← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 90

Sashe 38

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

......BANANA ISLAND, Cikin Jerin manya manyan gine ginan Hamsha ƙan masu kuɗi dake Cikin Unguwar Banana Island,
House No.242 dogon gine ne mai ɗauke da upstairs hawa biyu, Gidan tun daga waje zaka gane Asalin haɗuwar sa, Tsarin ginin Ƙasar INDIA ne, Daga jikin gate Ɗin gidan Anyi rubutu a wani ɗan ƙaramin allo cikin manyan baƙi aka rubuta, (MAJOR IBRAHIM KHALIL BICHI).

"Kai kawo take tsakanin kujerun cikin Makeken Parlourn Ta na ƙasa, wanda suka kasan ce, Silver colour Mai duhu, Sai mafan safa da marwa take Lokaci zuwa lokaci tana Duba Agogon dake ɗaure a wrist ɗin ta, Ganin kusan, 1Hours Tana Abu ɗaya hakan yasa ta samu guri saman kushin ta zauna da'alamar gajiya bayyana ne saman Fuskar ta, Sanye take cikin Shigar Alfarma Shadda ce a jikin ta Army colour, Anyi mata Aiki iya Saman Rigar Anzuba mata Duwatsu, Golden Colour, Tsarƙa da ɗan kunnan ta da Diamond sai Ƙalli suke, Fuskar ta fayau, Babu ko kwalli, Tayi Ɗaurin Ture kaga tsiya Akan ta, Abunka da Mai hasken fata Sosai Tayi kyau, idan kaga ta baza ka taɓa cewa tana da Manyan ƴaƴa Ba,
Wata Mata shiyar Buduwar ce tafita daga Wata hanya Cikin Parlourn, Da sauri ta ƙarasa Ta rungume Matar dake Zaune a Parlourn Ta baya,
"Oh Momma Allah kinyi kyau Wannan Duk kwalliyar Papa ce, Cikin wasa da dariya Buduwar tayi maganar tare da sakin Mahaifiyar tata Tazagayo gaban ta,
"Shukra Kinyi Waya da Papan Kune? Duk Nadamu Wayan shi baya Tafiya, Kusan Hours kenan,
"Kamo hannun Mahaifiyar tata tayi cikin nata hannun kafin tace, No Bamuyi waya Ba Amma Please Momma Calm down, duk inda yake yana lafiya insha Allah, So ki kwantar da hankalin ki,
"Kinsan Tunɗazun yacemin yana Hanya sun kusa ƙaraso wa, Kuma tun daga nan Banƙara samun shiba, At All saida nace karsuyu tafiyar mota.... Kiran da ya shigo wayar tane ya katse mata Sauran maganar, Cikin hanzari takai hannu Ta ɗauka, Ɗan guntun tsaki taja ganin Ba wanda tayi tsammani bane,
Kallon ta Shukra tayi Ƙasa ƙasa tace, Momma waye kiɗaga mana,
"Sajad Ne TafaÉ—a Tare da kara wayar a kunnan ta, "hello Kana ina Haka na kejin haya niya,

"Naje *Parkview* I'm on the way, Momma Papa Yace Sun kusa Shigowa Yanzu Haka Nayi magana dashi,
"Alhamdulillah Allah Yakawo su lafiya, Dama Tunɗazun Su nake jira Hankali na duk ya tashi saboda number ɗin Major ɓata shiga, Allah yasa yayi nasarar Tahowa Da ita,
"Wacece? Sajad Ya tambaya Anashi ɓangaran,
"Oho kana nufin bakasan abunda yakai shi Kano ba kenan, Banason ya dawo Bai same ka a gida ba kayi sauri ka ƙara su, Idan kazo yafaɗa maka dalilin Zuwa nasa Kano da kanshi, Bata jira cewar saba ta ajiye wayar,

"A hankali Shukra tace Momma, Allah yasa Papa ba ba gurin tsohuwar nan ya koma ba,

"Kallon gefan ido mai kama da harara Momma tayi mata tare da FaÉ—in, Waiku Meye yake damunku ne, Emm, nayi tunanin zaku taya mahaifin ku farin ciki ya shawo kan Mahaifiyar sa Amma shine kuke nuna rashin jin daÉ—in ku, To Wallahi kada ma kubari ya fahimci hakan daga gare ku,

