Sashe 11
Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan Uzuri har bakin mota ya raka Amana yana hawayen karya,yana to 'yata ga number ta a dinga tunawa da mu,ki tsare mutuncinki kamar yanda Na sanki da kamila,nutsatsiya,a yafemana Amana yar albarka ya karafashewa da kukan maula, driver kuwa Jan motar yayi ya dauki hanyar Gidan Alim,Amana kamar anyi mata bushara da gidan Aljanna saboda murna.
A lagos dinma wata tsantsararriyar GRA suka shiga wacce kaf lagos ba kamarta a kyau sai ka cika me Naira za ka Gina gida cikinta, yawanci turawa ne da sauran jar fata suke zama a cikinta,saboda komai nata tsarin turai ne,gidan da ya fi kowanne kyau,girma da tsaruwa suka nufa,wani gate katon gaske suka nufa wani remote driver ya matsa sai ga gate yayi sama ya dage kansa,abin fa ya bawa Amana mamaki da alajabi tunda take rayuwa bata taba sanin wannan unguwar ba,da badan ita bata da tsoro ba to da tuni ta fara kuka za a yankata,
Cikin harabar gidan kuwa ma'aikata da masu tsaro birjik,wasu sun hau tsani suna goge glasses Na windows,wasu Na bayin flowers wasu kuwa motoci suke gogewa dukkansu sanye da Uniform dark blue wando da riga fara,motoci ne birjik gasu nan sai ka rasa wacce zaka zaba,
Wani new design Na sweeming pool kamar kogi haka yake yabi ta wani lungu ya mike sosai ruwan garai garai blue shar dashi,
Driver ne yace fito hajia,Jakarta ya ja har ciki suka shiga,kalle kalle kawai Amana keyi,kofar ma wasu numbers akayi dialing,sanyi da kamshi ya bigeta,ga wasu kujeru a palon ko a film bata taba ganinsu ba,
Wata TV a jikin bango kusan Rabin bango,sai wasu manyan flowers suna walwal da haske tiririn kamshi Na fita daga jikinsu,sai wani center table Na glass,wanda shima matsa wani abu akeyi a jiki yana juyawa a hankaki,
Center carpet kuwa dake palon idan ka taka sai ka zata nutsewa zaiyi dakai cikin kasa,tana nan zaune tana baza ido wata dattijuwa ta kawo mata abinci saida ta cika gabanta da kayan ci da sha,
Amana da maza ta saba bata Hulda da mata hannu ta dagawa dattijuwar nan tace ai sai Iya Allah dai ya saka,kallo dattijuwa tabi Amana dashi tunda ga shigar Amana matar a ranta tace wai wa kuma Alhaji ya kwaso mana me kama da maza haka,
A mazan ma yan jagaliya,wani matsiyacin kallon matar tayiwa Amana tare da tabe baki taja tsaki tayi gaba,Amana wacce zuciyarta ke tafasa game da matar nan taso daukan mataki sai kawai ta shareta tare da Dora hannunta a kahon zuciyarta ta danne tana lallashin kanta tare da cewar sorry Amana calm Down be patients a fili takeyin maganar,Amana duk kayan dake jikinta ganinsu takeyi masu tsada Na yan gayu amma tana shigowa gidan Alim sai ta raina kanta gaba daya.
Top din data Dora saman rigarta ta cire ta Dora saman kujera ta gyara zamanta a kasa kan tiles ita Amana bata son zama ko kwanciya a kan laushi kujera ko bed
Shi yasa ta baje a kasa tare da jawo tiren abinci ta fara ci ba tsayawa hannu biyu ta jefar da cokular a kasa tasa hannu dayan hannun tana yagar kaza daya kuma ta dauki Apple ta balla,ta dauki kankakana,ta gutsiri waina ta dangwali miya,ta yagi kaza ta kora lemo ko ruwa ta ebo fried rice ta watsa a bakinta.
