← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 58

Sashe 2

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bashi da Amana,ko yarinya ka kawota gidansa riko sai ya ci amana ya lalata ta karfi,haka baki wasu su gudu wasu su tsaya su sha harka,yaransa ma sunsha kama Baba da mata,matansa har fakonsa sukeyi idan dare yayi,sabo da ko yar uwar matansa ne sukazo sai ya zaga wajensu ya kwashi Harka,
Bashi da abokin da ya wuce limamin garin domin halinsu daya,
Sulemanu Harka ko yarsa kaje nema idan baka da kudi to bazai baka yarsa ba,kuma idan kana zuwa zance wurin yarsa to sai ya dinga rokonka kudi,haka gaba daya sai Allah ya bashi yara gaba daya tantirai,Amana ce ta gari a hakan lol kaf gidan babu me nutsuwar Amana a hakan.
Mazan gaba daya wasu barayine,wasu yan wiwi,wasu yan Neman mata, domin suma suna lallabawa wajen baki masu sauka,na gidan aure ma ko wacce da rashin mutuncin da take shukawa a gidan mijinta,kullum a kawo kara da Sulhun yaran Sulemanu Harka ake,babu na ciki babu ga na wajen,kowa da halinsa,
Su Kansu yaran sun San basuyi dacen iyaye ba,su kuma iyayensu mata matsalarsu rowa, zagi da tsinuwa kala kala,sun gama raina mijinsu saboda ya zubar da mutuncinsa.a cikin labari zaku ci gaba da jin Halin kowa a Gidan Baki.

Amana kyakyawar yarinyace ta kwatance fara ce Amma ba kar ba,doguwace ga shape,duk inda kake neman diri to kazo wajen Amana, shekarunta 18 going to 19, gashine da ita ya wuce kafada kadan baki wuluk,gata da idanu dara dara masu tsananin kyau,gashin gira dumbul dashi,dan bakin nan cut,lips light pink,hancinta dan dai dai bai cika tsini ba kuma ba gajere ba,ga dimple idan tana magana bare tazo yin dariya,hakora yar yar dasu kar kar,saboda kullum cikin yin aswaki take ko yaushe,skin dinta me laushin gaske, gata da tsafta ba laifi.

Amana yarinyace me son al'adun maza,haka take tun tana karama rayuwarta da maza takeyi,shi yasa kaf garin wudil bata da kawa mace ko daya, sai Maza,bata da mutunci ko kadan idan ka shiga safgarta,ko uban waye komai girmansa,macece me karfi da zafin nama,ga juriya da taurin rai,idan fada ya hadaku tofa sai dai a mutu bata ji ba ta gani,idan ta fara dukan mutum sai ta gaji da kanta,kowa daya Santa tsoronta akeji ko a gidansu Amana sarauniyace dan ko waye bai is a ba,iyayenta kawai take dagawa kafa,
Ba wani abu na nafeela takeyi ba amma duk farilla tana cikawa,Sallah bata wuceta duk inda take,gata da son ilmi,gidansu ba a sasu a islamiyya bare boko amma har gona take zuwa tayo ciyawa ko kara ts siyar ta sayi littafan schl,haka ta gama primary yanzu tana ss2 a wata government schl ta garin,duk da ba wani turanci ta iya ba amma tana iya karantawa,haka islamiyya ma,tana da haddar izu 30 ga wasu littatafan tayi,duk gidan ita kadaice take zuwa schl,har yaran gidan sabo da tsoron Amana da sukeji take korasu makarantar Allo dolensu suke zuwa,

Kuma idan baka kawo mata haddar karatun ba sai ta farfasawa yaro jiki,ba ruwanta don kaninta har kashi ta tsaga masa garin duka bai iya karatu ba,har yayyenta tsoronta sukeyi sun san karfin Amana,ba mutunci ba daga kafa,shi yasa a gidan ita kadai ce take sa doka kuma dole abi dokar,

duk masifar Amana bata yi a schl tunda wani malami ya kusa korarta daga schl din gaba daya sai ta daina komai da take musu,sai kadan kadan takeyi, domin tunda ta fara schl take jibgar dalibai,tare da karya kafafun yaran mutane,domin har malami cin kwalarsa takeyi ta fesa masa mari,
Gata da kokari da tsafta,shi yasa aka bata head girl,tunda aka bata mukami idan yaro yayi late sukaganta a gate juyawa sukeyi gida sabo da sun San dole sai ta fasa ma jiki,ta gagari malaman bare abi wa yaro hakkinsa,

