← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 90

Sashe 87

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Momma "_Here we are, it has been Written, All praise be to Allah After a long illness that lasted for Five days, Today Saturday DR. SULAIM HAMEED ARAB has recovered. we pray that Allah grants him Continued Good Health_" Yakai ƙarshe yana kallon Mahaifiyar tasu,
"Cikin sanyin Murya Ta furta Waye ya É—ora,
"I don't know ooo Momma babu Suna a shafin da aka wallafa Amma Tabbas Sulaim ne Tunda har Hoton sa gashi an É—ora"
"Shiru Momma tayi Tamarasa tacewa Sannan ta kasa Zama Jaridar hannun ta ta cilla saman Table Sannan ta Fara Shafa Wayar ta Fuskar ta babu Annuri,
"Da Sauri Sajad Ya ruƙo hannun Mahaifiya tasu, tare da Faɗin "Wait Momma, Meye zakiyi"
Kallon shi tayi, Zankira Baffa ne? Saboda in tabbatar,
"Sorry My Happiness, Kafin ki kirashi Dan Allah ki sauke Fushin ki, Ni inaso yanzu Zan wuce Kano,"
"Shiru tayi tana kallon É—an nata kafin tace, Yaushe?, Da Yamma nan kabari sai gobe, ko kayi Booking Flight ne?
"No no Momma Yanzu zanyi Booking Kafin na shirya ko Flight ɗin 7:pm nasamu zanbi ko na 9:pm Just inaso kawai naga Big Broo yau, kar kice, No Please yafaɗa tare da haɗe hannensa Guri ɗaya alamar roƙon,"
"Murmushi kawai tayi wanda da gani kasan iya Fuska ne, Allah ya tsare Sai munzo Abunda tace kenan"
"Awwwn Good Mommy, gaskiya U are The best one Momma u are special to me I love you" ya faÉ—a tare da manna mata Kiss a goshi, ya haura Upstairs da sauri don fara shiri, Kasan cewar sa dogo sosai Kamar Mahaifiyar tasu, Dagani ko ba'a faÉ—a ba kasan Jinin Baffa ne,

Bin Bayan Sa da kallon Momma tayi Tana, Murmushi, tanajin soyayyar É—an nata har cikin ranta, Kamar yadda yake son ta Tabbata Sajad bai haÉ—a son ta da kowa ba, Haka itama Æ´ar uwar sa shukra,
Duban ta ta mai da saman wayar Hannun ta, Number ɗin baffa Tashiga kira wanda batada yaƙinin za a ɗaga don shi idan bai san da kiran kaba to ba lallai ka same shiba,
Can ƙasan zuciyar ta tana jin zafin Ace ɗan yayan ta Abin so a gurin ta, bashida lafiya har na tsawon kwana biyar Amma akasa gaya mata, Take zuciyar ta ta ƙara sama, Tana da zuciya Sosai ga saurin Fushi tsaye take akan komai jajirtacciyar mace tamkar namiji, har cikin zuciyar ta take jin, da ace wani ne yayi rashin lafiya ba'a sanar mata ba to Baza ta ne me kowa ba, amma Kash sai akayi rashin sa'a Masoyin ɗan tane wato Sulaim baza ta iya Sharewa ba,
Sau biyu Tana kiran Baffa amma ba'a ɗagawa har ta haƙura ta ajiye wayar, Ta zauna saman Sopar saiga kiran Baffa yana shigowa, Da sauri ta ɗaga tare da kara wayar a kunne,
"Assalamu'alaikum, Amincin Allah Ya tabbata ga mahaifi na, Allah yasa kuna lafiya,
"Ta ɗayan ɓangaran Baffa ya Amsa da faɗin, Albarkar Allah ya tabbata a gurin ƴa ta da Iyalan ta, Muna lafiya Allah yasa kuma haka,"
"Alhamdulillah Muna lafiya, Baffa Barka da Yamma"
"Murmushi Baffa yayi kafin yace Barka Bahijja, Faɗamin Meya faru waya ta ɓaki?
"Sai lokacin Momma ta sauke Nannauyar ajiyar zuciya wadda saida ta tafi da rabi da kwata na ɓacin ran ta, Baffa Ya jikin Sulaim?
"A karo na biyu Baffa ya ƙara sakin Murmushi, Don Tunda yaji tayi ajiyar zuciya yasan ta Sakko, saboda Sanin Halin ta Tsaf da yayi, Jikin ɗanki da sauƙi, ba a sanar miki ba Shine Na Fushin ko?

