← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 90

Sashe 30

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin ƙasaita Samrat yayi, Ta temaki kanta, yafaɗa tare da kiƙewa cikin isa da nuna Mulki, da'alama Salon mulkin su ɗaya da Sultan, Tamkar Yarima Sultan haka yake komai, Taku yake cikin isa da izza, yayi Shigar Riga da wando na Shadda ruwan ƙasa mai haske wanda akayi mata aikin Da zare Shima ruwan ƙasa amma me duhu, Rigar ta ɗan haura gwaiwar shi kaɗan akwai tsaga faga ko wane gefe na rigar irin aikin sarakai wanda shima anyi masa aiki siriri daga ƙasan shi, Samrat Kyakkyawan matashi ne mai jini ajika tauraron a gurin ƴan mata, Abun so ga kowa, farin jini ne dashi Sosai duk inda ya shiga sai ankalleshi saboda Aji da Mulki ga kyau ga sarauta kuɗi kwa ba'a magana, Shine ɗa ɗaya tilo a gurin Mahaifiyar sa, Wato Kilishi Aziza ƙanwar Sarki Yusuf Mahaifin Yarima Sultan, Samrat ɗan gata ne gaba da baya, Ɗan so ne Duk da yanada ƴan uba amma Shine nagaban goshi, Mahaifin sa Shine Sarkin *GOBIR* dake cikin garin Sakkwato, Samrat Shine ɗana na biyu A gurin mahaifin sa, Hakan Yasa Ake kiran sa Da Shattima, Samrat akwai izza amma bashida wulaƙanci, ga saurin sabo Saidai baya Ɗaukar raini akwai son girma, Ga shida farin jinin ƴan mata, Shiyasa baka raba shi da Waya kullum cikin Waya yake,"

*_Wannan kenan_*

*Suhaima*
Tsawon kwana Uku kenan haryanzu Bata dawo dai dai ba, Kullum cikin Tunanin yadda zata bulluwa lamarin Estate ɗin take, Gashi duk yadda taso ta manta da Sulaim acikin ranta ta kasa, Abunda ke damun sa ne kawai ke faɗo mata, sai taji Gaba ɗaya ta rasa sukuni, Tabbas Cikin Ranta Takejin baza ta iya barin Sulaim cikin halin da yake ciki ba, Har ga Allah tasan bata son Koda haɗa inuwa da Sulaim bata Sonshi bata son Ganin sa kamar yadda shima anashi ɓan garan haka, Amma idan ta tuna alkhairi da yayi musu A asibiti sai taji itama tana son saka masa da wannan alkhairin, Bawai don yaji daɗi ba sai don tana Saka alkhairi ga wanda yayi mata koda bai sani ba, sannan tana rama zalunci ko mugunta ga wanda yayi mata matuƙar taji bazata iya yafe wa ba,
Idan nace zan temaka masa shin ta ina mazan fara? Ta tambayi kanta, yau tsawon kwana uku bangan shiba dole idon inason Temaka masa To saida haÉ—in kansa, Maganar Mother ce tafaÉ—o mata cikin rai, _Suhaima ban turo ku don ku temakawa kowa ba kusani fansa ce kusani fansar muce_,
Ya Rabbi Suhaima tafaɗa A fili tare da dafe kanta, Ganin ta kasa samun wata mafita ne yasa ta miƙewa ta nufi Part ɗin Sulaim Tunawa da tayi gaba ɗaya Duk yau bata shiga sashen nasa ba",

Fitowar Sulaim, Yana sauri Saboda Yarima Sultan da Shattima Suna Kiran Sa a mota zasu fita, Yana sako kai Suhaima na kawo kai itama a dai dai ƙofar Shiga parlourn,

Karaf Suka haɗa ido, Da sauri Suhaima tayi ƙasa danata Idon, can ƙasan maƙoshin ta ta Furta,
"Barka da Yamma"

Batare da Sulaim yace komai ba yara ɓata ya wuce, Cikin Zuciyar sa ya Furta, Kodai Mayya ce Yarin yar nan" Bazata daina zuwar min part ba, Dole Baffa yasan Yadda zaiyi da ita, da wannan tunanin aka buɗe masa Mota Ya shiga,"

