← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 58

Sashe 57

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kunnensa Mum ta murde Amana tana dariya tace Mum kyaleshi dan Allah kin San halinsa da kafiya wlh idan ba haka ba aure zai fara nemowa kyaleshi ya kwanta,Alim yace gwara da kika samawa kanki lafiya dama wata ta manne min sai na nemota,Amana kamar zatayi kuka tace Mum kinji ko kyaleshi kawai,
Mum tace kinji kunya wlh kina tsoron kishiya ki zauna ya rainaki yana miki barazana da kishiya,
Sosa kai Amana tayi Mum baifa ce zaiyi ba nice dai nake tsoro kuma wlh idan yace zaiyi Allah saina ballata harda shi ma, murmushi Mum tayi tace ai nasan zaki iya aike kishiya ta shiga uku a hannunki,gwara karma mutum yayi domin korarta zakiyi da muguntarki kala kala,
Shagwaba Amana ta fara haba Mum ni Allah,Mum tace sai dai ki gayawa wani amma nice sheda,ni indai ina raye bazan bari ma ya miki kishiya ba,nasan ma bazai miki ba yanda yake Sonki,

Dadi Amana taji tace na gode Mum,koreshi ya tafi dakinsa,bige bakinta Alim yayi kadan ta kwalla kara,
Mum tace kwaji dashi can kunfi kusa,sai da safenku tare da kallon Alim tace ka kiyaye kaji na fada ma,ina ganin ba dai dai ba sai ka bar gidan nan ka koma gidanka,

Wannan yaro yana Shan kulawa wajen Amana,kullum yana hannunta ta hana kowa,da an karba zata dinga mika wuya tana lekensa,
Idan yarane ba manya ba Baza ta basu danta ba kar su jefar dashi ya fadi kasa wai,daga yayi uhum Amana dama kadan take jira zatace mikoshi na bashi ya sha ta karbe abinta,

Ko Alim masifa take masa wai yana shilla mata yaro zaiyi zazzabi,
Asiya dasu Badriyya kuwa da suka zo suna dauka kadan zata dan jira mintina kadan tace bani dana,har tsiya ake mata Amma Amana ko a jikinta,
Har ranar suna tayi dangi da abokan arziki ansha suna,yaro yaci sunan Aabid,Aabid ake ce masa,

An gama komai kowa ya koma gidansa,Mum kuwa da sauran dangi suna ta faman gyara Amana kamar sabuwar Amarya,
Alim dan albarka yayi dauriya da hakuri bai takurawa Amana ba sam,

Amma da kyar yake daurewa har sai da ya daina kwana gidan Mum saboda tashin hankali yake shiga yanda Yake kallon Amana tana kashe kala,gashi sai kara kyau da girma takeyi har akayi arba'in Aabid yayi wayo sosai gwanin sha'awa
Ranar kuwa da ta cika arba'in ranar Alim zuwansa gidan Mum yafi Goma yana jira yaga Amana ta Zama ready su tafi gida,Amma sai yaji Mum tace kano zasu tafi tare da Amana su zaga dangi,

Da bacin rai ya koma gida,Saida Amana suka gama zaga dangin lagos sannan suka wuce kano kwanansu 4 suka dawo lagos,washe gari Mum tace shirya maza na kaiki gidanki,wannan mijin naki kamar zai dakemu kina gani da kyar ya gaishe ni.

Amana ma tayi missing mijinta,har gida Mum ta kaita da yamma misalin 5pm,
Nan Alim ya fara fushi yana shagwaba,da kyar Amana ta lallashi abinta, yana dawowa daga Sallar magrib,yasa Amana ta kara bawa Aabid Nono ya koshi ya tattarashi ya kaishi wajen hajja,

Amana tace idan yayi kuka fa?,Alim ya ce can da matsalarsa yazo ya kankane komai ya barni cikin wahala,
Ranar Amana taga ta kanta a hannun Alim,ya gurjeta son ransa,

