← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 90

Sashe 84

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da hannu Princess ta nunawa Suhaima Part É—in Baffa, Zanje na ganshi kafin Su tafi,
"To muje Nima na duba shi Suhaima tafaɗa Harcikin ranta tana Tsammanin baza abarta tagan shi ba, Saboda taga Motoci sunfi Ashirin A gurin da'alama hadda baƙi aciki, Addu'a Suhaima tashiga yi Allah yasa Babu Mutane Huɗu a gurin,
"Sai da aka sanarwa Baffa Zuwan su, yabada umarnin Su shigo A Central parlour Suka sameshi, Daga Shi Sai abiyy Sauran duk Sun Fita Suntafi, Uncle Yusuf da Uncle A wanda a daran jiya ya sauka a Ƙasar, Da Daddyn Canada tare dasu Za'a tafi, Ƙasa mai tsarki, MADINATUL MUNAWWARA,
Ganin Suhaima Yasa Baffa sakin Murmushin Ƙarfin Hali wanda ko ba a faɗa maka ba kasan Yaƙeni, Shima ya rasa me yasa duk lokacin da zai ga Suhaima sai yaji Wani irin Farin ciki Aran sa, Kanta a ƙasa cikin girmamawa ta gaida baffa Ganin shi haka yasa taji ta ƙara rasa gaba ɗaya wal'walar ta Tausayin Dattijon ne yakama ta, shima kanshi Sai yanzu ta tuna rabon da tagan shi ankusa sati,
"Baffa dan Allah idan kun Bamu izini muna son mu duba Ya Sulaim kafin ku wuce, wannan itace mai kula da shahen part É—in sa itama tana son duba jikin nashi, princess ce ke maganar Saboda tsabar kuka muryar ta gaba É—aya ta dashe,

"Sosai Tausayin Princess yakama Baffa yasan ko ba a faÉ—a ba Sulaim abun sone ga kowa,
Jin Baffa yayi shiru ne yasa Princess tunanin Bazai bar suba, kodan yaga Fuskar Suhaima a rufe, Hakan yasa ta É—an matsawa Saitin kunnan Suhaima tace,
"Suhaima ki buÉ—e fuskar ki, idan ba haka ba bazai bar mu ba, kafin Suhaima tace wani abu suka tsinci muryar baffa na FaÉ—in,
"To Autar Maman ta Kutashi Muje ko,
Cikin jin daɗi da zumuɗi Princess tamiƙe Suhaima ma ta tashi suka bi bayan Baffa Har cikin Bedroom ɗin sa,

"Mamaki ne yakama abiiy Yana mamakin Wace wannan, Fuskar ta a rufe Kuma baffa Ya sake da ita haka Harcikin Bedroom ɗin sa, kawai dan ta kasan ce mai aikin Sulaim, Gashi Fuskar ta a rufe, Kai Tabbas akwai wani abu a ƙasa, Abiiy yafaɗa cikin Ransa Saboda shi bai taɓa ganin Suhaima ba sai yau,"

"Yarima Sultan, Samrat, Dr. Jabir Wanda basu daɗe da zuwa ba shida Dr. Anisha sunzu ƙara duba jikin Sulaim, Suhailat, Uncle Shaddad, gaba ɗayan su suna cikin bedroom ɗin baffa babu mai cewa ɗan uwan sa Ƙala, kowa tunanin da yake daban, daka kalli Fuskokin su zaga, tsantsar Tausayin Sulaim a tare da su bama kamar amininsa da gaba ɗaya ya zabure, baya cikin nutsuwar sa,

Jin Sallamar Baffa ne yasa gaba ɗaya suka maida hankalin su baki ƙofar shigowa, Dayake Bedroom ɗin Mai girman gaske ni Baza kace mutane ciki suna da ɗan yawa ba saboda tsabar girman Room ɗin Bayan tangamemen Bed Hadda Sait na kujeru, Kowa yana zaune a gurin sa,
Ganin Princess bai basu mamaki ba, Amma ita É—ayar wace? Abunda ke yawo acikin zuciyoyin su kenan,
Gaba ɗaya Suhaima saida ta tsargu jin idanuwan mutane nayi mata yawo ajiki, ganin ta tsaya ne hakan yasa Baffa Faɗin ƙarasu mana ƴa ta, A hankali Yarima Sultan ya ɗaga kai yana kallon Suhaima yaji wani irin DAM-DAM A ƙirjin sa har sai da ya dafe Saitin zuciyar sa, yana ambaton sunan Allah,

