← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 90

Sashe 90

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yanzu kowa ya ajiye baton duk wani ƙulli da makirci da wani da maganar mulki, bawai don abun baya ransu ba, kowa da abunda yake shiryawa, Sai zuwa bayan biki a ɗora sabon lale daga inda aka tsaya, ko wane mugu ya adana muguntar sa har zuwa a gama gaba ɗaya hidimar,

Yarima Sultan ne, Zaune a Babban Parlourn Galadima Murtala na sauƙar baƙi, Ancika gaban shi da nau'i Nau'in abinci kala kala, da kwandon kayan Mar'mari, Wanda aka lulluɓe shi da Lallausan yadin karan miski,
Daga ni kasan hankalin sa na wani gurin, Fuskar shi, Babu alamar wasa Ya haɗe cikin Shigar Sarakai ba ƙaramin kyau yayi ba, A gogon dake ɗaure a wrist ɗin sa yaduba, tare da sakin siririn tsaki,
Cikin Taku izza da isa Gimbiya Sultana ke taka wa taci ado Sosai Tayi kyau sai dai sai dai Tufafin da tasa Sam bai hau da Kwalliyar taba, Bayan ta kuyan gine guda biyu, A dai dai ƙofar shiga Parlourn suka ja suka tsaya, ita kuma ta tura kai ciki, Bakin ta ɗauke da Sallama, Fuskar ta ɗauke da Annurin ganin Abun ƙaunar ta,

Ciki Ciki Sultan ya Amsa Sallamar, Wanda badon, Bakin shi da taga ya motsaba da sai tace bai Amsa ba,
"Barka da Warhaka Yarima na Allah yasa kana cikin Aminci"
"Lokacin da na Ɗibar miki ya ƙare, Sai kuma wani lokacin Yarima Sultan ya faɗa yana miƙewa tsaye,
"Da sauri Sultana ta Miƙe itama, Haba Yarima Na kofa magana baka bani damar yi ba,
"Kin zaɓi Aure na ko? To kiɗau mata kan zama dani, Amma a yanzu lokacin ki yaƙare, yana kaiwa nan ya fara taka wa A hankali, sai kuma ya tsaya cak, ba tare da ya juya ba yace,"Haryan zu kina da zaɓi, da Sauran Dama, ki janye Aure na ko, ki Barshi wannan ba matsala ta bace, da hanzari ya ƙara sa fita daga Parlourn, Fadawan sa suka rufa masa baya,
Har ya ɗau tsawon lokaci da fita, Sultana bata daina kallon ƙofar ba, Can kuma ta Duƙushe Saman Gwaiwar ta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,

Ummul Bait Kallon Sultan tayi, Tace Yarima Kafara bujerewa magana ta ko?
"Cikin Sauri Yarima Sultan yace, tuba nake Amin Afuwa, Bana fatan Allah yanuna min Ranar da zan koda ƙin sauraron ku bare na bujerewa maganar ku,
"Ameen, Amma ai nace kaje Gurin Sultana ku tattauna, Kaji ko tana da buƙatar wani abu ko?
"Allah ya temaki ke daga can nake, na baro ta cikin Aminci,
"Masha Allah Amma kayi Sauri, Akwai wani Saƙo da ya iso Bayan Fitar ka,
"Allah ya ƙara miki Lafiya, Yarima zai so sanin daga ina saƙon yake,
"Sulaim ne Ya aiko, Zuwa ga Amaryar Yarima Zaka iya zuwa ka duba,
Shiru Yarima Sultan yayi yana mamakin Jin saƙo daga Aminin sa kuma Ta hannun Ummul Bait Sannan zuwa ga Amaryar ta, Me hakan ke nufi? Take yayi wa kansa Tambayar, Yaushe Aminina yazama Mara kirki yanzu goyan bayan Auren nan yake kenan!? Wallahi sai na rama,
"Allah yasa Yarima yana lafiya, Tunanin Meye kake?
"Murmushi ya ƙirƙiro tare da Faɗin, Alhamdulillah Ummee, ina lafiya,
"To zaka iya tafiya, sai ka duba saƙon Meye, Da'alama kaya ne,
"To na barku lafiya ya faÉ—a tare da fice wa yanufi Part É—in sa yana tunanin, irin Rashin mutumcin da zai wa Sulaim tun a waya kafin su haÉ—u, saboda dama sun tsara A Kano za suyi Walima,

