Sashe 76
Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin Khaltum ta tsorata ne yasa, Suhaima kwantar da Murya cikin sanyi, Tace Khaltum kiyi Hak'uri ba daniya nayi ba, Laifin kine, Naga kamar kinji babu daɗi, Akan Maganar danayi, banyi don in wulaƙan takiba, gyara nayi miki a matsayi na na ƴar uwar ki, wanda ko wani naga zai wulaƙan tamin ke sai inda ƙarfina yaƙare, princess kuma Tayi dariya ne saboda abun yabata dariya bawai don wulaƙanci ba, a iya jiya zuwa yau nafahimci hakan daga gareta, idan kika fahimce ta tanada sauƙin kai sosai batada matsala yanzuma na kira ta ne don in tambaye ta wasu abubuwan game da estate ɗin nan yadda komai zai zo min da sauƙi"
Murmushin yaƙe Khaltum tayi, tare da Faɗin Bakomai nasan baza ki cutar dani ba, Kun ƙara waya da Mother kuwa?"
Suhaima tace, A'a Bamu ƙara ba, Amma zanƙirata Idan katin wayar bai ƙareba, Khaltum ina kika samu wannan rigar Suhaima tafaɗa tana nuna rigar jikin khaltum da ɗan ya tsanta?
Ɗaguwa Khaltum tayi da sauri, don tama manta Suhaima bata santa da kayan ba, inda inda tafara, tama rasa Meye za tace saboda tasan ko giyar wake tasha idan Tabari Suhaima taji labarin tana tare da Wani ɗan cikin estate ɗin nan kuma a matsayin Saurayi har yayi mata siyayyar kaya, ai sai takasheta da duka😅
Tsareta Suhaima tayi da ido ƙarara tagano rashin gaskiya, cikin idon Khaltum ɗin amma sai ta basar, ta hanyar Faɗin inajin ki faɗamin,
Em'Am'Am dama budurwar danake aiki a Part ɗin suce tabani, Shine nikuma nasa yau don taji daɗi, Cikin Alamar rashin gaskiya takai ƙarshan maganar,
Hmm Suhaima tayi gajeran Murmushin mai ɗauke da Ma'anoni daban daban, Badamuwa Kiyi mata godiya sosai a madadi na idan nazo nima zanƙara yi mata,"
Ƙul ƙul" hantar cikin Khaltum takaɗa, Amma sai ta daure tace to Insha Allah,
Suhaima jitayi tama fasa faÉ—awa Khaltum Abunda ke faru, Muje nayi Salla ko? Naji har sun shiga masallaci"
Da sauri Khaltum tace A'a ni Zankoma saboda ina tsoron dare, tafaÉ—i hakanne tunawa datayi Tabaro Barrister Sulaiman a gate É—in shigowa part É—in Baffa yana jiran ta cikin mota kuma yace tayi Sauri dama shi yakawo ta,"
"Oh Allah Khaltum ke kam ki rage wannan tsoron naki mana ke komai tsoro yake baki, Shikenan nagode da ziyara, nima ina nan zuwa insha Allah kinga sauɗaya na taɓa zuwa aiki yamin yawa shiyasa,"
To Allah yakawo ki lpy Tafaɗa dai dai suna ficewa daga cikin Coffee gard ɗin, Suhaima tayi part ɗin hajiya Umma kai tsaye ita kuma khaltum ta miƙe ta nufi bakin gate daga can inda Barrister Sulaiman yayi Parking ta yadda ba wanda zai iya hango shi,"
*Ummeetha*
Tunkafin Su ƙarasa shiga Cikin Parlourn Ummeetha Ta hange su, Marhaban lale, Da zuwan, Shattima, Tafaɗa Fuskarta ɗauke da Murmushi,
Shima Shattima Murmushin Yayi, Dai dai Suna Zama Shikuma Yaje gaban Ummeetha ya russuna Cike da Girmamawa, Barka Da Warhaka, Umme Nayi Farin cikin Ganawa daku, Allah yasa kuna Lafiya,
Masha Allah Lafiya Alhamdulillah, Ya Kilishi Aziza Fatan Tana cikin Aminci, yaushe kuka dawo ƙasar?
