← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 90

Sashe 21

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Badon Saleem ya yadda ba yace "OK" haɗi da tashi yanufi Dinning Area Gaskiya Yarima Amin Afuwa Bazan iya haƙuri ba, wannan ƙamshin abincin saiya sheƙeni idan banciba, yana tafe yana magana harya kai dinning area ɗin yana ƙoƙarin buɗe babban Food Flaks ɗin dake saman Dinning ɗin ko zama baiyiba,"
Ringing ɗin da wayar Sa tashigayi ne yasa shi dakata wa, tare da dubawa waye yake son katse masa hanzari, _My Suhailat_ ne ya bayyana ɓaro ɓaro akan screen ɗin wayar, Flaks ɗin dabai buɗe ba kenan, ya koma cikin Parlourn ya zauna, yaciga bada wayar sa cikin shauƙi da ƙauna,

*Barrister Sulaiman*
Haba Uncle Mansur tunɗazun nake kiran ka amma baka picking, Muna cikin Babbar Matsala _You Know_ Yanzu Meye mafita game da wannan? Emm, idonsa ƙir akan Uncle Mansur wanda ke tafaman kai kawo acikin ƴar bukkar da suke ciki,"

Buga Table ɗin da Uncle Mansur yayi ne yasa Suhaima cin burki ta tsaya Cak, mamaki ne yakamata, jin ƙarar kamar faɗuwar wani abu daga cikin Bukkar wadda ko kaɗan bata kawowa kanta cewar mutane ne aciki ba, kamar zata cigaba da tafiya sai kuma taji tason ganin Meye yafaɗo daga ciki, jin ana magana ƙasa ƙasa ne yasa Suhaima saurin ƙarasa wa jikin Bukkar sosai tare da kasa kunne,

Uncle buga hannun ka saman table bashi ne mafita ba illa yaji maka cewo, kanutsu Kazauna munemo Solutions akan al'amarin nan don idan bamuyi da gaske ba to tamu tazo ƙarshe, Gashi mun narka dukiya akan kayan da suke hanya yanzu,"

Zama Uncle Mansur yayi kan kujerar rubar dake fuskan tar wadda Barrister Sulaiman ke kai, Hhmm Yanisa,
"Mafita ɗaya ce zuwa biyu cewar Uncle Mansur, mafitar farko shine, dole Jadawalin sunayen Sabbin Directors da Managers mucanza su zuwa sunayen mutanan mu, tahaka ne kawai zamu samu damar cigaba da gudanar da kasuwancin mu, sannan kayan mu da suke hanya, daga ƙasar JORDAN idan suka iso kaga cikin sauƙi zamu karɓa Tunda mutanan mune akan komai na Companies, kuma Tunda nine matemakin Hameed zanyi duk yadda zan iya wajan ganin ba'a canzawa Tankokin dake raba Kaya, Register ba har zuwa lokacin da kayan mu zasu iso,"

Duhu ne cikin Bukkar kasan cewar babu wadataccan haske, sosai Suhaima take kallon Uncle Mansur ta cikin wata ƴar Raga a jikin Bukkar saboda Bukkar saƙa ce, tagama shaida kamannin sa tsaf, saboda dama tafi ganin abu acikin duhu sosai, so take taga Fuskar Barrister Sulaiman amma abun yaci tira ƙeyar sa kawai take iya gani,"

Inajin ka Uncle naji wannan shawarar saura ta biyun,"

Uncle Mansur yace Eh to ta biyun mai wahala ce amma kuma babu wahala,

Kamar ya Bangane ba? Barrister yafaÉ—a yana gyara zama,

Kisa"

Zaro ido Barrister Sulaiman yayi jin Abunda Uncle Mansur yafaÉ—a, Kisa fa Kace,

"Taɓe baki Uncle Mansur yayi, Eh Kisa mana Meye Aciki da zaka wani Tsorata kamar yau muka fara"

"A'a Gaskiya Uncle kasan bana son Irin wannan nidai Duk abunda za ayi nafison abi taƙarƙashin ƙasa, Sannan kisan ai sau ɗaya muka taɓa yi shima Arashin makama ne yasa mukayi to amma wannan aibaikai na ayi kisa ba kuma kisan ma acikin Family ɗin mu wancan ma fa ɗan uncle Y..."

