← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 90

Sashe 50

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Galadima murtala ya ƙara tsanar ɗan uwan masa Yusuf amma dai baya nunawa a fili kullum ƙarashiga jikin sa yake domin son samun ma Kasar sa, amma ya kasa bashida burin da yawuce ganin babu ɗan uwan nasa a doron duniya gaba ɗaya,
Shikuma sai ya maye gurbin sa idan bai samu dama ba dole yaÉ—ora É—an sa wato mudassir yaya ga sultana.!!!

*_F pen's_*
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _Typing📲_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALIN MU ÆŠAYA_*

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

*_Fatima Y zakariyya👌_*
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 7️⃣�8️⃣📖

Sosai Galadima Murtala ya ƙara tsanar ɗan uwan nasa Sarki Yusuf, amma saboda tsabar makirci baya taɓa nunawa a fili, kullum ƙarashiga jikin sa yake domin yasamu ma Kasar sa, amma Allah bai bashi dama ba har zuwa wannan lokacin, bashida burin da yawuce, yaga babu ɗan uwan nasa a doran duniya gaba ɗaya,
Daga nan kuma sai ya maye gurbinsa na sarki, idan hakan bai samu ba, yaɗaukar wa kansa alwashin dole yaɗora ɗan sa mudassir, duk da a lokacin mudassir ɗin ƙaramine,

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Sosai bahijjah (Ummul Bait) tasamu karɓuwa daga wani ɓangare na mutanan masarautar saboda batashiga harkar kowa tsakanin ta da mutane kyautata wace sai girmama juna, shiyasa wasu keson ta bata da wulaƙanci Sam duk da irin matsayin da take dashi acikin masarautar gabas,
Duk da tana fuskantar ƙalubale dayawa daga ɓangaran Facalolin ta da kuma kishiyar uwar mijin ta wato Giwar sarki Adam me murabis, amma bata taɓa kulawa ba ita basune agaban taba batada wani buri daya wuce ganin ɗan ta Sultan yasamu lafiya yazama cikakkyan yaro mai lafiya da kuzari kamar kowane ɗa duk da wasu abubuwan dayake tamkar shafar aljanu ko asiri, kullum cikin addu'a take,

Lokacin tsohon sarki wato sarki adam yaɗaurawa ɗansa, sarki Yusuf aure da ƴar abokin sa wazirin Gombe, mai suna Fa'iza ba don sarki Yusuf ya so ba haka ya karɓi umarnin mahaifin nasa saboda bazai iya jayayya dashiba sannan yana ganin auran sa nafari yayi shine batare da sanin iyayen saba, kuma suka yi hak'uri ya zauna da matar,
Don haka dole shima ya karɓi nasu umarnin, amma tabbas aranshi yafison rayuwa da matar shi wato bahijjah,

Fa'iza ƴar gidan sarauta ce Tunda ta shiga masarautar gabas tasamu labarin, uwar gidan mijin ta, ƴan gudun hijirane ita da Mahaifiyar ta, shikenan tasamu damar rainata da wulaƙanci kala kala, Tunda sarki Yusuf yasamu labari sosai aranshi yaɓaci saboda bahijjah bata taɓa gaya masa abunda ke faruwa ba,
Da babbar murya yajawa Fa'iza wani kyakkyan kashedi tare da jamata layi, yafaÉ—a mata ta tsaya iya matsayin ta, idan ba haka ba zai iyarabuwa da ita don shi bai haÉ—a matar shi bahijjah da komai ba,

Ta razana kwarai dajin abunda sarki Yusuf yafaɗa, take taƙarajin tsanar Bahijjah aranta, tare da ɗaukar mummunan al'washi akan ta,
Lokacin da Fa'iza ta cika shekara É—aya a masarautar hakan yayi dai dai da haihuwar É—an ta na fari, wanda yaci suna Safwan, hakan yasa ake kiran ta da (ummu Safwan) bayan Fulanin sarki da ake kiran ta dashi,

