← Book details Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 55

Sashe 40

Bakar Daula Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana nan zaune Malam Liman suka
arasa wurinsa sai da kowannensu babu wanda ya iya tanka masa, da yake ya yi nisa a duniyar tunani ko motsinsu bai ji ba balle ya san suna kansa a tsaye.

Malam Bukar ya sunkuya zai yi masa magana bai ankara ba ya ga Muhammad ya zabura yana fa
in.

"Na tuna shi ne wallahi, shi ne ba ni ba ne na yi mata ciki, wallahi duk wanda yake son gani da idonsa zan kai shi har cikin fadar." Malam Bukar da tuni ya take
afarsa sai da ya shige cikin
akinsa ya banko
ofa sannan ya fara le
owa ta windo ya ce, "Malam Liman kada ka yo
akina da shi kai shi
akin Batula wallahi wa
anda aka sauke jiya ma ban sani ba ko suna la
e." Murmushi Liman ya yi a lokacin Muhammad ya ri
o hannunsa ya ce, "Wallahi Malam ba ni ba ne Yariman masarautar ne aikata abin da ake zargi." Malam Liman ya ja hannunsa ya zaunar da shi a kan kujera sannan ya ce, "Ita ma ai ba ta musa ba cewa ta yi Yarima ne ya
ata mata rayuwa." Da sauri Muhammad ya gya
a kai sannan ya ce, "Ba ni ba ne Malam wallahi idan ka ganmu kamar mu
aya da shi, don mahaifiyarsa har wurina ta ta
a zuwa tana yi mini albishir da mutuwa saboda an haifo mai kama da
anta." Kallon juna suka yi tsakanin Malam Liman da Malam Isa, Batula da ke tsaye ita ma jikinta ba
aramin sanyi ya yi ba.

Muhammad ya kalle ta ya ci gaba da yi mata
arin bayani don ganin ba ya wanke kansa duk da ya san mai wanke shi a wannan lokacin sai Allah.

Kyauta da ke cikin
aki ta fito hannunta
auke da jaririnta ta furta, "Tabbas Yarima ne don ya fi wannan zafin zuciya, ba shi da tarbiyyar ko ka
an don har mahaifiyarsa ya ta
a cewa zai yi mu'amala da ita." Lokaci
aya suka
auki salati cike da al'ajabi.

Kyauta ta
ora da cewar, "Ban san yadda zan fasalta abin ba amma haka kawai na gagara bambamce tsakaninsu." Batula ta ce.

"Kin tabbata Muhammad da Yariman Sarki Damina suna matsanancin kama?" Kafin Kyauta ta ba ta amsa ya kar
e zancen da cewar, "Wallahi-tallahi da gaske nake, ni da
an sarkin Ba
ar Daular nan muna matsanancin kama.

Haka Allah yake ikonsa na fi zargin shi ya sa ta
ora alhakin..." Muhammad bai
arasa maganar ba ya ga Batula ta yi sujjada a
asa ha
e da fashewa da matsanancin kuka.

Mamaki ne duka ya kama su ba tare da sun fahimci inda Batula ta dosa ba.

Tana
agowa ta share hawaye sannan ta
arasa wurin
akin Malam Bukar ta ce, "A baya na ci alwashin yanke duk wata ala
a da ke tsakanina da waccan Ba
ar Daular amma a yanzu ina me neman alfarma da ka yarje mini na jagoranci tafiyar, tafiyar da zan yi ta don tseratar da jinina daga halaka.

Tafiya mai
auke da sar
iya wacce warwarewatar sai na ziyarci Daular, tafiyar da za ta banka
a labulen sirrin da aka binne tsawon shekaru.

Tafiyar da za ta tona asirin azzalumai su girbi mummunan aikin da suka jima da shukawa, tafiyar da zan nuna wa Damina gaskiyar abin da ya jima da
aryata ni a kansa.

Don Allah kada ka yi mini iyaka don wannan tafiyar
auke take da
umbin nasara da yardar Allah, wa
anda suka binne rayayyiya za su wayi gari da ita har ta zame musu ciwon ido." A fili Malam Bukar ya sauke ajiyar zuciya ya furta, "Ba tun yau nake baki
warin gwiwa a kan haka ba, amma me ya sa kika sanyayar mini da gwiwa a game da zuwa cikin Daular?"
"A wancan lokacin babu wata hujja ko shadar da zan tabbatar da haka illa kamannin da nake yi da
ar uwata, na san wace ce Usaina da makircinta ta kan iya shirya zagon
asa
arshe reshe ya juye da mujiya." Ya gamsu sosai da kalamanta sai dai tsoro ne fal mamaye da zuciyarsa, duk da Muhammad bai fahimci maganganun Batula ba amma ya ba ta tabbacin zuwa cikin Daular ko don ya wanke kansa.

Haka daga
angaren Kyauta ta jaddada zuwa cikin Daular ko da a ce babu jaririn hannunata ballantana zuwanta dole ne ko don saduwa da mahaifiyarta, idan kuma ta yi rashin dace an hallaka mahaifiyarta sai ta san yadda za ta yi ta ku
utar da kanta.

Ganin halin tsoron da Malam Bukar yake ciki ya sa ta nuna masa koda ba zai bi ta zuwa Daular ba ita za ta yi shahada su tafi da su Muhammad.

Daga Malam Liman har Malam Isa babu wanda ya tanka game da tafiyar, daga
arshe ma sai suka yi musu sallama don sun fahimci sun gano bakin zaren kace-nace duka ya
are.

Batula da Malam Bukar ba
aramin godiya suka yi musu ba, Malam Bukar ya yi musu rakiya har
ofar gida.