Idan baka kashe ba to kai za'a kasheka uncle mansur ya katse masa hanzari, kuma ni inaji ina gani wallahi babu wanda ya isa yashiga tsakani na da kasuwanci na, bazan taɓa bari hakan ta faru ba, tunkafin a haifeka nake gudanar da irin wannan harƙallar kuma har yau babu wanda yasani, akan haka kuma zan iya kashe koma waye,"

_Enough Uncle_ Banason do guwar magana Bamu da lokaci, waye za'a kashe wanda kake ganin idan akayi hakan zamu samu mafita,"

Uncle Mansur yace Alhaji Hameed, idan muka kawar dashi to komai na Arab Companies zai dawo hannu na saboda nine matemakin sa kaga idan na koma matsayin sa ai shikenan kakar mu ta yanke saƙa,

_Uncle What Mean?_ Abiiy fa

Kallon Barrister Sulaiman, Uncle Mansur yayi, _Yes I mean_ Alhaji Hameed Imran Arab Uban Sulaim, ina fatan kagane, Wannan mutumin da kake gani mugun ɗan hana ruwa gudu ne, bashida kirki ko kaɗan idan aka kama mutum da laifi baya bari a sassauta masa, saboda haka shine ƙarshan matsalar mu,"

Shiru Barrister Sulaiman yayi ya zubawa Uncle Mansur ido yana sauraron shi,

Idan kuma ba haka ba abu na ƙarshe shine Samo HATIMIN MALLAKA, Ana samun shi to babu baton kisa ko makirci shi kaɗai ya ishemu samun Nasara,"

Uncle ina ganin muɗau Shawarar farko, Tunda kaima Kanada muƙami sosai a companies dole za ayi shawara dakai, sannan ana buƙatar sa hannun ka kafin Ɗaukar sabbin directors, sai muyi amfani da wannan damar mu canza record ɗin jadawalin suna yen dana mutanan mu, kaga da sunayen sunkai zuwa ga Baffa ai shikenan magana taƙare, HATIMIN MALLAKA, bansa ranzuwan sa hannun mu nan kusa ba, duk da munsan inda yake, amma akwai tsaro mai tsauri acikin office ɗin Sulaim sai munbi a sannu, Mubar Uncle Hameed zuwa nan gaba Ya fara ganin mutur ɗan sa kafin tasa,"

Wata irin Mahaukaciyar Dariya Uncle Mansur yasaki, Da kyau yaro na ina alfahari dakai wannan bayani naka yayi, Allah ya temaki Hameed da yabaƙunci lahira a kwanan nan amma yanzu kafanshi rayuwar sa,

Shiiiii" Uncle kamar akwai mutum a gurin nan fa ko kai ba kaji alamar hakan ba,"

Tsitt Uncle Mansur yayi yana ƙara kasa kunne, domin yaji hakan,
"A'a babu kowa fa anan kawai ka tsurgune, Amma ina zuwa kai tsaye Uncle Mansur yayi waje daga cikin bukkar don tabbatar wa,

" Cikin Zafin Nama Suhaima ta koma bayan waya bishiyar Mangwaro taɓuya amma tana lekyan sa,"

"NafaÉ—a maka babu kowa har baya na zagaya amma banga komai ba, yanzu dai yakama ta mu tafi Tunda munsamu matsaya,"

"Barrister Sulaiman yace oky Badamuwa Mugu Uncle kana zuba Life, ya faÉ—a yana sakin Dariya,"

Shima Dariya yasa kafin Yamiƙa masa Hannu suka Kashe, Ai ina jin daɗin harka dakai ɗana, Kafi Sauran iyayen naka, shi Ubanka Hasheem, nama rasa gane alƙibilar shi, amma da kake ganin sa ƙasurgumin mara gaskiya ne,"

Mai maƙon Barrister Sulaiman yaji haushi zagin mahaifin nashi da akai, saima yace, Nasani Uncle kuma ina lura dashi, amma har yau nakasa gane Meye yake aikatawa,"

"Karka damu zamu gano ya faÉ—a lokacin suna fitowa daga bukkar a tare,"

kowa motar sa yanufa kai tsaye suka wuce,"

Akan idon Suhaima suka bar gurin, kunnuwan ta sunji komai, wani irin mamaki ne ya É—aure mata kai, Batasan komai akan maganar suba, amma ta tabbatar wa kanta akwai matsala babba, sannan taji sun ambaci Sunan Sulaim shima hakan yabata mamaki, Taso ganin waye É—ayan amma bata samu damar hakan ba, HATIMIN MALLAKA Tabbas nasan wannan kalmar amma a ina?
Akwai aiki a kaina dole sai nagano komai game da wannan kurman Estate É—in mai cike da rikita_rikita, azzalumai da muggan mutane, da wannan tunanin ta nausa cikin wannan É—an dajin,"

*Sulaim*
A Nutse yake sakkowa daga upstairs ɗin cikin shigar kayan sanyi riga da wando ne masu jikin kuliya, black colour maɓallin su white ne masu girma, akwai kwala a jikin wuyan rigar itama anyi mata ratsin white, Yayi kyau Sosai hannun sa ruƙe da kofin Coffee sai tiriri yake,

Barka da fitowa aminina kayimin wayo ko Yarima Sultan ya faÉ—a tare da É—auke kallon shi daga kan Sulaim?

