← Book details Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 55

Sashe 29

Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya
an yi tafiya mai nisa sannan ya fara hango wa
ansu bukkoki, da sauri ya nufi wurin bai damu da jinin da ya
ata masa jiki ba kaca-kaca.

Tun daga farkon shigarsa cikin
aramin
auyen mutane suke bin sa da kallo, saboda kallo
aya za ka yi masa ka fahimci ba ya cikin hayyacinsa.

Duk in da ya ga taron jama'a da ya
arasa sai su dare a ri
a nuna shi ana guduwa, abin duniya goma da ashirin ya ha
e masa.

Yana niyyar juyowa ya ci karo da wani dattijon magidanci a kan jaki da alama daga gona yake, da sauri ya tare shi cikin magiya ya furta.

"Baba don girman Allah ka taimaka mini!" Mamaki ya kama mutumun ganin jikin Muhammad duk jini ya ce, "Yaro waye kai daga ina kake?" Muhammad ya ce, "Labarin da tsayi amma yanzu haka muna bakin kogon dutsen can har da mace yanzun nan ma ta haihu da
an uwana da ya rasa ransa duk suna can." Zaro ido dattijon ya yi yana kallon Muhammad ya ce, "Gawa fa yaro?" Muhammad ya gya
a masa kai ya furta, "Hatsari ne ya same mu a kan keken doki." Shiru Dattijon ya yi sannan ya furta, "Shi kenan mu je amma sai na
arasa wurin iyalina na sanar da ita abin da yake faruwa." Cikin jin da
i muhammad ya ce, "Ba damuwa na gode Allah ya biya ka Baba." Tare suka ci gaba da tafiya mutumin yana kan jakinsa Muhammad na biye da shi a
afa har suka
arasa
ofar gidansa mutane na biye da su da ido, a
ofar gida ya tsaya Dattijon ya shiga bayan wani lokaci ya fito mai
akinsa na biye da shi da alamu ba ta amince da taimakon da Muhammad yake nema ba don yankin nasu ya yi
aurin suna wurin
an fashi da makami.

Ganin Muhamnad ya sa ta yi turus ga wata matsananciyar fa
uwar gaba da ta ziyarce ta, ya russuna har
asa ya gaishe ta, ba ta amsa ba sai bin sa da take yi da kallo.

Shi
in ma kallonta yake yana ganin kamar ya ta
a ganin fuskarta, jiki a sanyaye ta furta.

"Yaro ka ji tsoron Allah ka ga har gida ka zo neman taimako, wanda na tabbata duk fa
in garin nan ba lallai ka samu wanda zai yi shahadar bin ka
ololuwar wurin da ka fa
a ba." Cike da girmamawa Muhammad ya
ago da niyyar ba ta amsa, haka kawai ya ji gabansa na fa
uwa ya
ura mata ido har sai da ta tsargu tana shirin yi masa magana ya furta, "In Allah ya yarda Baba za mu je lafiya mu dawo lafiya na yi miki al
awari." Jinjina kai ta yi sannan Dattijon ya ja jaki
aya ya mi
a wa Muhamad ya yin da shi ma ya hau
aya suka koma wurin da Kyauta take zaune.

Me ye harshensu?

Wace ce wannan matar?

Shin wannan jaririn
an waye na Usaini ko Yarima?
[2/7, 4:48 PM] Ameera Adam
: 56
Littafin ku
i ne idan kina bu
ata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank.

Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN.

Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Suna tafe Muhammad yana nuna masa hanya har suka
arasa, da farko wurin gawar Haruna suka tsaya.

Muhammad da kansa ya cicci
i gawar ya
ora ta a kan jakin da ya zo a kai, Dattijon ya
are wa kayan Haruna kallo ya ga kamar ya san irin launin kayan don sun yi masa kama da kayan bayi, ya kalli Muhammad ya furta, "Kai kuwa yaro daga wanne yanki kuke, saboda wa
annan kayan kallon sani nake yi musu?" Muhammad ya ce, "Baba mun fito daga cikin wata Daula ne." A razane tsohon ya
ago yana kallon Muhammad, ganin haka ya sa Muhammad ya sha jinin jikinsa ya
an sosa kai sannan ya furta.

"Ni ma asalina ba
an yankin ba ne farauto ni aka yi cikinta yanzu haka wannan bawan Allah da ya rasu shi da wani Dogari ne suka taimaka mini na fito daga cikinta." Gama jin kalaman Muhammad ya sa Dattijon ya sauke ajiyar zuciya yana fa
in, "Yaro tabbas ka auna arzi
i babu kokara a hannuna kuma ni ka
ai ne, domin wannan
anin garin nan namu da kake gani da a gaban mutanen cikinsa ka ce kun fito daga cikin Daular na tabbata sai sun kusan kwankwantsa namanka, gaba
ayanmu da kake gani babu wanda ba shi da tabon Daular nan matu
ar BA
AR DAULAR da na sani ce." Tsohon ya ri
e kunnensa da hannunsa
aya yana mai kallon Muhammad cikin
arfafa maganar da zai fa
a ya furta, "Ina mai jan kunnenka ko da wasa kada ka sake ka ambaci BA
AR DAULAR nan a cikin garin nan duk irin tambayar da za a yi maka ka ce daga wani garin kake, don na tabbata ka na furta sunan Daular ba za su saurare
arashen maganarka ba za su far maka." Gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke don bai san ta yadda zai fara gabatar masa da Kyauta ba, jim ya yi yana nazari na farko idan ya gabatar da ita taimakon da yake son yi musu zai rushe shi, na biyu kuma idan daga baya ya gane matsayinta zai ga kamar ya munafurce shi ne.

