← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 90

Sashe 14

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saleema da Gimbiya Sultana ƙawayene sosai, Sun haɗu a school, *(UNIVERSITY OF TORONTO)* A ƙasar Canada, acan gimbiya Sultana tayi karatun ta na degree, a gurin ƙarwar Mahaifiyar ta hajiya mai soro, saboda babu kowa a wajan ƙanwar maman nata shine su roƙi alfarma taje ta zauna musu acan har Allah yasa ta kammala degreen ta na farko acan, ita kuma Saleema dama can ne ƙasar su acan aka haife su gaba ɗaya, sosai jinin su ya haɗu saboda kusan halin su yazo ɗaya, akwai wulaƙanci ka girman kai, ita Sultana mulki ke yawo acikin jikin ta, ita kuma Saleema dukiya da gayu ga kyau, duk da itama Sultana ba baya ba, wannan shine dalilin shaƙuwar su komai tare sukeyi, har suka kammala a lokacin ne Sultana ta dawo gida Nigeria, tare da begyan juna ita da Saleema saida ko wacce tayi kuka lokacin rabuwa kamar baza su ƙara ganin juna ba har Airport saida Saleema taraka Sultana, sannan suka yiwa juna alƙawarin ziyarar junanan su lokaci zuwa lokaci," wannan itace alaƙar dake tsakanin gimbiya Sultana da kuma Saleema a taƙaice,

"Na daɗe inajiran wannan rana, naji daɗi sosai Gimbiya ta, Yarima Safwan ya ƙara she maganar tare da sakarwa Gimbiya shaheedah murmushi,"

"Martanin murmushin itama tamai da masa, Bakomai nima ina sonka saboda banfiye zama anan É—in ba shiyasa bana nuna maka hakan _But I love you_ Yarima Na,"

Sosai maganar ta ratsashi hakan yasa shi kasa mayar mata da martani,

Jin yayi shiru ne yasa tace Yaya Safwan kana lafiya dai ko?"

"Murmushi yayi sosai tare da dai dai ta nutsuwar shi, _ Nothing is wrong with me_ farin ciki ne ya hanani magana, _So I really appreciate you, and I love you so very much beautiful angel my world_"

Murmushin gefan baki ta sakar masa, cikin ranta kuma wani irin haushin sa take ji, ina ma Yarima Sultan ne ya agabana kamar haka yana faÉ—a min waÉ—an nan kalaman,

"Daga lokacin dana zama sarki a masarautar gabas za kizama uwar gida a gurin na, lokacin da naji ance wancan Sultan É—in kikeso, zuciya ta kasa jurewa tayi nashi matsanancin tashin hankali, saboda haka a yau basai gobe ba zan sanar wa da mahaifin mu mai martaba, kowa ya shaida gimbiya shaheedah ta zama ta Yarima Safwan sarkin gobe,"

Naji daɗin hakan tafaɗa tare da miƙewa, Nabar ka lafiya"

"ki huta lafiya yabata amsa a gajarce"

Tana shiga bedroom É—in ta ko zama ba tayi ba tayi dialing No. BaÉ—in Mahaifiyar ta, bugu É—aya aka É—auka,"

"Mom barka da yamma kuna lafiya ya yah Mu'azzam?"

"lafiya muke Allah yasa kema haka,

"eh Mom wlh kinsan banason wannan Safwan É—in ko? Amma yanzu saboda ke har lokaci na na bashi sai wani faÉ—amin magan ganun banza yake Mtss" taja wani dogon tsaki,

"Haba shaheedah ke miye ruwan ki ai ba dole saikin so shiba na faɗa miki, an tabbatar min da shine zai haukaragar mahaifin sa ba Sultan ba shiyasa nace ki amince masa kamar gaske, idan akayi auran muka karɓi mulki kinga sai ki rabu dashi ki aure duk wanda kike so, Emm don a halin yanzu na turo da takar da zuwa ga Sarki Yusuf Akan maganar, saboda haka koda yakira ki nasan zantambayeki shin kinason Safwan? kada ki nuna komai kawai ki amince,"
Don wlh nagaji da zaman Kano ina so nadawo masarautar mu, kina ganin shaheedah nida masarautar mu amma ankore ni nida ɗana ki tuna fa mahaifina, Allah ya jiƙansa Wanbai ne acikin masarautar nan amma akayimin haka,"

