← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 90

Sashe 78

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarima Sultan da mamaki yake kallon, Wayar sa, JERRY sunan da ya bayyana kenan Akan screen ɗin wayar sa, Har kiran ya yanke yana mamakin, ya akai take kiran shi, ko dai batasan waye take kiraba, Baigama tunanin ba saiga wani kiran na ƙara shigowa,

ÆŠagawa yayi, batare da yace komai ba,

Hello" Hello Princess tafaÉ—a Har sau biyu, Amma shiru, Ba amsa
Hello Idan anaji na ayi magana, Bansan Number É—in waye ba shiyasa nakira, "_Hello Can you Hearing me_

"Kina da Hayaniya gaki da Damuwa, Waya baki izinin kiran Layin nan?" daga can ƙasan maƙoshin sa yayi maganar tamkar mai ciwon baki,"

Laaa laaa Yaya Yarima, Barka da Dare Tuba nake Ayimin Afuwa,
Ya Yarima Allah kai na Musamman ne, Komai naka daban ne, _You are Special_
Nifa bansan kaina kira ba Kayi Haƙuri bansan Number ɗin waye ba shiyasa nakira don tabbatar wa,

Yaushe Nafara Wasa dake,?

Tuba nake Ranka ya daÉ—e, Allah bansan Number É—in waye bane, Kuma É—azun nazo Part É—in yaya Sulaim, Inason na tambaye ku ba'aga wata bane har yanzu, sai na tadda bakwanan,

Ya Yarima nagode Sosai Allah ya jazamanin ka, Alkairin Allah ya lulluɓeka a gaba ɗaya rayuwar ka, Kasan me yanzu Sabbin wayana biyu, Uncle Bello yasiyamin Sabuwa jiya, Gashi kaima Haka, mantawa nayi da kyautar Tunda na cire zuben shiyasa banbuɗe ba tun tuni sai yau,"

Sosai yaji daɗin Addu'ar da tayi masa, Jiyayi ɓacin ransa na sauka Sannu a hankali,
Haya niyar ki na damuna, Zaki samun ciwon kai ne? Yarima Sultan yafaÉ—a yana É—an haÉ—e rai kamar tana gaban sa,"

Sorry Ya Yarima Dama Allah ne ya dubeni na samu Number ɗinka, Da A daran nan driver zai kawoni nayi maka godiya, ina ƙara godiya sosai Ya Yarima,

Godiyar ta isa haka, cikin zuciyar shi ya furta hakan, Abunda ya lura dashi ɗabi'ar Family ɗin suce haka suna da Yawan godiya duk ƙanƙantar kyauta, wadda a zahiri ma sunfi ƙarfin ta,"

Jin yayi Shiru yasa Princess FaÉ—in Ya Yarima,"

"Ya Rabbi Wai yaushe nazama ya yanki ne? Banson kalan dangi,"

Cikin Shagwaɓa princess tace, Allah kai yaya nane kuma ni ina yayan dakai, koda kaibaza kayi ƙanwar dani ba, kuma Allah saina faɗawa ummeetha kace baka ƙawa dani"

Sosai yadda tayi maganar yaso bashi dariya sai kuma ya Basar, Yace To naji inda ake dole, ni ƙanwata Suhailat ce kawai, Idan kuwa kika ƙara kirana da ya yanki, sainasa, Anzane ki na tsawon kwana bakwai,"

Zaro ido waje princess tayi tamkar yana kallon ta, Please kayi haƙuri bazan ƙara ba,"

Dariya Yarima Sultan yayi, Yadda ba zataji ba, _Better_ kinte maki kanki,
Maza ki kwanta yanzu,
yana FaÉ—in haka ya katse kiran batare da ya jira cewar taba,"
Wani irin nishaÉ—i Yarima Sultan ya tsinci kanshi aciki gaba É—aya ya nemi damuwar sa ya rasa, Jiyayi dama ya cigaba da sauraron Shirmanta,
Da haka ya fita daga cikin motar Yanufi parlour kai tsaye, Baiyi tsammanin ganin Aminin nasa a parlourn ba, Sallama É—auke a bakin sa haka ya shiga,

Amsawa Sulaim yayi yana Kallon Sultan É—in,
"Saraki ina ka zauna ne?