Ganin shirun da Muhammad ya yi ya sa Tsohon ya le
a fuskarsa yana fa
in, "Yaro lafiya dai ko haushin gaskiyar da na fa
a ka ji?" Firgigit Muhammad ya
ago yana shafa fuska ya ce, "Ba komai Baba kawai dai ina mamakin yadda zalincin Ba
ar Daular nan ya zo har wannan yankin!" Dattijon ya girgiza kai cike da takaici sannan ya ce, "Gaba da wannan yankin ma idan ka je za ka ji zalinci wannan Ba
ar daular, don duk duniya ba na jin akwai yancin da ake sayar da zalinci ruwa-ruwa kamar Ba
ar Daula." Tafiya suka fara yi har suka nufi cikin kogon dutsen, tun daga bakin dutsen suka fara jiyo wani irin facali da ruwa kamar ana tsalle-tsalle a cikin ruwan da ke kwarara, Muhammad ne kan gaba yana shiga ya hangi jaririn a cikin ruwa a kwance yana bacci ba tare da ya lume ciki ba.

A
angare
aya ita kuma Kyauta tana tsakiyar ruwan tana kai duka da wani
aton ganye wanda duka ba su san na meye ba, mamaki ne
arara ya kama Tsohon ciki firgici ya dubi Muhammad ya furta.

"Kai yaro an ya ba a hanyar jahannama kake son
ora ni ba ka kawo ni wurin nan?" Kafin Muhammad ya ba shi amsa ya ji Kyauta ta ce, "Babu wanda ya isa ya hallaka mini jariri idan ba haka ba yau ko ni ko ku a wurin nan." Kallon tsaf Muhammda ya yi mata sannan ya fara matsawa wurin ruwan bakinsa
auke da addu'a, ya yi bismillah ya
auki jaririn wanda ta na
e shi da wa
ansu manyan ganye wanda da alama a cikin kogon dutsen ta tsinke su, wurin Dattijon ya
arasa sannan ya ce.

"Baba Ina neman alfarma a wurinka don Allah ka taimaka ka ciro mini babbar rigarka zan suturce mata jikinta." Da ya ke ya lura da yanayin suturar jikinta ganye ne kawai bai musa ba ya cire ya juya yana fa
in, "Kai amma wannan yaro ha
uwata da kai ba ta yi mini amfani ba, haka kawai ka ja ni hanyar halaka rana na ganina ina kallon tsiraici ban ji ba ban gani ba!

Astagafiirullah Ubangiji ka yafe minj wallahi zunubinka ya fi nawa don ni wallahi ko iyalina da take halaliyata ba na iya yi mata kallon
urulla, yo Allah na tuba kallon tsiraici ko kallon Jahannama?

Kai yaro dube ni nan, idan ka suturce ta ka same ni a waje zunubin da ka sa na kalla ma sai Allah ya yi mana hisabi da kai." Muhammad ya yi jim yana jin tsohon yana yi masa masifa har ya gama sannan ya ce, "Don Allah ka yi ha
uri Baba wallahi ba da wata manufa na kira ka ba." Dattijon ya waigo da niyyar yin magana karaf idanunsa suka ha
u da na Kyauta, ya
auke kai da sauri yana ri
e baki cike da takaici ya furta, "A'uzubillahi Allah ka mini tsari, wallahi yaro idan ka sake saka ni kallon tsiraici sai na gaura maka ba
in mari a kunci.

Kai ni dai ban san
addarar da ta na amshi tayin taimakonka ba, dama sai da Batula ta garga
e ni na
i waya sani ko rabon jahannama ta lashi rabonta ne ya kawo ni." Ya
arasa masifar yana fita daga kogon dutse, bin bayansa Muhammad ya yi da kallo haka kawai ya ji tsohon ya birge shi duk da masifar da yake yi don duk kalamansa suna kan hanya hakan kuma ya sake tabbatar masa da shi mutumin kirki ne, juyar da kansa
asa ya yi ya fara
arasa wurinta ya karanta mata addu'o'i yana sake tunkararta, ji ya yi ta
wallah wata iriyar
ara tana toshe kunnuwanta.

Tunkaro shi ta fara yi bai damu ba bayan ta fito daga cikin ruwan ya zura mata rigar hannunsa yana sake tofa mata Ayatulkursiyyu, a karo na biyu ta sake
walla
ara wacce ta fi ta farko.

Da sauri Tsohon ya fa
o cikin kogon dutsen yana fa
in, "Kai yaro ba
anyan jego gare ta ba Uban me kake yi wa
ar mutane da rauni a jiki?" A wannan karon kalamansa ba
aramin haushi suka ba shi ba, ya
ago a zafafe ya ce.

"Baba me zan yi mata kuwa?

Yarinyar da ba maharramata ba wai me kake nufi ne?" Sakin baki da hanci Dattijon ya yi ya ce, "Wai ka na nufin ba matarka ba ce?" Muhammad bai waiwayo ya kalle shi ba ya furta, "Eh ni ba abin da na ha
a da ita illah taimako!" Ya
arasa magana yana ci gaba da daidaita zaman rigar a jikinta.
Chapter 29 · 0% Book details