so dama kenan,an manne masa ana tsafi mayya.