← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 90

Sashe 17

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dafe kan Sulaim Ummul Bait tayi fuskar ta na gaf da tashi da'alama addu'a takeyi masa tadaɗe sosai tana yi masa, wanda yana kwance ko motsi ba yayi an ɗaura masa Drive, idanuwan Sa a rufe, fuskar tashi har taɗan faɗa, hakan sai yaƙaramasa kyau sosai,"

"Ahaka mai martaba ya iso yasamesu, ga Yarima Sultan tsaye, sai Saleem dake zaune daga jikin bango yana fuskantar gadon, gaba É—aya fuskokin su É—auke da Matsananci damuwa,"

Har ƙasa suka russuna suka gaida mai martaba, bai iya ko amsa musu ba hannu kawai ya ɗaga musu,

"Shiru sarki yayi yana kallon Ummul Bait nazarin ta yashigayi, Sosai yake ji daɗin yadda yasamesu tanayi wa Sulaim addu'a, tunani ya farayi cikin ransa ashe bashi kaɗai ke ƙaunar Sulaim ba yana son Yaron Tamkar Ɗan sa Sultan haka yake jin sa a rai,"

Ɗagowa tayi bayan ta kammala yi masa addu'ar, Fuskar ta babu yabo ba fallasa, ta dai dai ta zaman alkyabbar dake jikin ta launin ɓaki mai fararan duwatsu,
"kallon mai martaba tayi, Barka da zuwa Ranka tadaɗe Allah ya ƙara maka yawan Nasara,"

"Barka dai ya jikin nasa fatan Da sauƙi,"

"Alhamdulillah, tafaÉ—a tare da matsawa daga jikin gadon saboda mai martaba yasamu damar duba shi,"

"Sunan Allah É—auke abakin sa ya fara motsawa ahankali, ya ware manyan idanuwan sa gaba É—aya, tare da cire hannu ya dafe kansa alamar ciwo yake masa,"

Gaba ɗaya suka nufo gadon Yarima Sultan da Saleem, ganin mai martaba ya isa jikin gadon hakan yasa su dakata wa gaɓa ɗaya,"

Ɗakyar Sulaim yakai Dubansa zuwa gurin Sarki, Yinƙurawa yayi zai tashi, Sarki ya dakatar dashi tare da kama kafaɗun sa duka biyun Yamai dashi kwance, Allah yabaka lafiya Sannu da jiki, Allah yasa ka kasan ce cikin aminci da samun sauƙi, ka huta sosai,"

"Baffa inaso naga Baffa yanzu, Sulaim ya faɗa muryar shi tayi ƙasa sosai har lokacin bai cire hannun sa daga goshin saba,

Kasan cewar gaba É—aya sunyi shiru hakan ya basu damar jin abunda yace,
"Matsawa Yarima Sultan yayi kusa dashi, Alhamdulillah Sannu yakakejin jikin naka?

"Kallon sa Sulaim yayi, Tare da ruƙo hannun Yarima Sultan ɗaya, Aminina yaushe Baffa yazo nan Ina Baffa inason ganinshi yanzu,"

Baffa bai zo ba kamanta yanzu dare ne kayi haƙuri zuwa gobe zamuje zakaga Baffa, Emm

A'a Baffa yazo nan shine yayimin addu'a yanzun nan, naji hakan acikin raina, please ku kaine,"

"AÉ—an raunane Yarima Sultan yakai Dubansa kan iyayen nasa, yana nuna musu alamar suna jin Abunda Sulaim yake faÉ—a,"

Tasowa Saleem yayi ya nufi gadon Dai dai lokacin wayar Sulaim dake hannun sa ta É—auki ruri, kallon screen É—in wayar yayi, Ras Ras, gaban sa yafaÉ—i ganin, _Lovely Grandad_ a rubuce, ganin Saleem yayi shiru yana kallon screen É—in wayar ne gashi kiran ya katse wani ya sake shigowa,"

Saleem Lafiya dai? Yarima Sultan ya Tambaya,

Baffa ne yake kira,"
Tabbas ansanar masa Rashin lafiyar Sulaim yanzu ya za ayi,?