Cikin Harshen su ta cigaba da magana,

"Baffa Sulaim bashida lafiya na tsawon kwana Biyar Amma ban sani ba, kun cire ni daga cikin kune? Amin afuwa idan nayi Kuskure,
Shima cikin Harshen yabata Amsa,

"Biki laifin komai ba, Nasan idan kuka ji dole zakuzo Shiyasa na hana asanar wa kowa, Gashi Jamila har tazo bansan ina tasamu labari ba"
"Nagode da fahimta ta Daku kai Baffa Allah ya ƙara lafiya da imani, Muma muna nan tafe Jibi, Da gobe zamu taho to Major ya ɗakko Mahaifiyar Sa, kuma har yanzu Bamu samu fahimtar juna ba amma dai, Komai zai wuce insha Allah,
"Baffa yayi ɗan Jim kafin yace, ki kwantar da hankalinki, Kisamu fahimtar juna keda Sirikar ki kibi komai a sannu A wannan karon zakiyi nasara insha Allah, Addu'ar mu na tare daku baki ɗaya, Ki haƙura da zuwa Tunda nan da wani ɗan lokaci Za a ɗaura musu aure, Sai kuzo,
"To Baffa yadda kuka ce haka za'ayi, Allah ya kaimu Bikin sai mu taho baki É—aya, Amma Sajad Yana nan tafe yanzu haka yana shiri,
"Dariya baffa Yayi, kice sarkin Wasa zaizo ya dame ni, To Allah ya kawo shi lafiya, Allah kuma yayi muku Albarka,
"Itama murmushi tayi, tace Ameen Summa Ameen Kuhuta lafiya, Zankira É—ana Naduba shi"
"To Allah ya bada iko Baffa ya faɗa tare da ajiye waya, Yana Farin cikin jin ƴar tashi Tasaki ranta, Saboda yafi kowa Sanin Bahijjan Tun tana Ƙarama Akwai Rigima, Zuciya ga saurin Fushi Kaf ciki ƴan uwan ta Ba wanda ya isa ya taka ta Saboda tafiso zafin rai, duk rashin mutuncin Anty Jamila bata yi mata, Don tasan ba kyau idan kuwa Laifi akayi Har tsoron faɗa mata ake, Shiyasa hatta ƴaƴan ta suke Shakkar ta idan suka ganta cikin Fushi,

~ Sulaim ~

Wanka yayi Acikin toilet ɗin Baffa, Bayan ya fito, Sai da ya Murza Mayu ka kusan Kala Biyar A fatar shi, Sannan Ya fisa Perfumes a ƙalla sunkai ƙala huɗu Yahaɗa da Oud, Kayan da Yarima Sultan ya ɗakko masa Yasa, Shadda ce ƴar uban su Fara Tass, rigar ta ɗan haura gwaiwar sa kaɗan, Yayi kyau cikin Shigar Da kakkiyar Shaddar Sai faman ƙalli take Hular da yasa anyi Amfani Da baƙin Zare wajan yin ta, Gashi ya ɗaura Agogo A wrist ɗin Sa shima jikin sa Black Takalma ya zura Masu rufaffen Sama, Amma ya tsun ƙafar sun bayyana do gaye Farare Sai ƙafar ta Haska sosai acikin Black Shoe ɗin, Yayi shigar Favourite Colour ɗin Shi, Hannu yasa ya shafa, siririn Sajan Fuskar shi Wanda ya zagaye Fuskar Cikin wani irin Salo mai kyau da Ɗaukar hankali gashi Baƙi Wulik, Kwantacciyar Sumar kanshi wadda ta sakko har saman dogon wuyan sa itama sai ƙalli take tasha gara da mayuka Duk da yasa Hula Amma hakan bai hana ta bayyana daga bayan sa ba saboda ta sauka,

