← Book details Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 55

Sashe 14

Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shin duka bayanin da na yi maka sun tashi a iska ko kuwa kana wasu-wasin abin da na fa
a maka ne?" Girgiza mini kai ya yi sannan ya ce, "Na so a ce jinina ne zai kasance abin bautar Daular nan har
arshen duniya, dalilin zuwana masarautar nan kenan don hallaka wanda yake kan karagar mulki ko da kuwa mahaifina ne, saboda wannan Daular tana da martaba da daraja a idanun yankuna da dama.

Shin yanzu sai dai ina ji ina gani a ci gaba da ambatar sunan Sarauniya Shakumdum a kan idanuwana?" Gya
a masa kai na yi ina fa
in, "
warai kuwa haka abin yake domin zanen
addarar ba a kan zuri'arka ko jininka yake ba, sai dai wata
ila wata mummunar
addarar ta wanzu a kan wa
ansu daga cikin zuri'arka amma ba wannan ba.

Ita
in ta musammanan ce don ko a cikin Sarakunan da suka ri
e kambun mulkin masarautar nan babu kamarta, ban sani ba ko don ta ha
a jini da Sarki Musa ne ko kuma tsiron
addararta na tare da ruhinta ne oho." Ina zuwa nan a zance na mi
e tsaye na fara takawa har bakin wannan kafatariyar rijiyar na waiga ina kallonsa na yafito shi da hannu.

Bai musa ba ya taso har yana shirin wuce tsakiyar Tsibirin na daka masa tsawa da cewar, "Kada ka kuskura ka haure wannan wurin idan ba haka ba sai dai wani ba kai ba.

Ni da kake gani na samu wannan matsayin ne sakamakon jinin Sarki Musa da ke yawo a tsoka da gangar jikina, wannan rijiyar da kake gani ya ginata don kada wata hallita ta shallake iyakarta, ko tsuntsu ne ya tako nan sai ya ba
unci lahira balle
an adam.

Ko da rijiyar nan tana cikin tsibirina ban ta
a zuwa na ga abin da yake cikinta ba, don haka na hane ka da bijire wa umarnina." A sanyaye ya amsa mini, murya can
asa ya ce.

"Na yarda da batunka tabbas lamarin Sarki Musa ya shallake hankalin mai tunani." Gya
a masa kai na yi sannan na biya wa
ansu kalaman tsafi da mahaifina ya biya mini na hadda ce, ruwan da ya shanye saman rijiyar ne ya tsinke zaren carbin ragowar kwarin gwiwar da ke tattare da ni.

Da na sake tuna garga
in mahaifina sai kawai na yi ta maza na zura
afata
aya a ciki, ina nan tsaye wata matattakala ta bayyana a cikin rijiyar.

Lokaci
aya na ji gabana ya fa
i, kamar na fasa shiga sai kuma kalaman mahaifina suka sake dawo mini wa
anda ya jaddada mini su babu adadi a kunnuwana.

Ta maza na yi na taka matattakalar da
afata wani irin sanyi na ji ya ratsa ilahirin jikina, tun ina jin tsoro da fargaba har na ci gaba da tafiya ina
ara nutsawa ciki.

A lokacin da na kai
arshen rijiyar sai ruwan cikinta ya
afe kamar ba a ta
a hallitar koda
igon ruwa a cikinta ba, gunkin Sarauniya Shakundum na ci karo da shi a tsaye ta dafe tsohon cikinta da hannunta
aya,
ayan hannun kuma ta saka garkuwa alamar ta kare kanta da shi.

Ina shirn yin magana na ga hawaye na zirarowa daga kwarmin idanunta, wani irin tsiro ya kama ni zuciyata ta fara harbawa da
arfi kamar za ta hudo
irjina.

Ina nan tsaye na ga cibiyarta ta fara haske tana kawowa tana
aukewa, kamar yadda na mahaifiyarta Gimbiya Nuwaira ya ri
a yi a lokacin da tana
auke da cikinta.

Na samu wannan labarin daga wurin mahaifina don babu abin da ya rage mini a tarihin masarauta da sarautar cikin Daular tun daga farko har
arshe.

Matsawa na fara yi gare ta kamar wanda aka fisga haka na ji na matsa gab da ita kaina a daidai
aton cikinta.

Kamar almara haka naji kalamanta na ratsa ni da cewar, "Ka tabbata ka sanar da su sa
ona musamman ga Sarki Rani domin ba
aramin amfani zai yi musu ba, ni ce Sarauniyar wannan Daular ni ce abar bautarku don haka a wurina za ku nemi mafita tun da ni ce mai azurtaku da talauta ku.

Ka je ka gaya masa a yau aka dawo da bautata arzi
i da yalwatarsa zai dawo a cikin daular nan, na yi kewar ahalina na yi kewar Usanina amma ni na san lokaci na nan zuwa da zan
auki fansar abin da Alhasan ya yi mini da masoyina." Ban kai ga gama jin kalamanta ba a zabure na
ago ina sake bin ta da kallo cike da tsoro da mamaki, har lokacin hawayen idonta bai daina zuba ba ganin haka ya haifar mini da sanyin jiki.

Al'amarin Musa ya sake ratsa ni, na taka matattakalar benen na fara fitowa, ina fitowa daga cikin rijiyar ruwan da yake cikinta ya dawo.

Na sake biya
alasiman tsafi nan take murfinta ta rufe ta ruf, a wurin da na bar Sarki Rani a nan na fito na same shi.

