← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 90

Sashe 27

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama shi take kallon, Shiru Babu wanda ya tan kawa É—an uwan sa, idon sa yamar Kan Computer É—in sa ya cigaba da abunda yake, Wani irin haushi ne yakama Suhaima lallai wannan yarainamin wayo,
Kuma aini yakamata nafara yi masa magana ko? Ta tambayi kanta,

Ciki ciki ta furta Barka da dare,

Sarai yaji amma ko ido bai É—ago ya kalle ta ba bare tasa ran zai amsa gaisuwar tata,

"Wani irin haushine ya turnuƙe Suhaima, Mtsss duk laifina ne dana gaida shi, kuma wlh ba hakan ne zai sa nafasa rama wulaƙancin da kayi min ba, cikin ranta tayi maganar,

Kallon ta Sulaim yayi, Kin tsayamin akai, idan Akwai Aikin da zakiyi, kiyi ki fita, Tamkar bashine yayi maganar ba, Saboda can ƙasan maƙoshin sa yayi maganar, itama don tana dajine kamar miciji shiyasa har ta iya jin abunda yafaɗa,

Takaici ne Yahana Suhaima Magana, Idan banfita ba Meye zaka iya, cikin ranta tayi maganar,

Kamar Sulaim yasan Abunda tace, A fili yace Sai insa a fitar dake, cikin harshen su na Larabawa Yayi Maganar Suhaima taji amma batasan Meye yace ba,
Tab zagina yayi da yaran su kenan, wallahi bazan haƙura ba sai yafaɗa min wa yake zagi, da wannan tunani tafara taka wa zuwa inda yake zaune ko motsawa bai yiba..!!
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS ......✨�*
*_T.M.W_✍️*

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 3️⃣5️⃣�3️⃣6️⃣📖

*Suhaima*
Saida takai har tsakiyar parlourn Gab da Kujerar da Sulaim yake Zaune, Cak taja ta tsaya, kollon ta tamaida gefe tana zare ido shiru tayi Cikin Ranta tana Tunanin ta'inama zata fara,
Cikin Nutsuwa Sulaim ya sauke ƙafafuwan sa daga saman Tablet ɗin daya miƙesu, tare da Rufe Laptop ɗin ya ajiye ta a gefe, ya miƙe ya nufi Upstairs hannayen sa zube cikin Aljihun dogon wanda jikin sa, Batare da ya kalli ko inda Suhaima Take tsaye ba,

Haka yasa cikin zafin nama Suhaima Tasha Gabansa Ganin yana ƙoƙarin, Hayewa Sama Batare da taji Meye ya faɗa ba, wanda harcikin ranta take Ayyana Zagin ta yayi Da Larabci,
Ganin ta da Sulaim yayi A gaban sa yasa shi mamaki kamar wadda aka cillo, Abunda baya so kenan wani yasha masa gaba koda a Mota ne wani ya ari hannun sa koda bashi yake driving ɗin ba, Kaifafan idanuwan sa ya ɗago ya zuba mata yana mamakin ƙarfin hali irin na Yarin Yar, Take Sulaim ya ƙara shaida tabbas itace wadda nayiwa ƴar uwar ta aiki a hospital ɗina to Meye yakawo ta nan?, itama Ɗagowa tayi daniyar Yimasa magana Suna haɗa ido gaba ɗaya Suhaima, Taji ta kasa magana, Kwarjinin sa yakamata, wani irin Yar Taji _From Head to toes_ Kallon ta yaciga dayi da Shanyayyun idanuwan sa, Ya Rabb Ya Rabb yafaɗa cikin Zuciyar sa, saboda Harcikin ran shi bayajin zai iya magana da'ita, cigaba yayi data fi abunsa ganin Haka yasa Suhaima fara ja da baya yana tafe tana ja da baya, har sai da takai ƙarshe ta jingine da Handle Ɗin Stairs, saida yaji kusa da ita sosai, _So Tired_ Hannu Sulaim yakai Bayan Suhaima, Da Sauri ta runtse idon ta A tunanin ta ita zai ruƙe, Handle ɗin ya dafe da hannun sa ta yadda zai ji daɗin tsaiwar, Ɗayan hannun yasa ya tukare bango, gaba ɗaya yayi mata Cover, ya harɗe ƙafafuwan sa, Da'alama shi hakan dayayi ko ajikin sa,
Ke wace? Ki buɗe Wannan ƙazamar Fuskar taki, Wacece ki dakike son shiga rayuwa ta, Bana Son Ganinki idan ma aiki akakawoki nan ki canza Part, Cikin Nutsuwar Sa yake magana amma da'alama rashin Aɓace yake,