A fili cikin santi tace banza ta fadi Allah sakawa me gidan nan da Aljanna,wuyanta ta Sosa tace me bamu Allah ka bashi,Wanda bazai bamu ba Allah Bamu tare
Sai da taci tayi bamkam kadan ta rage,Karambanin Amana inda taga matar ta shiga nan ta mike ta fara lallabawa zata ga mene a ciki,handle din kofar ta murda a hankali sai ta ganta a wani daki ya gaji da haduwa,wata kofar ta bude ta cikin dakin sai ta ganta a wata doguwar Palo ya gaji da haduwa yasha kayan alatu,kara mikewa tayi sai taga wata kofar
Budewa tayi sai kawai ta ganta a wani makeken kitchen,hade da store,kofar baya kuma ta kitchen zaka fito compound,
Komawa tayi ta kara shiga kitchen nan fa ta kwashi kallo,fridge ta bude tare da dauko wata fura bowl guda dan karami tayi sanyi,a tsaye ta shanye furar tas ta ajiye bowl din ta dawo palon da take,
Wani cycle steps ta gani daga palon yayi sama,ga wata kofa opposite din wacce tabi dazu,nan ma kara budewa tayi bed room ne da toilet ciki,ta kara bude wata kofar sai ta kara ganinta a compound amma tana hango wasu part guda biyu a gidan da har can taje taga Ashe daya part din Na yan aiki mazane daya kuma part din Na baki ne da mata yan aiki,
Baki ta tabe tare da cewar ni dai bazan zauna a bangaren can ba wannan part Din da Alama shine Na Alim dan haka a nan zan zauna yafi haduwa kajifa Amana,har magrib tayi tana palon,cycle steps din nan ta fara takawa har ta haura sama,
Wow......nan Amana taga aljannar duniya kiri kiri,wakeken Palo ne yasha kujeru Na garari,ga dinning can gefe,wata tafkekiyar plasma TV,da wasu manyan speakers,flowers manya, sai tafkeken hoton Alim a manne,
Jikin bangon kansa abin kallon me,komai Na saman fari kal ne,Na kasan kuma peach color,yan aiki kuwa light brown ne nasu,
Amana fa ta gama rudewa da kallon haduwar gidan,wani kofa ta gani a cikin Palon guda biyu,daya ta nufa ta bude a hankali,wani tangamemen bed ne da sip zureriya,sai madubi,har bedsheet komai fari kal neat,
Ko ina gidan kamshin dadi da sanyin ac, daya room din ta bude subhannallah ta firta a fili komai fari shima yafi ko ina kyau da tsaruwa, komai Na dabanne,
Alim ta hango zaune kan sallaya yana Sallah, Aabid Na jikin gado a zaune yana game.
Asmabaffa
✳CIRANIN AMANA✳
40-45
By
AsmaBaffa
Murmushi Amana ta saki kana ta kutsa kai cikin dakin da sallama, a gigice Aabid ya waigo tare da kwala ihu ya rugo a guje wajen Amana tare da daka tsalle ya daneta yana oyoyo new Antyna I miss u,
Dariya Amana ta saki tare da kankame Aabid suna ta murna tana shafa masa kai,my sweet boy I really miss u,yau tare zamu kwana,za muyi wasanmu cewar Amana,shi kuwa Aabid Jan Amana yayi har Bed din Alim yana nuna mata game dinsa,
Amana kuwa ta manta da wani Alim dake zaune kan sallaya yana Azkhar,kan gadon ta haura tare da Aabid suka fara wasa ba ji ba gani sai dariya sukeyi,kafin kace me sunyi waja waja da bed din Alim,pillows duk a kasa rabin bedsheet dinma yana kasa,
Alim kuwa ba shiri ya daina azkhar tsananin mamakin me suffar maza ya rufeshi,idan banda rashin tarbiya taya zata shigo musu gida har bed room ta hau kan bed ko gaisuwa babu ba komai,in hakane ai tafi Aabid ma rashin tarbiya,ina bazai iya zama da wannan ba,
