← Book details Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 55

Sashe 23

Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wa
anda suke zaune a bakin
ofa tuni suka cika wandonsu da iska saboda tsoron kada hukuncin Kyauta ya biyo ta kansu, Usaina ta tashi zaune tana bin mutanen wurin da kallo.

Sannu a hankali komai ya nemi dawowa
walwarta, ta mayar da kallonta wurin Kyauta ta yi ta kai hannu ta fara laluba fuskarta.

Kamar wacce aka ce ta kalli gefenta tana sauke
wayar idonta a
asa ta ci karo da idonta
waya
aya a
asa.

Kallon Kyauta ta yi ta sa hannunta a cikin ramin idonta sai kawai ta fara ruwan hawaye, tun tana kuka na zuci har ya fito fili kunyar talakawa da mummunar
addarar da ta same ta ya mamaye ta.

Ta mayar kallonta wurin Sarki Damina da yake cikin mawuyacin hali ta furta, "Ka taimaka mana ka nemo mana Mai zamani ya kawo mana agaji." Wani irin dum!

Kyauta ta ji a kanta kamar an buga mata guduma sakamakon jin sunan Mai zamani, haka kawai ta ji sunan na yi mata yawo a cikin
walwarta sai dai tsananin ciwon da kanta yake yi ne ya rinjayi tunaninta, a gaggauce ta dubi Sarki Damina da Usaina ta furta, "Za ku zauna a
ashin ikona har zuwa lokacin da zan yanke muku hukuncin da ya dace da ku, don haka ina bu
atar hutawa." Mi
e wa ta yi har za ta shige ciki ta waigo wurin su Usaina ta furta, "
ofa a bu
e take ga duk wanda yake da ra'ayin bijire wa umarnina tsakanin kai da ita." Tana gama maganar ta shige ciki, da kallo duka mutanen wurin suka bi ta cike da mamaki.

Sarki Damina da Usaina ban da hawaye babu abin da suke yi,
aya bayan
aya mutanen wurin suka fara ficewa kowa da irin maganar da yake tofawa game da hukuncin da Kyauta ta yanke musu, gaba
ayansu babu wanda ya nuna rashin jin da
in hukuncinsu hasali ma kowanne zuciyarsa fes take sakamakon gashin
umar da Sarki Damina ya yi musu.

Sannu a hankali labari ya watsu ciki da wajen cikin Daular, Kandala na zaune da
an cikin jikinta ya fara turowa labarin ya isar musu.

Ta yi mamaki sosai da ta ji an ce Kyauta ce wacce take aiwatar da duk abin da yake faruwa, ba ta musa ba don ita ganau ce ba jiyau ba game da siddabarun da suke iya aiwatarwa a zamanta da su a lokacin da take cikin garin Dabur da ke Zangon maharba.

Wannan dalilin ya sa ta ci alwashin zuwa har cikin fadar don ta gano wa idonta ainihin abin da yake faruwa, farinciki ya kamata don ta tabbata samun yancinsu ne ya zo musu har gida.
angare
aya kuma bayan talakawa sun dawo hayyacinsu tozali suka yi da kayan amfanin gona ni
i-ni
i a gidajensu, lamarin da ya
aure musu kai don ko ka
an babu wanda ya ga gilmawar wanda ya dire musu.

Tun suna
ari-
ari har suka fara sakin jikinsu suka shiga yi wa juna barka don ba
aramin
unci da halin yunwa suke ciki ba.

A ranar cikin Daular sai ta zama kamar biki mutane suka shiga nuna farincikinsu a fili hatta wa
anda suke gidan matsnanciyar wahala da fasa duwatsu sun wadatu da samun abinci.

Sarki Damina shi da Usaina kamar wa
anda aka li
awa gam ko motsin kirki sun gagara yi balle su yi yun
urin arcewa saboda tsananin tsoro, wannan shi ne gaba da gabanta aljani ya taka wuta.

Boka mai zamani duk abin da yake faruwa yana daga cikin tsibirinsa yana kallo, ya yin da tashin hankali ya yi wa zuciyarsa
awanya ha
e da fargabar abin da zai faru da tashi rayuwar don ya tabbata ta su Sarki Damina ta zo
arshe.

Sai ya yi yun
urin guduwa daga cikin tsibirin zuwa wani yankin idan ya tuna ba shi da wata madogara sai ya ji ba zai iya barin tsibirin ba, domin da tsibirin ya saba nan uwa da ubansa kuma nan ne suturarsa da yake rufa wa kansa a siri.

Tsoronsa
aya Idan hankalin Kyauta ya waiwayo cikin tsibirinsa bai san ya zai yi ba, don haka ya yanke shawarar sake kiran manyan aljanun da suke taimaka masa ko za su taimaka masa su kar
i ro
onsa, amma abin da ya sake dagula lissafin rayuwarsa babu ko
ushin wani aljani da ya waiwaye shi balle ya saka ran za su taimaka masa.

Tun da Kyauta ta shiga
akin Sarki Damina wanda yaka cikin Fadar ta kwanta wani irin nannauyan bacci ne ya yi awon gaba da ita, ta jima tana bacci sannan ta fara mafarkin Usaini yana gudu wasu irin munanan hallitu biyu suna biye da su.

Da
yar ya samu ya tsallake wata
aramar
orama wacce ita ce ta so yi wa hallitun katanga da shi, tsayawa ya yi shi da hallitun suka fara kallon-kallo.
arasowarta wurin ita ma ta tsaya suna kallon juna, da tsayuwarta babu jimawa ta hango wata mata na mi
o mata hannu.