A hankali Suhaima ta Ware idanuwan ta Akan Fuskar shi Gaba É—aya ta takure babu yadda zatayi wani kwakkwaran matsi yasa hannun ya tare ko ina,
Cikin Jin zafin kalaman sa, ta furta Bansan ko ni wace ba, Sanin koni wacece bashida amfani a gurin kowa dake cikin dangin ku, Sannan babu mai ƙazamar Fuska sai Mutumin da baya Murmushi ko dariya babu annuri gaba ɗaya a tattare dashi, Abu nakusan Ƙarshe shine, idan Har baka son ganina to Saika ƙauracewa hakan, Ko kaɗau mataki akan hakan, zan cigaba da shiga inda nakeso acikin Estate ɗin nan matuƙar ina raye, maganar canza Part kuma Aiba kai ka kawo nib......

Cikin Tsawa Sulaim ya katse Suhaima, _Oh enough is enough I don't have time to listen to a Foolish girl like you_
_You think you can say whatever you want? I will shatter Your life And that your entire Family_ yakai ƙarshan maganar gaba ɗaya jijiyoyin kansa suntashi Fuskar tayi ja, Alamar ransa yaɓaci sosai,

"Murmushin takaice Suhaima tayi wanda har saida Sauti yafito, tare da FaÉ—in ka kwantar da hankalin ka, _I Maybe Nobody, but you destroyed my Family long ago. Now it's my turn to destroy yours, you've Just Started seeing my wrath, and there's nothing you can do about it!!!_

Hannu Sulaim Yakai Daniyar Fizge Mayafin da Suhaima ta rufe Fuskar ta dashi, Da saure ta ruƙe masa Hannu tayi Zaton Marin ta zaiyi,
"Wani Irin Rikitaccan Al'amari ne Ya faru, Gaba É—aya hannuwan su suka É—auki rawa, haÉ—i da Mannewa Tare da Fitar da wani Jan Haske mai duhu _Shocking_ Hannuwan sukai Wanda yasa Sulaim saurin ÆŠauke hannun sa tare da ja baya, Idon sa akan Suhaima,
Suhaima wadda tayi Suman tsaye Takasa koda motsawa da'alama Shock É—in bai sake taba, Batare da Sulaim yace komai ba da sauri ya haura Upstairs wanda sauri baya cikin É—abi'ar sa,

Suhaima saida taɗau tsawon lokaci kafin tasamu taja ƙafa jiki babu kwari, Ta nufi Part ɗin Hajiya Umma Zuciyar ta cike da Saƙe Saƙe da Tambayoyi, Shin waye yayi masa haka Meye laifin sa? Dama bashida Cikakkiyar lafiya cikin ranta take maganar, A zahiri kuma wasu Siraran hawayen tausayi ne Suka gangaru daga Kuncin ta, Da haka har tafita daga part ɗin, gaba ɗaya zuciyar ta takarye,
Ganin hajiya Umma Bata Parlour hakan yasa tayi tunanin Bata dawo daga Part ɗin Baffa ba, sai ta wuce ɗakin ta kawai, Kwanciya tayi idanuwan ta a rufe tana fuskantar Saman silin har lokacin Hawayen na gangarowa, Menene Mafita Ta'ina zanfara? Ana son kashemasa rayuwa kafin a kashesa gaba ɗaya, Suhaima ta rasa nutsuwar ta Tunda ta kama hannun Sulaim gaba ɗaya saida taji abunda ke faruwa dashi dakuma Abunda ke jikin sa, Tasan tanajin wani abu akan mutane matuƙar akwai Cutarwa a jikin su, tana kama hannun mutum ko shi yakama nata, Indai bashida lpy ko an masa wani mummunan abu to sai taji, hankalinta ya tashi sosai saboda bata taɓajin irin na Sulaim akan wani ba,
"Ware idon ta tayi wanda Suka canza kala zuwa, Rainbow Colour a wannan karon harja saida Suka yi saɓanin ko yaushe, kamar irin wadda tasha kuka ta ƙoshi,
Wayar ta data sa a charge taciro Tana kunnawa bisa mamakin ta sai ga Sim aciki babu wani dogon tunani, tasa number É—in Mother tayi Dialling cikin sa'a kiran ya tafi batayi tsammanin akwai kati ba gwadawa kawai tayi, bugu Biyu aka É—auka,
Wata irin Nannauyar ajiyar Zuciya Suhaima ta sauke, tare da goge hawayen idon ta,