Murmushi Sultan yayi najin daɗin ganin Aminin sa lafiya tare da ƙoƙarin ɓoye tashi damuwar don kada Sulaim ɗin ya gane wani abu,
"Barka da hutawa Aminina Allah yasa kana cikin farin ciki, ina cikin mota fitowa ta kenan,"

Sulaim yace, Wani abuna damun Saraki, Allah yasa lafiya,

Murmushi Sultan yayi, babu komai Ina lafiya kamar kai,

Sulaim
Kofin Coffee ɗin dake gabansa ya ɗauka ya kai baki, sannan ya ajiye, Banma san Yaushe kafara ɓoyemin Damuwar kaba,

Yarima Sultan har ya daina mamakin Sulaim yanzu, Saboda Koda yana dariya yana murmushi matuƙar akwai wata damuwa a ranshi wadda koda ta kwana biyu, ko Ba azahiraba waya kawai sukai sai Sulaim ya gane, Abun nashi da har tsoro yake bashi kamar wani Malamin duba, Amma yanzu ya daina mamakin, ya alaƙanta hakan da girman abotar su ne kawai dakuma sha ƙuwa,"
"Shikenan Sultan na neman Afuwa Ga Amininan sa, Insha Allah zamu zauna dan tattaunawa akan hakan"

Kallon su suka mayar Kan Samrat wanda ke sakkowa daga Upstairs hannun sa ruƙe da waya, da alama Chat yake mai daɗi, Saboda Annurin dake bayyane saman Fuskar sa,

Ƙarasa sakkowa yayi, tare da faɗin Barkan ku da hutawa, Allah yasa kuna cikin Aminci,

Yarima Sultan yace, Barka dai muna lafiya, Sarkin Chat Daddyn Soyayya, Da'alama an hau saman Network,"

Samrat
Saida yasamu guri Kusa da Sulaim ya zauna kafin yace, Prince kenan Bakasan Halin danake ciki ba yanzu,

Shattima Meye yake damun ka? Sultan ya tambaye shi cikin kulawa,

Ajiyar Zuciya Shattima ya sauke yajingina bayan shi, jikin kujerar, Yace Prince nafaÉ—a Wallahi nafaÉ—a,

What kafaÉ—a kuma, Ina? A wannan karon Sulaim ne yayi tambayar,

Saida Samrat yayi murmushi ganin duk sundawo da hankin su kanshi,"
Ya kalli Sulaim yace, (MAN) Nasan baza ku fahimta ba Amma tabbas na faɗa, Duk Ƙauna da soyayyar da Ƴan mata kenuna min, Kawai ina ɗan kula wasu daga cikin sune Saboda kada su faɗa wani hali, Bawai don ni ɗin ina son suba,
Amma gashi Acikin Ƴan kwanakin nan Nafaɗa ma tsananciyar soyayyar wata yarinya, Wadda bansanta ba bansan a inda take ba, pic ɗin ta kawai nagani, Amma ji nake idan narasa ta zan iya zaucewa, Ashe ada Abota nasani Bawai Soyayya ba"

Wani irin Naushi Sulaim Yakai masa A gefan hannun sa wanda Badon Allah yasa yayi saurin kaucewa ba, daya karya masa kafaÉ—a,

Yarima Sultan shima duka yakaimasa anashi ɓangaran, Shima cikin rashin Sa'a bai sameshiba, Saboda wani irin tsalle da Samrat ɗin yayi yana dariya,
"Au yanzu Saboda na faÉ—a muku sirrin raina shine zaku haÉ—u ku kasheni, Wallahi da Annata tayi shari'a daku,"

ANNA shine sunan dayake kiran mahaifiyarsa dashi, wato (Kilishi Aziza)

Yarima Sultan yace Ashe dama kai É—an iska ne bansani ba, Aiko Anna idan taji wannan ita dakanta zata sa mu huraka, Baccin ka maida mu sakar karu, shine zaka zauna kana faÉ—a mana kafaÉ—a ko Allah yasa ruwan maliya kafaÉ—a ba Soyayya ba,

Sulaim kuwa saboda tsabar takaici ya kasa ma magana, Laptop É—insa ya janyo, yabuÉ—e wanda shi bai san ma abunda zaiyi acikiba tsabar haushi NE Yasa shi buÉ—eta,

Samrat wanda ke tsaye daga can gefe, tun tsallan da yayi yafita daga cikin su, magana yafara cikin dariya wanda ba ƙaramin kyau dariya keƙara masaba, wanda har wushiryar sa dake tsakanin haƙuran sa ta gefe saida ta bayyana,
"You Guys dama haka kuke, Wallahi bawasa nake muku ba Nafaɗa ƙaunar ta, Gashi bansanta ba inaso kutayani samun Mafita, tacemin acikin garin Kano ɗin nan take, Amma naga kun tasomin kamar wasu mayun watan zakuna, To, Anna tana sona bata shirya rasa Shalelen taba,"

