← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 90

Sashe 3

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranki ya daɗe Shidin babaƙo bane a masarautar nan kowa yasan shi, ina tunanin kema don bakya ƙasar shiyasa biki sanan shiba, idan kika ganshi anan to tabbas Yarima na nan, sannan banida masani ya akan Sunan sa nafi jin kowa nakiran sa da Aminin Sultan,

Jinjina kai Gimbiya shaheedah tayi cikin ƙasan maƙoshin ta tace zaki iya tafiya idan da buƙatar wani abu zanne meki,

Angama, nabarki cikin aminci Gimbiya ƴar sarki jikar sarki, Allah yajiƙan Mahaifin gimbiya, Galadima Abdullahi Allah ya kyauta ta makwancin sa, takai ƙarshan maganar tare da miƙewa ta fice,

Lumshe ido Shaheedah tayi tare da ɗan jingina bayan ta da jikin kujerar, da alama ba bacci take ba, ta nutsa cikin tunanin da take wayar ta ta ɗauki ruri, ko motsawa batayi ba bare asaran zata ɗaga wayar, akaro na biyu wayar ta ta ƙara ɗaukar ruri, saida takusa tsinkewa sannan ta kai hannu ta ɗauki wayar batare da ta buɗe idonuwan taba,
Cikin sanyin murya wanda hakan kamar ajinin ta yake, "tace hello Mom barka da warhaka" tare da sa wayar a hansakowa, yadda da dawani akusa zai iya jin abunda tacikin wayar ke faÉ—a,
" barka dai shaheedah fatan kin isa lafiya, shiru Gimbiya shaheedah tayi batare da za tace wani abu ba,

Jin shirun yayi yawa ne Tace mom inajin kifa idan babu wani abu zan iya ajiye waya,

Magana akacigaba dayi ta ɗayan ɓangaran wadda aka kira da mom tace, " shaheedah ina son sanar miki dole zaki haƙura da Auran Yarima Sultan, ki auri yarima Safwan ɗan gidan Fulanin sarki,

Sai a lokacin gimbiya Shaheeda tabuɗe idanuwan ta ahankali, kafin tace komai Mom taci gaba da Faɗin," saboda munsamu tabbacin, Yarima Safwan ne zai gaji karagar mahaifin sa nan kusa, to kinga dole shizaki aura, domin lokacin cikar wasiyyar mahaifin ki yayi, kinsan dai haryana kan gaɓar mutuwa abu ɗaya yake faɗa, Mulki! Mulki!! Mulki!!!
Kada mubari mulki yabar hannun mu tun dashi mafarkin sa nason hawa karagar sarki mai cikaba, har Allah yayi masa rasuwa to dole ne É—ansa ya gada,
Shaheedah inaso kisani kece zaki iyadawo da martabar mu, amma hakan bazai samuba idan har ba auran Safwan kikai ba, Tunda sarki Yusuf yasa aka yimana korar kare acikin Masarautar nan nida ɗan uwa ki banƙara Bacci mai daɗi ba kema kinsani, sannan yakwace ki daga hannu na to nayi kuka kamar raina zai fita, amma gashi yanzu Rainon da yayi miki zai amfane mu, kice makasar su tabbas nasan zaki iya,

Wani irin doguwar ajiyar zuciya gimbiya shaheedah tayi kafin tace,
" mom kina son taso da abunda ya kwanta acikin zuciya ta pls kibar ni haka inason zan huta yanzu sannan zanyi tunani kan maganar auran Yarima safwan, kome kenan zamuyi magana amma pls kiyi takatsantsan saboda haryanzu aƙarƙashin kulawar, mai martaba sarki kuke,
Ina meƙa gaisuwa zuwa ga ɗan uwa na ina fatan zaki sanar masa idan na tashi zanne me shi awaya
Batare da jiran Cewar Mom ba Takashe Kiran "Ɗiff" tare da miƙewa ta nufi Bedroom ɗin ta,

