← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 90

Sashe 4

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranka ya daɗe tana sa shen kilishi Aziza, sunan ta Bahijjah, sannan ba ƴar kowa bace, Mahaifin ta Allah yayi masa rasuwa, sakamakon faɗan ƙabilanci da akayi a nahiyar su, Yanzu ita da Mahaifiyar tane suna aiki, a gidan su abokina wanda naje ɗaurin auran sa Mali,
Da fari nayi niyar tahowa da su daga bayan idan kun amince sun ƴan tu daga wahala, sai a ɗaura mana aure, to bisa al'adar garin mutum ɓako baya tafiya da ɗan garin kowa wanda ke zaune a garin, sai dai idan auran ta mutum zaiyi shine zai iya tafiya da ita, ganin irin halin da suke ciki ne na tausaya musu sosai shiyasa na amince a ɗaura auran sai mu taho tare, yakai ƙarshen maganar cike girmama da nutsuwa,

Zaka iya tafiya, sarki ya faɗa a taƙaice,

Russuna wa yayi sosai tare da Faɗin Allah yasa mai martaba bazai yi fushi dani ba domin hakan zai cutar da ni matuƙar cutarwa nabar ku lafiya, ya tashi jiki a saɓule babu kwari, saboda baya son ganin fushin iyayan nasa Sam, Faransa yana ayyana yashirya karɓar duk wani hukunci daga Alƙalan fada, hakan baidameshi ba, amma dai kome za ayi bazai iya ra buwa da matar saba wadda ganin farko yakamu da tsananin son ta, daga shekaran jiya zuwa Yau amma ji yake idan akarabasu tabbas ƙarshan rayuwar sa yazo,

Mai martaba yabi bayan ɗan nasa da kallon sannan yayi wani irin murmushin girma, harcikin ransa yana ƙaunar Yusuf sosai, kaf cikin ƴaƴan sa idan aka cire Aziza itama saboda ba Mahaifiyar tane,
Yasan Yusuf akwai gaskiya gashi da amana bashida son zuciya kamar ƴan uwan sa shiyasa afi shiga ransa sama da kowa acikin su, dole yasan Alƙalan Fada zasu yi hukunci amma dole zai nema wa ɗan nasa sassauci kan a rangwan tamasa.!!!

*_F pen's_*✍️
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _Typing📲_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALIN MU ÆŠAYA_*

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

*_Fatima Y zakariyya👌_*
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

*_Ina mai farin cikin sake haɗuwa daku a cikin Littafin AHALIN MU ƊAYA. Kashi na biyu, ina roƙon Allah ya amfanar da mu abin da ke cikin sa, akasin haka kuma da kuskure na ku watsar dashi gefe, saboda nima mutum ce kamar kowa zanyi dai dai zanyi kuskure, domin ɗan Adam ajizi ne, Allah ya shiga dukkan lamuran mu yayi mana jagoran ci_*

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 5️⃣�6️⃣📖

Kamar yadda Yusuf yayi tsammani hakan ne ya faru saboda Hajiya Baitu, ta buga ƙasa tayi tsalle tace ita sam sam bazata yadda da wannan auran ba, sai Yusuf yasaki matar sa Bahijjah,
Sosai mai martaba ya fahimtar da ita kan ta kwantar da hankalin ta amma tace ina ita fa bazata yadda da wannan ba, sai dai Yusuf yazaɓa ko ita ko matar shi,

Bawan Allah a lokacin baƙaramin tashin hankali ya shiga ba,

Mahaifin su ya kwantar mai da hankali kan cewa babu abunda zai rabashi da matar sa sai Allah, hakan kesawa ya É—an samu nutsuwa,

Sanda munafukai suka kaiwa Hajiya Baitu labarin, yarin yar da Yusuf ya aura, Æ´an gudun Hijira ne ita da mahaifiyar ta, sannan ba Æ´ar kowa bace aikin wanke-wanke da shara suke yi,

