← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 90

Sashe 73

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhaima nasan zaki iya saboda nafi kowa sanin koke wace, Amma kisani bantura ku don ku temaka wa ɗaya daga cikin Mutanan gidan nan ba, bari intuna miki fansace ta kai ku, kar kimanta wannan Duk wannan ƙulle ƙullen Sharrin Makirci ne da Sihiri, Daga yadda naji labarin yanzu nafahimci hakan, To wannan matsalar suce idan sun so suƙone kawunan su, bance kitemaki ko mutum ɗaya acikin suba, kibar su da Zaluncin su, ki tabbata abunda ya kaiku shine zaki tun kara, Baruwan ki da kunce wani ɗauri ko makirci,

Jin ana Biga ƙofa Suhaima saurin Faɗin Mother Ina zuwa zanƙara kira"

Lafiya dai ko? Mother tafaÉ—a itama da sauri,

Suhaima tace Eh lafiya ta katse wayar taɗau ƙaton hijabinta ta zura,

Tana buɗewa taga hajiya Umma ce kamar yadda tayi Tsammani, barka da dawo wa Tayi mata, sannan suka ƙarasa cikin parlourn, hajiya Umma ta shaida wa Suhaima Cewar Daga Gobe tana so tafara yiwa Sulaim Girki A part ɗin sa, Shiru Suhaima tayi batace komai ba iya kacin to data ce,"
Saƙon gajerene hakan yasa Hajiya Umma nagama Faɗa ta wuce Upstairs Tabar Suhaima Anan,

Tunani ne kala kala, Suka haɗewa Suhaima tama rasa wanne zatayi, Maganganun Mother, sai yawo sukeyi mata Acikin Kai, Tunanin Sulaim yafi ɗaga mata hankali da halin dayake ciki Yana cikin jarrabawa da wahala saboda shi kaɗai yasan abunda yake ji, Ta kasa gane shin tausayi ne ko menene, Gashi Mother tace kada ta ƙara temakon kowa, Tabbas itama tasan hakan amma ta rasa dalilin ta nason binciko komai, Jitayi Kanta har ciwo yake saboda rashin nutsuwar da take ciki,"

*Yarima Sultan*
Jiki babu kwari yake Tunkarar Part É—in Sulaim bayan Sun fito daga Meeting Wanda Baffa yace dole Sai ya zauna anyi dashi, ba don yaso ba, Bayan sa Dogarai ne guda uku suna take masa baya, waÉ—an da ya taho dasu daga Masarautar Gabas, Tausayin Aminin sa yake, Shin tayaya zai kalli wannan al'amarin Gashi Baffa yace nizan fara faÉ—a masa, Tayaya? Ta ina zanfara? Ya tambayi kansa cikin zuciyar sa,
mamaki ne ƙarara kwance saman Fuskar Yarima Sultan, ganin Mace Da Hijabi har ƙasa Ta fito daga Part ɗin Sulaim, to Wacece wannan, Da wannan mamakin Sultan ya ƙarasa Shiga Part ɗin Dogaran sa Suka wuce makwancin su da akabasu, Ganin Sulaim baya Parlourn ƙasa hakan yasa Yarima Sultan wucewa Sama Kai tsaye, bedroom ɗin sa ya wuce saboda ya gaji, ko kaɗan baya son wahala komai ƙanƙantar ta, Tafiyar da yayi daga Part ɗin Baffa Zuwa na Sulaim gani yake yayi wani gagarumin aiki, Yasaba hatta waya idan aka kirasa Sai an ɗaga masa,
Saida yayi wanka yasa kayan bacci sannan ya ɗora jallabiya asama, Yanufi Bedroom ɗin Sulaim Wanda yake da tabbacin yana Ciki Tunda bai ganshi A Parlourn saman ba, tura ƙofar yayi, Yajita a rufe hakan yasa shi yin knocking har sau biyu amma shiru da mamaki Sultan ya ƙara buga ƙofar, But ko motsi babu, Nisawa yayi kafin yaciru wayar sa ya shiga kiran Sulaim, Jin wayar akashe yasa hankalin Yarima Sultan ƙara tashi, Yana ƙoƙarin komawa ƙasa, sai yaji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar, hakan yasa shi tsayawa,

Kollon Sulaim Sultan yake wanda shima shi yake kallo da alama Sulaim ɗin wanka yafito saboda hatta gashin kansa ajiƙe yake da ruwa hakan yabawa gashin kan nasa damar kwanciya bisa dogon wuyan sa, juyawa yayi Yakoma ciki batare da yace komai ba, ƙarasa Shiga Yarima Sultan yayi,

Saraki Barka da dawowa Fatan kana cikin aminci, Allah yasa ba gajiya a tare dakai,

Alhamdulillah Ina lpy, Aminina Meye yake Damun ka,?

