← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 90

Sashe 69

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Gimbiya Shaheedah*
zaune gaban Mai Martaba kanta a ƙasa zama tayi cikin girmamawa da ladabi,

Ƴa" ta kada kiji shakkar komai, inaso ki bayyana min, Shin da gaske ne kinason Safwan, idan har bakya son shi to ki sanar min, A gaggauta Sanarwa da Mahaifiyar ki, Babu wanda ya isa yayimiki auren dole matuƙar ina raye,"

"Shiru Gimbiya Shaheedah tayi, Tasani har ga Allah bata jin koda É—igon son Yarima Safwan to amma yazatayi kodan Cikar burin su da son taga Mahaifiyar ta ta dawo cikin Masarautar Gabas Aita Amince ta aure shi, koda hakan zai cutar da ita, Da wannan tunani tayi amfani wajan É—agawa mai Martaba kai alamar eh tana son shi,"

Murmushin Girma Sarki yayi Yana É—auke ido daga kallon ta, Allah yayi miki albarka, Tashi kije,

Muskutawa Girbiya Shaheedah tayi tare da Matsawa gaban Mai martaba, kanta na aƙasa, Hannu tasa ta cire hular dake saman Alkyabbar ta, Taƙara russunawa sosai, Alamar Girmamawa,
"Allah ya ƙara maka yawan Nasara, Allah ya ƙara lpy, Ina godiya A madadin Mahaifina Nabarku lafiya, Tana kaiwa nan tamiƙe tafita cikin Nutsuwa kamar ta Allah,
Gaba É—aya yadda Sukai da Sarki ta kwashe ta sanarwa Mahaifiyar Su, A waya
"Mom Akwai wani labari ne game da Æ´ar ki?

"Hmm Nisa wa Mahaifiyar Tasu tayi, Eh To Ansamu labarinta amma ba'asan inda takeba, haryanzu anakan nema, nace masa wlh idan ba'samu min Æ´ata nanda 2 Months to zan makashi a kotu, Haka mukai dashi, Yanzu dai kome kenan zan sanar miki game dahaka,
"Naji daÉ—in yadda kika amince da wannan auran Nasan, Al'Adar Masarautar nan ne ba'a saka biki dayawa, Idan yayi nisan duniya shine Wata biyu, kinga komai ya kusa dai dai ta kafin nan angano inda Æ´ata take,"

_Anyway_ Duk abunda kenan zamuyi waya, bata jira cewar Mahaifiyar tasuba ta kashe kiran, kamar wanda ake jira tana Kashewa saiga Kiran Yarima Safwan yana shigowa, Kallon Screen É—in wayar Gimbiya Shaheedah tayi, ganin Sunan Yarima Safwan ya bayyana hakan yasata Jan wani Dogon Tsaki tare da kyau da kai gefe,"

Zarah kinga kiƙaleni Zaman mezanyi wlh gara inkoma gida, bazan iya jurewa ba, inaji ina kallo tsawan shekara ta nawa a Masarautar nan, Tun bansan kainaba, ina dakon Soyayyar Yarima Sultan, Amma Ace Wai Yanzu Gimbiya Sultana za'a aura masa, kinga kenan Annuna ni bare ce ba'ƴar gida ba, wani sabon kukan Siyama Taƙara fashewa dashi tare da tura rigar da ke hannun ta cikin akwatin data cika ta danƙare da kaya,

Siyama kennan Wlh idan kikai haka kinbani kunya cewar Zarah, Nayi tunanin kinada wayo ashe bahaka bane, idan kika tafi soyayyar barin zuciyar ki zata yi? da haka gara ki zauna a goga dake inyaso duk abunda zai faru ya faru, dakike maganar, keba ƴar cikin Masarauta bace shiyasa akai miki haka, shin wane tabbaci kike dashi kan cewa, ansan kina son Yarima kisani Siyama idan Kin manta bari natuma miki nan Masarautace ba Normal Gida ba, da kowa zai san abunda kake ciki, Wannan yaƙin nakine idan kika tafi babu wanda kikayi wa sai kanki,
Fulanin Sarki (Ummu Safwan) dakike gani Yanzu bata mu takeba Amatsayin mu na ƴaƴan yayyen ta, Taɗanta kawai take burin ta taga ya hau kujerar Mulki, A gaskiya bazan ɓoye miki ba Siyama bazan yi, Asarar zaman Shekarun danayi ba, Dole sai nayi aure acikin Masarautar nan kowaye zan aura kuwa,"