"Sorry My love Nifa ba haka nake nufi ba, Momma Idan biki manta ba lokacin da Papa ya ɗauke mu Har wannan, bush village ɗin, Matar nan A gaban mu ta Mari Papa Sannan tace Kice kika rabata da ɗan ta, Ta zageku da cin fuska a gaban mu nida ya Sajad, Haba Momm....Hawaye da suka gangaro daga Idon Shukra ne yasa ta kasa ƙarasa maganar ta,
"Cikin sigar Lallashi da Kwantar da hankali Momma ta janyo ta jikin tana shafa bayan ta cikin kwantar da hankali tace, "My Noor nasha faɗa miki ba'a rama mugunta da mugunta Idan aka biye wa zuciya to babu abunda Zai wuce a rayuwa, Kisani Shi Alheri dan ƙone, Komai yayi farko ai yana da ƙarshe, Haƙuri baya taɓa faɗuwa ƙasa banza, Allah yana sane da kowa, Grandad ɗin ku ɓata da laifi koni ce abunda tayi shine zanyi, Tsawon shekaru Ace ɗanta baya tare da ita Alhalin yana raye Dole Zatayi zargin matar shi, Bazan so ace matar da Sajad zai aura nima tayi min haka ba,
ÆŠago da Shukra tayi daga jikin ta Sannan Tace, Daughter nasan duk yanzu baza ku fahimci hakan ba, Amma akwai lokaci, tafaÉ—a tare da sharewa Shukran hawayen idonta,"
"Alright Momma ya wuce, Yanzu ya maganar Zuwa na, Kano
Tana nan amma Nace miki gaba É—aya zamuje,
"To Momma Wallahi kawai so nake naga Suhailat Amarya, duk da har yanzu bata faÉ—amin ba, Sai Y saleem ne yafaÉ—a min Da muka haÉ—u a....
Ke waya faÉ—a miki amarya na faÉ—ar bikin ta to,
What amma Meyasa? Shukra ta Tambayi Mahaifiyar tasu tana jiran Amsa,
"Saboda kunya, " Oh oh Allah momma nizan iya faɗawa kowa nawa, tafaɗa tare da miƙewa tana dariya,
Baki sake Momma ke kallon Shukra, tare FaÉ—in, to ni mezan miki ai dakin dawo kinfaÉ—a min waye mijin, Itama tana dariya Tayi maganar,

Wace Momma....
"Hajiya Bahijjah Imran Arab, Itace ƴa mace ta fari a gurin Baffa, Mafi Soyuwa A gurin shi, A kaf cikin ƴaƴan shi mata, hakan yasamu a saline da Sunan ƴar uwar shi da taci, Bugu da ƙari, Sai ta ɗakko kamannin waccan Bahijjan Sai yake jinta tamkar, Ƴar uwar tasa wadda ita kaɗai ce ƴar uwar sa a duniya kuma ya rasa ta,
Bahijjah Na zaune a garin Lagos Ita da mijin ta da ƴaƴan ta guda Biyu, Sajad ne baffa sai Shukra, Rayuwa suke mai tsafta da bawa juna kulawa, Rayuwar Farin ciki Suke sosai, Major Ibrahim khalil mutum ne Mai son ƴaƴa Amma hakan bai hana su Bawa yaran su ingantacciyar Tarbiyya ba, Bahijjah Arab Babbar Ma Aikaciya ce, A ƙungiyar Kare Haƙƙin mata wato (HUMAN RIGHT) Anan Cikin Birnin ikko.,