Suhaima har cikin ranta taji babu daɗin Abunda yayi mata, Amma Saita share, Lokaci na farko da Suhaima tayi wa Sulaim Uziri, gane take duk abunda yakeyi, Rashin lafiyar sace Sanadi, Wannan dalilin ne yasa ta Shanye wannan wulaƙanci,"
"Aikin take hankali kwance tagama komai kamar yadda ta saba Hatta abinci gaba ɗaya ta kammala, Wanda yanzu itace Mai kula da Abincin Sulaim Tunda hajiya Umma ta bata Umarnin Yimasa Girki Kullum, Ayyuka sunyi mata yawa amma Ahaka take ƙoƙarin ganin tagama komai, Sauri sauri take wajan jira Abinci A Dinning, Saboda yau tana son zuwa tsohon Part ɗin Sulaim, na House ɗin Alhaji Hameed (Abiiy),

Bayan ta kammala a tsakiyar parlour, Ta samu Princess tana ƙoƙarin zama a kujera da'alama shigowar ta kenan,
Murmushi Princess ta sakarwa Suhaima, Laaa Mai Rufaffiyar Fuska, Ya kike? Nazo inata sallama, nazaci Babu kowa anan,"

Suhaima itama Martanin murmushi ta maidawa Princess, duk da bata ganin Fuskarta,
Ina lafiya Salma, ya kema ya kike, baza kidaina cemin mai Rufaffiyar Fuska ba ko nafaÉ—a miki suna na Suhaima,"

Princess, Gaskiya idan biki buÉ—emin Fuskarki nagani ba, Bazan daina faÉ—a ba, ace kullum mutum fuskar shi a rufe,
Idan kaga yadda Suhaima da Princess suke, Saikayi tsammanin sun daÉ—e da sanin juna, Kamar ba shekaran jiya suka fara haÉ—uwa ba,"

Mai Rufaffiyar Fuska, Yaya Sulaim baya nan ne,? Gurin sa nazo..!!!

_F Pen_✍️
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS ......✨�*
*_T.M.W_✍️*

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 3️⃣9️⃣�4️⃣0️⃣📖

*Princess*
Mai Rufaffiyar Fuska, Yaya Sulaim Baya nan ne? Gurin sa nazo, Tayi Tambayar tana kallon Suhaima"

ÆŠan jin Suhaima tayi, har tabuÉ—e baki zatace yafita sai kuma Tace, Bansani ba Amma dai nima ban ganshi ba Tunda nazo,

Oky badamuwa, Muma dawowar mu kenan Muka Sauka a part É—in Grandad shine nazo nagai dashi,

Ganin Princess ta sake Sosai da ita, Yasa Suhaima, tabbatar wa kan Princess batada matsala, Jitayi tana son Tambayar ta princess É—in Wasu abubuwan game da Estate É—in,
Batare da wani Dogon tunani ba, Suhaima ta dubi Inda Princess ki zaune, Tace Yauwa Salma, zan iya tambayar ki dan Allah idan babu damuwa?"

Princess wadda ke ƙoƙarin meƙewa da niyar tafiya, Jin abunda Suhaima tace, yasa ta Sakin Murmushi ta koma ta zauna, laaa Bakomai ki tambayi duk abunda kike son ji, idan nasan amsar zan faɗa miki"

"Sosai Suhaima taji daÉ—in, Maganar da princess tayi, Yauwa nagode Amma Muje waje Cikin Harabar Part É—in Nan sai muyi maganar"

Hakan yayi, don Wallahi idan Yaya Sulaim yazo ya gammu a parlourn sa, mun Banu, Princess tafaɗa dai dai Suna Fita daga parlourn hannun ta ruƙe da wata ƴar madaidaicir jaka ta Kwali An rubuta *DOLLARS KITCHEN* sai akayi zanan fork da Shawarma Ajikin Jakar,

Kindai Banu, Ke kaÉ—ai Donni Bai siyasa yamin komaiba, Suhaima tafaÉ—a cikin ranta, Kujerun kaba ne a gurin wanda akayi su cikin wani Salo mai kyau dake Cikin Harabar Part É—in daga gefe kaÉ—an , Gurin Tamkar garden, Saboda yanayin Sa, Amma ba garden bane gurin hutawa ne da shan coffee kamar yadda aka rubutu daga jikin wani É—an Allo,

Tunkafin Suhaima ta Zauna Idon ta ya hango mata Khaltum Na Nufo Part É—in, Saboda daga inda Suke Ana iya ganin komai duk da an zagaye Gurin da Glass,
Zaman Da Suhaima batayiba kenan Tana jiran zuwan Khaltum, ta tsaya atsaye ne yadda Khaltum É—in zata fi gano ta,