Tana Lafiya Saƙon gaisuwa Agareku, Kilishi tace A gabatar, Cikin Satin nan muka dawo,
"To muna godiya, idon ta tambayar kan Sultan, Yarima Fatan kana Lafiya, Sai a lokacin shima ya tashi yaje gabanta don Su gaisa, Saboda su haka al'adar su take, idan zasu gaida babba wanda suke jin kunya to sai sunje gaban shi, Sannan basa gaisuwa cikin gaisuwa, Ana gaisawa da Wani suma Su miƙa tasu, Basayin haka,"
Saida Suka gaisa Sosai, Sannan shima Sulaim ya matsa su gaisa, Nazari Sulaim Ummeetha ta shiga yi, Ganin yafaɗa tunani ta fara kodai rashin lafiyar sa tata shi kwana 2 bata sani ba, Ko kuma labarin Auran sa Da Saleema ne yasa shi canzawa haka, Tausayin shine ya lulluɓeta, tsakanin ɗa da uwa sai Allah, Tasan Zuwa Yanzu yasani amma bazai taɓa yi mata maganar ba,
Ita dai taji daÉ—in hakan sosai Amma taso ace matar wata ce ba Saleema ba, Taso ace É—anta yasu Macen da zata kula dashi sosai, Saboda Saleema ita kanta So take a kulada ita, Amma ya zatayi Dole Zata so Saleema kodan Alkhairin iyayen ta akan Sulaim, da su baki É—aya"
Part ɗin Baffa Suka wuce Acan ne, Baffa Yake ƙara Sanarwa Sulaim Maganar Auren Tsakanin shi da Saleema ƴar gidan Uncle Bello, dakuma Barrister Sulaiman shida Sabrina ƴar gidan He Excellency Sambo, Sai Saleem da Suhailat Ƴar gidan Alhaji Hameed Arab Ƴar uwar ka kenan, Ina fata Yariman Gabas ya Sanar maka Zuwa nan da Wata biyu masu zuwa insha Allah cikin sai kufara shiri, kame Fuska Baffa yayi maganar saboda kar Sulaim yace baya so,"
Sulaim Wanda gaba ɗaya Hankalinsa ma ba a gurin yake ba, Ba abunda yace jiyaye kawai bazai iya Zama ba gwara yaje ya kwanta ko yasamu sauƙin, Nauyin Da zuciyar sa tayi masa, Tashi yayi hakan yasa Suma duka Suƙa miƙe Su kayiwa Baffa Sallama, kana Suka wuce, Dama daga Asibitin Sulaim suke, Yaje ɗakko wani File, Gaba ɗaya Sungaji kamar waɗan da sukai tafiyar ƙasa,"
"Kace gaba É—ayan ku angwaye ne, Gaskiya dole nima na nemo matar Aure Bazai yiyuba da Auranku nikuma ina binku a baya ba Shattima yafaÉ—a yana kallon Yarima Sultan,
Yarima Sultan yace Shine Angwan nace maka zanyi Aure ne?
A'a baka faɗamin ba saboda banida mahimmanci a gurinka, Amma naji daga Babbar Taska Majiya mai ƙarfi,
Kallon bangane abunda kake nufi ba, Sultan yayiwa, Samrat yana neman ƙarin baya ni,
ÆŠagamasa gira Samrat yayi, Eh Baka faÉ—a min ba, Mai martaba sarki ya sanar dani, Shine kuka haÉ—a baki aka samuku lokacin biki É—aya ko, Dan nakun ma yace Wata Biyu ne,
"Common Samrat, Banfahince abunda kake faÉ—a ba"
"To Meye baka fahimta ba, Komai kasani, Bikin ka mana kaida Gimbiya Sultana, Da Safwan Shiga Gimbiya Shaheedah, jiya Mai martaba ya sanar a babbar fada, Amma dai kusan kwana 4 da tsaida ranar, nima Sha'afa nayi banyi maka maganar ba sai yanzu danaji anyi wannan, Amma gaskiya Prince ku yaudare ni Ai ko a waya sai kusanar min da cewa aure zakuyi nima na shirya"
Kallon Shattima Yarima Sultan yake, Irin kallon ka zare ɗin nan, Aure kuma Gaba ɗaya Sultan ya marasa Tunanin Meye zaiyi, Ya kasa yadda gani yake tamkar a majigi, Yasan dai Samrat bazai taɓa yi masa ƙarya ba, To Amma ya akai niban saniba, cikin wannan tunanin yaji motar ta tsaya cak, Alamar Sun ƙaraso, Sulaim ne yafara fita, sai Shattima wanda ke zaune gidan gaba shima yafita, har ya fara tafiya sai ya dawo ɗan leƙawa cikin motar yayi kaɗan,
Prince lafiyar ka kuwa, ka fito mu tafi naga Tunda nayi maka maganar nan ka canza, Allah yasa ban ɓata maka rai ba,
No Shattima badamuwa kaje gani nan shigowa yanzu, Yarima Sultan yafaÉ—a. Yana gyara zaman sa acikin motar,
A fito lafiya abunda Shattima yace kenan, Ya juya shima ya nufi cikin Part É—in wanda Sulaim har ya shige,
"Barin Shattima a gurin keda wuya, Yarima Sultan ya ajeye wata nannauyar ajiyar zuci, Tare da Dannawa Ummul Bait kira,
Bayan Sun gaisa, Kamar kullum, Sultan ya Fara magana,
"Allah ya temake Ummul Bait Yarima yasamu wani baƙon labari, shin akwai abunda ke faru acikin Daular Sultan ne?