"_Oh god please Mom enough is enough_ manah ya isa kinsan banason irin maganganun nan, komai zai wuce zamu dawo da komai hannun mu, Yanzu anga Æ´ar taki ko har yanzu,"

"Ba agan taba amma ana kan bincike, dole azzalumin mahaifin ta ya dawo min da Æ´a ta saboda wlh shi ya É—auke min Æ´a tsahon shekaru nan,

" _Any way_ Mom za aganta idan ma shi ya É—auke ta dole ya dawo da ita, shiyasa tun farko nace kada ki aure wannan mutumin, amma kikace a'a komai _Normal_"
"Allah yabamu alkhairi zanyi wani abu yanzu _I will call you back_ batare da jiran abunda za tace ba ta tsinke kiran,

_____---------_____

"Nayi waya da Baffa na sanar masa muna nan tafe gobe da izinin Allah"

Kallon Yarima Sultan, Sulaim yayi, Eh ya faÉ—a min, Allah ya kaimu,"

"ameen y rabb, cewar Yarima Sultan, Idan muka fita sallar magrib, zamu wuce ziyara ko?"

Sulaim yace Ziyara zuwa ina?"

"Ɓangaran baba waziri mu gaida su ummeetha sai mu dawo sashen Ummul Bait itama mu gaisa, Hakan yayi? Emm"

"Babu laifi Allah yakaimu idan yayi maka nima _is fine_"
Ya faÉ—a tare da É—aga wayar Dr.jabir,
Magana sukai sosai Sulaim ya sanar masa yana nan dawowa gobe sannan zai shigo hospital zuwa _next day_"

To Allah ya dawo dakai lafiya, a miƙamin gaisuwa zuwa ga Sultan, cewar Dr.jabir"

"yana jinka yanzu haka"

ÆŠan É—aga murya kaÉ—an Dr.jabir yayi tare da FaÉ—in Allah ya temaki Yarima barka da yamma,

Murmushi Yarima sultan yayi saboda yasan Dr.jabir sosai, Yarima baya amsa gaisuwar waya, idan anaso aganni ina masarautar gabas,

"Tuba nake Ranka ya daÉ—e cewar Dr.jabir amin afuwa yanayin aiki ne yazo da haka amma ina nan tafe, kaina bisa gwaiwa ta,"

"to babu laifi likita bokan Turai ya aikin?" inaso a dubamin zuciya ta a wanke min ita yafaÉ—a cikin sigar wasa,"

"Dariya Dr.jabir yayi sosai, Ranka yadaÉ—e wlh nima babban likitan nakeso ya dawo yadubamin tawa zuciyar saboda ciwo take, ciwon so yakama min ita"

ÆŠil ÆŠil Sulaim ya katse kiran, jin Dr.jabir ya fara maganar So,"

Murmushin girma irin nasu na sarakai Yarima Sultan yayi, aminina Meye laifin mu da za a katse kiran muna gaisawa,

Kallon ƙasan ido Sulaim yayi masa can ƙasan maƙoshin sa ya furta _I don't know_

Shikenan yanzu dai gobe jirgin safe zamubi saboda mu isa da wuri, don kada zuciyar Dr.jabir tayi bonben, yafaɗa dariya ƙunshe abakin sa,

"PillowSulaim ya ɗauka na kujerar dayake zaune tare da jefa wa Yarima Sultan, ya mutu kafin muje ƙarewar bonben"

"Hannu yasa ya ruƙe pillown da Sulaim ya jefa masa, Haba aminina Har yanzu ba kadai na wasan yara ba, gashi kuma muna ta shirin aurar dakai, "

"Gaba É—aya annurin fuskar Sulaim saida ya É—auke, tsam ya tashi kai tsaye ya nufi bedroom, bansan lokacin daka zama haka ba, Sultan ka koyi hayaniya ga damuwa, ya faÉ—a tare da shige wa room É—in"

"Hhmm" kawai Sultan yace shima ya miƙe yanufi nashi bedroom ɗin, domin fara shirin sallar magrib,

"Auta yaushe kika fara ƙarya bansani ba, inaso kifaɗa min gaskiya kice wadda kika yiwa Yarima Sultan Zamiya ranar da yayi hawa ko?"