A lokacin ne matar sarki Abdullahi mai rasuwa, tasa wasu ƴan fashi shiga cikin masarautar don yin gagarumar sata ta manya manya dukiya hadda hatimin Zaki na masarautar kasancewar na ƙarfe mai darajane zinare, tare da samun haɗun bakin wasu manya manyan mutane acikin masarautar da fadawa,
Cikin rashin sa'a aka kamasu, sanda labari ya risketa cewar ankamasu take ta haÉ—a kayan ta tsaf daniyar guduwa ita da É—an ta mu'azzam, sai shaheedah wadda bata haura wata takwas ba a duniya,

Ƴan fashin da akakamasu da fari sunyi gaddama wajan faɗan gaskiya amma da sukaji azaba mai radaɗi, babu shiri suka bayyana wadda ta sasu tare da magoya bayan ta,
Cikin sauri sarki yabada umarnin azo masa damar É—an uwan sa Abdullahi, bata samu nasarar guduwa ba aka caff ke ta, kuda aka zauna zaman shari'ar sirri saboda duk cikin gida ne sarki yabada umarnin kada a fitar da maganar,
Koda aka tambaye ta Meye dalilin ta na aikata hakan, babu wata kwakkwarar hujja, bata bayyana musu gaskiya ba, hakan yasa alƙalan fada yanke mata hukunci, nabarin cikin masarauta gabas na har'abada babu ita ba masarautar, tare da barin garin Barno gaba ɗaya, cikin tsananin tashin hankali da danasani mara amfani ta kwanta ta shiga kuka da ban hak'uri amma ina, babu wanda ya saurare ta,

Mai martaba sarki Yusuf yaroƙi alfarmar alƙalan fada kan cewar, Tunda ita kaɗai tayi laifi ayi wa yaran afuwa abarsu a cikin masarautar su rayuwa ƙarƙashin kulawar sa,
Nanfa aka sake sabon zama, saidai sarki bai samu yadda yake so ba, saboda ƙin amincewa da sukai tare da Faɗin saidai akarɓi jariryar wato shaheedah, itakuma ta tafi da mu'azzam, babu yadda sarki Yusuf ya iya haka ya hak'uri yakarɓi shaheedah tare da damƙa amanar ta a hannun matar shi ummul bait, cikin farin ciki da jin daɗi ta karɓi shaheedah,
Cikin adalci irin nasa yasa aka kai ta har airport tare da mallaka mata hamshaƙin gida acikin garin Kano, ya buɗe mata account wanda za a rinƙa sama ta kuɗe koda yaushe, tare da damƙa mata gadon ɗan ta mu'azzam baki ɗaya wanda mahaifin sa ya bari sai yabar na shaheedah a hannun Ƙanin sa Galadima Murtala,

Cikin kuka tabar masarautar gabas, wanda son zuciyar ta ya janyo mata, nasa Æ´an fashi suyi gagarumar sata saboda tana ganin, sarautar da take kwaÉ—ayin mijin ta yayi to babu shi a duniya, tanaganin bata da wani mahimmanci acikin masarautar, babu abunda zata samu sai abunda mijin ta yabar musu, shiyasa ta aikata hakan,

Wannan shine dalilin barin Mahaifiyar Gimbiya shaheedah daga cikin masarautar gabas tare da ɗan ta mu'azzam wanda hakan yasa ta tsani kowa dake cikin masarautar tare da mummunan al'washi aranta sannan tayi alƙawarin koba daɗi ko bajima sai ta dawo masarautar gabas tare da ɗan ta kuma sai ya mulki masarautar sannan ta ɗauke ƴar ta da aka karɓa, da wannan tunani takoma garin Kano cikin baƙin cikin karɓar mata ƴar ta shaheedah da akayi,

ƙarshan taƙai taccan tarihin Sarki Yusuf Adam shareef kenan,

"Mukoma asalin labari"

*_GARIN KANO_*

Railway Quarters Arab Estate.....

