← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 58

Sashe 3

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama Baba ya gyara kusa da Amana,tare da riko hannunta,kwace hannunta Amana tayi tare da cewa Baba ni ka daina rikeni kar nima ka mai dani irin watsatsun matan da kake Harka dasu,haba Amanata nifa Babanki ne duk abinda zanyi bazanyi da yarana ba,to naji Baba mene ne,yawwa Amanata so nake kema na turaki Lagos Neman kudi,kije Cirani kiyi Sana'a ki dinga samomana kudi,watakil ma Allah ya baki miji me kudin gaske a can ko? Dariya Amana tayi cike da jin dadi zata bar jarabar gidansu,tace Allah barmin Baba,wlh sai Baba,shi yasa watarana kake birgeni idan kayi tsiya ta wani wajen sai kayi dadi ta nan,Allah dai ya biya.
Dadi Baba yaji yanda zai dinga tsula tsiyarsa Amana bata gidan bare ta dameshi da wa'azi.

Kallonta yayi yace yawwa ta wajena,kudi zan baki masu yawa Wanda zasu isheki amfani a can Lagos kafin ki fara Sana'a.
Sa'a dai sa'adai Baba cewar Amana tana murmushi.

Nan da sati biyu zaki tafi Amana,akwai abokina zan masa waya shi zai kaiki wajen kwana,amma Baba ba irinka bane ko ?ai shi Amana daban yake yawwa yanzu naji batu Allah kaimu sati biyun cewar Amana, Baba yace kinga duk manyan maza na suna jahohin kudi cirani,amma basa tsinana min komai sai lalacewa da suka kara yi,

Duk cikinsu babu Wanda yaje lagos suna cross river wasu suna Abuja,wasu Enugu,jibi Hamaza na turashi nassarawa lafiya amma jibi da yazo gida doya kawai ya kawo min,sai 3qurtr da ya zo dasu,dariya Amana tayi tace Baba rannan saura kadan na masge Hamza bashi da mutunci har ni zai zaga,shi din banza,Baba ne yayi dan turancinsa daya koya a garin Tafa kusa da Abuja,yace control control Amanata,

Cike da farin ciki Baba ya fito,
Amana shirin Makaranta tayi ta fito tare da yin ball da wani pow da ta gani a kofar dakinsu,tayi gaba zuwa schl.
Sabon Malami ta tarar a jinsu har an shiga,cike da gadara tana budawa ta shiga class din,Malamin ta gani a kan wata kujera da ba Wanda yake hawanta a ajin sai ita,
Wajen malamin ta karasa tare da cewa daga wannan kujerar,mamaki ne ya kama sabon malamin,yace ke dan uwarki ni zaki fadawa haka,sa'an ki ne ni? Kujerar daga gidan ubanka kazo da ita,ko ta ubanka ce cewar Amana,bude baki malam yayi,yan class kowa yayi luf,
Ke wlh sai na koreki daga schl din nan bari na fadawa p.c hannu Amana ta tura a aljihu tace uwar principal zaka fadawa,p.c yaci uwarsa ka fada masa ni Amana na fada uban p.c yaci Uban sa,

Kujerar ta janye malamin na kai ta zame kujerar da karfi ya fadi kasa ta matsa gefe ta zauna tare da harde kafa daya kan daya.malamin mikewa yayi tare da karkade rigarsa ya fice fuuu wajen p.c,
Wajen principal yaje ya fada masa komai,principal dai ya gaji da halin Amana,nan take aka karkada kararrawa aka tara Assembly duka makarantar,

Guri yayi tsit PC yace ina Amana Suleiman Harka?da sauri tace yes gani nan,nasan a kaina akayi taro, ko bakace ba zan fito gani,
Ta fito ta tsaya gaban dandazon mutane hannayenta biyu cikin Aljihu tana kallon kowa dai dai,PC yace kinwa sabon malami rashin tarbiya da cin mutunci gaban aji?yes nayi masa kuma ko gobe ya kara zan sakeyi masa komai naga dama,
PC ne ya daka mata tsawa ke yar matsiyata,yar gidan Sule tantiri me Neman mata bafa tsoronki akeyi ba,wlh yau sai kowa ya zaneki a malaman schl din nan cewar pc,