Zarah kennan, na daÉ—e dasanin Fulani batamu takeba dama akwai Wata manufa aranta nason haÉ—a aurena da Yarima Sultan, Zan aure Sultan Dole, Sannan zan bata mamak..... Ganin Fulani ta shigo Ko sallama Babu hakan yasa Siyama Saurin haÉ—e ragowar Maganar ta,"

*Fulani*
Kallon Siyama take har saida Siyaman ta tsargu, Cikin ranta tafara tunanin ko dai taji abunda Suke tattaunawa tsakanin su ne?
Ɗauke idon ta tayi tamayar kan zarah wadda gaba ɗaya tagama saddaƙarwa Fulanin taji su,
"Tunda buku iya gaisuwa ba bari inyi abunda yakawoni, Ke Siyama Naji labarin kina kuka zaki koma gidan ku, To inaso kusani babu inda zaki tafi, yanzu dan asara da shiririta Akan Namiji kike wannan kukan, to bari na shaida miki, bikiyi kukaba sai nangaba, idan kika shiga hannun mai ban haushi nan, duk ƙoƙarin danake akan ku wato bakwa gani ko, to Shikenan yanzuma ga hanya nan tashi ki tafi dan Allah tafaɗa tare da nuna mata hanyar fita da ɗan ya tsanta, Masifa Fulani take ta inda take shiga ba tanan take fitaba, Dama Dole zaki aure Sultan mana, Koda kikaji labarin za'a aura masa Sultana ai bikiji ance banda keba, to ku fita idona wlh, ke kuma zarah kinzauna kinkasa falafalan kunnuwan ki kina saurarona idonki akaina don rashin kunya, saura naji kinkira Yaya, kinbata wannan labarin Tunda duk abunda akai saikin faɗa mata, ke kuma kicigaba da kuka karki fasa,
Fuuuu, Fulani tajuya tafita alkyabbar jikin ta sai share hanya take,"

Kallon kallo tsakanin zarah da Siyama, gaba ɗaya suka taɓe baki, Zarah hadda Rakiyar harara ta haɗawa Fulani, Falafalan kunnuwa gasunan Maƙale a Ƙiyar ɗanki, tafaɗa tare da murguɗa baki saboda abun yaɓatawa zarah rai, wai mai falafalan kunnuwa,"
Abunda Zarah tayi Saida yaso bawa Siyama dariya,"

Bayan Mai Martaba ya kammala Faɗawa Ummul Bait, Za'asa ranar aure tsakanin Yarima Sultan da Gimbiya Sultana, Sosai Al'amarin ya taɓa mata zuciya, Kwata kwata bataji daɗiba har cikin ranta take jin ɓacin rai, Amma saboda Girmamawa da Mulki ko a fuska bata Nuna ba, Fatan Alkhairi kawai tayi tana tunanin yadda Sultan zai karɓi lamarin,

Mai martaba ya ƙara da bayyana mata, Za ahaɗa Dana Yarima Safwan da Gimbiya Shaheedah, Sannan akwai Siyama ƴar gidan yayar Fulani (Ummu Safwan) data bayyana Soyayyar taga Sultan, Amma wannan Bamu karɓa ba na barshi zuwa nan gaba za'a bashi zaɓi akan hakan idan yanada ra'ayin sai ya aure ta, Sarki na magana amma hankalin sa nakan Ummul Bait, Wadda duk yadda taso taɓoye halin da take ciki nadamuwa lokaci ɗaya saida Mai martaba ya fahimci hakan,

"Duk yadda Ummul Bait taso daurewa, Batasan lokacin da wani Siririn hawaye ya gangaro Saman kuncintaba, da sauri takai hannu ta É—auke shi, Amma ina Mai Martaba ya riga daya gani,

"Bahijjah Auren Sultan ne bakya so ko Auren Sultana da Yarima ne bakyaso? A zahiri nayi tsammanin Wannan abun Farin ciki ne a garemu amma naga saɓanin hakan daga gare ki,"

Allah yatemakeka bakomai Allah yasa Albarka aciki idan na ɓata muku rai Allah ya huci zuciyar Adalin sarki, Mahaifi ga Yarima Sultan, Duk hukuncin da ka zartar akan kowa dake ƙarƙashin ka ai dai dai ne, Bana ƙin jinin Mai Martaba, Sultana Ai ƴa ce a gurin mu baki ɗaya, Allah ya Tabbatar da alkhairi,"