"Iska Yarima Sultan ya furzar, huuuuu, batare da yace komai ba,"

"Shi ko Sulaim ya ƙara rufe idon sa kamar mai bacci amma duk yana jin su baya son Magana ne kawai"

ÆŠana Meye yakemaka ciwo Yanzu?, Ya tsinci muryar Ummu Bait kunnuwan sa,"

"Buɗe idon yayi ahankali tare da Sakin murmushin ƙarfin hali, Ummu lafiya nakejina alhamdulillah babu inda kemin ciwo yanzu,"

"Itama murmushin ta sakar masa, har kanka baya maka ciwo? Ta sake tambayar sa ganin har lokacin yana dafe dakan,

"Eh ya rage ciwo sosai, Ina godiya amadadin uwata,"

"Wannan murmushin bata ta sake sakar masa kafin tace to shikenan ka huta sosai kaji Karka damu kanka munanan tare dake, zuwa gobe zakaga Baffan ka insha Allah",

"ÆŠaga mata kai kawai Sulaim yayi ba don itaba to tabbas yasa aranshi sai Yakoma Kano a daran saboda ji yake kamar ana kiran sa, dole yana son ganin Masoyin kakan sa wayo baffa,

"Kallon Saleem sarki yayi tare da bashi umarnin ya ɗaga kiran Baffa wanda yake ƙara shigowa Aƙaro na Huɗu,"

Ɗagawa Saleem yayi tare da ƙara matsawa kusa da Sulaim sosai yasa wayar a speaker, Sallama yayi cikin muryar mai kwarjini da dattaku,"

Da sauri Ummul Bait tadafe Kujerar dake kusa da ita jintana ƙoƙarin faɗuwa, wani abune ya ratsa mata tundaga tafin ƙafar ta harcikin kwaryar zuciyar ta, jin muryar Baffa, Batasan dalili ba kasa tsayawa tayi cikin ranta taji cewar tabbas ta ƙara koda minti 1 ne mutumin nan ya ƙara magana zata iya faɗuwa,
"Russunawa tayi kaÉ—an kafin tace Ranka ya daÉ—e a fito lafiya, Aminin Sultan yana godiya bisa kularwa mai martaba,

"Kallon ta mai martaba yayi yana son gane Meye dalilin canza war ta lokaci É—aya ganin bata cikin nutsuwar tane yasa shi FaÉ—in, A sauka lafiya,

Ina Sulaim?"
Abunda Baffa yafara tambaya kenan jin Saleem ne ya amsa Sallamar,

Gashinan Kansa ne kiÉ—an yi masa ciwo,"

"Subhanallah Ya jikin nasa amma dai Da sauƙi, Kodai ayi masa Booking jirgin ƙarfe tara ku taho?"
Baffa ya faÉ—a cikin muryar damuwa,

Ji Sulaim yayi kamar yace eh ganin har Lokacin Mai martaba nanan shiyasa Yayi shiru,"

A'a Baffa zamu biyo jirgin safe insha Allah jikin da sauƙi fa,"

To bani shi Sulaim ɗin inji, ƙara matsar da wayar yayi saitin Bakin Sulaim sosai, Baffa Barka da dare, Nayi kewar ka,"

"Sosai Baffa yayi Murmushi wanda harta cikin wayar saida Ya bayyana, Nema nayi kewar ka sosai Ya jikin naka ina fatan dai babu abunda ya faru,?

Eh babu komai dama ciwon kaine yayi sauƙi,"

Hannu Sulaim yakai tare da karɓar wayar daga hannun Saleem, take ya maida kiran Video Call,
Saida suka yi magana sosai suna kallon juna, Ashe a kwance kake Fuskar ka ta É—an FaÉ—a Naga yanayin gadon da kake kai kamar na Asibiti,
"Eh ina asibitin cikin masarautar Nayi kewar ka dayawa shiyasa, Sulaim ya faÉ—a hadda murmushi,

Shima Murmushin Baffa Yayi, sai da ya tambayi Mai martaba sannan ya tambayi Yarima Sultan,

Suna lafiya ga Yarima Anan kusa ai,"

Dariya Baffa yayi kace jinya Suke, Allah yasa sarkin magana baya takura maka, take Sulaim yakai duban sa Kan Saleem suna haÉ—a ido Sulaim yayi Murmushi, gashinan ai mai hali baya fasa halin sa, Sosai Saleem ya É—aure fuska Tamau, don yasan dashi suke dama shi Baffa yake cewa sarkin Magana,"

"Da haka sukai Sallama, zuciyoyin su Fal da farin ciki, kowa ya samu Nutsuwa, Baya Sulaim ba hatta Saleem da Yarima Sultan sunji daÉ—in ganin Sulaim cikin yanayin farin ciki gashi ya warware lokaci É—aya,"