Lafiya dai? ki zauna mana princess tafaÉ—a tana kallon Suhaima,
Lafiya yanzu zan zauna, Ganan Æ´ar Uwata ta taho So nake ta ganni,
Princess tace, Ayya dama kinada Sister anan?
Eh ina da ita, Suhaima tabbata amsa a gajar ce,
Cikin nutsuwa Khaltum taƙarasu inda Suke Tunda ta taho Suhaima take kallon ta Tunda ga sama har ƙasa Saboda Tsabar mamakin ganin Khaltum da kayan da batasan ta dasu ba, Sabuwar Arabian Gown ce Ajikin ta Red colour ƙirar Dubai rigar Ta haɗu Sosai Ta ɗaure zaran Rigar Zuwa bayan ta, gashi rigar ta amshi jikin Khaltum ɗin Kasan cewar tana da ɗan garin jiki, Sannan tayane kanta da mayafin Rigar wanda bawani girma ne dashiba"

Da wannan mamaki Suhaima tasamu Guri ta zauna, Cikin Ranta tama rasa tunanin da zatayi, Na inda Khaltum ta samu wannan rigar, wadda tasan ko ba'a faÉ—a mataba mai tsada ce,

Babu ko alamar Wani abu A fuskar Khaltum, itama ta zauna, Murmushi Ta sakarwa Suhaima, Ganin princess yasa ta yin mamaki, Masha Allah Ina Suhaima ta samu wannan kyakkyawar, Ashe itama tafara shigewa cikin ƴan gidan shine ni zata hanani, gara da Allah yanuna min, dama itace matsala ta, waya sanima ko itama tayi Saurayi Acikin ƴan gidan, Uhm taya zatayi wani saurayi kullum fuska a rufe, wani ɓangaran na zuciyar Khaltum yabata Amsa,"
Da Sauri Khaltum ta miƙawa princess hannu Da Nufin Su gaisa, Sai a lokacin princess ta kalle ta sosai, Tare da ɗauke kai gefe,
Barka da Zuwa, Abunda princess É—in tafaÉ—a kenan Tare dayin murmushin gefan baki kamar na dole, gaba É—aya taji Khaltum É—in bata yimata ba Sam," haÉ—uwar jini ce ita kuma sam jinin su bai haÉ—uba

Suhaima ta lura da hakan, Amma sai ta share suka gaisa da Khaltum É—in sosai, Tare da nunawa junan su kulawa na rashin ganin juna a kwana biyun,
"Princess Ga Khaltum, Ita ce Æ´ar uwata a gaba É—aya duniyar nan,"

"Khaltum kema ga Princess Salma, Tanada kirki sosai,"

Ƙara washewa baki Khaltum tayi, Saboda ita dai a rayuwar ta tana son taga kyakkyawan mutum, bama ace tasan shi, tofa kobe kulataba ita saita kula shi, Bare wannan da take ganin ta kamar a Indian film Mamaki, matake da taga sunajin hausa,
" Sannu Princess Ya kike Khaltum tafaÉ—a tana kallon ta"

Princess Tace lafiya fatan kema haka, bata jira cewar Khaltum ba
Tafara Fito da Shawarma daga cikin wannan ƴar jakar kwalin Wadda aka Rubuta Dallors Kichen, Guda Uku ce Shawarmar Acikin wata farar takarda kamar tissueee park, saida tafara miƙawa Suhaima Sannan tabawa Khaltum duk da itace mafi kusa da ita,

Bayan Suhaima ta karɓa saida ta jujjuya ta A hannun ta Sannan tace, Nagode

"Murmushi Princess tayi, tace Haba kinada yawan godiya kamar Anyi wani abu,
Yanzu ki tambayeni abunda kike son Tambaya kafin na tafi, Saboda inason komawa House É—in mu Before Magrib,

Nima Nagode Princess, Khaltum ce tafaÉ—a, Saida Fuskar Salma ta canza Saboda bata son A katse mata magana,

Khaltum Meye haka? Suhaima tafaÉ—a tanaÉ—an zaro ido waje,

Cikin Rashin Sanin Abunda tayi, Tacewa Suhaima Mekika gani?
Chapter 30 · 0% Book details