← Book details Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 55

Sashe 41

Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai san dalili ba haka kawai tafukan hannunsa suke yin wata irin sa
a, daga cikin sa
ar sai ya ga ruwa mai
an yan
i na tsirowa.

Kuma idan ya ta
a wurin ko ka
an ba ya jin zafi balle ya ce ko ciwo ne, sai idan ya kwanta bacci yana tashi zai ga wa
ansu
ananan
wari zagaye da wurin da wannan ruwan yake fita suna tsotsa.

Wannan lamarin ba
aramin
aga masa hankali ya yi ba, a
angare
aya kuma yunwa da tsananin zafi ya galabaitar da su har suke neman
aukar rayuwarsu, saboda ruwa ka
ai sai su wuni su kwana ba tare da sun saka shi a baki ba.

Sannu a hankali tsamin ala
ar da ke tsakaninsu ya ja baya sai dai daga shi har ita babu mai kula wani idan aka cire gaisuwa ita ka
ai take gifta musu, Muhammad ya yi mamakin sauyin kulawar da yake samu daga wurin Batula don ya lura haka kawai za ta zauna ta ri
a jan shi da hira, tun yana
ari-
ari har ya fara sakin jiki da ita.

Kyauta ta watsar da makamanta sosai take kulawa da jaririnra, sai dai babban abin da yake damunta bai wuce matsalar hannunsa da ta lura ba ya iya motsa su ba.

Ita kuma kunya take ji ba za ta iya tambayar Batula dalilin haka ba, kamar Batula ta san abin da yake cikin zuciyarsa ta samu Malam Bukar game da maganar.

Ya
arfafi gwiwarta kuma ya nuna mata kada ta sake ta nuna wa Kyauta abin yana damunta idan ba haka ba Kyauta ta rikice mata nan take.
[2/7, 4:48 PM] Ameera Adam
: 64
Littafin ku
i ne idan kina bu
ata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank.

Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN.

Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

A daddafe Batula ta bari Kyauta ta yi kwana arba'in shi ma don ya zame musu al'ada mai jego bata ta
a fita har sai ta zubar da waka, kafin su yi arba'in Batula da kanta ta ha
a mata magungunan gyara jikinta ya yi kyau ita da jaririnta sun yi
ul Kyauta har wani irin haske ta
ara, ganin zaman nasu ya mi
a ya sa Muhammad ya fara zama
an gari don shi da Malam Bukar suke fita gona kuma rabin aikin shi yake yi.

Wannan abin da Muhammad yake yi masa ba
aramin da
i yake ji ba, da daddadare bayan sallar isha'i kuma ya wuce masallaci
aukan darasi.

Ranar da suka yi kwana bakwai a ranar Malam Bukar ya ba da wani bunsurunsa aka yi wa jaririn hakika, Muhammad da kansa ya yi wa jaririn hu
ubar suna Abubakar.

Kyauta ba ta damu ba don a baya ta ci burin idan ta yi aure ta haihu in namiji ta haifa za ta yi wa mahaifinta magaji idan mace ce kuma ta yi mata magajiya, amma silar gur
atacciyar hanyar da ya biyo ya sa ba ta yi ja a kan maganar sunan ba.

Zamanta da su sai ta fara jin kwa
ayin yadda suke gudanar da addinsu cikin tsari da sanin ya kamata, abin yana birge ta don wani lokacin idan aka kira salla har tuni take yi wa Batula.

Su kansu su Muhammad sun lura don haka suke ci gaba da kyautata mu'amala da ita, Addinin ya yi mata har a zuciya amma ba ta jin za ta iya rabuwa da addinin da suka gada tun iyaye da kakanni wato addin maharba na bautawa abin bauta.

Abubakar yana
ara wayo kamanninsa da na Muhammad a kullin sake bayyana suke yi, haka kawai ta ji
aunar jaririn da Muhammad na ratsa zuciyarta duk da har lokacin ba ta da tabbacin Muhammad jininta ne, don haka kullin sai ta yi yun
urin sanar da shi alamu sun nuna shi
an Sarki Damina ne sai tsoro ya mamaye zuciyarta, a kan dole ta ha
urtar da zuciyarta zuwa lokacin da gaskiya za ta yi halinta.

Saura kwana uku su tafi Muhammad ya sanar da Malam Liman ga mamakinsa sai ji ya yi ya amince zai bi su har cikin Daular, wannan maganar ba
aramin da
i ta yi wa Muhammad da Batula ba.

Malam Bukar shi ma ya bada goyon baya sai dai ya ce ba zai yadda ya kutsa kai cikin Daular ba har sai ya ga yadda hali ya kasance, zuciyar duka mutanen uku fes kowa da abin da yake hangowa na nasara a zuwan da za su yi cikin Daular.

Kaya suka ha
a masu yawan gaske suka shirya komai a daren da za su tafi, hattar guri da abin sha sun tanada, dama tuni Malam Liman ya garga
e su da kada su sake su furta yankin da za su nufa, ya samu Malam Isa ya sake jaddada masa ri
on al
warin da ya ba shi na kada ya fa
a wa mutanen gari wannan Daular suka nufa, cike da aminci ya amsa masa sannan suka yi sallama.

Asubar fari bayan sun yi sallah tun gari bai gama wayewa ba suna idar da sallah Batula ta goya Abubaukar suka
auki hanya suka fara tafiya, jakunan Malam Bukar guda hu
u suka
iba shi kuma Malam Liman ya
auko na shi daga gida suka nausa cikin daji suka ci gaba da tafiya.