Kunya ta sa Kyauta ta yi saurin shigewa
aki don sai a lokacin ta fara tuna irin rashin mutumcin da ta rin
a yi wa Muhammad.

Daular Sarki Damina.

A lokacin da Boka mai zamani yake zaune a cikin tsibirinsa haka kawai ya ri
a jin wata irin ku
au!

A cikin kunnuwansa, daga baya wata irin tsawa ta fara tashi a ciki, yana yun
urin mi
ewa ya ga rijiyar ta fara wata irin tafasa ruwan ciki ya fara katantanwa.

Hankali a tashe ya mi
e yana
ingisawa saboda tsufa da rashin
warin jiki, ya bi ta wata
oyayyar
ofa da babu wanda ya san da ita ya fice don tseratar da rayuwarsa.

Ya tabbata wannan harsabibin ruwan ba zai ta
a saurarawa duk wanda ya samu ba.

Tafiya ya yi mai nisan gaske ta can bayan gida sannan ya yada zango a cikin wani faffa
an dutse, dutsen daga gefensa akwai wata
ofa da za ta iya shigar da mutum ciki sai dai daga waje babu wanda zai iya tantance abin da yake cikinsa.

Daga gefen dutsen ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya da
yar, da rarrafe ya rarrafa gefen wata
orama ya kwanta.

Sai da ya mayar da numfashi sannan ya saka kansa ya fara shan ruwa saboda matsananciyar
ishirwar da ta addabi shi.

Sai da ya ji ya
oshi sannan ya sake rarrafawa ya koma can mazauninsa na farko, sauke ajiyar zuciya ya yi yana runtse idonsa.

Yau ita ce rana ta farko ya fito daga cikin tsibirinsa kacokan ba tare da tunanin zai koma da baya ba, shi kansa bai san wurin da ya dosa ba ballantana ya nema wa kansa mafaka ba.

Haka ya yi ta zama yana sa
a da warwarar abin da yafi dacewa da rayuwarsa, wata zuciyar kuma ingiza shi take da ya kashe kansa ya huta ko ya huta wannan sabuwar rayuwar da zai fara fuskanta, don ya tabbata iko da
arfin mulkin bokancinsa a cikin Daular ne kawai.

A yadda aka san rashin imanin sarkin Daular ya tabbata idan ya je wani wurin ya ce daga cikinta ya fito sai ya kwashi kashinsa a hannu, da ya ga ya rasa madafa sai kawai ya yi kwanciyarsa a wurin ya tsunduma tunanin asarar kayan tsafe-tsafensa da ya bari a cikin tsibirin.

A
imauce mutanen cikin Daular kowannensu ya fara nemawa kawunansu mafaka, sai dai wani abin da ya ba su mamaki lokaci guda suka nemi duk wannan annobar ruwan suka rasa.

Duk da haka ba su saki jiki ba har sai bayan wani lokaci da komai ya lafa, sannu a hankali iyayen da suka rasa
ansu suka fara bibiyar cikin gawarwarkin da ke warwatse a filin suna kuka,
an da suka rasa iyayensu sai koke-koke suke suna ambatar sunayensu.

Suna cikin wannan yanayin suka ga Sarauniyar ta bi hayar gidan horo, ba a
auki lokaci ba suka ga ta dawo fuskarta
auke da farinciki.

Tsayawa ta yi a bakin tsibirin tana bin su da kallo sai kuma ta bushe da dariya, mamaki ha
e da tsoro ya lullu
e su.

Carko-carko suka yi suna jiran ji daga gare su, sai da ta ga sun gama taruwa sannan ta ce.

"Wannan abin da muka aikata ba komai ba ne matu
ar za a samu wa
anda za su bijirewa umarninmu, muna fatan za a ji abin da muke fa
a kuma a yi mana biyayya sau da
afa." Zuciyoyinsu cike suke da
aci, zafi da rauni sakamakon mummunar
arnar da aka yi musu daga
arshe kuma babu jajantawa ana son sake ci gaba da bautar da su, wasunsu ba su iya amsawa ba sai hawaye da suke sharewa yayin da wa
ansu suke kukan
asan zuciya.

Babu yadda suka iya haka suka ci gaba da bin abin da Sarauniya kuma abar bautarsu take so.

A
angare
aya suna mamakin sauyin da suka gani a tattare da ita don sun san da farko sun ga tausayi
arara a
wayar idonta.

A yanzu kuma tsantsar tsanar su suke gani a cikin idonta, don haka al'amarin cikin Daular ya sake tsananta a wurinsu, suka fara fuskantar azabtacciyar rayuwar da har gara wacce suka fuskanta a hannun Sarki Damina.

Yunwa da azababbiyar rana ta saka su a gaba, ga aikin wahalar da suka yi ba dare ba rana, sannu a hankali suka fara sabo da wahalar sai dai kallo
aya za ka yi musu ka fahimci suna cikin mawuyacin halin.

Kamar wa
anda aka girke haka Sarki Damina da Usaina suke zaune a wurin da Kyauta ta ajiye su, idon Usaina tuni ya fara fitar da wani irin mugunyar ruwa mai wari da
arni, tun Sarki Damina yana yi mata alkunya har ya fara nuna mata warin idonta na matu
ar damunsa.

A ranar kuwa Usaina kamar za ta cinye shi
anye duk da ita ma tana jin warin idon nata, babu yadda ya iya haka ya ja bakinsa ya tsuke don har kawo wannan lokacin akwai ragowar sihirin da ta yi masa wanda ko ka
an ba zai iya musa mata ba.
Chapter 40 · 0% Book details