Take Hajiya Baitu tasa aka kira mata Yusuf É—in saboda tsabar tashin hankalin da take ciki, yana zuwa tabashi umarnin sakin Matar shi Bahijjah, ko kuma ta tsine masa, saboda ta tsani talaka batason koda haÉ—a hanya dashi ne bare har su zauna inuwa É—aya,

Aganin ta hakan shine mafita, tana tunanin zaijayo mata abun kunya, da surutu acikin masarautar,

Bisa al'adar masarautar babu sakin aure idan batare da kwakkwaran dalili ba,

Cikin tsananin tashin hankali Yusuf yake neman afuwar Mahaifiyar tashi da ta sassauta masa amma bazai iya sakin matar shiba,

Koda buÉ—ar bakin ta, sai cewa tai, Magaji idan har kaga matar ka ta zauna zaman aure a masarautar nan tu tabbas bana raye,

Saboda É—an fari ne shiyasa bata iya kiran sunan sa saidai tace magajin sarki ko kuma magaji kawai,

Ɓangaran Giwar sarki kuwa ita ma hankalin ta duk ya tashi saboda auran Yusuf ɗin, ada tana ta farin ciki yaƙi aure, to yanzu gashi yayi idan kuma haka ne to dole shizai gaji mahaifin sa, ba ɗan ta Abdullahi ba wanda saboda yazama magajin sarki, tayi masa auran wuri amma gashi tsarin ta ya rushe,

Ita ko Bahijjah da Mahaifiyar ta wadda take kira da ummee sa'ada da kagansu kaga jinin Larabawa, Dan ma wahalar rayuwa ta maida su abin tausayi,
Amma alhamdulillah suna samun komai najin daɗin rayuwa yadda yakamata agurin Aziza wanda acikin masarautar take auran ɗan ƙanin mahaifin su, sosai take bawa su Bahijjah kulawa saboda Yusuf yabata labarin komai, saboda tausayi har saida tayi kwalla ta tausaya musu matuƙa,
Bugu daƙari tana ƙaunar ɗan uwan nata Yusuf sosai duk cikin su tafi shaƙuwa dashi, duk wata shawarar ta dashi takeyi shima kuma nasa ɓangaran haka ne,

Har zuwa lokacin Hajiya Baitu taƙi yadda da auran Yusuf da Bahijjah,

wanda ita Bahijjan batasan wainar da ake toyawa ba acikin masarautar,
Bugu da ƙari bata ganin Yusuf ɗin kullum saitayi kwana biyu bata ganshi ba saidai bata taɓa damuwa ba saboda Aziza kullum saitaje ɓangaran da suke har taɗan jasu da hira tare da ƙara kwantar musu da hankali duk da ba sa wani fahimtar mai take cewa sosai kasan cewar bata jin Hausa yadda ya kamata wani abun zataji amma baza ta iya mai dawa ba sai kaɗan kaɗan,
Ita ku Mahaifiyar tata bata ji kwata kwata kur mace, wanda ada tana magana kamar kowa sannan tanaji kamar kowa, lokaci ɗaya ta koma haka tun faɗan ƙabilancin da akayi a kyauyen su, ta rasa ɗan ta mafi soyuwa a gare ta sannan ta rasa jigon rayuwar ta mijin ta, shikenan ta koma kurma bata ji bata mayar wa,

Hakan yasa Bahijjan bata damuwa saboda dama ita bawani sabawa tayi dashi Yusuf ɗin ba, batasan Meye soyayya ba soyayya ɗaya tasani itace ta iyayen ta sai kuma ɗan uwanta tilo da ta rasa a rayuwar ta hakan yasa take jin wani ɓangaran na zuciyar ta na sanar mata baza ta taɓa samun maka manciyar wannan soyayyar ba, ita dama babban dalilin ta na auran shine saboda mahaifiyar tane, tasamu hutu a rayuwa, ganin auran take tamkar almara,

A kullum tunanin sa ɗaya Bahijjah baya son kullum ya ringa zirga-zirga a sashen Aziza har mutanan masarautar su fahimci wani abu saboda babu wanda yasan inda matar Yusuf ɗin take, kawai sun sandai yayi aure amma ba wanda ya taɓa ganin matar sai Gimbiya Aziza,
Yafi son sai komai ya dai dai ta daga ɓangaran Hajiya Baitu, tare da jin hukuncin al'ƙalan fada, wanda sunkai tsawon kwana uku suna zama kan maganar auran da zartar da hukuncin da ya dace,