Da sauri Sulaim Yakalle Shi Yana mamakin yadda Sultan ke saurin gane damuwar sa, ya daÉ—e da Tabbatar wa kansa idan aka cire Ummeetha da Baffa to kaf duniya babu wanda yake saurin Fahimtar halin dayake ciki kamar Amininsa Yarima Sultan,
Bana jin daÉ—i ne, _but now is okay Everything is fine_

Lpy ka kashe wayoyin ka? Yarima Sultan yaƙara Tambayar sa,

Lafiya, Abunda Sulaim yace kenan, Yana ƙoƙarin kauda Damuwar sa, Sosai Suhaima Ta tsaya masa acikin Rai, jin tsanar Yarin yar yake har cikin zuciyar sa, Baya fatan koda ƙara ganin ta, Ganin Sultan ne yasa shi rage jin zafin dayake ji acikin ransa ga kanshi yana ciwo duk saboda ita, Don ma yasakarwa kansa Ruwa shiyasa yaƙara jin sauƙin abun,

Kayi Dinner? Sultan yakatse masa Tunani,

Sulaim yace A'a Maybe anjima zanyi, Idan kai kayi Fine Yafaɗa yana ƙara hawa saman bed ɗin sosai, Saboda ji yake kamar kanshi zai fashe daƙar yake magana a Hakama wai don Sultan ne da wani ne bazai koda tankamasa ba,

Ganin Hakan yasa Yarima Sultan ƙara tabbatar wa kansa Sulaim ɗin sa ba lafiya ba, shima bai ƙara cewa komai ba, Ya tashi ya ɗakko Tablet ɗin da yasan Sulaim yanasha idan yana irin wannan yanayin, Ya ajiye ta saman Bedside Drawe, kasan cewar acikin wata ƴar ƙaramar roba Suke, Yafita Don Samawa Sulaim Tea yasha kafin yasha Tablets ɗin,"

*After Three days Ago*

Horn Take tafaman yi, Amma babu alamun wanda ke cikin motar zai motsa bare tasa ran zai matsar da motar daga hanyar daya babbake, Ganin hakanne yasa Suhanna Fitowa daga mota taɗan tsoƙe kyakkyawar Fuskar ta Da gani basai anfaɗa maka ba zaka gane jinin Arab ce, Cikin ɓacin rai Taja dogon Tsaki Ta kwankwasa glass ɗin motar wanda yake Tinted ne akaro na Biyu, ahankali glass ɗin motar ya fara Zugewa,
Cikin Sanyin Muryar ta tafara magana wanda ita a ganin ta takai ƙarshe wajan ɗaga murya,
Haba Kai yanzu kayiwa kanka Adalci kenan, kazo ka tsaya A hanya sai horn akeyi maka bakasan uzirin Mutum ba, Amma babu alamar zaka Motsa daga hanya, Shiru babu Amsa Hakan yasa Suhanna ƙara harzuƙa ta leƙa cikin motar Driver kawai tagani..!!!

_F Pen_✍️
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS ......✨�*
*_T.M.W_✍️*

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 3️⃣7⃣➖3️⃣8⃣�

*Suhanna*

Ƙara harzuƙa tayi taleƙa cikin motar don ganin wane ɗan gwanar ne aciki da har ya isa tazo tana mai magana kuma yana ji, koda taleƙa cikin motar driver kawai tagani,
Kamar baza tai magana ba sai kuma, tace kai waye yabaka izinin tsayawa Anan? Sannan bakaji ina maka horn ba kokai kurma ne? A fusace Suhanna ke maganar saboda ranta yaɓaci,

Kiyi haƙuri Madam, nima umarni nake karɓa bazan iya matsawa konan da canba matuƙar ba'a mani umarni ba, Drivan yafaɗa cikin girmamawa batare da ya kalle Suhanna dake tsaye saitin murfin ƙofar gidan gaba,