"Kallon ummeetha princess Salma tayi, rau rau tayi da ido alamar zata yi kuka, ummeetha nace bane bace bafa,"

"To shikenan basai kinmin kuka ba, ina zoben hannayen ki?

"Da sauri ta dubi hannun nata, take ta diriri ce abunka da wanda bai saba da ƙarya ba, em em dama cirewa nayi suna ɗaki duka..!!

_F Pen_✍️
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _Typing📲_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅
Ko

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 1�9⃣➖2�0⃣�

Dasauri princess ta kalli hannun ta, take ta diriri ce, cikin kaÉ—uwa tace, em em dama cirewa nayi suna É—aki na ajeyi duka,

"Kul kika ƙara yimin ƙarya, Ranki zai ɓaci Ummeetha tafaɗa tare da kafe princess da ido,"

Allah Ummeetha baƙar ya bane, bari na ɗakko miki kigani ma,

Oyah É—akko nagani muje ni zan jira ki a parlour atare suka fito daga masaukin ummeetha,

Princess wadda dama hanyar guduwa take nema da sauri ta tashi ta nufi bedroom É—in da aka sauke su, ita da suhailat, da Saleema, babban room ne mai É—auke da 2 bed aciki,

Bayan ta shiga É—akin zare ido tashiga yi tarasa Meye mafita ga Ummeetha na parlour tana jiran ta, Tunani tafara ko tabi ta window takoma, sashen Yarima Sultan tace yabata zoben da ta bashi,
"wani irin farin ciki ne yakamata ganin ta samo mafita, shima idan na koma kamani zaiyi Tunda É—azu nayi masa life kafin nafiito Cikin ranta tayi wannan tunanin, a fili ta furta koda idan na koma zai kashe ni ne wlh sainaje Yabani zobinana kafin ummeetha ta gane,"

" Takawa take cikin nutsuwa da yanga shigar riga da wando tayi, rigar har gwaiwa gaba ɗaya black colour sai ta yane kanta da J.C veil white colour tayi kyau sosai, hannun ta riƙe da jaka tasa takalmi mai tsini sosai shima white duk da tana da tsayi, tayi shigar black and white, ne Saboda Dr. Sulaim tasan favourite colour ɗin shine, wanda tayi tsammanin ranar zai dawo

"Dr.Jabir wanda harya buɗe murfin mota zai shiga kenan, ganin Dr.Anisha gurin sa take tunkaro wa hakan yasa shi tsayawa batare da ya shiga ba sannan bai rufe murfin motar ba ya ruƙe da hannun sa ɗaya, Tunda ta taho yakasa koda ɗauke idon sa daga kanta,"

Murmushi Dr.Anisha ta sakar masa,

"Kasa daurewa Dr.Jabir yayi take ya lumshe idon sa haɗe da dafe saitin zuciyar sa cikin ransa ya furta ya Allah kakawo min sauƙi cikin son Yarin yar nan,

Dai dai ƙarasuwar ta, ta kalleshi sosai
"Yauwa Dr. Dama inata addu'ar Allah yasa baka wuce ba gashi yamma yayi sosai, so idan babu damuwa ka ajiye ne a gida mana,"

"Oky ba matsala" abunda ya faÉ—a kenan fasa shiga mazaunin sa yayi saida yaza gaya ya buÉ—e mata harya juya daniyar komawa ya shiga, sai ya tsinci muryar ta tana tambayar shi,

"_when Dr. Sulaim will come back_ nakira wayan shi baya picking up, Allah yasa lafiya ko kayi magana dashi ne?"

"_I think tomorrow He on the way_ insha Allah, daga haka yashige mota, cikin ransa yana jinciwon shi yana wahala akanta amma ita hankalin ta nakan wani,"
Chapter 14 · 0% Book details