Amana yar rigima ce sosai,tunda aka haifeta Ummanta ta zabi wannan suna Amana aka radawa yarta,wajen aiki kuwa ta iya girki kala kala domin Amana har wajen wata Bilkisa me tuwo tuwo take zuwa tana tayata girki ta bata kudi,dasu take biyan bukatunta da dama,
Amana Ummanta bata da halin kirki,ga son kudi,bata iya taimakawa yaranta da ko kwandala,kowa yaro da babba dake gidan Sulemanu Harka Neman na kansa yakeyi,kowa ta kansa yakeyi babu me taimakon wani da ko kwandala,gwara Amana tana bawa babanta wani abun idan ya rasa,har su Hamza takan sai musu kokon safe watarana,sabo da Amana ta fisu zafin nema,ba ruwanta kullum cikin Neman hanyar samu take,kuma in taje neman aiki wajenka tofa dole ne ka bata aiki tayi ma,kuma sai ka biyata dai dai da guminta, sauran yan matan da basuyi aure ba maza suke damfara da yaudara su sami kudin sabulu da sauran kayan sawa,shi yasa suka fi Amana sutura da yawa,sabo da Amana bata da saurayi sai abokai,bata da kayan sawa,atamfarta kodaddu kala 2ne sai tsimmokaran da take sawa,suma wasu wandon duk na su Hamza ne da kannenta,take dauka idan zasu jefar sai ta karba ta wanke taci gaba da sawa tana hadawa da rigar atamfa,Ummanta tana Sana'a tana samun kudi amma sisi bata iya bawa Amana,hatta kokon Safe sai dai Amana ta siya, idan ba kudi ta tafi wajen abokanta maza ta samu,amma tana bawa kannen Amana Maza,basa shiri da Amana da Ummanta sabo da Umman Amana tafiso Amana ta dinga damfarar maza tana samo musu kudi,amma Amana taki yarda kuma bata da me sonta.

Shi yasa Amana tace abokai maza sunfi mata muhimmanci,ga kyauta,gashi basu fiye gulma da hassada irin ta mata ba,Namiji ko ya kuke mutunci zaka moreshi,sabanin mata da yawa sai su dinga yi ma hassada ma,idan sunga ka fisu sai gulma da bakin ciki.
Yawan Hulda da Maza yasa Amana takeyin acting din maza, sauran yan uwanta duk Suna Neman mata,matan ma sabo da son kudi Neman maza sukeyi,Amana ce kadai cikinsu Bata ma da saurayi bare ma ya taba jikinta,kuma mazan da take Hulda dasu tsoron jarabar Amana sukeyi ko yatsanta basa rikewa.

Ci gaban labari

Amana ce ta tashi da asuba tayi Sallah sannan ta fito wajen Ummanta dake gaban murhu zata dama kokon siyarwa,naira ashirin Amana ta mika mata ba wata gaisuwa ba komai,duk dama gidansu haka suke ba a gaishe da kowa,ungo wannan kudin Umma a bani koko damun farko nake bukata kuma yaji gaya a dauraye masa kai da gasara sosai,karba Umman tayi ba kunya tace kawo robarki,tana kwobarewa da takama ta mika mata,koko na a dauraye masa kaifa da gasara in baiji wlh gobe wajen su Zainaba zanje na siya,

To karki isheni kamar wacce ta bani million,cewar Umma,wucewa Amana tayi wajen kakarsu Ille tace karbi tsohuwa bani kosan 10 bana bukatar raini shi yasa kikaga ni komai siya nake da kudina,ba a min kallon banza saboda ni da kudina nake gadarata,iya kudinka iya shagalinka,ille dai shuru tayi tare da zubawa Amana kosanta tace ga gyaran biyu nan nayi miki,Amanace tace kwashe abinki zuciyata bata mutu ba bare ki fadawa danki kin ci dani,na girmi tallafinki,babu Wanda yake ci dani a gidan nan, Ille ce ta kwashe kosanta guda biyu jeki matsiyaciyar yarinya,shegiya wulakantacciya.