Cikin Nutsuwar sa Ya taka zuwa Babban Parlourn Baffa Inda kowa ke zaune, shi ake jira, A lokacin har Su ummeetha sun Dawo daga Asibiti wajan Saleema Wadda Tunda taji labarin Sulaim ya farfaɗo itama ta miƙe, daƙar aka samu Tabari ruwan da akasa mata ya ƙare, yana ƙarewa aka sallame ta suka yo gida,
A hankali yakai Duban sa cikin Parlourn Idanuwan sa, Ya tsayar Guri É—aya cak,
Ganin yayi tsaye bashi da niyar zama ko magana, hakan yasa Baffa kallon sa Ganin ya zubawa window ido hakan yasa baffa meƙewa don ganin Meye Sulaim ɗin ya shagala da kallo haka,
Suhaima Suhaima ce, kallon ta yake ko motsa kwayar idon sa ba yayi, Itako tsaye take tana ta faman Kallon wata pink Flower Wadda tayi Wasu Korayen Furanni Masu kyau hakan ya ɗau hankalin ta har ta tsaya tana zubawa Flower ɗin Bottle water ɗin hannun ta a hankali tana murmushi Kamar bata da wata damuwa, Duk da Fuskar ta a rufe take Hakan bai hana Sulaim kallon ta sosai ba, Murmushi Baffa yayi ya ƙara duban ta wadda ita bata masan Suna yi ba,

Kama Hannun Sulaim baffa yayi, Da sauri a É—an razane Sulaim É—in ya dube shi, Tare da FaÉ—in "Baffa na Barka da Yamma"
"Barka Sulaim zauna ko" Baffa ya faÉ—a yana nuna masa Kujerar kusa da tashi,
Zama Sulaim yayi yana bin kowa da kallo, Duk wani masoyin Sulaim Zuciyar sa ƙal take da Farin cikin ganin Sulaim ɗin saman ƙafa fuwan sa, Ga wani irin kyau da ya ƙara daka ganshi zaka gane kwanciyar hankalin dake saman Fuskar shi ba irin ta baya bace,
Jam'u Sulaim yayi wajan gaida iyayen nasa Fuskar shi baya bo ba fallasa,
Saida kowa yayi masa ya jiki, Hadda baƙi acikin mutanan dake zazzune cikin Babban Parlourn, Mahaifin Dr. Jabir Wato Alhaji Idris Aminin Baffa shima yazo, Ga su Dr. Anisha, Hadda ɗan gidan gwamna Abokin Sulaim ne sosai Amma shi da muƙarraban sa Suna part ɗin Sulaim ɗin zai same su acan, Daga masarautar Gabas Ƙanan Yarima Sultan Twins Suma sun zo, Tasleem da Tasleema, Sannan baba Waziri Amma shi har Yakoma, Sosai Arab Estate ta karɓi baƙuncin Manya manyan mutane ɓaki Daga ɓangarori daban daban Wasu basu ma samu ganin Sulaim ɗin ba, Kiran waya kuwa hadda ga, _UNITED STATE_ Birnin _Las Vegas_ Abokan Aikin Sulaim Da waɗan da Sukai karatu tare a Babbar Jami'ar, _HARVARD UNIVERSITY (Massachusetts)_ America🇺🇸
Abun Har ya dai na bawa Sulaim mamaki ya koma bashi tsoro, Shidai ya rasa bakin Magana ya rasa wanda zai tambaya Wace irin rashin lafiya yayi Bai sani ba, Har ya gaji da amsa kira, duba saƙonni kuwa baya ma bi ta kansu, Shima kanshi yaga An wallafa Samun lafiyar shi a twitter Amma bai san Waye ba,
Sai da akayi kwarya kwaryar Walima Sosai a kaci aka sha, Duk Sulaim na Zaune Amma baisa ko ruwa a bakin sa ba, Gab da Magrib Suka Tashi bayan Baffa yayi Wasu jawabai Da jan hankali Da Nuna Farin cikin Sa na FarfaÉ—owar Sulaim,
Kai tsaye Sulaim, Yarima Sultan, Shattima Suka Wuce Part ɗin Sulaim ɗin don gaisawa da wasu baƙin, Kafin su wuce Masjid Inda yaga Suhaima ɗazun Nan yake tafan bi da kallo Amma babu Alamar ta,
Chapter 87 · 0% Book details