~ Suhaima ~
Zaune take inda tasa ba zama, a kowa ne dare, Sulaim na tsaye daga gefe kamar dole hannun sa ruƙe da Cup mai ɗauke da Black Tea aciki, Kallon gefan ido Sulaim yayi mata Ganin ta zubawa Guri ɗaya ido ne yasa shi kai nashi idon gurin,
"Suhaima ce tace, Bana son a tsaya min akai, Naji daÉ—i zaka zama Ango jibi, ka daina zuwa inda nake,
Duban ta Sulaim yayi sosai, Amma dai kamar kinada Taɓin Hankali, ko kin manta nan ɗin Mallaki nane, kin takuramin kin shiga rayuwa ta, ina so dama in sanar miki, Da zarar angama Wannan Bikin Zanyi maganin ki,
"Suhaima tace, Wani lokacin kamar ba kai ba, Saboda kana da abun dariya, Ba mamaki inada Taɓin hankali, Amma koda nan ɗin yake mallakin ka, tunda kaga ina zuwa sai ka huƙura saboda akwai abunda nake yi anan ɗin, Amma kada kadamu kan ka dan baza ka taɓa sanin ko Meye ba, Sannan kamar yadda kake jira agama biki kayi magani na, nima hakan kawai nake jira"
"kamar yadda kike zuwa nan saboda wani abu nima Ina da nawa dalilin, Wanda bazai sa saboda ke na bari ba, idan kina buƙatar kaɗai cewa to ki canza guri, Dama irin ku marasa gaskiya ai dole su runga zama su kaɗai, Bansan dalilin daya sa baffa ya yadda dake ba, Yakai ƙarshan maganar yana kai cup ɗin Black tea ɗin bakin Sa,
"A É—an zabure Suhaima ta furta, Inna lillahi wa inna ilaihi raji un, wanda yayi dai dai da Shima Sulaim ya furta, Ya rabb me wannan yana kallon sama,
"Wannan shi ne karo na biyu da Suhaima ta kalli Sulaim sosai, Cikin yanayin mamaki ta Furta, Shin Dama kaima kana ganin abunda nake gani anan,?
"Kema kina gani?Shima da mamaki ya tambaye ta,
Ɗaga masa kai tayi alamar eh, Harcikin zuciyar ta tana ƙara tsinkewa da Al'amarin, Ta taɓa tambayar Princess ko tana ganin abunda take gani a gurin Tace mata, A'a Suhaiman ta ƙara nuna mata Amma tace ba abunda taganin, har mata so mai da Suhaiman mahaukaci ya,
Shima Sulaim mamaki yake taya akai Suhaima ke ganin abunda Ya tabbatarwa kansa shi kaɗai ke ganin sa, Tun yana ƙarami acikin Estate ɗin, A kwai lokacin da ya taɓa faɗa wa baffa, Suka zo tare Baffa baiga komai ba, Sai sukai tunanin wai aljanune suka buɗe masa ido, Yaƙara tambayar Sultan still amsar ɗaya ce babu abunda shima ya gani, Tunda ga lokacin ya tabbatar wa kansa shi kaɗai ke ganin Abun,
Tabbas akwai wani abu a ƙasa, Suhaima tafaɗa tana kallon Sulaim shima ita yake kallo..!!!

ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAHI!!
ALHAMDULILLAHI!!!

*_Anan ne nakawo ƙarshen Littafin AHALINMU ƊAYA BOOK 2 sai mun haɗu acikin AHALIN MU ƊAYA Takun Ƙarshe Insha Allah, ina roƙon Allah S.W.T Yasa damu da Alkhairan sa, Allah ka haɗa mu aladan, kuskuran dana aikata acikin wannan littafi Allah kaya femin_*,

*Kuci gaba da bibiyar, Alƙalamin Fatima Y zakariyya (Tymer's Henna)✍️ don samun da ɗaɗan littattafan Hausa novels📚*

_Ƙirƙirarran labari ne, idan wani ko wata yaji yayi dai dai da rayuwar sa ko wani labarin to, Arashi akasamun, Kuskurana da zaku tsinta aciki kuyi watsi dashi saboda nima ƴar Adam ce kamar kowa zanyi kuskure zan aikata dai dai,_

*_Godiya ta musamman gare ku Masoya na Alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke a Faɗin duniya, Allah ya faran tamuku ya albarkaci rayuwar mu baki ɗaya, Allah ya sakawa iyayen mu da Mafificin alkhaeri, Ka gafar ta musu, kabiya su da aljannah ma ɗaukakiya🤲🤲🤲_*

*NOTE! NOTE!! NOTE!!!*
_Gamasu Ƙorafi ko shawara, ƙofa a boɗe take, zaku iya nemana ta wannan number ɗin 08141825210 WhatsApp only,_
Chapter 90 · 0% Book details