← Book details Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 55

Sashe 20

Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Soyayyar matar da tausayin abin da Yarima ya yi wa mata ya mamaye ta, ta mi
e tsaye a hankali.

Wani Dogari ta yafito da hannu ta furta, "A kai ta kyakkyawan muhalli zan turo a ba ta magani." Kallon Yarima ya yi a tsorace don yana tsoron kada ya yi laifi a wurinsa, a
angare
aya ita ma yana fargabar abin za ta yi masa.

Ya yi ta maza ya kira sauran Dogarawan, suna shirin
aukan Mahaukaciyar ta fara fisge-fisge tana cewa.

"Wannan ma da kuke gani 'yata ce amma ta guje ni saboda na yi mata rowar tuwona.

Ba zan baki tuwo ba ni ma yunwa nake ji, wayyo Allah!
afata ta karye.

Saboda na hana shi tuwo ya
arya mini
afa." Har Dogarawan suka bar wurin Mahaukaciyar ba ta daina surutai ba, idanun Kyauta na kanta har aka fice da ita.

Jiki a sanyaye ta koma kan karagar kunamarta ta mayar da kallonta wurin mutanen da suka yi carko-carko cike da mamaki, hawayen jinin da ke
arin bushe wa a fuskarta ta goge sannan ta ce.

"Abin da na fa
a a baya shi zan maimaita ina son ganin mai ri
waryar masarautar nan a cikin fadata." Wa
anda ba sa nan Boka mai zamani ya bada labarin Sarauniya kallon juna suka ri
a yi suna
us, ya yin da wa
anda suka san da labarin suka ri
a yin
asa da murna suna tofa albarkacin bakinsu.

Jin wa
annan surutun ya sake fusata zuciyar Sarauniya ta buga musu tsawa, jiki na karkarwa suka bazama a guje kai tsaye suka wuce gidan Sar
ki Damina.

Yarima ya waiga wurin Muhammad a fusace kafin ya yi wani yun
urin ya hura masa wata iska a hannunsa na dama, wani irin sanyi ya ji har cikin
ashinsa wanda ya haifar masa da wata irin rawar jiki kamar yana jin sanyi.

Murmushin
eta Muhammad ya sakar masa ya furta, "Wannan ka
an na yi maka idan har ba za ka fita daga rayuwarmu ba." Yana gama maganar ya matsa daga wurin,
ayan hannun Yarima ya saka ya ri
e hannunsa saboda wani irin tsuko da hannun yake yi masa.

Tun yana tsaye har ya dur
ushe lamarin da ya ba wa tsirarun mutanen wurin mamaki da tsoro, sarauniya na daga zaune ta kalle shi tana sakar masa wani shu'umin murmushi.

Ya jima a wurin sannan ya mi
e sai dai hannun tuni ya saki yaraf!

Da alama shanyewa ya yi don ba ya iya sarrafa shi da kansa.

Cikin layi ya fara tafiya taga-taga ya bar wurin, Sarauniya ta yi
wafa sannan ta mi
e a hankali ta fara takawa har cikin fadar.

Tashinta ke da wuya tawagar kunamin da suka yi mata kujera suka rufa mata baya.

Cinciridon mutanen zagaye
ofar gidan Sarki Damina suka yi kamar yadda ake zagaye waina da mai, sai dai gaba
ayansu cirko-cirko suka yi aka rasa wanda zai tunkari cikin gidan domin ya sanar masa da sa
on Kyauta.

Hayaniya ce take tashi tun Dogaran
ofar gidan suna
arin daidaita su har abin ya gagare su,
aya daga cikin Dogaran ne ya shiga cikin gidan a harabar gidan ya samu Baiwar Usaina ya shaida mata abin da yake faruwa, mamaki ne ya kamata don har sai da ta le
a da idanunta.

Kai tsaye
akin Usaina ta
arasa cikin girmamawa ta furta, "Barka da huta wa Gimbiya." Da ido Usaina ta bi ta ba tare da ta amsa mata ba saboda wata irin izza da take ji a kanta tun bayan fitowarta daga
akin Sarki Damina.

Jin shiru ya sa Baiwar ta fahimci uwargijiyar tata a sama take don haka ta sake russunawa ta furta, "A gafarce ni ranki ya da
e dama Dogari Yaro ne ya sanar da ni wani muhimmin sa
o." Tashi zaune ta yi ta mayar da hankalinta wurin baiwar a gadarance ta furta.

"Gaya mini abin da yake tafe da ke." Sosa kai ta yi sannan ta ce, "Dama talakawa ne suka yi dafifi a
ofar gida, an yi musu tambayar duniya sun ce sai Mai martaba ya fita za su tanka." Ido waje Usaina ta zaro don ko a mafarki ba ta jin talakawan cikin Daular za su aikata haka saboda yadda suke tsoron Sarki Damina ko mutuwarsu ba sa tsoro haka.

Jinjina kai ta yi ta furta, "Ki je zan samu mai martaba." sunkuyawa Baiwar ta sake yi ta furta.

"Godiya nake ranki ya da
e." Usaina na mi
ewa ta nufi
akin Sarki Damina, a kwance yake da alama bacci ne ya
auke shi ba tare da ya shirya masa ba.

Da shigar Usaina ta zauna a gefensa ta fara tashinsa, zumbur!

Ya mi
e sakamakon baccin da yake yi ba na da
i ba ne duba da mummunan mafarkin da yake tsaka da yi.

Ajiyar zuciya ya ri
a saukewa kamar wanda ya ci gasar tseren gudu, sai da ya
an shiga nutsuwarsa Usaina ta dube shi tana cewa.

