← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 58

Sashe 52

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jansa gefe Amana tayi tace haba honey jirgi zaka biya musu,harara ya balla mata,pls kaji da kudin nan fa mene amfaninsu,to bari ni na biya musu a nawa kudin,Alim yace gwara da kikace ke ni dai bazan yi asarar kudina ba bare waccen munafukin yaron wlh karya kara zuwa gidana,kuma baza a bashi kanwarki ba salon a dinga zumunci dashi yana kallonki yana jin dadi,ko ya zauna da Salma ya dinga tunanin kamar kece.
Suyi sauri su bar min gida.

Amana kuwa Bedroom dinsu ta koma tare da jawo wardrobe wajen da Alim ke ajiyar kudi da yawa ta ebo tare da dubawa a hand bag, Alim yana Palo a kwance ta wuce da sauri ya jawota ina zakije ya kuma ganinki ya dinga sonki,yana sha'awar min ke, zuwa zanyi na sallamesu,kudina kika ebo? Yeah cewar Amana kudinmu dai,zauna to naje ni na sallamesu idan akan jirgine zan biya amma ki zauna baza ki kara lekawa Palo ba sai sun tafi,
Ai dai mayi Sallama ko da Deeni ne cewar Amana,Alim ne ya fita tare da banko kofa,yana zuwa yasa driver ya kaisu airport sannan yace tace ku gai da gida,Deeni kuwa yasan Alim ne ya hana ta fitowa sabo dashi,kawai sai yace ni dama Abuja zan wuce ba sai ka bani komai ba na gode ina da returning ticket dina,Alim yace Good tare da tabe baki,haka suka tattara driver ya kaisu suka ware,Deeni dama da kudinsa shi yana da sana'a.
Alim kuwa masu aiki ya kira yace su kara share masa Palo su goge shi tas su sa air freshener da yawa da turaren wuta,wai dan karma Amana taji kamshin kalar turaren Deeni kwaro domin Deeni kwaro dan gayune sosai kuma kyakyawane ba laifi,

Deeni kwaro kuwa Bai zarce ko ina ba sai kano har gidan su Amana,yaje cikin gidan ya gaishe da Umman Amana yana ta zura Ido ko zaiga kanwar Amana ya so ta ya aureta,yana zaune da Umma suna hira sai ga Salma ta shigo kuwa daga makaranta Salma yan Ss3,ai kuwa Deeni yaga Salma kyakyawa itama yar caras da ita,
Umma ya tambaya Umma wannan yarkice? Umma tace yar gidan Inna ce kishiyata, nan ya shiga ina..Ina...da kyar yace Umma zata bani ita,Umma kuwa taga Deeni ya shiryu sosai gashi dan garinsu tasan asalinsa tace me zai hana idan tana sonka,ka nemi soyayyarta.

Salma ce ta shigo dakin Umma tare da cewa Umma ina su Inna da sauran yara? Umma tace sun tafi gaishe da yayan Babanki Alhaji Shehu,zasu biya gidan sauran yan Uwa ma sabo da kulla Zumunci,
Shagwaba Salma ta fara wai Umma amma basu jirani ba nace zanje gidan Anty Maimuna fa,Maimuna itama yayar su Amanace me aure da yaranta.
Deeni a ransa yace naga waje irin wannan shagwaba haka me birgewa,
Salma gaishe da Deeni tayi sannan ta fita tana fushi,
Mikewa Deeni yayi tare da yiwa Umma Sallama zai tafi Adamawa,har kudi ya bawa Umma,

Umma ta kwalawa Salma kira,Salma na zuwa Umma tace kinga wannan Saurayin daya fita? Salma tace eh,to Sonki yakeyi kuma mutumin kirki ne,Antynki Amana ma ta sanshi sosai,maza kije Ku gaisa ki rakashi zai tafi gida a garinmu Adamawa yake.

Salma murmushi kawai tayi tare da zurma hijab ta fita wajen Deeni,jikin kofa ta samu Deeni yana jiranta,cike da kunya taje wajensa suka gaisa,Deeni da idonsa yake a tangare tuni ya tsara Salma saiga Salma kamar ta Dade da saninsa Suna ta hira,duk yaron da ya shigo in dai kanin Salma ne ko kanwa sai Deeni ya bashi Dari biyar sabuwa kar,
Haka suka gama Hira ya tafi tare da karbar Number Salma.

Gwaggo dasu Inna kuwa kaf yan uwan Sulemanu sai da suka je suka basu hakuri suka ce kuma za a ci gaba da zumunci,sosai sunji dadi,Alhaji Shehu yace zasu je har gidan su Amana da Badriyya da sauran yaran Sulemanu inda zasu ga mazauninsu a kara karfafa Zumunci.

Amana tana zaune Alim ya shirya zai fita office,Amana tace dan Allah Baby kaje Dani kaji gidan so boring idan baka nan,
Lallashinta ya fara tare da rungumeta yana goga fuskarsa a wuyanta tare da magana a hankali,ba dadewa zanyi ba,kinga anjima su Asiya zasu zo da Autan Mum,idan mun tafi kinga ba kowa gidan ko,kai ta girgiza shike nan to bari na jirasu,
Zagayowa yayi da ita gabansa tare da fara kissing dinta,ya naga kamar kina fushi,murmushi tayi ba fushi nayi ba kawai dai banjin dadi ko period dina ne zaizo I think,har yau bamu samo Aabid ba?na zata ma mun samu dana ga kina wani kiba da kyau,

To da alama bamu samu bafa dan Allah kayi sauri ka dawo a kara nemowa ko zamu dace kafin period yazo kasan yanzu mahaifa ta bude,na matsu a samu Aabid dina,dariya Alim yayi tare da cewa ai kece idan nace a kwana ana yi sai kice waye waye ai gashi nan anji samowa, shagwaba ta fara masa da badan ya daure ba bazai iya fita ba,
Yana fita ta zauna tare da kiran Badriyya suna ta Shan hira,bayan sun gama ta kira Sakeena ma,ta koma su Hamza da su Anty Maimuna,Sadiya da sauran yan Uwa.