A hankali Muhammad ya fara takawa har zuwa wurin matar, ganin haka ya sa hallitun suka waiwayo wurinta da niyyar halakata ta bu
e bakinta wuta na fita da niyyar halaka.

Firgigit ta tashi zaune jikinta na wata irin karkarwa a lokacin dare ya tsala, lokacin kusa
arfe biyun dare ban da kukan tsuntsuye da na
ananan dabbobi babu abin da yake tashi.

Yun
urawa ta yi ta fito a wurin da ta bar su Usaina a nan ta same su a zaune suna baccin wahala, kai tsaye ta fara tafiya a cikin filin masarautar ba tare da ta san in da za ta je fa
afarta ba.

Tana cikin tafiya ta ci karo da shi a tsaye a jikin bishiyar
orawa, hannunta ya janyo ta fa
a jikinsa har tana shirin
walla
ara ya ha
a fuskokinsu wuri
aya yana sakar mata murmushi, cike da tsana ta kalle shi tana yun
urin
wace jikinta.

Ri
e ta ya yi tsam a jikinsa cikin kunnenta ya furta, "Ba za ki ta
a guje mini ba!

Ki sa wa zuciyarki ni naki ne." Fisge jikinta ta yi da
arfi cikin tsana ta furta, "Har abada ba zan gaji da furta maka kalmar tsana daga bakina ba, na tsane ka ba na
aunarka kuma ni ce ajalinka." Tana rufe baki ta ji ya sake janyo ta jikinsa yana shafa cikin jikinta ya furta, "Na ji da
i da kika aminta da ni a wannan lokacin, na kuma amince da
aunar da kike mini don haka zan ci gaba da baki
warin gwiwar yaudarar Usaini kamar yadda kika
aukar mini al
awari." Mamakin kalamansa ne ya kama ta tana
agowa da niyyar ba shi amsa ta ci karo da Usaini a gefe yana kallonsu, gabanta ne ya fa
i ras!

Hankalinta ya kai
ololuwar tashi, ta
wace jikinta da
yar tana fa
in.

"Ka tsaya ka saurare ni Usaini." Bai tanka mata ba ya girgiza mata kai jiki a sanyaye ya fara tafiya, yana gaba tana biye da shi sai dai ya
an yi mata nisa har wuce
angaren gidan yari.

Yana shiga Kyauta ta rufa masa baya tana shiga mamaki ya kama Dogaran
ofar, bin ta suka yi da kallo aka rasa mai bakin magana.

Wuri-wuri ta fara yi tana kalle-kalle kamar tana neman wani abu.

Kai tsaye
akin Muhammad ta wuce sai dai duhu ya sa ta gagara gane abin da yake ciki.

Wurin da Dogarawan suke a tsaitsaye ta koma ganin ya sake yamutsa hanjin cikinsu a tunaninsu wani laifin suka aikata, tana zuwa ta
auki
aya daga cikin itacen da ke ci da wuta.

Kai tsaye
akin Muhammad ta nufa ta tura
ofar ta fara tafiya har zuwa wurin da yake kwance, a takure yake a kwance kallo
aya za ka yi masa ka fahimci bai ji da
in kwanciyar ba.

Kyauta na ganin shi ta jingine itacen ta
arasa wurinsa ta zaune ha
e da jingina kanta a jikinsa tana fashe wa da matsanancin kuka, sama-sama cikin baccinsa ya fara jiyo shasshekar kukanta.

Firgigit ya tashi a tsorace don ba
aramin razana ya yi ba, gefe ya matsa yana sauke ajiyar zuciya a tsorace ha
e da furta.

"Ya Ilahi!"
agowa ta yi tana kallonsa take kanta ya fara sara mata ta saka hannuwa biyu tana dafewa, daga wurin da yake tsaye ya furta.

"Baiwar Allah me na yi miki, me ya kawo ki
akina?

Me ya sa kike son jefa rayuwata cikin tashin hankali?

Me ya sa kike son
ulla mini zargin da babu mai fitar da ni sai Allah." Hawaye ne bibbiyu suka ci gaba da zarya a fuskarta ta lallashi kanta da
yar tana fa
in, "Me ya sa kake nisantata?

Idan a kan maganar Alhasan ne ta yaya ba za ka yi mini adalci ba?

Ka koyar da ni soyayyarka a lokacin da ban saba ba, ka
ora mini nauyin abin da yake ciki a yanayin da ban zata ba.

A yanzu kuma ka na son yin wasa da rayuwata a lokacin da ban yi tsammani ba, me ya sa kake son
ullo da irin wasan nan a tsakaninmu alhalin ka san ba zan iya jurewa ba?

Yanzu za ka nuna mini kulawa da soyayya daga baya ka nuna mini ba haka ba, shin ba ka tausayin halin da nake ciki ne, ba ka ganin ka na azabtar da ni da soyayyarka?" Kan Muhammad ba
aramin
aurewa ya yi ba, ko ka
an ya gagara fahimtar in da maganarta ta dosa.

Ya ha
e fuska sosai yana nuna mata hanya ya furta.

"Fita ki ba ni wuri idan ba haka ba zan fitar da ke!" Cak ta tsaya tana kallonsa, a zuciye Muhammad ya ja hannunta har zuwa
ofar
akinsa yana fitar da ita ja
ofar da
arfi ya saka saka
ta.

Dur
ushewa ta yi tana wani irin gunjin kuka mai tsuma zuciya, karo na farko da ta ji da-na-sanin afka wa soyayyarsa.

Da ace wani zai gaya mata Usaini zai guje ta tana iya sa wa a datse rayuwarsa amma sai ga shi yana
arin juya mata baya, kamar daga sama ta riski muryarsa yana fa
in.
Chapter 23 · 0% Book details