← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 90

Sashe 86

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhaima tace, Allah yasa baza ki damu da abunda zan tambaya ba, Abu na farko inason Sanin, House nawa ne acikin Estate É—in nan, Sannan Suwaye Mamallakan su?

"ÆŠan Jim Princess tayi tana kallon sama Alamar tunani, can sai tace, Gaskiya bazan iya ganewa ba, Amma mu duba Google Map zamu Iya Gani, TafaÉ—a Tare da kunna Wayar hannun ta, Tashiga Shafawa tana research,
"Yauwa matso ki gani Ma tsawa Suhaima tayi kusa da princess kaɗan, ita dai babu abunda take ga newa, saboda ba abunda take gani sai sararin Sama niya, A ƙalla, Muna da 12 House Acikin Estate ɗin nan ga Sunan kingani, Princess takai ɗan ya tsan ta saman Screen ɗin tana nunawa Suhaima, Ɗaga mata kai kawai Suhaima tayi,
"Acikin House Sha biyu, ko wanne da Sunan Mamallakin sa ajikin Titin dazai sada ka da house É—in, Kinga Æ´aÆ´an Baffa maza Tara 9 ne, kowanne acikin su yana da house a cikin estate É—in nan duk da wasu ba'anan suke zaune ba, Amma duk lokacin da suka zo To suna sauka a house É—in su, Sai House na goman shi ne na baffa, Sauran Biyun kuma babu kowa a cikin su, Babu ma Number ko suna a jikin Board É—in su, Bansan na su waye ba, Sannan acikin ko wane house akwai Part uku 3 Wani House É—in kuma part HuÉ—u 4, "Like this,
"And then, Mamallakan su, Sune kamar haka, Na farko, Baffa, Abiiy, Daddyn Canada, Uncle A, Uncle Shaddad, uncle Hasheem, Uncle Sambo, Uncle Aliyu, Uncle Mansur, "And Last Uncle Yusuf, Sune Mamallakan Amma wasu ba'anan suke ba, Yanzu haka dai Uncle Bello da Uncle A, Suna nan, Uncle Ali ne baya nan Acikin waɗan da ba a ƙasar nan Suke ba,"
Gaba É—aya bayanin Tamkar a waya take kwararo shi, saboda tanayi tana kallon wayar ta,

Nisawa Suhaima tayi Jin surutun yayi mata yawa, kuma ita duk ba wannan take son ji ba, Princess kuwa babu alamar gajiya a tattare da ita tace Yanzu sai Meye tambaya ta gaba,

"Idan babu damuwa zan iya ganin Hotunan su,?
Dariya Princess tayi, Tace To bari na Duba miki, kamar Suhaima ta tuna wani abu sai tayi saurin FaÉ—in, Ina son ganin hoton su ne don ingane Su saboda ni babu wanda nake iya ganewa a cikin su Saboda kusan kamar su É—aya, Cikin sigar wayo Suhaima tayi maganar tana Kallon princess dan ganin Reaction É—in ta,
Ita ko Murmushi tayi batare da ta kawo komai a ran taba tace to, Har cikin ranta take jin Suhaima ita dai Allah ya haɗa jinin su, Ba a matsayin ƴar aiki ta ɗau Suhaima ba, ita a matsayin ƙawa ta ɗauke ta, Duk da bata taɓa ganin fuskar taba kuma bata damu ba, don Su basa takurawa mutum akan abinda baya so ko baiyi niyya ba,"
Princess tace kinga wannan, Abiiy shine Mahaifin mu, Ya Sulaim, ya Rafiq da Taufiq, Sai Anty Suhailat sai ni Auta, ta nuna kanta Murmushi Suhaima tayi tace Ashe Rigimar ba banza ba Auta ce,
Suhaima ta gane shi, shine ta gani É—azu a parlourn Baffa,
Haka Princess ta shiga nuna mata su É—aya bayan É—aya da Suna yen su, har su mai Girma Hasheem Saida ta nuna mata, Murmushi kawai Suhaima tayi Tanajin wani abu acikin ranta, Yauwa Princess wannan waye?
Suhaima ta faÉ—a tana nuna Uncle Shaddad,
"Wannan Shine Uncle Shaddad, Bawan Allah ba ruwan shi, Baya magana, baya shiga harkar kowa, yanada matsalar tunani acikin kwakwalwar sa,
Ya taɓa samun wata Matsala ne a rayuwar sa? Suhaima ta tambaya,
"Eh Da bahaka yake ba, Nima bansan lokacin da ya koma hakan ba, ina ƙarama a lokacin da abun yasa me shi, A yadda labarin yake, Yarasa wasu mutane masu Matuƙar mahimmanci a rayuwar sa, Yasa matar sa da ƴar sa, wadda ita kaɗai, Matar shi ta haifa, sai aka kashe Matar, lokacin ƴar tana ƙarama, Ba'afi kwana Uku da rasuwar matar tasa ba, aka nemi ƴar aka rasa, wanda har zuwa wannan lokacin ba'asan inda take ba ta mutu ko tana raye, Allah masani, Haka Baffa muma yaba mu labari, Shiyasa Yakoma haka lokaci ɗaya ya daina magana yaƙi aure yafiso ya kaɗai ce shi kaɗai a ko wane lokaci, Wasu lokutan har kuka zakiga yana yi, Abun tausayi,