"Assalamu'alaikum aka faɗa ta ɗayan ɓangaran"

"Mother Suhaima, tafaÉ—a tare da fashewa da kuka"

"Suhaima Suhaima ta, Ƴata kukan me kike, ko acikin Suma nake idan naji muryar ki sai nagane, Faɗamin kukan Meye kike waya taɓaki, Ina tare dake Kullum saina ganki cikin bacci na, duk shigar daƙiƙa ɗaya da fitar ta saina yi muku addu'a inada yaƙinin ko ina kuke Allah yana tare daku bazai bare a cutar min dakuba ko a wulaƙan Taku, ku ba jinin daza a tozarta bane, nayi Zaman jiran kiranki Suhaima har nagaji amma ban fidda Raiba kullum cikin zuba ido nake,"

" _My Mother, My World desire My only Mom in the world I really really Messed you_ Mother Fatan kina Lafiya, Bazan iya tuna A rana Saunawa nake iya tunaki ba, Kice kullum abakina, Munyi kewar ki sosai" Suhaima tafaÉ—a tana Murmushi jin daÉ—i,

"Nasani ƴa ta danaji murmushin ki harnaji daɗi, Da kukan Meye kike Idan ban mantaba nafaɗa muku, kuka bana mu bane wannan hawayen adana su za'ayi akwai lokacin amfanin su, Tunda na iya turaku inda bansan kowa da komai ba kuma kuma ba kusan kowa ba a gurin ba nagane addu'a ita ce matakin nasarar ba kuka ba, Allah nabarma komai kuma inada yaƙini akan hakan, yanzu kuna ina?

"Muna Arab Estate Mother muna lafiya cikin aminci da kariyar Allah A yau Gani cikin Inda na daÉ—e ina nema amma Haryanzu Ban Aiwatar da Komai ba nasan zakiyi Fushi da hakan,"

"Murmushi Mother tayi wanda har Suhaima saida taji, To Alhamdulillah Ina Khaltume na, Ya kuma haƙuri da Halinta dan nasan tana nan tanayi"

"Tanan lafiya ba guri É—aya muke ba shiyasa Amma zan haÉ—a ku zuwa safe insha Allah"

"Suhaima nasan Kuna Arab Estate, Saboda hajiya fanteka takirani a waya tacemin wai ku gudu tanemeku ta rasa, Hankali na ba ƙaramin tashi yayi ba, Sai na tuna dako, kewa ce sannan nasan dole Kinsamu Estate ɗin nan, da biki samu ba da baza kubar gidan taba hakan yasa na ɗan kwantar da hankali na, Abunda nakeson ji Tayaya kuka iya shiga sannan a wane hali ake ciki yanzu,"

" Tunda ga Farko har ƙarshe Suhaima saida ta kwashe labarin komai ta faɗawa mother tun daga sanda Suka shigo Kano har kwanciyar Khaltum a Asibiti da yadda akai Suka shiga Cikin Arab Estate da yadda Baffa ya karɓe su, Da abubuwan da tagani, Da file ɗin da tayi musanyen sa na Uncle Mansur, Babu abunda taragewa mother aciki, Labarin Sulaim kawai taɓoye mata, wanda itama kanta bata san dalilin ta nayin hakan ba, bata taɓa jin akwai abunda zai zo taɓoyewa mother ba, amma yau gashi takasa gaba ɗaya jitayi harshan ta yayi mata nauyi,
Chapter 27 · 0% Book details