← Book details Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 55

Sashe 3

Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga gefen Usaini Boka Rabo ta hango ta danne masa
afafuwansa ta yadda ya gagara motsawa balle ya ja cikinsa ya taho gare ta, kallon Sarki Alhasan ta yi tana shirin yi masa magana ta ji ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya.

Firgigita ta farka a hargitse, Usaini ne ya fa
o mata a rai ga mafarkin da ta yi yana kai kawo a
walwarta.

Yun
urawa ta yi ta nufi
akin da Usaini yake bacci hannunta
auke da itacen da take haskewa, tana shiga ta ga wani
aton kwa
o ya gudu daga wurinsa da ya fice ta window.

Mamaki
arara a fuskarta ta furta, "Kwa
o a wannan lokacin me ya kawo shi?" Tana haska wurin Usaini daga wurin
afarsa ta na jini yana bin wurin, gabanta ne ya fa
i tana matsawa ta ga babu
an yatsa
aya daga jikin yatsun
afar Usaini.

Hankali a tashe ta nufi
akinta ta
auko wani garin magani wanda ita kanta ba ta da tabbacin zai magance ciwon da ke jikinsa, ta fara
a masa.

Ta samu jinin ya tsaya sannan ta gyara wurin, daga gefensa ta ra
a ta zauna, a hankali ta fara gyanga
i gajiya da bacci ya sa ta
ingire ta yi bacci.

Sanu a hankali tun Sarauniya ba ta saba da yanayin jinyar Usaini ba har ta saba, sai dai rashin dawowar amintaccan Bawanta ne ya fi
aga hankalinta.

A wannan lokacin da Boka Rabo ya nuna mata halinsa na zahiri ya sa ta daina aminta da kowa a cikin masarautar, da a ce Usaini yana cikin lafiyarsa shi me mutun na biyu da take ganin za ta iya ba wa amana shi ma zuciyarta za ta yi wasu-wasi domin tun da ta fara mallakar hankalinta ta san waye Boka Rabo da gudumawar da yake ba ta.

A ranar ta
uduri niyar sake tasar wani Bawan da zai nemo mata Bokaye daga sassan garuruwa, kwatsam tana cikin nazari sai ga shi ya shiga fadar tafe da wa
ansu Bokaye biyar.

Biyu matasa ne ya yin da ukun suka kasance tsofaffi tukuf, wani fa
i ne ya lullu
e Sarauniya tamkar wacce aka yi wa bushara da warkewar Usaini.

Nan take ta sa aka
auko Usaini da ya la
ume wuri
aya kamar kayan wanki, a rumfar (Falo) farko aka ajiye Usaini
aya bayan
aya Bokayan suka fara shiga suna jarraba na su tsafi da sihirin don ganin sun tashe shi amma babu wani sauyi.

Haka Sarauniya ta ri
a kawo lada tana biyansu
aya bayan
aya suka fice daga fadar cike da takaicin rashin nasara, saboda Bawan nan ya al
awarta musi samun gwaggwa
an lada daga wurin Sarauniya matu
ar suka warkar da shi.

Ganin ba a dace ba ya sa Sarauniya ta bar
unbiya-
unbiya ta fito ta ba za mutanen gari a kan su nemo mata masu maganin gargajiya,
an bori da Bokayan da za su warkar da shi.

Wannan dalilin ya sa masu magunguna da matsafa suka bu
e cin kasuwarsu da tsinke a cikin Dular sai da kullin lamarin Usaini
ara ci baya yake, a wannan lokacin cikin Sarauniya ya shiga wata bakwai.

Ya fito sosai kamar ba cikin fari ba don wasu daga cikin mutanen yankin sun yi tsammanin ta shiga watan haihuwarta.

Ana cikin haka watarana haka kawai mahaifina ya shirya mini doguwar tafiya zuwa yankin Yamma, na yi matu
ar mamaki don na rasa dalilinsa na yin haka.

Ban musa masa ba don na san kome yake shiryawa ba zai cutar da ni ba, ina ji ina gani da asubar fari na bar yankimu na nausa yankin da ya tura ni wurin amininsa da ke
asar yalwa.

Tafiyar Boka mai zamani da kwana biyar watarana Boka Rabo ya taka cikin Fadar Sarauniya, ta yi matu
ar mamaki da ganinsa ba ta ta
a tsammaninsa ba.

Mazauni ta nuna masa sannan Fadawan suka fice suka ba su wuri, Boka Rabo ya kalli Usaini da ke gefe a na
e ya bushe da wata shu'umar dariya ya ce.

"Majiyanciya barka da rana." Maganar ba
aramin
ata ranta ta yi ba, ta shanye
acin ranta ha
e da sakin murmushin
arfin hali ta ce.

"Barka dai sarkin maciya amanar duniya." Boka Rabo ya yi dariya har ta tafi ya bata amsa da cewar, "Duk cin amanar da zan yi ban ka mahaifinki ba, ni asalin
an garin nan ne tun iyaye da kakanni.

Mahaifinki tsintacciyar mage ne, idan ana maganar cin amana babu kamar mahaifinki.

Yanzu da za a nutsa da bincike baki cancanci zama Sarauniya domin mahaifinki bai gaji sarauta ba.

Don haka abin da ya kawo ni kenan, ina mai baki shawara da ki daina wahalar da kanki a wancen abin." Boka Rabo ya yi maganar yana nuna Usaini da ke kwance sannan ya ci gaba da cewa, "Wallahi ba zai tashi ba, ni nake gaya mik mutuwa zai yi don haka ki ba ni aron kunnenki tun wuri tun lokaci bai
ure miki ba ki amince da bu
atar
an'uwansa.