Shiru Mai martaba yayi yana kallon ta harcikin zuciyar sa yaji daɗin Maganganun ta, itace mace mafi soyuwa a gurin Mai martaba, Tausayin tane yakama shi, yasan Dole zataji babu daɗi kasancewar tana matuƙar ƙaunar ɗan nata, Tunawa dayi tayi rashin Wasu mutane masu Mahimmanci, Arayuwar ta kuma jigo a rayuwar ta, hakan yasa ya ƙara jin tausayin ta, Tabbas badan Na 'Amincewa Galadima Murtala ba dana bawa Mahaifiyar Sultan haƙƙin ta na uwa akan ɗan ta, aikin gama ya riga ya gama, Saboda magana biyu ta ƙananan mutane ce,"

"Ummul Bait sosai take tausayin kanta da ɗan ta, Batada kowa daya rage nata a duniya sai ƴaƴan ta da mijin ta, Sultan Shine Take ɗauka amadadin komai, Taso ace yasamu mace ta gari saboda kwanciyar hankalin sa da nata, tasani sarai Hajiya mai Soro bason ta takeba, bason Yarima Sultan Suke ba, Dole akwai wani abu a ransu, Sannan ga Siyama yarinyar da kishiyar ta ke ruƙu, Tasan Tunda Mai martaba ya faɗa dole za'ayi auran, Tayaya ɗanta zai zauna tsakanin azzalumai Amatsayin matan sa, dole akwai wata manufa acikin auren nan, idan ta tuna hakan shike ƙara ɗaga mata hankali Bakomai ba, shikenan bashida wani zaɓi,"

Ganin Ummul Bait ta tsunduma Duniyar Tunani, yasa mai martaba sakkowa daga saman gadon Sarautar shi yazauna kusa da ita saman Lallausan carpet cikin Turakar sa, Idan yaganta cikin damuwa sai yaje ya rasa nutsuwar sa, Zai iya haƙura dakomai Akan shiga damuwar ta saboda yana jin ta amanar sa ce, Batada kowa sai shi, Shine silar zuwan ta nan ɗin, hannun ta ya kamo cikin nasa cikin sigar rarrashi ya fara kwantar mata da hankali har saida yaga Tasamu Nutsuwa sannan hankalin sa ya kwanta,"

*_ARAB ESTATE_*
Kallon kallo ake tsakanin Sulaim da Suhaima A tsakiyar Parlourn Jikin Suhaima Har lokacin Rawaya yake, da 'alama bata gama dawowa hayyacin taba,"

" _Who are you?_ Ahankali Sulaim ya furta hakan, still idonsa nakan Suhaima wadda fuskar ta gaba É—aya a rufe take,

Suhaima wadda ta ruƙe Hannun Akwati, burin ta kawai tabar Part ɗin, Haushin Sulaim take ji sosai Take ta tuna Abunda ya faru tsakanin su, A asibiti, Saboda tsabar ƙarfin hali irin nata itama, tace masa, Kai waye?
Saboda tsabar mamaki kasa cemata komai Sulaim yayi, Yana ganin tazo masa part sannan tana Tambayarshi shi waye,

Takusa dashi tazo ta wuce hannun ta ruƙe da akwatin da ta ɗakko wadda Batasan komeye aciki ba, Banida lokacin ka Yanzu amma Kabari zamu haɗu, tafaɗa a zuciyar ta tare da zuge glass door ɗin Parlourn tafita abunda, ganin ta yasa driver saurin ƙarasuwa da sauri ya karɓi akwatin yasa a mota suka tafi,
Na tabbata ƙarfin addu'a ne yasani fitowa daga ɗakin nan lafiya, a fili Suhaima tafaɗa Sai kuma tasaki Murmushi mai Sauti, Lallai akwai lauje cikin naɗi akwai Babban ƙulli acikin Estate ɗin nan, Su Suke kashe Junan su, Banfara don Nadaina ba wannan Bakomai bane, Magana Suhaima take bata damu da tunanin Driver najin taba Komai a fili take faɗa, Shin menene Mafita? Mother Yes Mother Uwata maganin kukana insha Allah A yau zanyi waya dake dole za sanar miki da komai, Tafaɗa a lokacin har su hau titin Alhaji Imran Arab,

Sulaim ya rasa Meye dalilin da yakawo shi part É—in tsaye yayi tunbayan Fitar Suhaima yake mamakin ta, Ganinta da Akwati yasa shi Tunanin Baffa ne ya aiko ta, Ta É—auka, Amma Yarinyar batada kunya,"

*Saleem*
_My Suhailat_ kinaso nima nayi kuka ne?

Suhailat wadda ke sharar kwalla da sauri ta girgiza kai, A'a yaya Saleem,
Chapter 69 · 0% Book details