← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 58

Sashe 40

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu ma tana dakan geron ta tuno Alim sai hawaye tana yi Hawaye na bin kuncin ta,Malam Nuhu dake gefe yana jin radio ya mike yau ga kwarzababbiyar yarinya yar iska ke zan koreki fa daga gidana kullum cikin kunci da kuka ko uwarki aka yimiki iyeeee nace Ubanki aka miki? Ke kenan a gidana kullum cikin shigar yan iska kike kina nuna tsaraici,shi yasa ma ga badayanki zubin karuwa shaddar kasuwa ce dake wannan anya jikata tace ba musaya akayi ba,Umma dake wajen Murhu haushin Babanta taji yana zagin yarta sai taji tausayin Amana kuma,mikewa tayi tace ajiye dakan muje ciki muyi magana ba musu Amana ta shige daki tsoho ya dauki Salati yace Hauleeeee Hauleeeee yau ni Ubanki zaki nunawa kin haihu niiiiiiiiii....sai ya saki kuka.

Umma daki ta samu Amana kwance bisa tabarma tana sharbar Kukan takaici tayi rashin Uba da miji yanzu da Ubansu ya na raye duk Lalacewarsa ai gidansa zata zauna,a da suna ganin Baba bai musu rana ba bashi da amfani a garesu sai gashi tun ba a je ko ina ba mutuwarsa tasa sun ga rashin Uba babban wani abune a rayuwa,

Da da Mahaifa sai Allah Umma ce ke lallashin Amana tace kiyi hakuri kinji tashi ki siyo abunda kike so yau kici kinji,Amana bata ce komai ba,Umma ta rasa abinda zata cewa Amana ta sata nishadi Umma gani take yau kudi zata kashewa Amana sai tace Amanan Baba ko za kici mitimis?saida Amana tayi murmushi,Umma taci gaba zan kashe miki kudi ko mene fadi kinji,shuru Amana tayi tare da goge hawaye,Umma tace Aya fa? Dan tamatsitsi?dabino?awara?gurasa?ko dan silif zaki siyo flour kiyi? Amana tace ni kaza nake sha'awa dan Allah Umma ki sai min a ribar da muka samu,Hangame baki Umma tayi tace yo ina kudin kaza yake ke Amana wannan ai zalincine da mugunta har Kaza fa?

So kike ki karya jari canja wani kinji yar Baba,Amana kuma a duniya kazar take son ci,haka tasan Umma ba siya mata zata yi ba,sai ta hakura tace Umma to ki siya min kasar calabar da Aya.
Umma tace ko kefa zauna da kaina zan siyo miki ma,A mana insha'allah sai mijinki Alim ya dawo da kafarsa ya nemeki har ki ja masa aji da yanga ko?kyalkyal Amana ta kyalkyale da dariyar Jin dadi tare da furta ai Sai Umma,Amana sai nishadi Umma bata taba birgeta ba irin yau,tunda Umma ta ambaci Alim ta gamawa Amana komai a duniya.
Umma kuwa mamakin Yarta takeyi yanda take matukar son Alim haka,

Umma tace tab Amana ni kuwa me Alim yake miki ne kike sonsa haka?ko kanki bakya so haka,Amana cike da fara'ar da ta Dade rabonta da yin irin ta ta fara magana Umma baza ki gane ba komai Alim yi min yake Umma komai da kika sani,Umma tace komai? Amana tace komai Umma bazai fadu ba ina fada miki Umma Mijina karshene a komai da kika sani wasu suka rab....sai kuka wiwi Amana ta fara,sannan tana murmushi sosai ga hawaye tace Umma Allah uban giji ya daidaita ni da mijina,Umma Alim mutum ne,Mijina yayi Umma nayi dace,hawaye ya kwararo mata taci gaba da sambatu Umma Alim abin so ne dan ina Jin kunya ne da kullum sai na dinga baki labarinsa abubuwan da yake min.