Tafiya suka yi mai nisan gaske sai da rana ta fito sannan suka zauna suka fara karyawa, kallo
aya za ka yi wa Muhammad, Kyauta da Batula ka fahimci suna cikin tsananin farin ciki.

Sai da suka ci abinci suka yi
at Kyauta ta ba wa Abubakar ya sha sannan suka sha ruwa suka huta babu jimawa suka ci gaba da tafiya, tafiya ce suka yi mai tsayi babu abin da yake tsayar da su daga cin abinci, kama ruwa sai kuma sallah.

Sai da suka yi tafiyar kwana biyu sannan suka isa babbar hanyar da za ta sada su da
ofar shiga cikin Daular.

Haka kawai ta ji gabanta na fa
uwa jikinta ya
auki rawa kamar mazari, sunkuyar da kanta
asa ta yi tana share hawaye musamman da ta tuna ranar da za a fitar da ita daga cikin wannan Daular, Muhammad na ganin haka ya kawar da kansa don baya
aunar ganin wani babba yana kuka a gabansa.

Malam Bukar ne ya kalle ta ganin duk yanayinta ya sauya ya sa ya ce, "Ki
arfafa gwiwarki kada ki bari magautanki su ga zubar hawayenki don kada su yi tsammanin sake yin nasara a kanki." Bata iya amsa masa ba saboda yanayin da take ciki idan ta ce za ta yi magana kuka ne zai iya
wace mata, ta gya
a masa kai ha
e da goge hawayenta.

Har suna gab da
arasawa ba
ofar Malam Liman ya dubi Batula da Kyauta ya ce su saka
ankwalayensu su rufe fuskarsu don gudun kawo tsaiko a tafiyarsu.

Muhammad ya yi na
i shigen na buzaye, sun jima a tsaye yana tsara musu yadda za su samu shiga kuma su fito lafiya ba tare da an samu matsala ba, kuma sai da suka tsaya suka yi sallah raka'a biyu tare da addu'ar Allah ya
ora su a kan abin da suka saka a gaba.

Suna zuwa bakin
ofar Dogarawa suka tsayar da su, sai da suka yi musu tambayoyi Malam Liman ya ri
a amsa musu cikin hikima duk da gabansa sai tsananta fa
uwa yake, Dakarun
ofar ba su zurfafa musu bincike ba don gani suke me za su tsaya bincike tun da gari banza ma zuwa ake farautar mutane balle su da suka kawo kansu nama ya zo har gida.

Sun dai saka su ajiye Jakunan saboda a
a'ida babu wani mutum da zai shiga ciki har zuwa fadar Sarauniya haye a sama jaki ko doki.

Kamar yadda Malam Liman ya shaida musu sun zo ne ganin Sarauniya takanas wani Badakare ya yi musu rakiya, suna tafe jikin Batula ban da karkarwa babu abin da yake yi.

Bin wuraren ta yi da kallo ganin har yanzu wa
ansu gine-gine kamar yadda ta bar su haka yake, sunanufar fadar Sarki Damina ya sa hawaye ya ci gaba da zarya a furta.

Muhammad kuma a cikin zuciyarsa yake Hamdala don ya tabbata daga nan cikin masarautar zai
ara gaba, don yana addu'ar Allah ya wanke shi a idon mutane.

Tun da su Batula suka shiga ake bin su da kallo musamman Muhammad da kowa ya san yana ciki ba shi da lafiya, suna gab da shiga cikin fadar kamar an ce Muhammad ya juya ya hango
an'asabe.

Cikin shau
in ganinsa ya
walla masa kira, sororo
an'asabe ya yi yana kallon Muhammad da tsananin mamaki.

Sai kuma ya sakar masa murmushi yana fa
in, "Muhammad kai ne ko idona ne?" Muhammad ya ce, "A'a gizo nake yi maka ." Ya
arasa maganar yana murmshi, yana kallon wurin Kyauta ya ga ta dafe kai cike da damuwa tana
an runtse idonta, da sauri ya matsa kusa da ita ya furta.

"Me yake damunki?" Runtse idonta ta sake yi ta ce, "Kaina ne Muhammad kaina." A daidai lokacin suka shiga cikin Fadar Kyauta tana tafe tana layi kamar za ta fa
i, suna shiga cikin Fadar sai ji suka yi ta
walla
ara ha
e da yanke jiki ta fa
i.

Da sauri Badakare ya buga mata tsawa ya
arasa wurinta ya
aga bulalar hannunta ya zabga mata, tun kafin ya sauke hannunsa Muhammad ya wanke shi da mari.

A hargitse Kyauta ta mi
e ta fuska mayafin da ta rufe fuskarta da shi, kusan daskarewa Badakaren ya yi saboda tashin hankali.

Kallonsa ya mayar wurin karagar da Sarauniya take zaune ya yi ya ganta a zaune
yam ko motsi ba ta yi ba sai ma wani irin murmushi da take saki.

Ya sake mayar da kallonsa wurin Kyauta da ke tsaye, yana shirin yin magana ta wanke fuskarsa da mari take ya fa
i ko motsi bai
ara ba.

A wannan karon hatta su Muhammad sun razana da ganin yadda ta zame musu guda biyu, kafin wani lokacin tuni
ofar fadar ta
inke da mutane kowa tururuwa yake ya gane wa idonsa.
Chapter 41 · 0% Book details