Kafin Suhaima ta buɗe baki tayi magana, princess Tamiƙe tare da Faɗin, Suhaima zandawo Nayi mantuwa, Ɓata jira cewar Suhaima ba ta tafi cikin sauri,

"Shiru Suhaima tayi Kamar tana Son Tuna Wani abu, Can ƙasan maƙoshin ta ta Furta, Sajeedah Gidan hajiya Fanteka Tabbas, Ita ce ƴar Wannan Uncle Shaddad ɗin..!!!

_F pen_
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS...✨�*

*_T.M.W_*✍️

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

*_TEAM FIVE STARS💫_*

*TAURARI BIYAR*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 4️⃣9⃣➖5�0⃣�

~ Suhaima ~

Shiru Suhaima tayi kamar tana Son Gano wani abu, Can ƙasan maƙoshinta ta Furta Sajeedah, Gidan hajiya Fanteka Tabbas Itace Sajeedah itace ƴar wannan Uncle Shaddad ɗin, Hanneyen Ta ta haɗe guri Ɗaya tare da ɗaga kan ta Sama Alamar Tunani,

~~~

Da sauri Anty Jamila ta taro Mama Bilki Ganin zata Faɗi ƙasa, Dafe kai Tayi cikin Tsantsar Tashin Hankali ta Furta "Mun shiga Uku Ina Aljanar Yarin yar Take Ta gudu Wallahi ta gudu Cikin Ruɗu Mama Bilki Ke maganar ko ga haɗiyar yawu bata yi"

Ido A war waje Uncle Mansur ke kallon Inda Suka É—aure Suhaima Amma babu ita ba Dalilin ta, Tashin Hankali Da ba'asa masa rana,
"Kun barni a duhu fa Wai ina Yarin yar take? Anty Jamila tafaɗa tana sakin Hannun Mama Bilki da ta ruƙo,
Wani irin Kallo Uncle Mansur yayi mata kafin yace"Ai bansan ke ma kauniya bace sai Yau Tunda bakya iya ganin abun da muke gani"
"He Excellency Sambo Yace Duk inda Yarin yar nan Take Tana cikin gidan nan Dole tana nan baza ta taɓa tsira ba"
"Nifa har yanzu bangane ba Naga lokacin da muka zo Ƙofar nan a rufe take da Kwaɗo Ga kuma key Amma Kuma kuna maganar wai ta gudu To ta ina? Anty Jamila ce ta ƙara magana Tana Kallon su Fuskar ta da Alamar koƙon to,
"Mama Bilki wadda Tunda tayi shiru gaba É—aya ta susuce, zuciyar ta Suya kawai take mata, Cikin Hassala da fushi tace Kinga Jamila yadda Idon ki Ya gane miki ba labari ba ne Muma haka muka gani, Idan baza ki iya shiru ba to ki koma gidan Mijin ki"
"Haba Mama Daga magana Kuma sai a hauni da faÉ—a Bafa ni nakar Zomon ba, Saboda ban gane ba shiyasa na tambaya, Amma.....
"Kina ƙara magana sai kin fita, Da sauri Anty jamila ta dubi Sambo Yana muzurai ganin hakan ne yasa Ta ja bakin ta tayi Tsitt,