Ae naji gwara ni ummata bata haifi me bin mata ba,kin haifo Baba kin jawo mana bamuyi dacen iyaye ba,duk mun lalace,wa yasan me kikayi lokacin kuruciyarki,shi yasa Baba ya gadoki,kisa ya kori waccen yan fulanin daya kawo gidan nan,wlh idan na kara kama Baba dasu suna iskanci a dakinsa sai na dagargaza musu kai,

Ille ce ta fashe da kuka kowanne yaro yazo yaci mata mutunci akan ta haifi Sulemanu Harka.

AsmaBaffa

Comments dinku shine jin dadina fans tnx a lot.

✳CIRANIN AMANA✳

5-10

By
AsmaBaffa

Haka Sulemanu Harka ya shigo ya riski mahaifiyarsa tana kuka,lafiya Iya?gata nan Amanace tsinaniya taci min mutunci,cike da takaici Baba ya kwantarwa da Iya hankali ya mike ya nufi wajen Amana a fusace,Amana tana shan kokonta da kosai,ya fado dakin,Gani yayi fuskar Amana ba rahma nan take ya tsorata yace haba Yar Amanata a dinga salalawa Iya mana,a hankali fuska a daure tace an gama Baba,amma ka fada mata bana so a dinga taimakamin a gidan nan,tunda an San baza a iya tsinana mana komai ba to a daina yi min rangwami da sauki ko arahar abinci bana bukata,da kudina nake Harkata,shi yasa nima nake bearing da Amana Suleiman Harka a schl,

To Amanata a dinga hakuri kinji,sai Baba kar kaji komai,Baba jiya ma fa na kamaka wlh da wata yangwadaddiyar tsohuwa,saura kadan na fasa muku kai,kawai dan Kaine Baba,dan Allah Baba idan iskancin nan zakuyi ka dinga tafiya inda baza mu ganka ba,Amana zamu bata fa dama leke kike min a zaure na?to ka daina mana?cewar Amana,

Kaci sa'a wlh na tuna kai Babane da tuni na Tara ma mutane,wai Baba baka jin kunya ka tsufa haka,kasan bala'in da kake dorawa kanka kuwa,?uwaki Amana kiyi min Addua nima ina so na daina na kasa,ban San dalili ba,wlh na gaji da bata lokacina ina ma Addua Baba bazan iya ba,yanzu kai dadi kakeji da muka zama haka,kalli yaranka fa yanda kowa yake babu na gari,

Ni kadai ce bana iban Harka nan irin taka,kana yawa fa Baba idan na gaji nima na kusa, zan kwace kawai nima nabi sahu,Haba Amana me kike fada haka cewar Baba eh wlh Allah kawai nima fuskewa zanyi na amsa sunan Amana Harka.
Wlh Baba duk randa na kamaka tsanarka nakeyi,bana son ganin ka,jeka kawai Baba za kasa na kasa shan koko na Wanda ba wani ne ya sai min ba da kudina nake harkata.
Baba jikinsa yayi sanyi Amma bazai iya daina halinsa ba,ya rasa dalili,
Amana duk tafi bashi matsala a gidan sabo da tana masa nasiha amma bazai iya dauka ba,gwara kawai ya turata Neman kudi kudu ya huta da halinta,kuma da alama zata nemo kudi sabo da Amana tafi kowa a gidan zafin nema,ga juriya da kwazo.ga karfi ga bala'i dole za a buga da ita,
Amana ita kadai tafi duk yayansa Amfani a gidan,gata me tsananin kyau da diri.
Chapter 2 · 0% Book details