Sunji dadinsu sosai,Alim kara nutsewa yayi akan so da kaunar Amanarsa,
Kullum yana manne da ita ba sauki ba daga kafa,itama Amana hakan take irinsu daya.
Saida Alim yayi Hutu na 2wks sannan ya koma aiki,

Wata yarinya ce wacce sukayi university da Alim a london Teema take matukar son Alim,kullum sai tazo office dinsa kan ita sai ya aureta,Alim Amanarsa ta isheshi,bazai iya mata kishiya ba Sam,
Yanda yake mutuwar son matarsa me zai ci da wata,yayiwa Teema bayani amma taki yarda,shi kuma Bai son wulakanta dan Adam musamman yanda sukayi schl daya,yana ganin mutuncinta.

Yauma kamar kullum tana office dinsa,dabara ce ta fado masa yace Baza ki iya kishi da matata ba,Teema tace haba dai ai ni nafi karfin ko wacce kucaka, ka kirata mu hadu kaga yanda za ayi sai abinda nace dole ma ta hakura,
Murmushi Alim yayi,Teema da kuri tace kirata mana tazo na fada mata amma da sharadi idan ta yarda dole ka aureni,Alim yace kwarai kuwa.

Amana ya kira a waya tana jikin mirror tana sheka kwalliya ta daga,Alim yace kizo Office yanzu wata tana son ganinki wai zata aureni zata iya kishi dake shine nace kinfi karfinta ni mijin tace ne amma taki ji,wai sai ta ganki.

Kamar an watsa mata ruwan Zafi haka Amana ta mike, gyale ta figa a hannunta ko yafawa bata yi ba,Aabid dama yana wajen Hajja,motar da tafi ko wacce tsada da kyau a gidan ta shige tare da fisgarta sai office din Alim,Teema kuwa harda fitowa waje tana jiran Amana,
Alim sai dariyar mugunta yakeyi yasan yau Teema ko mari daya ne sai tasha a hannun Amana,

Motar Amana ce ta Parker tun daga parking kasan ba lafiya,tana fitowa Teema ta sume a tsaye ganin Amana,tunaninta Amana ba wata me kyau ko hadaddiya bace tunda tasan Mum kewa Alim aure,
Tun kafin Amana ta karaso daga yanda Amana take tafiyar gadara da takama gashi kana ganin idanunta kasan a bushe suke sun goge da duniya,
Duk wajen ya dauki kamshin Amana,shigarta kanta abin kallo ne wajen tsada da haduwa,
Alim ya fito waje yana ta faman murmushi da Ido ya nunawa Amana Teemace me son zama kishiyarta,Teema kuwa ta maza tayi,tare da hade rai wai itama shegiya ce,wajen Alim ta matsa tana masa wani kallo,
Hannu ta daga wai zata rike hannun Alim,dan Amana ta gani tasan suna soyayya.

Kafin ta ruko hannun Alim,Alim yayiwa Amana magana da Ido wai kullum haka take takura masa a Office,shi wlh ya gaji zai aureta,Amana da hannu ta yanka wuyanta wai sai ta yankashi,murmushi yayi,Teema kuwa taje tana hada hanunta dana Alim wai zata rike, Amana ta fincikota baya tare da kifa mata maruka har uku,
Tare da shake Teema ke karamar yar Iska kin sanni kuwa,Teema Ido ya firfito sai hawaye,sakinta Amana tayi tare da ja baya tana, bana Cece kuce da mutum na wuce nan,Dalla ja rubabben bakinki dake yar kauye zaki taba mijina da kazamin Hanunki kwartuwa ana zubar da aji ana bin maza,nafi karfin kishi dake,
Warning na miki kika kara zuwa Office din mijina sai nayi daga daga dake, Alim munafuki harda cewa sorry Teema kinga abinda nake fada miki gashi fuskarki ta kumbura kika ki yarda,ba laifina bane,