Tana gamawa ta fada kitchen tare da shirya lafiyayyen girkinta,ta kara gyara gidan ko ina neat,Alim minti kadan zai kirata yaji wai ko period yazo sabo da sauri yakeyi kar yazo baiyi komai ba,
Wanka Amana ta fito tare da yin Sallar sa'asar ta shirya cikin Atamfa fara me zanen baki Riga da skert dai dai ita Dinkin zamani tayi matukar kyau Sosai duk wanda ya kalleta sai ya kara,tana fesa turare taji door bell,takawa tayi har kasa ta bude kofa Asiya ce da Autan Mum suka kwada Sallama tare da shigowa,
Amana da fara'a mutunci hade da karramawa ta tarbesu har palon Sama ta kaisu,suna ta hira ta cika musu gaba da lemuka da ruwa hade da dambun naman kaza,
Asiya tace na girmeki nesa ba kusa ba ni Antynki ce amma ya zanyi matar yaya dole nace miki Anty,dariya sukayi Amana tace ya Zama dole kuwa ko na fada masa ya zaneki.
Asiya tace rufa min asiri da masifar ya Alim akanki.
Yanzu dai ankon biki na kawo miki fa gashi kuma zan fada miki shirye shiryenmu sai kiji ko zaki kawo idea,
Auta yace hmm Anty Asiya zumudi sai mijin ma ya rainaki wlh danma ya Ahmad ne me hakuri,kin fiye zumudi,Amana tace jinji yaro da'allah rufe mana baki manya na magana.
Dariya sukayi duka,domin Autan Mum ya girmi Amana sosai.

Suna ta hira da tsare tsaren bikin Asiya sai ga Matar Ya Nura ta zo itama tare da mijinta Nura babban yaya,nan suka kacame da hira da nishadi,Amana da Asiya suka jera abincin da Amana ta dafa kala wajen uku,Asiya ta dauko wani mugun azababben foodflask guda hudu ta kawo,Amana da Sauri tace ke yan mata wannan na me aiki me gayya ne,na Oga kwata kwata ne,ko a Ido kin San na me girma Alim ne angon....kasa karasawa tayi saboda hada ido da sukayi da ya Nura,wayancewa tayi da murmushi tana sosa wuya,Asiya ta sheke da Dariya tare da matar Nura suna tsokanar Amana su Na Ogan zasu ci,
Amana ta kwashe flasks dinta ta mayar kitchen,ta bar musu nasu suma masu kyau amma ko kafar na Alim basu kama ba,

Alim ne ya shigo palon da Sallama yagansu suna ta ciye ciye ana ta labari,
Dan Zama yayi suka gaisa yana musu sannu da zuwa Amma idonsa yana ga Amana yana aika mata da kallo tare da harara wai bata je ta tarbeshi ba,
Kunya taji tare da dauke kai,ina zuwa Alim ya shige bedroom, Amana tana so taje wajensa tana dan Jin kunya wai zata yi musu wayo tace Asiya Amarya bari na dauko miki wani abu ko zai miki,zuruf ta shige dakin Alim,
Tana tafiya suka kama dariya wannan yarinyar da abin dariya take cewar matar Nura,Nura yace ina ruwanki yan sa Ido,

Alim daga shi sai towel iya kugu zai shiga wanka,yaji Amana ta rungumeshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayansa,
Sai yanzu zaki wani zo,murmushi tayi yi hakuri kunya nakeji ta ya Nura,
To ya Nura tsaya ki gani shi a gabanki zaiyi abinda yaga dama da matarsa.

Muje kayi wankan kawai,suna shiga toilet yace sai ta shigo sunyi kuma ba iya wanka zaiyi ba ta gane nufinshi kin yarda tayi tace ni bana son kara wanka ga baki munyi kuma dadewa zamuyi fa,
Jeki to karki Dameni da Surutu kuma karki kara cemin kina son Aabid tafi, Amana magana tayi bata fito ba kamar kunkuni,Alim yace me kikace,Amana tace a'a cewa fa nayi Allah zai kawo ai,oh Allah ya taimakeki kuma idan banyi ba baza ki samu Aabid ba yarinya,
Dole ma kayi min na samu,toilet Alim ya shiga,Amana ta bishi ciki,to mene zaki kalle min tsaraici kuma? Dariya tayi ba kallonka zanyi ba kayi wankanka,a toilet din ta nemi waje gefen Bowl din wankan tayi zaman ta,Alim ya fara wankansa,tace haka akeyin wankan,shuru ya mata,can baka sabulunba fa,
Sabulun ya mika mata ungo karasa,hannu tasa zata karba ya jawota tana ihu ya tsundumata ciki tare da danna shower ruwa shaaa ya jikata gaba daya,

Ruwan na zubowa ya tubeta gaba daya ya sake mata sabon wanka,sai kukan shagwaba takeyi masa,
Sai da ya gama murzata son ransa da kyar ya hakura towel daya ya daura musu tana cikin jikinsa kamar masu koyon tafiya suka fito ko mai bata shafa ba tasa doguwar Riga brown color ta dan gyara fuskarta sosai sannan ta zurma hijab har kasa wai kar su Asiya su gane anyi wani abu gashi har ta sake wanka ta canja kaya.tana fitowa suna kallonta suka San anyi wani abu domin rigarta ana hangowa ba kayan dazu bane,
Chapter 52 · 0% Book details