_TAƘAI TACCAN TARIHIN MASARAUTAR GABAS_👌

*_Waye sarkin Yusuf shareef???_*

Masarauta ce mai tsohon tarihi sarautar Zaki, mutanan yankin, shuwa Arab asalin su ƴan yankin ƙasar Larabawan Africa ta kudu, wanda suke, kasuwanci, da auratayya tsakanin mutanan arewa hakan yajawo yawan su cikin garuruwan Nigeria bama kamar garin Maiduguri yankin barno State,

Mai martaba sarki shareef zaki, shine sarki a wancan lokacin kafin zamanin, sarki adam shareef zaki, wanda asalin sunan sa ba shareef bane,
Kasan cewar su gadon shareefai shiyasa suke amfani da shareef asalin kakan su kenan, ZAKI kuma shine tambarin MASARAUTAR saboda ƙarfin mulkin da take dashi ga arziƙi da izza, bayan rasuwar sarki shareef zaki, mulki ake gudanar wa mai cike da adalci da tsafta duk wani wanda ke ƙarƙashin sarki adam shareef zaki baƙar ramin daɗi yake jiba saboda adalcin sa da son al'ummar dake rayuwa aƙarƙashin mulkin sa,
Allah ya azurta shi da Æ´aÆ´a guda biyar 5 huÉ—u maza mace É—aya , Yusuf, Murtala, Mahaifiyar su É—aya, Abdullahi, Kabir, Mahaifiyar su suma É—aya, Sai Aziza wadda ita kaÉ—ai ce a gurin Mahaifiyar ta kuma tarasu, itace matar sarki Adam ta biyu 2

Ƴaƴan sun tashi cikin rashin jituwa tsakanin su babu wata kwakkwarar shaƙuwa tsakanin su Aziza sai ta tashi a ɗakin Hajiya Baitu, saboda matsalar iyayen su mata basu da haɗin kai ga kishin jaraba, ko wacce tana nuna tafin ɗaya saboda duka auran gida ne Ƴaƴan sarauta ne,
Mahaifiyar su Yusuf, Murtala, itace uwar gida, wadda suke kira da Hajiya Baitu, bata ɗaukar raini akwai son mulki ga isa da nuna iko, tana matuƙar ƙaunar Ƴaƴan ta sosai, ita ta aurar da aziza saboda hannun ta tayi rayuwa tun tana ƙarama maman ta tarasu, tasamu gata sosai daga gurin Hajiya baitu,

Kowa cikin mazan burin sa yaga yazama shine magajin karagar, sarki Adam, banda mutum É—aya Yusuf babu ruwan sa da mulki hasalima shi ba mazauni bane kuma shine É—an fari a gurin sarki adam, Æ´an uwansa ne kaÉ—ai suke bidirin su,

Mahaifiyar, Abdullahi, Kabir, itace matarshi ta uku ta ƙarshe kuma wadda suke kira da Giwar sarki, tunkafin a haifi aziza sarki adam ya aure ta, saida ta yi haihuwar fari wanda ɗan ta na farko Abdullahi, kafin Mahaifiyar aziza itama ta haihu bayan haihuwar tata ba jimawa Allah yayi mata rasuwa,

Sosai sarki yaji mutuwar ta saboda yana so ta sakamakon tana da hak'uri ga kyau da kai baruwan ta da kowa bata da wani abokin faɗa, hakan yaja mata soyayyar mutanen gidan dayawa, wanda hakan baƙaramin ciwo yake yiwa, Hajiya baitu ba, amma da ta mutu saida jikin ta yayi sanyi sosai itama taji babu daɗi duk da ada bata sonta,
Hakan ne ma yasa ta ɗauki ƴar ta aziza tamkar ita tahaife ta cike da so da ƙauna da bata kulawa tamkar yadda Mahaifiyar ta zata yi mata bata bari aziza tayi kukan maraici ba, saboda ita tamayi zaton Hajiya baitu ce Mahaifiyar ta, saida Giwar sarki ta taɓa goran ta mata sannan tasan ba ita tahaife taba, ahaka babu abunda ya canza,

Rayuwar su na tafi cike da rikice-rikice, kowa da abunda ke zuciyar sa burin kowa acikin su yaga shine asama É—aya,