Ina
arasawa wurin ya ta
a jikina, a yadda na lura yana cikin tashin hankali.

Ina shirin magana ya katse ni da cewar, "Shin wani mummunan abu ya faru da kai ne?" Girgiza masa kai na yi ya ci gaba da cewar, "A lokacin da ka shige cikin rigiyar take komai ya
auke rijiyar ta shafe kamar ba a ta
a wanzar da ita ba, ka dubi darajar sarauniya Shakundum ka sanar da ni." Murmushi na yi don gaba
aya Sarki Rani a tsorace yake, abin da na lura shi kura ne shi ga tsoro ga ban tsoro.

Idan ba ka fahimci waye Sarki Rani ba za ka
auka cikakken jarumi mara tsoro ne, amma da ka yi mu'amala makusanciya da shi za ta fahimci mugun zabo ne matsoraci.

Duk abin da Gunkin Sarauniya ya sanar da ni shi na gaya masa da garga
in da ta gaya mini, jikinsa a sanyaye ya amsa mini da alamun gamsuwa a tattare da shi.

Mazanina da nake gudanar da al'amuran tsafina na koma na zauna, Sarki Rani ya saka
afa ya fice daga cikin Tsibirin yana mai jaddada makirci da hatsabibanci irin na Sarki Musa.

Tun a lokacin da Sarki Rani ya fita daga tsibirin Boka mai zamani ya ri
a sa
a da warwarar a kan abin da ya gaya masa game da Sarauniya Shakundum, ganin wannan tunane-tunanen ba zai kai shi ba ya sa ya watsar, washegari ya bada umarni aka tara dubban jama'ar cikin Daular ya sake zartar musu da dokar bauta wa Sarauniya da ambatom suananta a duk wani abu da suka saka a gaba.

Camfi gaskiyar mai shi.

Tun daga ranar da suka koma bautar Sarauniya suka fara fuskantar sauyi daga wasu daga cikin al'amuran da ya ta
are musu.

Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya har komai ya koma musu daidai kamar lokacin da suke cikin wadata, Sarki Rani ya sake jaddada dokar Farautar Bayi da Maharba domin ya lura a duk lokacin da aka dawo da bayi sai ya samu wani tagomashin alheri daga gare su, arzi
i da duk wata dukiyarsu tana zama mallakinsu ya yin da yake za
ar duk macen da ta yi masa kyau budurwa ko mai aure ya mayar matarsa.

Ya ci gaba da kafa dokoki da azabtar da talakawa da
ananan yara, mutanen cikin Daular suka zama ba su da wani
anci da gatan sai yadda Sarki Rani ya yi da su.

Kowanensu na tsoron kada ya sa
a wa umarninsa ya sa a hallaka shi har lahira, ni kuma na ci gaba da gudanar da al'amuran bokancina har kawo wannan lokacin.

A kaf mutanen da suka yi zamani da Sarauniya babu wanda ya yi tsawon kwana kamar ni, don haka babu wanda ya san kamannin Sarauniya sai ni da na yi saura daga cikin talakawanta.

An yi Sarakuna kala-kala a cikin Daular nan kuma gaba
aya sun fito ne daga gidan Sarki Gauta wanda zan iya ce muku dukkansu zuri'ar Sarki Rani ne har kawo wannan lokacin da Sarki Damina yake mulki, akwai rikitattun al'amura da za su ci gaba da faruwa wanda ni kaina na gagara gane mafita da hanyar magance su.

Kamar yadda na fa
a muku a baya, tabbas Usaini na cikin Daular nan haka Sarki Alhasan ita kuma Sarauniya Shakundum ba sai na sake tuna muku ita ba."
Ajiyar zuciya mutanen wurin suka sauke gaba
aya, Sarki Damina fuska a ha
e ya furta.

"Ya kai wannan Boka mai
auke da wannan dogon labarin, shin kana nufin ni karan kaina na fito daga zuri'ar Sarki Rani kenan?" Boka mai zamani ya ha
e fuska yana
arin mi
ewa ya furta, "Damina me ya sa kake son ka ri
a dawo yamma arewa?

Shin ba ka ji kalaman da na gaya maka ba ne ko sai na sanar da kai asalinka ba ku gaji wannan sarautar ba ne?" Usaina da ke gefe ta yi karaf ta ce, "Kada ka ci zarafin mijina a idon Talakawansa don ko ka
an ban aminta da wannan labarin
anzon kuregen naka ba." Boka mai zamani ya
aga kafa
a alamar ko a jikinsa yana cewa, "Wannan ya rage na ku, iya abin da na sani na sanar da ku.

A wannan halin da muke ciki a cikin Daular nan hatta
an goye sai yadda za ta kasance da shi, Usaina ki yi ta kanki
urar da ke gabanku ko za a
arar da duka kogin cikin Daular nan ba za ta kwantar da ita ba." Yana gama maganar ya fara tafiya, daga can gefe wata irin guguwa suka hango ga wata irin ku
a dake ratsa kunnuwansu.

A zabure mutanen wurin suka tsaye suna kallo ciki har da Sarki Damina da Usaina, sannu a hankali guguwar ta ci gaba da tunkaro su har ta yi dirar mukiya a tsakiyarsu.
[2/7, 4:48 PM] Ameera Adam
: 47
Littafin ku
i ne idan kina bu
ata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank.

Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN.

Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.
Chapter 14 · 0% Book details