karya kake Saminu PC,gaka nan bakin kwarto dan iska,wlh akan ka zagi iyayena ko ku dakeni gwara na bar makarantar,babu Wanda ya isa ya taba iyayena ya kwana lfy,makarantar ku din banza shegu gaba dayanku,PC ne ya cakumo Amana da niyar dukanta nan Amana ta riko makwallaton wuyan PC kamar zata zareshi daga wuyan,ba shiri PC ya saketa,amma Amana zagi takeyi iri iri sai da ta gaji ta kada kai ta kalli PC tare da cewar Wanda ya kirkiro boko ma yaci uwatas,uban uban uwar Bokon an daina bokon dan uwarsa.ta kada kai ta bar schl din,tazo bakin gate zata fita ta tsaya ta zubawa me gadi rankwashi kwas,sannan tayi gaba,

bagazan bagazan ta shiga gidansu,ba Wanda ta kula ta cire uniform dinta ta tattarosu waje ta hada da jakar schl din da littafan a tsakar gida ta zuba musu kananzir ta cinna musu wuta,bal bal suna ci har suka kone kurmus,sannan ta kwashe tokar ta watsar a waje tana bin iska tace bye bye Boko ni da zan tafi Cirani Lagos garin turancin da Bokon gaba daya,
Wani Nishadi taji ya mamayeta da ta tuna zata tafi lagos,

Wanka tayi ta sa wani wandon jean kato Tsoho tukuf gwiwar duk ta yage,tasa rigar Atamfa katuwa ta kai cinyarta,p cap ta sa wata kalar tsohuwa tukuf da ita,ta fita,wani Namijine ya ce sai Amana ya garin ne,kallonsa tayi easy T.j easy dai,ya kk?lfy Amana ,kwana 2,wlh tj wai schl ne zasuyi min iya shege tuni na kwancewa PC number 8 dinsa,dariya tj yayi yace bakya farke shege ko ki kiramu muzo da yaranmu a yi maganinsa haba Amana ya kike masu sauki ne,kyalesu nayi kawai sabo da Lagos zan je Baba,
Iyye kice kin kusa fasowa gari gaskiya Dad dinku yana birgeni,murmushi me kyau Amana tayi ina zuwa tj ku zama cikin shiri zan muku hanya kuma kuzo, sai Amana cewar tj ya zaro 200 ya bawa Amana ga wannan kya danyi eh yane,godiya nake tj,haba share kawai aike tamuce,jiyafa Majalisa ta cika ana ta jiranki baki zo,ai ina nan zuwa yau,sai mun ganki.

Rabuwa sukayi da tj,wasu yan matane sukazo wucewa sunci kwalliya yan makarantar k.u.t wudil ne,sai yanga sukeyi suna yiwa Amana kallon banza,bata kula su ba.har wani turanci sukeyi su a dole yan University suna degree,tafiya Amana tayi tana kwobarewa tare da takama tana wani budawa,

Shekewa sukayi da dariya suka tafa,wata a ciki tace oh budurwa har budurwa kyau iya kyau amma jibi ta kashe kanta,
Amana dai bata kulasu ba,sai wata tace inye kaga maza fa,wannan da gani shaye shaye takeyi,ko ciwon hauka ya kamata,
A fusace Amana taci birki tare da juyowa,ganin yanda amana ta canja lokaci daya yasa yan matan nan suka tsorata,zasu yi gudu gashi sun sa takalmi me tsini da damammen skert,

Daya Amana ta cakumo ta hau dukanta sai da ta karya mata hannu daya,sauran su biyun sun fara gudu Amana ta damkosu saida ta sumar dasu sannan tayi gaba abinta ko juyowa batayi ba,

Ran Amana ya baci ta fasa zuwa inda tayi niyya ta koma gida,Ummanta ta gani tana yin Alalar siyarwa ta Rana,can gefe Amarya tana Awarar siyarwa,Goggo shinkafa da miya,Hajiya shinkafa da wake duk na siyarwa.
Ko wacce ranar girkinta ita zata ci da Sulemanu Harka da sana'ar da takeyi.kowacce tana ci da kanta da yaranta,Amana kuwa ummanta bata bata sai dai ta siya,sabo da bata da saurayi.