Saida yasamu guri cikin kujerun parlourn 1siter ya zauna daga gefan Yarima Sultan ya ajeye cup É—in hannun Sa saman table, Murmushin gefan baki yayi, Tuba nake Allah ya huci zuciyar Saraki,"
Saleem yafita ne?"
Sulaim ya tambayi Sultan,

"A'a yana dinning ba kaji motsi ba Dr.Jabir yazo suna tare" nima fa jiranka na tsaya yi amma ƙamshin abincin nan haryan zu yana shiga hancina, cikin wasa yakai ƙarshan maganar"

Muje muyi Dinner Sulaim ya faÉ—a tare da wucewa gaba,"

Sosai Yarima Sultan yayi mamaki yau Sulaim nacewa aje aci abinci lallai wadda tayi girkin nan taciri tuta, Bamusu yamiƙe yabi bayan sa,

*Dr.Jabir*
"Nifa Tunda nake bantaɓa cin irin wannan abincin ba,

"Kaima kennan Dr. Wlh niban masan shiba Allah yasa _My Suhailat_ ta iya irin sa,

Dariya Dr.Jabir yasa ai inaganin sai na tafi da abincin nan gida,"

Kada ku kware fa,"

Kusan a tare suka kai duban su kan Yarima Sultan dai dai suna Zama shida Sulaim,"

Gaba ɗaya suka sa dariya banda Sulaim, Dr.Jabir yace A' Ranka ya daɗe kun ƙarasu kenan ai dole ni zanyi saving ɗin ku, take ya ɗau plate yayi saving Sultan da Sulaim,"

Shiru babu mai tankawa É—an uwansa saida suka gama, Saleem saida ya cinye nashi tass, Dr.Jabir ma haka, Sulaim baiwani ci dayawa ba, Yarima Sultan yafishi ci dayawa saboda abincin yayi masa daÉ—i sosai ji yayi tamkar Ummul Bait ce tayi girkin yanayin É—anÉ—anon,"

Badon Sulaim baiji daÉ—in abincin yabar shiba Sosai yayi masa daÉ—i, saida yaji cikin sa yayi masa nauyi, bashida cin abinci sam ahakama wai yaci dayawa, tashi sukai suka nufi Parlour

hannun Dr.Jabir ruƙe da cup Methor joice ɗin da Suhaima tayi ne aciki, shifa abincin ya tafi dashi sosai,"

"Saleem yace Gaskiya hajiya Umma ta kauta yau ɗaya dai tayi abun arziƙi, zanje na tambaye ta sunan wannan abincin datayi sannan na roƙi alfarmar zankawo iyalina a koya mata,"

Dr.Jabir yace nima zan raka ka Ashe Hajiya Umma ce tayi aini nayi tunanin aure DR. Yayi bansani ba😂

To bansan dai takamaiman wanda yayi girkin nan ba nima ganin sa kawai mukai,

Jin abunda Dr.Jabir yace hakan yasa Sulaim ƙara kame fuska,"

"Koma dai waye yayi girkin nan Muna godiya, Yarima Sultan ya faÉ—a tare da zama, Ashe Saleem kayi iyali ba labari naji kana shirin kawo ta koyan girkin gargajiya,"

Dariya Saleem yayi, Allah ya temakeka zandai yi tukunna,"

Dr.Jabir yace Au ashe girkin gargajiya ne ai wannan yafi nazamanin ma daÉ—i shi zan koma ci kullum amma idan nasamu mai daÉ—in wannan"
Dr. Barka da dawowa fatan kun iso lafiya?"

Kallon karaina min hankali Sulaim yayiwa Dr.Jabir, Sai yanzu ka ganni kenan, lafiya muka sauka fatan kana lafiya, ya aiki,"

"Ayimin afuwa na sha'afa ne duk abincin nan ne yaruÉ—ani, ina lpy aiki alhamdulillah,"

Cikin nishaÉ—i dajin daÉ—in hirar da suke, gaba É—aya suka nufi Masjid don gabatar da sallar Isha,
Chapter 21 · 0% Book details