Suhaima kanta a ƙasa ko idon ta ta ƙibasu damar gani gashi gaba ɗaya ita suke kallo, A bakin Gadon da Sulaim ke kwance Suka tsaya, Sai a lokacin ta ɗaga idon ta ta sauke akan Sulaim Taɗau tsawon lokaci tana kallon sa kafin, Ta Tace Allah ya bashi lafiya,
Ameen Baffa ya amsa, Princess ma addu'oi tayi wa ɗan uwan nata sanan taka baya, A hankali Suhaima takai du banta, kan mutanan Room ɗin ganin Sun maida hankalin su kan wani abun yasa, Suhaima ƙara fakar idon kowa ta matsa Saitin Sulaim sosai ta gefe, Wani abu ta furta asaitin kunnan sa na dama Cikin sauri A hankali kuma wanda koda a kusa da ita kake baza ka iya jiba,

Abun mamaki da Al'ajabi, Sulaim ya saki wani irin Ƙaya taccan Murmushin gefan baki wanda har saida Kyawawan haƙoran sa suka bayyana, Sannu a hankali yafara ware Idanuwan sa Cikin Na Suhaima..!!!

_F pen_✍️.
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS...✨�*

*_T.M.W_*✍️

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

*_TEAM FIVE STARS💫_*

*TAURARI BIYAR*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 4️⃣7⃣➖4️⃣8⃣�

Abun Mamaki da Al'ajabi, Sulaim Yasaki Wani irin Ƙayataccan Murmushin, Gefan baki Har saida kyawawa Kuma fararan Haƙoran sa Suka Bayya na, Sannu a hankali ya fara Ware idanuwan sa cikin na Suhaima,"

Saboda Tsabar Mamaki, Saida Baffa Ya zare Farin Glass É—in Idon Sa, Yana Zaro Su waje kaÉ—an, "Azza'Wajalla Baffa yafaÉ—a Cikin Mamaki, Kaf Cikin ÆŠakin shi kaÉ—ai ne ya Kula da abunda Suhaima tayi Da kuma, Murmushin da Sulaim yayi Gashi Yanzu ya buÉ—e ido,
A hankali Baffa ya taka zuwa Gaban Gadon Sosai, Wanda Har wannan lokacin idon Sulaim na cikin na Suhaima, Duka su biyun Kallon Juna Suke Kamar Masu Son gano wani abu a tsakanin su, Lokaci É—aya Murmushin Saman Fuskar Sulaim ya É—auke, Amma Bai bar Kallon Suhaima ba,

"Sulaim Baffa ya Furta A hankali,"
Sulaim aka Ambata Amma Saidai kowa dake Cikin Bedroom É—in Ya dawo da kallon Sa Gurin Baffa, Wanda yayi dai dai Daganin Idanuwan Sulaim a buÉ—e, Ganin Hankalin kowa ya dawo gurin Hakan yasa Suhaima zare jiki A hankali taja baya Kafin ta silale daga ÆŠakin,

Yarima Sultan, Ba'a hankali yake tafiya ba, Sannan babu Hanzari acikin yadda yake Takun nasa, Baza ka iya tantance a wane hali yake ciki ba, Saida ya ƙarasa bakin Bed ɗin da Sulaim ke kwance, Fuskar shi ɗauke da Bayya nannan Mamaki, Yarasa Meye zaiyi Farin ciki ko Tambayar Yadda akayi Aminin sa ya Buɗe ido, Sosai ya rungume Sulaim dake kwance Yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, Shima Sulaim ɗin ƙara Rungumo shi jikin sa yayi,
Cikin Nutsuwa Yarima Sultan ya zare jikin shi, daga na Sulaim dan ƙara kallon Fuskar shi, Ya tabbatar hakanne ko kuwa gezo idanuwan sa keyi masa,

Kowa ya kasa magana gaba É—aya su zagaye bed É—in wasu na Murmushi wasu na hawayen farin ciki,