Wajen Amarya Amana ta nufa tare da mika mata kudi Bani ta Naira Dari nama biyu zakisa min kuma Manya,harara Amarya ta watsa mata,ubanki ne ya bani kudin?ko bashi ya baki ba wlh in bakisa 2meat ba sai na tankadar da tukunyar miyar baki dayanta,ba shiri Amarya ta zuba mata shinkafa da Nama biyu manya harda gyaran guda,karba tayi tare da cewa cire gyaranki,na fada muku ku daina yi min mutunci a kan na siyi abunku,bana son a dinga taimaka min,
Gyaran da Amarya ta sa mata ta cire tace jeki yar Iskar banza.

2weeks ta cika Amana ta gama shirin tafiya Lagos,fitowa tayi sanye da wani 3qtr jean Wanda wandon kaninta ne Yusuf ta yanke da Almakashi ya dawo gajere,wata falkekiyar t-shirt din Hamza ta sa ja ta gama kodewa da jemewa,siririn gyale ta daura a kanta,da wata kwarababbiyar Jakarta karama tasa yan tsummokin kayanta ciki,

Umman Amana sai murna takeyi zasuyi kudi,yarta ta tafi Lagos,yan gidan suma dadi sukeji masifaffiya zata tafi su Shana,Babane ya kalli Amana sai da dariya ta kusa kwace masa irin wankan lagos da tayi,Babane yace Amanata ki canja kaya jibarki kamar inyamura haka zaki je lagos?Yo Baba so kake nayi yawa,Lagos ce fa gwara na saje dasu.

Har tasha Baba ya kaita ya biya mata kudin mota sannan ya bata dubu Hamsin saboda kafin ta fara aiki,sosai Amana ta Adana kudinta,gashi irin katuwar mota ta hau lexs,
Amana anyi kicin kicin cikin Arna,motarsu ta tashi sai washe baki takeyi tana yin guntun turancinta,sun kwashe tafiya me nisa cikin duhun dare,har sun wuce rabi sun kusa zuwa,kitttt driver ya gangare kasa yana ihu yan fashi,ai kuwa sai karar bindiga ce ke tashi,Amana ko a jikinta,nan yan fashi suka fito da kowa waje,motoci suka gani birjik an taresu,ga wasu motoci daban na Alfarma sun kai wajen 10 a Jere,daga gani na wani me kudin ne,Amana motocin me kudin kawai take kallo ta manta a gaban yan fashi take,

Wani daga cikinsu ne ya bugawa Amana tsawa amma ko tsoro baiga taji ba,su Kansu yan fashi dariyar shigar Amana sukeyi,wani azababben gaye me tsananin kyau da kowa yake tunanin Bature,kyau kamar Aljani,da ganin yanda yake tafiya Naira ta ratsashi,sai kallonsa akeyi kowa,yan fashi ne suka nuna shi da bindiga tare da nuna masa wata tsohuwa sukace kayi sex da wannan maza ko yanzu mu aikaka lahira,
Wani takaici da bakin ciki ya mamayeshi,sai hawaye a idon wannan hadadden saurayi suke zuba sharrrrr,tsohuwa da kamar kakarsa ce,gata Arniyace,kuma shi da bai taba zina ba ko da budurwa sai wannan tsohuwar,cikin matsanancin tashin hankali ya riska,tare da dana sanin zuwa Kano a mota,bai bi flight ba,

Amana ita kanta sai taji saurayin ya bata tausayi,taya zata iya cetoshi,sai kallo take kare masa,gashi kamar Aljani sabo da kyau,a ranta tace wannan da gani bature ne Allah sarki ko Hausa ma naga Alama baya ji.

A ranta tace dole na taimaki me kyan nan,Amana ce ta buda tare da kwobarewa da 3qutr tanta,tace easy sir easy dai,wa yace daku ba ku ba,ai wlh ba mazaje sai ku,duk wajen nan Matane,Allah dai ya biya ogoginmu,sai Mazaje,irinku kuna birgeni Allah wlh ba a shiga dawa dan karya, haka Amana taci gaba da yi musu kirari sosai,murmushi ogan yayi na jin dadin yanda Amana take kodasu,
Chapter 3 · 0% Book details