← Book details Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 58

Sashe 5

Ciranin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Key din dakinta ya bata ta shiga harda toilet,ko ciwon raunin da yarabawa suka ji mata bata ji,wanka tayi a toilet din room dinta,ta sa wata rigar atamfa da wani falkeken jean blue,ta fito har wajen tsohon nan,tace Man tashi maza ka rakani kasuwa,yanda yaga Amana a dire gata komai da jikinta takeyi ba wani lako lako,tsorata yayi ya sata a gaba har kasuwa,ta siyo tabarma,da risho da kayan girki,Tsoho yace ke da zaki siyo katifa yan mata,
Tsoho kenan ka gane Neman kudi nazo ba jin dadi ba,shi kuwa Tsoho sai kallon Amana yake yana lashe baki,a ransa yace dole na dandana wannan yar chamai mai din.

Har tukunya Amana ta siyo guda biyu,komai biyu ko daya take siya har ta gama suka koma gida,yau baza ta fara girki ba,a kasuwar ta samu wata me saida doya da miya,nan ta siya taci a wajen,ta siyawa tsohon ma,harda shan lemon kwalba,
Wani me shayi da kwai ta gani tace ayi min hadin kauri,ta manta yanda zata fada da turanci sai tace thick thick tare da gwadawa da hannu 2 cups harda Tsoho,saida suka koshi sannan ta ga wani bahaushe me gashin kaza taje ta siyo biyu manya ta dauki tata ta bawa tsoho tasa,sannan suka Shiga Taxi har gida,
Tsoho dai sai mamaki yakeyi,tare da jin dadi ya samu budurwa me kudi,zai like mata ta zama kawarsa.

Dakinta ta shirya tsab sannan ta fara zaga gidan sannan ta dan leka waje ta kai 1hr a waje amma kafin kace duk ta fara sabawa da mazan layin nasu,ganin kudin da me kyau ya bata suna da yawa har wasu ta siya abinci suka ci,wasu lemo ta siya musu,duk majalisar data je ko shago sai ta raba musu lemuka sunsha hira,kullum haka takeyi har ta kwashe 2wks a lagos,duk ta saba da mutane amma iya maza,dan bata saurarar mata ita,
Yanzu da kaje Layin kace Amana kowa ya Santa,gata dama da karambani,ko mai ta gani sai ta koya kuma ta iyashi,har yau bata samu aikin yi ba,yayin da kudin me kyau daya bata suka kusa karewa,abin na damunta gashi tsohon nan yaki nemo mata aikin,
Amana tana ganin rayuwa kala kala a lagos gasu da Neman mata kamar yan akuya,ita kanta duk abin ya isheta,ko wanne yace zai kawo mata hari,baren ma tsohon daya bata masauki ya dameta da zuwar mata cikin dare wai sai ta yarda sunyi xxx ita kuma baya tsarinta tana tsoron Allah,

Amana zuwanta lagos ta kara wayewa da gogewa fatarta ta kara haske sosai ta kara yin smooth,ta zubar da kayan da tazo dasu daga kano ta siyi wasu wajen 10 amma fa duk ba skert ko doguwar Riga,gaba daya wando dogone pencil da 3qtr maka maka kamar yar America,kamar ta hada dangi da lilwayne wizzy yanda take Burma wanduna manya ga T-shirt dinta har gwiwa suke kawo mata wai shigar kamala takeyi sabo da masu kawo hari hh, p cap kuwa ta siyi kala Uku masu dan kyau,
Har inner wear ta dan siyi abunta,always pad ma da yawa ta siya ta ajiye,Amana har ta fara koyon yarubanci,ga broken English, ga grammar ma tana karuwa sosai yayinda kudinta suke barazanar karewa.ta fara Shiga wani hali

AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳

15-20

By
AsmaBaffa

Amana tana haki tare da addua ta koma gida,Dan Uzuri me gidansu ta gani a tsakar gida suna ta fada da karuwan gidan,sai bin Amana yakeyi da kallo yana lashe baki,yanda yaga zaman lagos yasa Amana ta kara fari sosai tayi yar kiba ga uban hips da breast masu matukar birgewa,yau ya kashi takobin dolene ta bashi zumarta ya sha,ya gaji da hakuri,kuma Dan uzuri gani yakeyi Amana yar iska ce itama karuwa ce duba ga yanda take Hulda da maza da abubuwan da takeyi tare da yanayin shigarta,kai kana kallon Amana zaka San cikakkiyar wayayya ce,

Sai dai zargi da zato ya jawo ya fassara Amana bai bai,domin Amana babu namijin daya taba koda rike mata hannu da niyyar iskanci,ko saurayi bata da shi,har so take taga Wanda zaice yana sonta zai iya aurenta a suffarta,gashi tasan babu me sonta,ta cire a ranta baza ta taba aure ba saboda babu me sonta a haka,itama har so take ta ganta ta dawo kamar mata masu aji da birgewa amma ta kasa.
Da dare misalin 2am tana bacci akan yar tabarmarta,ji tayi kamar ana shafata a hankali dama ita bata da nauyin bacci,firgigit ta farka,mutum ta gani kwance a jikinta touch light ta haska sai ga Dan Uzuri makale a jikinta,Tsoho dashi ko kunya baya ji dan ya girmi babanta ma
Mikewa tayi tare da cewa tsohon banza fitar min a daki wlh iya kwadayinka baza ka sameni ba dakiki,zama Dan uzuri yayi yana mata magiya kan ta amince masa,ka tashi ka fita kafin na kar Karyaka,haba tawan Amana ta,nifa abokin Babanki ne ko dan wannan kya taimakamin,nasan ma kin San komai da ganin Alama kema yar gari ce cikin harkar zumar nan,a fusace Amana ta suri Tsoho Dan uzuri ta bugashi da kasa tare da daga kafafunsa ta lankwasa su saura Kadan su balle kana ta daukeshi ta jefashi waje ai kuwa Dan Uzuri ya saki kara da kuka,

ji kake garam ta kulle kofar ta tare da cewa dan iska ragowar wiwi,ko karfi babu dan kwaya duk ya tsiyace kwanjalallen banza,wannan in banda cuta me zai shafawa mutum,shi da Baba duk together Allah shiryesu,
Ta kwanta tana tunanin halin babansu duk shi ya ja musu,sai ga hawaye idon Amana sharrrr sabo da tuna yan uwanta da gidansu da tayi da mamanta,tare da halayen family nasu,gasu kowa ya tarwatse a gidan babu wani na gari.
Bata marmarin ta koma gida Sam ko kadan,mikewa tayi ta daura Alwala ta fara nafeela ganin bacci ya gagareta,ga tunanin yanzu bata da wani aikin sunyi fada dame shayi,dole gobe ta fita Neman wani.

Washe gari kuwa haka ta dan sha tea dinta tare da siyo kosai tayi Karin safe,ta yi wanka hade da shiryawa cikin wata farar T-shirt fara kal kal siririya dai dai jikinta amma me tsayin gaske ta kai gwiwarta gaban rigar da hoton mace me gashi pink,wandon jean tasa black da fari fari a cinya yayin da wani aka yanka gwiwoyinsa crazy jean dai shi ba 3qtr kuma ba dogo ba gashi birmeme irin nasu wizzy,jikinsa duk aljihuna,wata farar p cap tasa gashinta ya wuce kafada ta tufkeshi ta cusa a cikin hular amma dole ya fito,takalmi tasa black flat me igiya baki,tayi kyau,bata fiye sa dankunne ba,powder kawai da lipstick ta shafa ta fesa body spray dinta me dadin kamshi sai shining takeyi ta fito,amma matsalar bouncing takeyi tare da kobarewa tasa hannu biyu a aljihu,