Umma harda kwalla tace kullum zan dinga tayaki da addua yata.
Fita tayi da kanta ta siyowa Amana Aya da calabar harda Rabin kaza gashashiya sai da Umma ta siyo mata,Amana bata zata ba Allah sarki Uwa me tausayin yayanta.

Nan Amana ta zauna a tabarma ta dinga Garza,
Umma na kallon ta da tausayi.

Kusa da gidan da Amana suke makwaftansu akwai wani Deeni kwaro tantirin dan iskan gari ne,tunda yaga Amana ta fita tallan kunu yaji a duniya Bai taba sha'awar mace ba irin Amana,a ransa yace ko hannun Amana ya shafa sosai to ko ranar ma dan ta shi ya mutu,
Sabo da haka duk unguwar ake ce masa na me Kunu ko hannunta ka shafa sai ya karasa musu da ko yau namutu.

An fara Zafi sosai a Adamawa nan su Amana suka dawo suna kwana a tsakar gida,Amana tana can karshen gidan kan tabarma ta shige cikin net dinta sabo da sauro
Umman Amana ma tana tsakar gidan farkon gidan cikin Net,haka Malam kuwa yana can cikin daki,

Cikin tsakar dare Deeni kwaro ya taka katangar gidan ya dane tare da lekowa a hankali,sai yaga mata biyu saboda duhu gashi baya so Amana ta farka tayi ihu ya kasa shafa jikinta,haka ya shiga gidan ta saman Katanga sadab sadab ya shige cikin Net din Umman Amana ya zata Amana ce, kawai ya ya kara shigewa jikin Umma sosai ya fara shafa jikinta,Umma cikin bacci taji ana shafata ta manta Sulemanu Harka ya rasu cikin magagin bacci tace uhhmmm......Sulemanu....Sulemanu a'a....a'a mene haka Sulemanu,kaji jarabar taka ko,Da gudu Deeni kwaro ya fito fit kamar walkiyya Umma ta dawo hayyacinta ta jawo rigarsa baya ai kuwa Deeni kwaro ya cire rigar cikin zafin Nama ya barwa Umma a hannunta ya tsallake ta Katanga ya fece,

Umma ta fara kuka da kurruwa Sulemanu ya jawo mana yayiwa matan wasu wlh dole ayiwa nasa wani tsohon zan samu na aura kafin wani ya min Illa ohhh yau na gane da saurana Ashe saurayi haka na bi na ai sai aure,
Tashin Amana tayi tace tashi dan Ubanki mushe kina can wani zaimin fyade,bazan iya zaman nan ba wani satin zamu koma gidan Babanki gwara gidan Mirgayi wlh ina gama takaba zan samu sakarkarin dattijo na aura domin ubanku ya jawo mana sai mun tsare mutuncinmu.

Amana sabo da murna harda tsalle da kyar ta iya bacci sabo da murna zata koma wajen yan uwanta,murnar Amana dayace tasan dole bikin Huzaifa da Badriyya Alim zai zo ko don Huzaifa to dole ta ganshi ko taji sanyi.
Malam Nuhu kuwa dadi yaji zasu bar masa gidansa wani satin.

Alim duk abin duniya ya masa Zafi shirye shiryen bikin Huzaifa sukeyi kuma shine kan gaba shi ya tsaida dashi zuwa Adamawa neman Amana.
Washe gari Amana ta tashi fes cikin tsananin murna,karin Jin dadi n Amana Umma tace ta daina talla kudin da suke dashi ya ishesu har su koma gidan Baba Mirgayi.
Yau Amana ta fita siyo kayan miya a hanya garin tsallaka kwalabati kafarta ta goce ta fada katon Kwalabati marar ruwa cikinta ya bugu sosai nan take cikin ya juya sai jini ya yanke mata sosai yake ambaliyar fita daga kasanta,Amana ihu takeyi tana wayyo Allah dana dana zai mutu na shiga uku dana wayyoooo dana kar ka tafi me kama da ubansa,kai nake sa rai zan haifa na dinga ganinka kamar babanka 'yata ko dana me kama da Alim dina,
Gudan jinin Alim,zarota mutane sukayi da kyar ta kara dafe cikin taci gaba wayyo dan Halak dan Alim,wlh Alim ne yayi cikinka mijina Alim a gidan aurenmu,Ka tallafamin kaine shedata da zan wanke kaina wajen babanka,
Deeni kwaro ne ya taho da gudun tsiya masoyiyarsa ta samu matsala yace mahaukata kun tsaya my love tana gabanku shinfide cikin wani Hali kun kasa kaita asibiti sai kallonta kukeyi kuna kallon daga inda jinin ke fitowa kuna Jin dadi kuna kissima surart a zuciyoyinku,to gurin yafi karfinku,daga wanda yayi mata cikin sai nine kadai zan San wajen nan,