Idan kuma kika bijire za ki kai kanki ki baro, don idan za ki tara bokayen duniya wallahi ba zai ta
a samun lafiya matu
ar ba ni na bayar da makarin ba.

Idan kuma kin ga na amince da baki makarin sihirin jikinsa sai kin amince da sharru
ana da na Sarki Alhasan." Boka Rabo na zuwa nan a zancensa ya mi
e har ya je bakin
ofa ya juyo ya ce, "Kada ki manta jama'ar gari babu wanda ya san ina da hannu a cikin ciwon Usani, idan za ki kwana kina gaya musu babu wanda zai aminta da batunki.

Dalilina na ha
a kai da Sarki Alhasan ya gadar mini da wani sirrin la
ani wanda ya dafa
ana boka mai jiran gado Boka zamani don haka.

Don haka na taimaka masa muka binne sirrin baiwarki, muka binne ruhin masoyinki uwa-uba muka binne la
anin samun lafiyarsa wanda tono ni sai ni da na binne.

Idan har kin ga kin sake samun wannan baiwar sai dai a wata rayuwar taki ta gaba, na tabbata kafin ki sake dawowa na bar duniyar zuri'ata ma ba ta nan idan ya so sai ki
auki fansa akan wanda kika ga dama." Yana gama maganar ya fice daga cikin fadar.

A bakin harabar fadar ya tsaya ya yi yekuwar mutane, kafin wani lokaci tuni wurin ya cika ma
il.

Sai da ya
are musu kallo sannan ya fashe da matsanancin kuka, mamaki ne ya kama su.

Wasu daga ciki suka shiga fargabar ko wani abu ne ya faru da Sarauniya, sai da ya yi mai isarsa sannan ya fara cewa.

"Na tara ku ne domin na tabbatar muku da sarauniyarmu na cikin wani sakamakon ciwon da ke damun masoyinta, don haka ya kamata ku du
ufa wurin nemo masu magungunan da zai warkar da shi domin yana cikin matsananciyar jinya.

Duk irin
arfin tsafi da sihirina na gagara aiwatar da komai, yanzu haka da
yar na lallashe ta amma tana cikin matsanaciyar damuwa." Duk maganar da Boka Rabo yake yi Sarauniya na zaune tana jin sa, don haka takaici da ba
inciki ya mamaye ta.

Tana jin sa ya gama maganar ya sallami mutanen suka kama gabansu, sai dai a yanayin muryoyinsu da ta ji sun shiga damuwa da jin kalaman Boka Rabo.

Wa
annan maganganu ba
aramin
aga hankalin Sarauniya ya yi ba, daga
arshe ta gagara ha
uri ta samu Boka Rabo a kan ya sanar da ita shara
an da za su gindaya mata idan ta ji za ta iya sai ta amince.

Lokacin da Boka Rabo ya ji batun da Sarauniya ta zo masa da shi sai da ya yi dariya mai isarsa, takaici ne ya kamata amma ta ha
ura ta shanye damuwarta tana sauraransa.

Kallonta ya yi ya furta, "Shara
i ma farko dole za ki je Masarautar maharba a na ne Sarki Alhasan zai sanar da ke shara
i na biyu.

Idan ya gaya miki shara
i na biyu ki dawo ni zan sanar fa ke shara
i na
arshe, na yo ratsuwa da abin bauta ruwa na ke ba matu
ar kika bi umarninmu sai bu
atarki ta biya." Da yake zuciyar Sarauniya ta suke kai tsaye ta amince da kalaman Boka Rabo, abu
aya ta
udurta a zuciyarta ba za ta ta
a auren Sarki Alhasan ba ko da kuwa ita ma sai asirce ta, ta koma kamar yadda Usaini ya koma.

Farinciki ne
arara ya bayyana a fuskar Boka Rabo don haka ya furta, "Ina yi miki fatan nasara, sannan ina mai yi miki albishir da dawowar mahaifinki nan ba da da
ewa ba." Cak Sarauniya ta tsaya ta kasa gaba da baya, ganin haka ya sa Boka Rabo ya ce, "Zuwan mahaifinki ba zai ta
a canza rubutacciyar
addararki ba, idan ba ki manta ba tun kafin tafiyar mahaifinki ba shi da wani tasiri a Daular nan hatta siddabarunsa sun ja baya, kin ga kuwa babu abin da zai iya aiwatarwa." Jinjina kai Sarauniya ta yi cike da
ashewar zuciya ta furta, "Ko da zai zo yanzu ba na bu
atar taimakonsa, zan tsaya a kan
afafuwana.

Zan sadaukar da komai saboda soyayya, zan yi duk wani aikin wahala saboda soyayya amma ina mai tabbata maka ba zan ta
a sadaukar da soyayyar Usaini ga waninsa.

Idan ka na mafarkin Alhasan zai same ni ka daina ko da zan rasa Usaini na yi rantsuwa da tasirin baiwata ba zan ta
a aurensa ba.

" Tana gama maganar ba ta jira cewarsa ba ta fice daha cikin tsibirin, ka tsaye
akin da Usaini yake kwance ta je ta same shi.

Duk abin da ya faru tsakaninta ta da Boka Rabo sai da ta sanar masa, ta kira wa
ansu manyan bayinta biyu ta sa aka
auki Usaini aka saka shi a cikin keken dokin da za ta tafi, duk wani kayan bu
ata sai da ta
auka tun daga abin ci da na sha da ganyane da da za ta ri
a sauya wa Usaini.
Chapter 3 · 0% Book details