Tana fitowa tayi ido hudu da Dan Uzuri ya zura mata ido tare da marairaicewa yana mata shagwaba pls babyna aji tausayina mana,wani kallon banza ta watsa masa,sauran karuwan dake gidan su suka kalleta tare da tabe baki,
Ta fara tafiya suka kyalkyale mata da dariya,dawowa tayi a fusace dama haushinsu take ji,wani ruwa ta gani cikin bucket a wajen pampo dauka tayi cak tare da juye musu shi a jiki,ta fara ball da botikin robar saida ta ragargazashi sannan tace ugly prostitute with ur big mouth tayi waje,arnan karuwan nan sun tsorata da bahaushiya Amana mukus sukayi.

Duk inda Amana ta ratsa a lagos gaisuwa ake kaiwa wajenta,saboda girman kai irin na Amana bata taba nuna talaucinta,bata wulakanta kanta,da ta roki wani kudi gwara ta kwana da yunwa, bata harkar karanta shi yasa kayanta masu yar tsada take siya,
Da ace a kauyensu ne to da sai tayi shigarta ko wacce iri tunda kowa yasan asalinta kuma ga talauci bata samun kudi sai yan dabaru,amma yanzu alhmdllh tana samu dole ta kankaro girmanta da mutuncinta, ba raini bata son a rainata shi yasa kullum ake ganinta kamar me kudice.

Direct wani lafiyayyen wajen suya ta nufa wajen masu kudi ne da manyan yara su ke zuwa wajen.manyan guys both christains da musulmai suna zaune a kujerun dake wajen wasu na cin abinci wasu suna jiran take away,
Da ganin wajen Kasan bana talaka bane,a me kudi ma sai ka isa zaka shiga wajen,shiga ciki Amana tayi tana bouncing tare da sa hannu daya a aljihu daya kuma tana danna karmar wayarta touch screen amma yar karama da ita.

Chewgum take taunawa a hankali bakin yake motsawa sai ka kula sosai zaka gane tana cin chewgum, duk da masu kudin gaske ne a ciki kuma manyan yara babu ruwan wani da wani,ba Wanda zai kalleka ma kowa harkar gabansa yakeyi,amma Amana tana shiga wajen duk Wanda yayi tozali da ita bazai so yayi missing kallonta ba,sabo da ko iya tafiyar ta yanda take gadara kamar yar wani shugaban kasa,tana budawa,ga tafiyarta kanta a mazanma sai manyan shegu su keyin irin tafiyar da Amana keyi,ga p-cap dinta yanda ta wani kusa rufe mata ido,Riga har gwiwa ga creazy wizzy jean habawa ai kowa kallonta yakeyi,gata yar fara me kyau sai shining takeyi ga shape,sai ta birge wasu yayin da wasu ta basu dariya,
Kowa dake wajen maza da mata dariyar Amana yakeyi,ita kuwa ko a jikinta,

Manager wajen ta kira a waya sai gashi ya fito wani katon Igbo Arne,yasan Amana ta taba taimaka masa sanda wani yazo zai yankeshi da wuka,ita ce ta taimaka masa,dan haka ya fito da fara'a dauke da murmushi a fuskarsa,yana zuwa ya mika hannu tas suka tafa,da karfi yace Hausa girl How far noooo?tsaki taja tare da riko hantsar wandonta tace a dey woooo bro Steven ,how u na?am fine,wani yorubane ya shigo Frnd din manager shima yasan Amana nan ma suka tafa yana up my girl,u r shining beb,murmushi tayi me kyau wanda ya sumar da mutanen wajen,that's my man cewar Amana,taci gaba man I need a job here,life no easy my man,u know everything Sir,u know how things work,murmushi manager yayi never mind my Frnd u don't have problem with that.nan manager ya bawa Amana aikin me kawowa mutane Abinci,
Chapter 5 · 0% Book details