Ina Hasheem? Mama Bilki ta Tambaya tana Duban su É—aya bayan É—aya, Da sauri suka shiga waige waige, Mamaki ne yaka masu Ganin baya nan, Babu wanda yaga fitar shi amma tabbas Sunsan tare Suka Shiga É—akin,
Fita Mama Bilki tayi Zuciyar ta a da gule Sannan, can ƙasan ranta Tafara zargin Babban ɗan nata,

Mai Girma Hasheem, Kai kawo yake Daga Bangon Kudu Zuwa na Arewa acikin Kata faran Parlourn sa na Alfarma wanda ya gama Gajiya da haɗuwa, Da kagan shi zaka gane ba'a cikin Hayyacin sa yake ba, Babban tashin hankalin sa shine Yau tsawon kwana 3 mudubin tsafin sa bai kawo haske ba, Gashi ya kasa samun Labari daga ƙungiyar su ta (SECRET SOCIETY) Yasan Hakan ba ƙaramar Matsala bace a gurin sa, Yayi sadaukar war Amma Dodon Tsafin Yaƙi Karɓar jinin,
Suhaima ce tafaɗo masa arai hakan yasa yasaki wancan tunanin ya faɗa nata, Yadda yake hango Tsantsar Tsanar sa acikin idanuwan Suhaima Yake Lokacin da take Kallon sa cikin Tsana da ƙama, Da Idanuwan ta Tamkar Mashi, Shi ba wannan ne damuwar sa ba So yake yasan wacece sannan Me Alaƙar sa da ita don yasan Tabbas akwai Matsala, Amma Yana jin ya shirya Tunkarar ta, Yana wannan Tunani Barrister Sulaiman ya shigo yasa meshi Har lokacin yana kai komo,
"Abba Lafiya Dai?
Da katawa Mai Girma Hasheem yayi Tare da Kallon sa, "Em Lafiya, Yau kaje Office kuwa? Ya Tambayi É—an nasa,
"Naje, Abba ka zauna Zamuyi magana,
Zama Mai Girma Hasheem yayi Saman Kujera mai Mazaunin Mutum Uku 3 siter ya ɗora ƙafar sa ɗaya saman ɗaya,
"Yace Ina Sauraron ka,

~LAGOS~Banana Island

Momma Momma,

"Ya Allah Waye haka Zai ƙarar min da Suna, Hajiya Bahijja tafaɗa Tana ƙoƙarin Sakkowa daga Upstairs Hannun ta Ruƙe da Jaridar Yammacin Ranar,

Kallon Sajad tayi Tare da FaÉ—in wani aiki sai kai, lpy kakemin irin wannan kira haka tamkar makaho"

"Momma, I couldn't Believe what my eyes were Seeing"

"Ƙarasa sakkowa tayi daga Upstairs, Tace me kagani, Nasan ka sarkin Gane gane da labarai"

"Sajad yace Momma wannan ba labarin banza bane abune wanda ya shafe mu, Naga ansa Yau tsawon 1 week brother bashida lafiya,"

"Brother Wane brother kuma?

"Brother Sulaim Allah Gashi yanzu nake gani,Amma Momma ko kifaÉ—a min Yadda yayi maganar tamkar zaiyi kuka,

"Banida labari gaskiya ban yadda ba mugani Tafaɗa tana karɓar wayan hannun shi,

"Bayan ta duba Miƙa masa tayi batare da tace komai ba,
Chapter 86 · 0% Book details