← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 90

Sashe 89

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kena son shiga rayuwa ta, Shinke wace?" That's last Question About who are you,"
"Good it's the only solution, da haka kayi da tuni ka huta, Zan ƙara faɗa maka Sanin koni wace ce bashida wani amfani a gurin kowa dake Cikin Ahalin ka,"
"Murmushin gefan baki Sulaim yayi Yace, Kin temakeni Nasani, Amma ban saki ba, Saboda rayuwa tace,
"Tamkar shirme na ɗauki wannan maganar, Saboda, Idan na bari Ka mutu a hannun wasu ai nayi asara, Daga nan har zuwa wani lokaci Matuƙar ina raye bakai ba koma waye bazan bari Wani abu yasa meshi nabari ya cutu Kuma ina da yadda zanyi, bazan bari hakan ya faru ba, sai idan kwanan mutum ne ya ƙare ba yadda muka iya da ƙaddara, Zan kula da kowa, Saboda inaso komai ya ƙasan ce na musamman kuma faruwar hakan ya zama a hannu na, Ita fansa a jini take yawo, har sai lokacin da aka aiwatar sannan ake samun salama, amma ba kowa ke gane hakan ba Ɗan halak kaɗai kijin hakan,
Zanso kayi farin ciki na wani É—an lokaci Saboda ku É—in Fansar rayuka ne,

"Idan ki kai magana da yawa, Kaina zaiyi ciwo bana son hayaniya,
"Murmushi mai Sauti Suhaima tayi Kafin tace karka Damu, Shima wannan Lokaci ne kuma za kadai naji,
"Ban yadda dake ba kullum Fuska a rufe, Sulaim ya faɗa yana kallon wata Flower data zuba Furanni ƙana na,
"Kamar yadda nima ban yadda dakai ba, ba mamaki nice baka yadda dani ba, To ni kowa ma ban yadda dashi ba, Tana kaiwa nan Ta miƙe ta nufi Hanyar fita daga Gurin,

Bayan Ta tafi ya daÉ—e a gurin kafin shima ya tashi, Zuciyar sa Fal Da tunanin Kala kala game da Suhaima,
Baya Son ganin Yarin yar Sam Amma koda yaushe Ta tsaya masa a rai,
A gogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun sa ya duba ganin dare ya ja, Yanufi ciki A parlourn Sama ya samu Yarima Sultan Zaune Mulkin nan ya Motsa Rannan a haɗe, ƙarasawa Sulaim yayi kusa da shi Sosai ya zauna,
Kallon shi Yarima Sultan yayi, Yace "Amini na me matsalar ka?
Murmushi Sulaim Yayi yace"Nothing is wrong with me" Kana son yimin wayo Saboda kasan naga damuwa A tattare da kai ko,
Shima Sultan É—in murmushi yayi, yace Nima Lafiya kamar kai, Gobe zan koma Masarautar Gabas insha Allah,
Da sauri Sulaim ya ruƙo hannun Sultan yace, Aminina Munyi maka laifi ne?
"Dariya Sultan yayi, Yace Gaskiya Dr. Kana da Matsala, Meye na Shiga damuwa, Yanzu haka Ba jimawa Ummul Bait Ta kira ni Tace, Inzo gida Gobe, Bata Saurare niba ta kashe wayar, Gashi inason Fara shirin komawa South Korea 🇰🇷 Saboda aiki na, Ɗan Jim Yarima Sultan yayi Fuskar sa ta ƙara Bayyana damuwa ƙarara,
"Calm down Saraki Komai Mai sauƙi ne, kar kadamu" We are together At Any moment"
"I know, Muna Tare Amma Bana son Maganar auran nan, kuma Nasan shine Dalilin kiran,
"Shiru Sulaim yayi Don shi har ga Allah ya ma manta dawani batun Auren da Aka sa,
"Wace Zaka Aura?
"Yarima Sultan yace, Sultana, Da ita suka haÉ—ani,
"Kallon Shi sosai Sulaim yayi, jin kusan damuwar Su É—aya da Aminin nasa, Yace Amma baka son tane?
"Shiru Sultan yayi, har saida Sulaim ya ƙara Magana, "ina jinka Kafaɗa min mana,
"Just Bata cikin tsarin irin Matan da nake so, At all Batsari na bace kuma ni bana son ƙaramar Mace, Shekarun ta Basu kai irin yadda nake so ba,
Dariya Sulaim yayi, Saraki Duk bansan wannan ba, idan Shekarun Sultana Sunyi Kaɗan Ƴar shekara nawa kake so?
"Hhm Aminina Baza ka gane ba, Sam Bata cikin Tsari na ne, Bazai ma yiyuba Wallahi."_I Must warn this girl. If She Doesn't say she's cancelling this Marriage, then Surely, she will Regret marrying me_"
"Dafa ƙafaɗar shi Sulaim yayi, Yace kayi haƙuri Saraki Bayayya ga iyaye Dole Na Tabbata Baza suyi komai don su cutar damu ba, ina so kada kayi wani yunƙuri, kamiƙa komai ga Allah, zanso kasaki Ranka kayi Farin ciki, Sultana zata iya zama yadda kake so bayan Auren ko, Emm"
"Murmushin yaƙe Sultan yayi, tare da faɗi komai Ya wuce Amma dole sai na fara jamata kunne, ta janye maganar auren Da kanta idan ba haka ba zata ga abunda bata so, Yanzu kai ya maganar naka Aure, Har yanzu banga Saleeman ba,
"ÆŠaure Fuska Sulaim yayi Tamau, Nifa ban tsara Wani aure yanzu ba, Inada plan da yawa sai na fara gyara aiki na Sannan komai zaimin dai dai, Ita fa wannan Yarin yar Tanada Damuwa, Ga hayaniya tana son takura min, Ban masan ta yadda zan iya zama da ita ba,
"Idan ka nuna baka so Zata bari, Yarima Sultan yafaÉ—a yana kallon sa,
"Oh Matsalar ta ne, Ni ba ruwa na Idan suka ajiye ta ta gaji da zama Dole zata tafi, Saboda bazan taɓa iya Cutar da jinin Uncle Bello ba, kuma ƙanwa ga, Saleem ɗina" Kawai bana son wani Aure gaba ɗaya yanzu, ba da ita ba koma da wace,