Allah idan ka ƙara cewa kafaɗa ɗin nan sainasa an ɗaure ka, Idan bama kaiba waye yake soyayya da wadda bai sani ba baisan asalin taba, maybe ma Aljana ce,

Prince, bakasan Meye so ba sai Allah ya jarab ceka da son wata zaka gane hakan saima idan ita bata sonka gwara ni yanzu Wannan masoyiyar tawa tana Sona, idan kace aljana ce, ba mamaki, Saboda kyanta ba irin na mutane bane, kafin kasamu kamar ta saika tona,

Kallon bakada hankali Yarima Sultan keye wa Shattima, To naji, Amma ya sunan ta?

Da sauri Samrat yadafe goshi tare da FaÉ—in _Oh God Allah niban masan Sunan taba No Name_ Amma dai nafaÉ—a, yana kaiwa nan ya haura Upstairs da sauri yana dariya,"

*Saleema*
Ƙawata Yanzu tafiya, zakiyi?

Maleeka tace, To Amarya idan ban tafiba kwana kikeso nayi anan, Yanzu dai Gaskiya Namiki Murnar Samun Sulaim É—inki,

ÆŠan far Saleema tayi da ido tace Emm kedai bari Wai damma biki ganshi ba Amma zantura miki hoton sa, Ta waya Anan zaki gane waye Ya Sulaim danake faÉ—a miki kullum Zake gane nafi ko wace mace sa'a a duniya,

Eye lallai to Shikenan inajira, Yanzu dai Nima nawa Sadaukin Na mota yana jirana, Kinga dare yana ƙara yi, da Wannan Estate ɗin naku da mutum sai ya ɓace acikin sa bai saniba, Amma Saleema karki manta da Shawarar dana baki Ki jarraba kigani, Maleeka takai ƙarshan Maganar Suka sa dariya A tare,

"Na gode da ziyara zanyi komai yadda kikace, ki gaida Khaleel É—in naki,"

Saida Saleema ta raka ta har Gurin Su mommy tayi musu Sallama kafin ta kai ta bakin ƙofar shigowa parlourn, ta tafi ita kuma ta juya ciki,
Saleema fa kai ya ƙara girma, Gani take gaba ɗaya Ta mallaki Sulaim hakan yasa Ko magana bata fiyaye sosai ba, Batare da tabi takan kowa dake Parlourn ba ta wuce Sama abunta, Gimbiya Sultana ce tafaɗo mata arai, Take taji bari takirata ta sanar mata,"

"Bugu É—aya gimbiya Sultan ta É—aga kamar mejira," Hello Wallahi Bello Arab bakida Kirki Ashe har zaki iya Tafiya bikimin sallama ba"

Saleema tace Ayya to kiyi haƙuri mana kiji Meye Uziri na, naji kamar kina cikin farin ciki,

To inaji dama yanzu fa zankira ki sai kuma ga kiranki, Ina so inyi miki Albishir kafin kiji Abakin wasu, Yarima Sultan yazama mallakin Gimbiya Sultana,

Saleema ta furta Wow Sultana really?
Ai duk abu É—aya ne abakin namu, Nima nazama Mallaki Ya Sulaim, daga nan zuwa 2 months Amma Gaskiya namiki Murna,"

Da gaske mana, Amma wane Sulaim ÆŠin? Badai Aminin Sultan ba,

Shi mana, kinsan ai Cousin Brother nane, Saleema tafaÉ—a cikin NishaÉ—i dajin daÉ—i,"

Ɗil Ɗil, Gimbiya Sultana ta katse kiran batare da tace komai ba, Da mamaki Saleema ta ɗauke wayar daga Kunnan ta Jin Sultana ta katse mata kira, kallon Screen ɗin wayar take cike da mamaki, Can kuma ta taɓe baki tare da ɗaga kafaɗa irin na _I don't care_ ɗin nan,"

*Suhaima*
Har ƙara juyawa take, Tana kallon Uncle Shaddad, Wanda take mamakin Meye yake a zaune shi kaɗai Acikin dare, Gashi babu kowa a kusa dashi ko waya babu A hannun sa bare tace wani abun yake,
Tabbas ta gane shi tasha ganinshi shi kaɗai a zaune gashi baya magana, Bata taɓa kawo komai a rantaba sai yau, ko dai yanada damuwa ne? Tayiwa kanta Tambayar, Take taji tana son Jin wani abu akan shi,
Chapter 78 · 0% Book details