Kallon A gogon hannun ta tayi, Tare da jan dogon tsaki, Umarnin waye kake karɓa? Ta tambayi Drivan,

Da hannu yanuna mata Bayan motar alamar yana ciki, Koda Suhanna ta ƙara zura kanta sosai bata ga kowa ba babu abunda tagani, sai wani irin wani irin dadda ɗan ƙamshin Turare mai Sanyi, Gashi ya haɗu da sanyin, A.C, Batare da ta ƙara cewa komai ba ta ƙara duban A gogon Dake ɗaure a tsintsiyar Hannun ta da alama sauri take akwai gurin da zataje, kai tsaye ta wuce Security Room ɗin Arab Estate wanda ke maƙale daga gefan babban Gate ɗin Shiga Estate ɗin, Tunkafin ta ƙarasa, Chif Security ɗin dake kula da gaba ɗaya Cameras Ɗin Estate ɗin ya hangeta ta ciki camera ganin Suhanna Room ɗin take Tunkara tasa shi saurin Fitowa saboda yasan gaba ɗaya Ahalin Arab Estate, daga kan ƴaƴa har jikoki yana da hoton kowa saboda tsaro yasan ɗan gida ya san baƙo,

Cikin Girmamawa Securitin ya russuna a gaban Suhanna wadda gaba É—aya annurin Fuskar ta ya É—auke, Ranki ya daÉ—e barka da Yamma Allah yasa dai lafiya?

Ko kallon shi ba tayi ba ta wuce tare da FaÉ—in Muje ciki,

To yafaɗa tare da saurin wucewa gaba yafara buɗe mata Ƙofar tashiga sannan shima yabi bayan ta,
Computer Room ne mai Girman Gaske, gaba ɗaya ɗakin Kayan na'ura ne aciki duk inda ka kalla videon wani ɓangare daga cikin Estate ɗin ne tun daga titin farko Na shiga cikin Estate ɗin har ciki, Shiru Suhanna tayi tare da Goya hannuyen ta Saman ƙirji, tare da zubawa Computer ɗin dake haske Bakin gate ɗin ido, wannan motar take kallo saida ta daɗe tana kallon motar kafin ta juya ta kalli wannan security ɗin,
"Wannan motar waye? Ta tambaye shi

" Ranki ya daɗe Bansani ba, Amma da'alama babban baƙone nasamu labarin zuwanshi tunjiya amma bansan waye ba"

"Jin jina kai Tayi, Oky Amma daga Wajan wa kasamu Labarin Zuwan nashi, Baƙon waye?
Ranki ya daɗe Bansan Baƙon waye ba sannan kiran daga Babban Sashe yazo amma bansan waye ya sanar ba,

Inaso a ƙarasa kulle General Gate kada kabari motar ta shigo har sai nabaka izinin, Suhanna tafaɗa Tare da Samun Guri ta zauna cikin ɗaya daga cikin kujerun Room ɗin, Fuskar ta babu alamar wasa tayi maganar, Ganin haka ne yasa Securityn saurin Amsawa da To yakarasu yayi kamar yadda tace, zuciyar sa cike da tsoron kada wani abu ya biyo baya yasan akanshi za'a huce, Dama Gate ɗin inda yake a zuge ko rabi bai kaiba, bai wuce inda mota ɗaya zata wuce ba, Wanda da Anbuɗe shi gaba ɗaya, motoci biyar ma zasu iya Wucewa a lokaci guda harma da ragowa,

Idon Suhanna nakan Computer É—in tana kallon motar wadda aka kulle gate É—in aka barta a daga waje dama bata shigo ciki ba, Sun tsaya ne a hanya,

Wallahi gwara inyi asarar Zuwa Gurin aikin nan yau inga iya gudun ruwan Mutumin nan, ko mace cema oho, Zan nunawa wannan mai wulaƙan cin koni wace acikin Estate ɗin nan, saina nuna mishi shi ba kowa bane, Cikin Ranta Tayi maganar a fili kuma Tace Wani Wayema yace Arufe gate abar wannan ƴar hanyar?

Security É—in wanda tuni ya cigaba da Harkokin sa na kula da Cameras, yabata amsa da cewa, ALHAJI ARAB ne,

Baffa kuma, To Meyasa? Ta tambayi kanta,
Chapter 73 · 0% Book details