A haka Suka Cigaba da Hirar su Cikin nuna Kulawa da damuwar Juna, Daga yadda Suke Maganganun zaka fahimci Gaba É—ayan su basa Son auren, Sai da Dare ya raba sosai har lokacin, Samrat da Sajad basu dawo ba,

Tunda ga Wannan rana Kullum Sulaim da Suhaima sai sun haɗu a wannan Garden ɗin, Dama Sulaim, Yana Son kaɗai cewa shi kaɗai Duk lokacin da yake baƙatar hakan wannan Garden ɗin ne wajan zuwan sa, Sai Allah yasa wa Son Gurin Itama Kullum idan bata jeba Sai taji duk babu daɗi,
Wata rana ya riga ta zuwa wata rana ta riga shi zuwa, Basa kula juna wata rana kuma sukan yi magana jefe jefe, Har sai ran kowa ya ɓaci acikin su, Sulaim yarasa dalilin Ɗaya sa ta shike son shiga rayuwar sa, ita kuma ta rasa dalilin daya Kullum yake Bibiyar ta,

***Niko Nace Lallai Suhaima Sannu da ƙoƙari kizo har part ɗin Mutum Kuma ki ringa tunanin ya na bibiyar ki😂***

~ Barrister Sulaiman ~
"Haba Beb dan Allah kiyi haƙuri yanzu idan kika tafi ina zakije Nace miki fa, Ana ɗaura aure na da Sabrina zan mai dake gida Sannan babu wanda ya isa ya hana ni zama dake Tunda a yanzu kin zama mallaki na,"

Cikin Zafin rai, khaltum ta Fizge hannun ta, cikin Kuka ta furta, Gaskiya Nidai ka mai dani ko kabar ni natafi yau kusan Tsawon Wata guda Ina cikin wannan ƙaton gidan ni kaɗai wata rana Ka kwana wata rana kabar ni ni kaɗai, ina kake so na tsoma raina Karaba ni da ƴar uwa ta yanzu nasan kullum cikin ne mana take don baza ta taɓa gajiya ba, Tunda mun riga munyi Aure kawai mu koma, cikin Kuka Mai sauti takai ƙarshan maganar,