Ganin Basuda Niyar magana Hakan yasa Sulaim tashi Zaune yajin gina Bayan sa Jikin Fuskar Gadon, kamar bashi ba Kallon Yarima Sultan yayi Wanda shi kaÉ—ai ne Zaune kusa dashi,
"Saraki Lafiya? Sulaim ya tambaya Fuskar shi É—auke da Annurin da Abaya babu,
Kamar ƙaramin yaro Yarima Sultan yakama hannun Sulaim tare da Faɗin. "Aminina shine kayi dogon Bacci ko Barka da tashi Ya jikin naka Ina fatan baza ka ƙara irin wannan Baccin ba"
"Sosai Sulaim yayi Murmushi, "Easy Man, Bacci Kuma Kana so kayimin Sharri ko, Baffa kana jin fa, Sulaim yakai ƙarshan maganar yana kallon Baffa,
Baffa ya kasa Magana Yara sama mezai yi don Farin ciki Gashi yaga Sulaim ya tashi da wani irin Canji Kamar bashi ba,
"Ya Rabb Kallon Meye kuke min? Sulaim ya ƙara magana Yana kallo Su Princess dake Tsaye Suna Hawayen Farin ciki, Jin sunyi Shiru babu Amsa, Sulaim yace lafiya dai? Kukan Meye kike Yana faɗar haka idon sa ya sauka Akan Suhailat itama tana Matsar kwalla,
ÆŠan zaro ido Sulaim yayi Tare da FaÉ—in, "Ya Salam, kuzo kaina kuna kuka Wane abu ya faru ne, Yaushe nafara wasa daku? Cikin Harshen Su yayi maganar" tare da É—aure fuska kaÉ—an,

Baffa Ganin Zasu da gulawa Shalelen nasa Zuciya, Yasa shi faÉ—i, Tunda kungan shi kuma ya Farka zaku iya tafiya,
Da sauri Princess tace "Allah nayi Shiru"

Sai da kowa ya É—an murmusa, banda Sulaim da Aminin sa,
Kallon ta Sulaim yayi tare da Faɗin zonan, Babu tunanin komai a zuciyar princess ta taka zuwa Bakin Bed ɗin, DUK da a tsaye take hakan bai hana Sulaim kai hannun Saman kanta ba yayi mata Wani kyakkyawan Ranƙoshi A tsakiyar ka, Wanda yasa saida ta ɗan durƙushe Tare da Faɗin wash, Kafin tamiƙe Yarima Sultan ya ƙara mata Wani Ranƙoshin A saitin inda Sulaim yayi mata, "Wayyo Allah Ummeetha Sun kashe..... Kallon da Sultan ya watsa mata ne yasa ta saurin haɗeye kukan ta,

"Dariya Sosai Dr. Anisha tayi, Cikin dariyar tace, Sannu Dr Lallai jiki yasamu Allah ya ƙara Lafiya, Gashi har zaku kashewa Autar Ummeetha kai,"

"Sulaim yace, Dr. Ya aikin?
"Aiki Ba daÉ—i Kuma ba'a bari Alhmdllh"
Dr. Jabir Yana murmushi, Yace Sannu Dr. Ya jikin ka?
"Sannu kuma Nida ba noma Kaga inayi ba Sannun Meye za kaimin, Sannan Waye yace maka bani da lafiya? Sulaim ya faÉ—a yana kallon DR.Jabir,
Dariya Dr. Jabir yayi kafin yace Allah ya huci zuciyar ka,

Samrat,"Man Gaskiya Ka ruɗani ka rikitamin tunani nifa Tunda nake Ban taɓa ganin, Abun Al'ajabi irin wannan ba, Rashin lafiya Lokaci ɗaya, Kuma Har After 5days Mutum Na Bacci, shi ba mutuwa yayi ba ba kuma Suma yayi ba, irin A'amarin nan ko a film ban taɓa gani ba, It Shocked me and Frightened me."

Yarima Sultan yace Shattima, da ɗan ƙarfi Kallon sa kawai Samrat yayi tare da yin shiru da'alama ya gane abunda Sultan ɗin ke nufi,

Suhaima kuwa Bayan Tabar Bedroom É—in batare da kowa ya kulaba, Baffa ne kaÉ—ai Yaga Lokacin da tafita, A parlour ta ga abiiy zaune inda Yake, Saida A wannan karon waya yake, Sai lokacin tasamu damar kallon shi sosai batare da ya kula da hakan ba, Sosai Suhaima taga Kamannin sa da Sulaim, saidai kawai Abiiy yafi kama da Hajiya Umma, Ya É—akko Kamar Buzaye Sosai,"
Chapter 84 · 0% Book details