Wata rana kwatsam Yusuf ya dawo daga ƙasar Mali, bayan ya hallaci ɗaurin auran abokin sa da sukai karatu tare, kai tsaye ya wuce fada gurin mai martaba sarki, ya sanar masa da magana yazo kuma mai girma,
Mai martaba yabada umarnin ya shiga har tura kar sa domin suyi maganar, hakan kuwa akayi, cike da girmamawa Yusuf ya gaida mai martaba sarki adam,
Gani Yusuf É—in yayi shiru hakan yasa sarki faÉ—in inajin ka, zaka iya gabatar da komeye a zuciyar ka,

Ranka ya daɗe ina neman gafara da kuma afuwa tuba nake bisa babban laifin dana aikata a gare ku batare da shawarar ku ba Allah yasanya nutsuwa da haƙuri a zuciyar mahaifi na,

Sosai sarki ya kalli É—an nasa Yusuf, Allah yagafar ta mana baki É—aya, inajin ka yusufa jeka kai tsaye kan maganar ka, Allah shine mafi sannin dai dai, sannan shine sarkin dabaya kuskure mai yafiya a koda yaushe ga wanda yayi laifi kuma ya tuba tsarki ya tabbata a gareshi,

Cike dajin daɗin furicin mahaifin nasu Yusuf yace, Allah ya ƙara maka yawan nasara, Yusuf yana tare da Iyali, ya furta hakan tare da ƙara yin ƙasa da kansa sosai cikin jin nauyi da kunya da kuma tsoron abunda zai biyo baya,

Ɗan muskutawa mai martaba yayi cikin son jin ƙarin bayani abunda ɗan nasa yazo dashi, ganin alamar hakan ne yasa Yusuf ƙara gyara zama sosai ya cigaba da Faɗin,
Ranka ya daɗe, anɗaura min aure safiyar jiya, a ƙasar Mali,
Allah ya sanya hak'uri acikin zuciyar mahaifi na, ni mai laifi ne, na shirya ko ban shirya ba dole na karɓi hukunci, amma ina neman afuwa da kuma yafiya a gurin sarki mai adalci tuba nake, yana kaiwa nan yayi shiru,

Sosai sarki Adam shareef ya girgiza dajin lamarin auran da Yusuf ɗin yace yayi, yasan ɗan nasa ko maganar aure baya so ayi masa bari har ace ga mata, mahaifiyar sa Hajiya baitu tasha nuna masa ƴan mata kala kala ƴaƴan manya da sarakuna wasu matan ma suke kawo kansu, amma bai taɓa kulawa ba saidai ma ransa yaɓaci,

Saida sarki ya gama nazarin Yusuf É—in kafin yace,
Yusufa ai duk abunda kaga ya faru to dole Allah ya riga ya tsarawa bawa tunkafin wanzuwar ransa a duniya, bazai ce naji daÉ—in auran da kayi batare da sanin muba ba, sannan bazance banji daÉ—i ba saboda ai dama abunda nadaÉ—e inaso kayi kenan, kaine babba amma Æ´an uwanka biyu, sunyi aure, to Alhamdulillah,
Allah yasa albarka Allah yasa kubiyun alkhairan juna ne,

Da mamaki Yusuf yaɗago kaɗan ya kalli mahaifin nasa abunda bai yiba tunza mansa, sosai yayi mamakin jin furucin, da sarki yayi take zuciyar sa ta mamaye da wani irin farin ciki, dama babbar damuwar da shine mai martaba idan ya amince to duk wani abayansa yake hatta ita Hajiya Baitu wadda itama yana fargabar abunda zai fito daga ɓangaran ta gashi matar da ya auro ɗin ba ƴar kowa bace hasalima ƴan gudun Hijira ne to tabbas akwai matsala idan Hajiya Baitu taji haka don bata son talaka ta tsani hada inuwa da wanda ba kowa bane,

Cigaba da magana mai martaba yayi, "zamu zauna da Mahaifiyar ka insha Allah, sannan akwai hukunci akan ka na karya dokar masarauta wanda sanin kankane bane zanyanke wannan hukuncin ba, Alƙalan Fada suke da wannan alhaƙin,
Yanzu ina ka ajiye ita iyalin naka sannan Æ´ar waye?? Sarki yayi masa tambayar a jere,
Chapter 3 · 0% Book details