Mai martaba yana daga zaune Saman wata haɗaɗiyar kujera wadda aka ajiye ta saboda zuwan shi, Cikin ransa ya ƙara jinjina shaƙuwar dake tsakanin Sulaim da kakan nasa Baffa, da haka shima ya miƙe tare da yiwa Sulaim fatan ƙara samun lafiya, sosai suka yi godiya gaba ɗayan su, Saleem da Yarima Sultan suka raka sarki har ƙofa sannan Fadawa suka rufa masa baya, Su kuma suka koma Gurin Sulaim,"

*_Wannan kenan_*

"Bayan da Su Mommy da Suhailat da Saleema busuyi ba don abar su suga Sulaim amma akace Yarima Ya hana Abar kowa ya Shiga Princess kuwa tuni tasamu hanya ta shige basu sane ba saboda ta kware wajan fakar ido ta saci hanya, Sukuwa su mommy haka suka hakura suka koma ita da Suhailat Saleema kuwa guri tasamu tace tana nan har a fito mata da yaya Sulaim É—in ta,
"dama Ummeetha tace ita babu inda zata bawai don bata son ganin halin da ɗan na take cikiba, A'a sai dan karar da taga kowa yayi mata hadda mai martaba tasan duk inda Sulaim yake yana cikin ƙoshin lafiya wannan shine dalilin ta nacewa babu inda zata,

Gwaggo Murja tasan dama kome take baza abarta ta shiga ba shiyasa ma bata ce zata jeba, Bayan fitar su mommy Ummeetha sosai ta kwantar mata da hankali kan cewa kada tadamu, Dama Sulaim É—in yanayin irin wannan lokaci zuwa lokaci koda babu hayaniya,"
Da haka tasamu gwaggo taÉ—an saki ranta,"

Mai martaba na fita Aka sanar wa Yarima Sultan zuwan Baba Waziri, take yabada izinin ace ya shigo, Tunda yasan Sulaim jikane a gurin Baba waziri, Bazai iya hana shi shigaba dama yana ganin mutuncin sa,*

"Princess wadda ke tsaye bakin ƙofar shiga ɗakin da Sulaim ke ciki, An hana ta shiga wasu dogarai guda biyu ruƙe da MASHI Dogaye ga kuma bindiga irin ta da rataye a wuyan su Suna tsaye suke gadin ƙofar babu wanda ya isa shiga sai wanda Yarima Sultan yabada izini, Babu yadda ta ita ta koma gefe tajingina tayi tayiwa kanta alwashin wlh saita shiga taga ɗan uwan ta,
Cikin ranta ta furta aikin banza, Abakin ƙofar shiga asibitin anzuba waɗan nan saƙagunan sannan, anan ma ƙofar shiga anzuba su sai kace a kwantar da wani shugaban ƙasa ko sarki kuma nasan duk aikin sarkin iyayen nan ne Yaya Yarima, Mtsss taja ɗan gajeran tsaki, tana cikin masifa ne ta hangi baba Waziri da sauri taje gurin sa kallon ta yayi yana mamakin Meye take a gurin,

Dan Allah kaka kabarni nashiga wannan babbar rigar taka mu wuce tare, muna shiga sai in fito,

Dariya sosai tabashi, hakan yasa shi kasa magana, shi dama babu ruwansa gashi da wasa da dariya da jiko kin sa, aiko haka princess yashige Babbar rigar Sa, kasan cewar dogaran nan kansu asama yake hakan yasa basu kula da abunda ke faruwa ba,

"Suna shiga ɗakin kafin su ƙarasa ciki ta fita daga cikin rigar tashi, wanda shi har a lokacin dariyar abun yake,"

Duba jikin Sulaim É—in Baba Waziri yayi tare da yi masa Addu'oin samun lafiya, sai bayan ya fita, kawai Saleem yaga mutum,
Kallon ta yayi sosai princess ce,

Ke waya kawo ki nan?, Saleem ya tambaya, cikin mamaki,

Gaba É—aya hankalin su ya koma kanta hadda shi kanshi Sulaim É—in,

Nazo duba yaya Sulaim ne,"

Mamaki ne bayyane saman fuskar Yarima Sultan, shin Kodai Yarin yar nan aljana ce, ya tambayi kansa taya akai ta shigo batare sa izinina ba,

Cikin nutsuwa ta ƙarasa bakin gadon, Yaya Sulaim Sannu ya jiki,?

Kallon Sulaim yayi sosai koba komai yasan Æ´an uwansa sun damu dashi, Alhamdulillah Auta kena lafiya kuwa? Idon ki yayi ja,

Cikin farin cikin yau yaya Sulaim ya kula ta sosai ta furta, lafiya ƙalau nake,"
Chapter 17 · 0% Book details