Teema share kwalla tayi tace amma Alim kayi asarar halinka wlh,sam bansan haka ka Zama lusari sakarai ba,kai da kake dodon mata amma mace yarinya karama jibi yanda ta ke Baka Umarni,Alim yace uhm wlh kuwa ganemin hanya Teema aini a kanta na gama lalacewa,ta shanyeni na shanyeta idan ba ita rayuwata Baza ta yuwu ba,kinganta to bana jin yaren kowa sai na Honey ta,

Teema fuska kumbure tace Allah yaji kanka Alim,wlh ka haukace aikin banza kayi asara dai,kuma marin da tamin Allah ya Isa wlh Bazan yafe ba,
Alim yace taba mata miji da kikayi bata ce miki Allah ya Isa ba sai ke dan ta dan mareki,hukunci ta miki a duniya kafin Allah ya miki nasa,karki sake ki zagi mata ta wlh a nan zansa a tara miki gajiya uban waye ya kawoki Office din mijinta,
Amana tace a bar mana Office yanzu ehe, Baby muje gida an tashi a Office yau Baza ka zauna ba sai gobe kuma,
Alim yace an gama ranki ya dade,ya kwaso wayoyinsa ya rufe Office yabi Amana,yace Securities su kai motocinsa gida Madam tace a tashi a Office haka,
Amana harda jin dadi Alim yabi maganarta,abinda idan yaga dama idan ta yi ba dai dai ba sai ta gane kurenta ba wani mijin tace.

Teema kuwa motarta ta shiga tace Amma na maru wlh,wannan jarabace da ace na kulata Dukan tsiya zata min,ga shegen iya mari,hannunta laushin tsiya Amma idan ta dakeka sai kaji ajikinka,
Kamar namijine ya mareni,yaje ya zauna da jarabar matarsa,mijin tace shege,dan iska,tsinanne ta dakeni Amma ko a jikinsa koma ya mata fada.wannan Alim ai shine dan iskan marar mutunci suje can su karaci jarabarsu ko kallonsa wlh Bazan kara ba tunda bashi da mutunci haka Teema ta dinga zage zage har ta koma gida.
A ranar ta nemo tsohon saurayinta me sonta da take masa wulakanci suka shirya zai turo ya kwashi tsohuwa Teema..domin Teema Sa'ar Aleem ce 33years itama.

Amana a mota sai faman dariya sukeyi da Alim yanda Teema tayi,Amana tace sai ni wlh har aja Dani ko wacce shegiya ce, tana driving Alim ya mika mata hannu ta rike tare da hadewa da sitiyari tana tukinta,

Tana Driving Alim na tabe tabensa a jikinta,yana dora hannunsa a kirjinta Amana tayi slow da mota ta kara fincikar motar,yana kara tabawa Amana ta gangare kasa tace zo ka karbi driving bazan iya ba ai sai kasa muyi hatsari ai,
Dariya Alim yayi tare da cewa na gaji ban iyawa,na daaina tabaki muje pls,
Driving taci gaba har gida,

Wannan shekarar Amana da Alim sukaje aikin Hajji again suka koma umrah tare da Aabid dinsu,Amana na zuwa schl tana karatunta sosai yanzu tana final year,

Salma ta gidan Deeni kwaro tana dauke da ciki haka matan su Hamza ma,
Shekarar Aabid biyu a duniya Amana ta samu ciki za ayiwa Aabid kani ko kanwa,
Murna sukeyi sosai,tana gama degree dinta da wata biyu ta santalo Danta Namiji shima,
Ranar suna aka sa masa sunan Baban Amana Sulaiman suna ce masa Irfan,

Aabid an girma an zama dan saurayi,
Amana tana jin dadinta suna zamansu lafiya ita da Alim da yaranta,
Sai abinda sukeso, har ansa Aabid a schl, Amana ba abinda bata Yiwa Alim don ta faranta masa,sai abinda yakeso,kullum Amana cikin gyaran jiki da kwalliya a haka take kara susuta Alim,ya gama matowa a kanta,akan Amana sai dai a mutu,
Chapter 57 · 0% Book details