Night 10:04pm
Alhaji imran tun ranar dayayi ar'ba da fuskar Suhaima wani abu wanda ya rasa Meye shi, ya tsaya masa acikin kai, tunani kala kala acikin kwakwalwar sa, mutanan da suka kasan ce wani jigo na rayuwar sa, wanda azahiri sun daÉ—e da shuÉ—ewa, sune suka dawu cikin tunanin sa,
Cikin ransa yafara tunanin Tabbas ita ɗin wani ɓangare ne na rayuwa ta, tabbas fuskar ƴar uwata nake gani atare da yarinyar nan, shin su waye iyayen ta? Zanso ƙara ganin fuskar ta, duk da taroƙeni batason wani bayan ni yaƙara ganin fuskar ta acikin gidan nan,

Jin shirun yayi yawa ne hakan yasa Hajiya umma ƙara matsawa kusa da kujerar da Alhaji imaran ke zaune tare da ɗan bubbuga kujerar da ƙarfi,

Cikin nutsuwa yakai dubansa kanta, tare da FaÉ—in yaushe kika zo nan?

Zama Hajiya umma tayi tare da FaÉ—in, Haba alhaji najima da zuwa, ina ta magana amma kana can duniyar tunani, Meye yake damun ka har haka?

Kallon ta alhaji imran yayi sosai kafin ya numfasa, tare da FaÉ—in ba wani abu bane kawai ina tunani kan rayuwa ne,

Amma kuma alhaji kasan an hana tunani saboda lafiyar ka amma sai kazo Kazauna kai kaÉ—ai karinga irin wannan dogon tunanin emm wanda na kai tsawan minti biyar anan ina magana shiru,

Murmushi baffa yayi, to likita na tuba nake bazan ƙaraba yafaɗa cikin sigar wasa,

Murmushi itama tayi irin nasu na manya, tace ko dai kewar shalelen naka kakeyi?

Sosai yaƙara faɗaɗa murmushin nashi jin an'ambaci sanyi ruhin sa Sulaim, ai yanzu bajimawa muka gama waya, yace ma yanan tafe gobe insha Allah zaibaro Barno,

Masha Allah, to Allah ya dawo dashi lafiya zaizo ya cigaba da yi mana miskilancin nasa sarkin rashin fara'allah yasa kafin ya taho daga masarautar subashi sarkin marasa fara'a, takai ƙarshan maganar tata da dariya,

Shima dariyar baffa yayi tare da FaÉ—in kibari idan ya dawo sai kifaÉ—a masa da kanki,
Sai yaÉ—ora da FaÉ—in, Mero dama inaso muyi magana shiyasa nace kizo ina neman ki, Mero shine sunan da baffa ke kiran Hajiya umma kennan idan yakasan ce da gashi sai ita ne,

Gaba É—aya hankalin ta tamaida shi kan baffa tare da FaÉ—in inajin ka alhaji,

Akwai wata yarinya da na ɗauke ta ita da ƴar'uwar ta, suna cikin estate ɗin nan, neman aiki ne yakawo su, to amma na ɗauke ta tamkar ƴa tane, inaso ta zauna a gurin ki zata rinƙa kula da Part ɗin Sulaim dake wannan house ɗin namu, Tunda ya dawo nan gaba ɗa,
Ganin Hajiya umma tayi shiru ta tsuramasa ido hakan ne yasa shi yin shiru domin bata damar faÉ—ar abunda ke bakin ta,

Kamar me jira tafara da Faɗin, alhaji wacece Yarin yar sannan kuma a ina kasan ta, banji labarin taba, kuma kasan bama ɗaukar ma aikata, sai ƙarshan shekara, sannan Meyasa zata kula da ɓangaran Sulaim bayan kasan halin sa bayasan komai da ya shafi mace,
Gaba É—aya a jere tayi masa waÉ—an nan tambayoyin, wanda ita batasan ma tayi masa ba,

Saida ya tabbatar ta gama sannan yaɗora da, Kikwantar da hankalin ki nima bansan komai akanta ba, sannan zata zauna dake kamar yadda nace, taɓan garan Sulaim kuma mai sauƙi ne nasan yadda zanbullu masa ya fahimta cikin sauƙi, sannan yarin ƴar nan kema kina ganin ta zakiji ta kwanta miki a rai, da sannu kuma zamu fahimci komai akanta, sannan abu na ƙarshe kada wani ya kuskura yace tabuɗe masa fuskar ta, saboda ta roƙeni wannan alfarmar, batason kowa yaga fuskar ta idan lokacin bayyana hakan yayi dakanta zata buɗe Sunan ta Suhaima,
Chapter 50 · 0% Book details