Bayan alƙalan fada sun yanke hukunci, hukuncin da yakawo surutai kala kala acikin masarautar, wasu yayi musu daɗi wasu kam bahaka suka soba,

Lokacin da labari ya riski Yusuf na hukuncin da aka yanke masa cewar Bazai ƙara fita daga ƙasar Nigeria ba zuwa ko wace ƙasa har na tsawon shekara 20, yaji babu daɗi sosai amma da ya tuna, akwai farin cikin ransa atare dashi wato Bahijjah sai yaji komai yawuce Bakomai zai iya haƙurin zama koda kuwa har ƙarshan rayuwar sane,

Wannan kenan

A daran ranar da a kasanar da bikin tariyar matar Yarima Yusuf, a daran Hajiya Baitu tace ga garin kunan,
Yusuf yayi kuka sosai na rashin Mahaifiyar su, sannan yaɗora alhakin mutuwar tata akan shi saboda yaƙibin umarnin ta na sakin matar shi, shikuma yana bin umarnin mai martaba ne, wanda yace duk runtsi bai yadda ya rabu da itaba, koda bayan ranshi ne saidai ita Hajiya Baitun ta haƙura da nata auran ƙarshe mai faruwa ta faru,

Tunda ga wannan rana Murtala ƙanin Yusuf ya ƙara tsanar ɗan uwan nasa saboda yana ganin shine silar kashe musu Mahaifiya tundaga nan ya ɗau alwashin ganin bayan Yusuf ɗin tare da iyalin sa,
Gimbiya Aziza itama tayi kuka sosai wanda har saida hakan yaja mata rashin lafiya mai tsanani kafin Allah yabata lafiya amma ita Sam bata É—ora wa Yusuf laifin komai ba, cewar ta lokaci ne yayi,

Saboda rasuwar aka ɗaga tariyar Bahijjah a ɓangaran da sarki yasa aka gyarawa Yusuf ɗin idan zai zauna da iyalin sa, kamar yadda ya mallakawa sauran ƴaƴan nasa mahalli a wani ɓangare na masarautar,

_BAYAN WATA ÆŠAYA_

Sarki Adam shareef ya sanar da MURABIS É—in sa sannan ya maida É—an sa Yusuf a madadin sa, zai hau karagar sa ta mulki,
Sannan ya tabbar da ranar tariyar Bahijjah itace ranar da za anaÉ—a Yusuf amatsayin sarki a masarautar Gabas,

Ba iya cikin masarautar ba hatta masarautun dake makwaf taka dasu saida suka É—auka da surutai kala kala, kowa nason jin Meye dalilin yin MURABIS É—in sarki adam,
Hankalin mutane dayawa ya tashi acikin masarautar, ɓangaran giwar sarki ba a magana, Tunda taji labarin MURABIS ɗin mai martaba kawai tasa aranta ai ɗanta Abdullahi shi zai maye gurbin sarki amma ina saitaji akasin haka,
Saida ta suma yakai sau 4 ko 5 cikin ƙanƙanin lokaci taba zama wajan malamai tsibbu da bokaye,

Shiku sarki ya toshe kunnuwan sa baya jin komai yaƙi ɗaukar shawarar kowa, sannan yaƙi faɗa wa kowa Meye dalilin sa nayin hakan,
Shi kaɗai yasan abunda ya hango, yasan idan har ya bari sai ya mutu za ayi sabon naɗi, to tabbas akwai gagarumar ƙura da tashin hankali da zalunci haɗi da maguɗi wajan ɗora wanda bai daceba tare da raban kan iyalin sa shiyasa yayi hakan wanda dama shi ya daɗe yana son yayi MURABIS ɗin yaɗora Yusuf to ganin bashida aure shiyasa bai taɓa tada maganar ba,
Chapter 4 · 0% Book details