Amana dai ta fara fita daga hayyacinta sai nishi takeyi tana Dan Alim...shedata...dan Alim
Habawa ai tuni Deeni kwaro ya Sureta tare da tare napep sai asibiti.

AsmaBaffa

Tnx alot readers.
CIRANIN AMANA

160-165

Official

By
AsmaBaffa

Dukkan yan AsmaBaffa fans club godiya gareku da jinjina.love u all

Da sauri Deeni ya shiga da Amana cikin wani private hospital nan danan akayi emergency da ita likitoci suka rufa a kanta,komawa Deeni yayi tare da sanarwa Umman Amana da Malam Nuhu,a sukwane suka rufta asibitin,Umma sai kuka takeyi tana ohhh na jawo miki,na jawo miki masifa Amana Ashe kaddarace ta kawoni na daukoki nan Adamawa,
Deeni ne ya biya kudin asibiti da komai da aka bukata domin Deeni kwaro akwai neman kudi baya talauci..

Duk iya kokarin da likitoci sukayi dan ganin Cikin Bai fita ba amma abu yaci tura domin tun kafin ma a kara so asibiti ciki ya zube,dan haka suka mata wankin ciki,sai allurai da magunguna na Karin jini da sauran abubuwa,Deeni Kwaro kuwa maltina carton 3 ya kai da madara peak ta ruwa kwali biyu,sai kuma kullum da kalar naman da yake kaiwa asibiti wajen Amana.
Amana kuwa bata magana sai yanda akace da ita,da ance yi zata yi bari zata bari,kai ko gabas kace kalla zatayi,arewa,kudu,
Sai hawayen da basa tsaya a idonta,tasan yanzu ita da Alim sai a darul salam dama da cikin ta dogara idan ta haifa dole zaiyi ko kama da Alim sai ya San da gaske shine Ubansa to gashi ya zube.
Umma kuwa ko a asibitin gasa Amana takeyi sosai tana gyara ta cike da tausayi,
Satinsu guda aka sallamesu,Deeni kam yayi Namijin kokari,sai yanzu ya gane lallai son Amana yakeyi,kuma yaji labarin tana da aure,hakan yasa ya tattara soyayyarsa da kwadayinsa ya kara gaba dan karma ya dinga ganin Amana yana Jin wani abu ya koma daga gida sai wajen aiki,sanadin hakan Deeni kwaro ya daina halayen banza ya samu shiriya Sanadiyyar Amana me Kunu,Amana ma batasan yana yi ba,sunje dai har gidan su Deeni sunyi Godiya sosai,sai lokacin Maman Deeni ta basu labarin Deeni da komai har shiryuwarsa sanadin Amana,ai nan take ya birge Amana ta dinga yi masa fatan alkhairi,Amana ta bashi Address dinsu na gidan Baba.Deeni dai ya karba kawai amma bazai je ba tunda Amana Nada aure, kuma ga kunyar shiga net din Umman Amana da yaya satin Amana biyu cif da yin Bari yanzu kam Umma gyarata tayi sosai a saboda Shan madarar rakumi da sauran Abubuwa yasa Amana ta maida jikinta tayi sumul sumul tayi kyau na ban mamaki sabo da kayan da Umma ke bata tana ci da Sha na gyara,
Chapter 40 · 0% Book details