Yasamu labari kenan, Ummul Bait tafaÉ—a Cikin ranta, A fili kuma tace, Abubuwan da Suka faru bayan barin Yarima Daga Masarauta ai Suna da yawa, Kozan iya jin wanne, Yarima ke nufi?
Shiru Yarima Sultan yayi babu Amsa, duk da a waya ne bazai iya ce mata maganar Aure ba,
Yarima Na bisa layi kuwa? Ummul Bait tafaɗa daga ɗayan ɓangaran hadda Ɗan ƙunshe dariyar ta,
"Allah yaƙara miki wayan nasara Sultan nakan layi,
To shikenan nizan Sauka akwai abunda zanyi yanzu, bata jira cewar Yarima Sultan ba ta kashe wayar,
Kamar Yarima Sultan zaiyi kuka hake yake bin wayar da kallo kamar mai Son gano wani abu a ciki, Tabbas ta tabbata, Amma me yasa za'ayimin haka, Ji yaye bai yadda ba hakan yasa tunanin sa yabashi damar kodai yakira mai Martaba ko Allah zaisa shi ya faÉ—a masa abunda ke faruwa,
"Hakan kuwa a kayi, Dialling Wayar Sarki yayi, Tayita ruri ba'a ɗaga ba, Hakan yasa bai ƙara kiraba, Saboda bai san wane uziri Mai martabar yake ba, yana cikin dogon tunanin nasa sai ga kiran Sarki na shigowa, Da sauri ya ɗaga, Tamkar yana Gabansa haka ya Russuna Ciken tsantsar girmamawa yagaidashi sarki,"
Murmushin Farin cikin Jin muryar Yarima Sultan Sarki Yayi, Saida ya tambayi Baffa yana lafiya da Sulaim, Sannan yaÉ—ora da FaÉ—in,
"Yarima dama inason zankira ka kan wata magana, Nasan zuwa yanzu labari ya riskeka, To inason kafara shirin dawowa, Masarautar Gabas Don fara shirye shiryen Aure Tsakanin ka da Sultana, Tunda Kuna son Junanku Alhamdulillah, sai É—an uwanka da Safwan da Shaheedah Æ´ar gidan marigayi Galadima Abdullahi,
Yarima Sultan hi yayi gaba É—aya Duniyar tana masa Yawo a saman kan sa komai na juya masa, Yamai rasa Abunda Zaice,
Sultan kana lafiya kuwa?
Da sauri yace, eh Ranka ya daɗe, Insha Allah zan sanar da ranar dawowar tawa Allah yasaka da Alkhairin sa Allah ya jiƙan Sarki Adam Shareef,"
Ameen Summa Ameen, Mai Martaba yafaÉ—a yana kashe wayar,"
Mamaki yake sosai, Yana tunanin yaushe yace yana son Gimbiya Sultana, waye yahaɗa masa wannan tarkon da makircin, Yasan da sarki yasan baya son ta Bazai taɓa yadda asaranar nan ba, saboda yana cikin dokar masarautar gabas, Ba'a auran dole ga kowa,"
Tunanin mafita ya fara, Amma ya hanga tako ina babu, Shiru yayi yadafe kansa princess ce tafaɗo masa cikin Zuciya, Tunawa yayi, da wayar da yabata da sabon Sim a ciki sannan ya ɗau number ɗin Layin, hakanan yaji yana son, jin shirmanta, numbar ya shiga lalube, yayi Save ɗin numbar da JERRY hadda emoji na Murmushi a gefan Sunan, sai kuma yaji kamar kada yakira, kamar wanda aka zungura kawai ya Danna kira, Saidai anyi rashin sa'a wayar a kashe take, hakan yasa shi ƙara zamewa ya kwantar da kansa jikin kujerar Motar da yake kai, ya lumshe ido ya tsunduma duniyar tunani,"