"Yanayinka ya nuna mini rashin nutsuwarka, ba ni labarin mene ne yake damunka?" Runtse idonsa ya yi ya bu
e sannan ya furta, "Mutuwa na gani da
wayar idona!" A yatsine Usaina ta furta, "Mutuwa fa?" Gya
a mata kai ya yi ya ci gaba da cewa, "Yau shekara goma sha bakwai kenan rabona da yin mummunam mafarki irin wannan." Usaina ta ta
e baki ta ce, "Mu ajiye wannan a gefe, alamu sun nuna tsoro da kwarjinin da ke tattare a idanunka sun kau daga zu
atan talakawa." Da mamaki ya dube ta zai yi magana ta dakatar da shi da cewar, "Ka da ka
ata yawun bakinka domin gani ya kori ji, talakawa na
ofar gida sun yi zuga an tambaye su sun ce ba su da abokin magana idan ba kai ba." Ran Sarki Damina ba
aramin
aci ya yi ba, ya mi
e da sauri ya
auki wani ganyen dabino ya cire na jikinsa ya
aura shi a
ugu, hularsa ta farin
arfe ya
auka ya
ora rai a
ace zai nufi hanyar fita Usaina ta furta.

"Bai kamata ka saka
afa kai ka
ai ba domin ina da muradin zartar da u
ubar a kansu bayan taka, saboda
acin rai bai tanka mata ba ya jinjina kai suka wuce Usaina na gaba Sarki Damina biye da ita a baya.

Tsayuwar da Sarki Damina ya yi ce ka
ai ta tabbatar musu da tsantsar
acin ran da yake ciki, yana shirin yin magana
aya daga cikin Talakawa ya furta.

"Ranka ya da
e Kyauta ce ta turo mu wurinka." Ras!

Gaban Sarki Damina ya fa
i amma sai ya ha
iye tsoronsa, takaici ya mamaye zuciyar Usaina a ranta ta take fa
in.

"Wannan tsinanniyar yarinyar ni ce ajalinta idan ba ta yi wasa ba." Sarki Damina ya yi gyaran murya a daidai lokacin Waziri da mu
arraban cikin fadarsa suka
araso hankali a tashe suna cewa, "Mai martaba akwai gagarumar matsala." Wa
annan kalamai na su Waziri ya sake haifar masa da fa
uwar gaba, ya dakatar da su Waziri don ba ya son a fa
i wata
arakar da za ta sa talakawansa su raina shi.

Ya mayar da kallonsa wurin talakawa sannan ya ce.

"Ina jin ku me yake tattare da ku." Cikin ha
in baki suka furta, "Kyauta ta ce tana bu
atar ganinka a fada cikin gaggawa." A fusace Sarki Damina ya buga musu tsawa yana cewa, "Matu
ar ba ku bar wurin nan ba hukunci mai tsanani yana iya bi ta kan kowannenku." Yana gama maganar ya shige gida.

Usaina ta dubi babban Dogari ta furta, "A kashe duk wanda ya yi gangancin tsayawa a nan wurin bayan shiga ta cikin gida." Tun bata rufe baki ba wurin ya yamutse da kuruwa cikin tashin hankali kowa ya yi ta kansa, Dogaran da aka ba wa umarni nan take suka fara zartar da hukuncin Usaina.

A lokacin da ta shiga cikin gida ba ta samu Sarki Damina a
aki ba don haka ta fara nemansa, jin motsinsa a ban
aki ya tabbatar mata da ya tafi yin bayan gida.

Tsaki ta yi don ba tun yau ba tsoro da raunin zuciyarsa yake ba ta haushi ba, ko ita da ta kasance mace tana da dakiya da rashin tsoro balle shi da yake jagorantar al'umma.

Wa
anda suka fara yin gaba tuni suka isa Fada suka sanar mata da abin da yake faruwa, ranta ba
aramin
aci ya yi ba, don haka ta mi
e a hankali ta koma kan
asaitacciyar kujerar da ke cikin karagar ta zauna.

Ta mayar da kallonta wurin kunamin tana cewa, "A zartar da umarnina nan take." Tana gama maganar kunamun suka fara wargatsewa suna tafiya da sauri suka fice daga cikin fadar, tun fitar bakin
ofa ta fara jiyo ihun tsirarun mutanen da ke wurin sakamakon harbin kunamun da suke yi musu.
[2/7, 4:48 PM] Ameera Adam
: 51
Littafin ku
i ne idan kina bu
ata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank.

Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN.

Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Runtse idonta ta yi zuciyarta ba da
i sakamakon ihun da talakawanta suke yi, ta yi haka ne don ta nusar da su bambamcin da ke tsakaninta da wanda yake mulkarsu.

Idan ba haka ta yi ba ta tabbata zai yi wuya su fuskanci ita ce mamallakiyar Daular da abin da yake cikinta, wa
ansu Dogarai biyu ne suka ratso ta jikin bango suka russuna a gabanta.

Kallonsu ta yi tana shirin yin magana suka furta, "Barka da hutawa Sarauniya kuma abar bautarmu Shakundum." Zuciya a raunane ta furta, "Barka dai." Cikin girmamawa suka furta, "An yi shuka ranki ya da
e kamar yadda kika fa
a." Jingina ta yi da jikin kujerar ta kai hannu saman fuskarsa ta ce, "A gaggauta ciyar da talakawa don suna cikin wani yanayi." Cike da girmamawa suka amsa mata sannan suka sake ratsa wa ta jikin bango, hannunta ta kai saman cikinta tana sake jin wani farinciki na ratsa ta musamman da ta tuna da
an kalaman da Usaini ya furta mata.
Chapter 20 · 0% Book details