"Oh my god, Beb Kiyi shiru kukan ki na tadamin hankali kinsan ina son ki, Zama mu koma Soon Bawani long time NE ba, ko two weeks bazai kai ba, kuma ina tare dake, yanzu idan muka je ke a matsayin mata ta, akwai damuwa ne,
Yanzu kin haƙura ko? Zan siya miki duk abunda kike so ko Meye shi matuƙar da kuɗi ake siya,
Da sauri Khaltum ta goge hawayen idon ta tare da washe baki, To Shikenan na haƙura amma yanzu ka kaini inda mukaje ran nan ɗin nan,
Murmushi Barrister Sulaiman yayi don ya gane inda take nufi, Gaba É—aya yagama gano Khaltum Indai da abun duniya to tabbas mantawa take da komai, amma shi son gaskiya yake yi mata,
"Yauwa yanzu naji kince na Rabaki da Æ´ar uwar ki, Dama kina da Æ´ar uwa a cikin Estate É—in mu?
"Cikin dabir dabir tace, A'a Kawai ba ruÉ—e ne shiya Amma bani da kowa, Maganar Suhaima ce ta dawo mata cikin kai, wanda tace mata katta sake ta bari wani yasan su biyu ne,
"Ɗaga ƙafa ɗaya yayi tare da taɓa baki, OK yanzu ki shirya sai mu tafi ko?
Tun kafin yagama rufe baki Khaltum ta Nufi bedroom É—in ta da gudu, ta faÉ—a toilet, Shikam Murmushi kawai yayi,

~ Suhaima ~
A yau kiran da tayiwa wayar Mother yafi ÆŠari, Take tausayin kanta ya kamata, tafara tunanin ta yadda zataje Garin su can Bichi Don Duba halin da mother É—in take ciki, Abun ya fara bata tsoro, a iya sanin ta Mother bata kashe wayar ta, Kuma Ta tabbata ba rashin Caji bane, Don Basuda matsalar wuta, Koda matsala ta samu A iya Tsawon Kwanakin nan sana da wata ÆŠaya ai yaci ace ko gurin masu caji take,
Tuni jikin Suhaima ya bata ba lafiya ba, Khaltum ce ta faɗo mata a rai Kasa daure wa tayi Wasu siraran hawaye suka zubo nata, Yanzu Shi kenan na zama ni kaɗai, Khaltum ina kika shiga Me yasa zakimin haka Why khaltum, kar kibari Arabamu ina tare dake, Sosai Suhaima tashiga sun bato ita kaɗai, daga ƙarshe ta yanke Shawarar Duk yadda zatayi wajan Zuwa Bichi sai tayi don Dubu mother ko zuciyar ta Ta samu salama,
A yanzu ji take komai yazo ƙarshe tagama gano komai da kowa acikin Estate ɗin jira kawai take lokacin fara gabatar da hukunci yayi, kuma bata son fara ai wayar da komai Sai ta fara faɗa wa mother,"

*BARNO STATE*
_Masarautar Gabas_
Gaba ɗaya hankalin kowa dake cikin Masarautar, Ya koma Gurin shirye shiryen biki Sosai kowa ne ɓangare an kaca me da hidima, ko wane sashe da irin shirye shiryen da Suke,
Gaba É—aya hankalin kowa ya koma gurin shagalin Bikin Yarima Sultan da gimbiya Sultana, Yarima Safwan da Gimbiya Shaheeda,
Mai Martaba yabada umarnin A faɗawa Ummu Mu'azzam Mahaifiyar Su Gimbiya shaheedah, An bata izinin halartar bikin ƴar ta, Amma baza ta wuce kwana uku ba, lokacin da saƙon ya risketa Ba laifi taji daɗin hakan, Tunda batasa rai da wannan alfarmar ba, Itako Gimbiya Shaheeda sosai tayi baƙin ciki Ace wai Mahaifiyar ta Sai an bata izinin Zuwa shagalin Auran ta kuma shima sai an ƙa'ide mata kwanankin da zata yi,
Ji tayi ai kodan wannan wulaƙancin sai tasan yadda tayi Mulki ya dawo hannu yayan ta mu'azzam kodan jin daɗin Mahaifiyar ta,
Chapter 89 · 0% Book details