Rashin tarbiyarta yayi yawa da kuruciya da hauka,ran Alim yayi matukar baci kan abinda Amana tayi yanzu,wata razananniyar tsawa ya daka musu,wanda suka gigice gaba dayansu,musamman Aabid nan take ya fashe da kuka saboda ya tsorata sosai,
Cikin tsananin fushi Alim yace ke baki da hankali?baki da tarbiya?dabbar inace ke?dakikiya jahila wacce bata san me takeyi ba,jakace ke?wa ya baki damar shigowa har part dina,kuma bedroom har bed dina,zaki shafa min cuta a bedsheet,dakikiya dan Na daukeki aiki ba dama Na baki da zaki zo ki min halin mahaukata ba,
Da karfi yace get out now,Amana wacce mamaki da bakin ciki suka taru suka cunkushewa a zuciya,idonta ya kada yayi jajir tabbas yau da badan Alim bane Wanda Allah ya sa mata tsoronsa,kunyarsa da kwarjinin da yake mata to da wani ne yau sai dai a dauki gawarta ko tasa,amma Alim ne tsoronsa takeji amma duk da haka Amana sakkowa tayi daga bed din tana kumbura tare da cijewa,tace hey Baabaa control mana ya kake yawa,hannuna tasa biyu a aljihu tana tafiyar gadara,wannan ai yawa ne master eh idan dan Na hau Bed dinkane ai sai kace na sauka,ya zaka dinga zagina,
Bed din ta nuna masa idan akan wannan bed din ne easy master ni laushi bai dameni ba ko a kujera bana zama bare bed a dalilin danka Na hau,amma ka sani bed dasu kujeru basa birgeni,kaci sa a Kaine ka zageni haka,cije lips tayi jajir dashi gwanin sha'awa tace a kiyaye master tayi gaba abinta ta dawo palon kasa Wanda aka ajiyeta tun farko.
Alim kuwa mamaki ya gama kamashi yayi mutuwar tsaye,Aabid kuwa kuka ya sa an yiwa new Anty fada,kukan ne ya dami Alim,ba shiri ya figi hannun Aabid ya sauko dashi palon kasa wajen Amana,Amana ta bararraje tayi mala mala a kan tiles tana tunanin duniya,kawai tuna irin zagin da Alim ya mata takeyi,
Idonta ya tara kwalla du duniya babu Wanda ya taba zaginta haka sai me kyau,sabo da bakin ciki kawai kuka Amana ta fara babu damar ramawa.
Yana zuwa da Aabid ya ganta haka kallo daya yayi mata ya dauke kai Aabid ya jefa a kan cikinta,a firgice ta mike ba tare da tace komai ba tsaki taji ya ja tare da ficewa daga gidan gaba daya tare da escort dinsa.
Sai lokacin Amana ta sauke ajiyar zuciya tare da saurin kallon Aabid tace kai yaro Daddynka masifaffe ne wlh,idan Na gaji guduwa zanyi,Aabid kuwa dariya yayi kamar me hankali yace Anty me kirkine Daddyna,zai daina fushin fa.
Suna zaune suna kallon cartoon wannan matar ta dazu ta dawo tana watsawa Amana kallon Banza tace taso ki dauko jakarki Na kaiki dakinki,Amana bata ce komai ba ta dauki Jakarta hannunta rike Dana Aabid har part din yan aiki mata aka kaita,mata birjik kowacce da uniform dark blue skert da Riga me cola da dogon hannu fara kal,sai gyale dan siriri fari.
Ko wacce bin Amana take da kallo,sun ganta kyakyawar budurwa ajin farko,ga shigar niggogi tayi abin dariya,ko ina matan dariya sukeyi suna gulmarta,
Bata kulasu ba amma sun ga dan gidan Oga Alim a hannunta,wannan ya nuna me renon dansa ya dauko,