***Wannan Kenan***

Rayuwar Jin daɗi ko Farin ciki Babu ita a cikin Arab Estate, Tsawon kwana Huɗu kenan Sulaim bai far faɗo ba, A halin yanzu kowa yasan Sulaim bashida lafiya, Wa suma sun fidda rai, Kwanan Su uku A Asibitin Ashshifa Sunyi bakin ƙoƙarin su, A lokacin Har Abulƙasim ya dawo daga umara, Manyan likitoci Larabawa da Turawa Sunyi aiki Sosai akan Sulaim amma babu wani canji, Sun tabbatar da, Lafiyar ƙalau Komai nashi na aiki yadda akeso, A yadda bincike ya nuna Haryafi wani cikakken mai lafiyar, Kuzari da Sauran abubuwan da ake buƙata,
Shidai ga shinan kwance Kamar me bacci, sai wani irin kyau da yake ƙarawa,
"Abulƙasim ya Tabbatar wa Baffa cewar Wani Baƙin Asiri ne Ya karye Wanda akan Sulaim ɗin akayi Shiyasa Har zuwa wannan lokacin yagaza Farfaɗowa Abun na sakin shi Sannun a hankali, Magunguna kala kala, Na wanka da a turare Da nasha Wanda aka haɗawa Sulaim ɗin Anason Bayan ya farfaɗo Yayi amfani da su,
"Cikin Muryar Tashin da kwantar da hankali, Abulƙasim yacewa baffa, "Alhaji Ka kwantar da hankalin ka dan Allah, Kasan Ita ƙaddara Babu wanda ya isa ya kauce wa faruwar ta, Saidai mutum yayi addu'ar Allah yasa tazo masa da sauƙi, Wannan yaron Na tausaya mishi sosai, Ya daɗe da lalura a jikin shi amma buku taɓa tunanin Yi masa maganin Islamic ba, A yanzu haka Akwai Sihiri ajikin sa wanda yake aiki kusan Tun lokacin da aka haife shi, Anyi masa Sihiri kusan uku a jiki kuma duk na cutar wa yanzu Ga ɗaya ya karye wanda tabbas akwai Silar Warware warshi, inaso Idan Allah SWT Yasa ya farfaɗo to, zaku Bamu shi Tsawon Na wata guda insha Allah komai zai dai dai ta, A Hakama don yanada Ruƙon Ibada Sosai, shiyasa Amma da Wani ne bama lallai ya tashi ba, Saboda Ai niyar kashe shi akai, Abun ya daɗe yana cin jikin shi, Muna roƙon Allah yabashi lafiya Mai ɗorewa,

"Ameen baffa ya Amsa Zuciyar shi kamar zata fito saboda tsabar zafi da raÉ—aÉ—i, bunu abunda yake ji Aransa sai tsantsar tausayin Sulaim, Waye yayi masa haka? Meye laifin sa? Baffa ya tambayi kansa batare da Yasan Amsar ba,
Abulƙasim da Baffa lokaci ɗaya Suka fito Daga cikin Babban Office ɗin Abulƙasim, A lokacin angama Shirya komai da cike ciken ta kaddu Na Sallama, har bakin mota Saida Abulƙasim ya raka baffa, Dama shi Su Uncle Yusuf suke jira, Yana shiga Suka Tafi,

A motar Asibitin Aka maida Sulaim gida Wanda Yarima Sultan ne kawai aciki, Sauran duk suna biye dasu a wasu motocin,

Su Ummeetha na fita Saiga Su Baffa Sun sako kai Cikin Jerin gwanon Motocin Arab Estate Motar a Asibitin ce a tsakiya,

Ta glass ɗin mota Ummeetha ta hangi dawowar su Jitayi Tamkar ta fita taga ɗan ta sai taga, Ai Saleema ma ƴace a gurin ta, Tunda taji labarin rashin lafiyar Sulaim yau kwanan ta biyu kwance a asibiti yanzuma gurin ta zasuje, Kullum cikin kuka take taƙi cin abinci Drive kawai aki samata, Idan kaga ta buɗe baki to Sulaim zata furta, kowa yayi kukasan Suna ma cikinyi Tunda kullum sai sunyi, Ummeetha baiwar Allah Tarame ta ɗanyi duhu, A Hakama wai dan Tayi tawakkali,

Suhaima Gaba ɗaya ta rasa Meye yake mata daɗi a duniya, Wayar Mother bata shiga, Gashi Tun ranar da taga Khaltum ita da Barrister Sulaiman da daddare bata ƙara sata a idon taba, taje neman ta yafi sau a irga, Suma kansu Masu aikin House ɗin sunce Tsawon kwana uku kenan basa ganin Gilma warta,
Tana Cikin wannan Tunani, Ta hangi Princess Tana tunkaro ta Fuskar ta tayi jajir, Alamar taci kuka ta ƙoshi, Idanuwan ta duk sun faɗa ciki, Da sauri Suhaima ta Nufe ta, Tare da Faɗin Princess lafiya kuwa?
Ina lafiya Suhaima Kina nan Amma biki san Ya Sulaim bashida lafiya ba yau kusan kwana Huɗu ko biyar, Yanzu haka Sundawo daga asibiti kuma ance bai farfaɗo ba, Ya Yarima yace around 4pm zasu wuce, Birnin Jidda, ganin kuka yaci ƙarfin ta yasa Suhaima kamo hannun ta duka biyun, tare da Faɗin, Y Rabb wallahi bansan bashida lafiya ba nayi tunanin yayi tafiya ne, Allah yabashi lafiya Yanzu ke ina zakije?
Chapter 38 · 0% Book details