← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 90

Sashe 36

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Ummeetha tayi Kafin tace, bakomai kawai inajin yanayin babu daɗi ne, Nama ƙoshi, Tana gama Faɗin haka ta miƙe Kuci Gani nan zuwa,

Suhailat, Rafiq, Taufiq, Sakeema Princess Da ita kanta Mommyn A tare suka bi bayan Ummeetha da kallo Saboda basu taɓa ganin ta a irin wannan yanayin ba, Tana cikin damuwa Amma bata son su gane Saboda koda sun tambaye ta batada Amsa,"

Bedroom É—in ta tashiga, ta zauna A bakin Makiken gadon ta, Saida tayi É—an Jim nawani lokaci, kafin ta janyo wayar ta ta dannawa Abiiy kira, miss call, sai akira na Biyu ya É—aga,
Jin tayi shiru ne yasa shi FaÉ—in Lafiya kuwa?
Yana jin babu daɗi Saboda yasan Dole hankalin ta zai tashi sosai Matuƙar taji,"

Ta ma rasa abunda za tace, Am dama naga kai da Daddyn Yara Baku shigo Yin Breakfast ba, Shine nace bari nakira naji lafiya,

Har cikin Ransa yasan ba wannan ne dalilin daya sa ta kira ba, Amma sai yayi murmushi yace, Lafiya Alhamdulillah,
Zamu shigo yanzu Akwai abunda muke yi,

Cikin sanyin Murya Ummeetha tace to a gama lafiya, Sam ba haka taso ba taso ace yayi mata maganar Sulaim wanda take jin kamar Akwai abunda ke faruwa, Ita dai ba faɗa mata akai ba, Amma tsakanin ɗa da uwa sai Allah, Soyayyar tafi ƙarfin Soyayya, sai dai A kira hakan da Rayuwa da ƙauna,

Bayan ta kashe Wayar Sulaim ta kira wanda wannan shine kusan miss call na 25 da tayi masa, tana shiga Amma ba'a ɗagawa, Hakan yasa hankalin ta kasa kwanciya, Da ace a kashe taji wayar tasan dama Sulaim gwanin kashe waya ne don kada A dameshi, Amma tasan koda Zaiga kiran kowa A duniya yaƙi ɗagawa to Ba shakka banda Nata,
Tana cikin Wannan tunanin ne saiga kiran Abiiy yana shigowa wayar ta, Hannun ta Narawa ta É—aga saboda tsabar sauri,

Abiiy Tunani yayi Gara yafaɗa mata, Ko koba komai yasan addu'ar uwa akan ƴaƴan ta karɓaɓɓiya ce,

Sulaim Bashida lafiya Amma inaso ki kwantar da hankalin ki, Bance kuma Kifaɗawa kowa ba, yanzu haka Baffa da yana gurin sa, Ankira Abul ƙasim, To Amma ba asameshiba Sai ƙasim ɗin yana hanyar zuwa,

Nannauyar A jiyar Zuciya ummeetha ta sauke, Allah ka dubi Bawannan naka da Rahma kayaye masa abunda ke damun sa, cikin ranta tayi maganar A fili kuma tace to Allah ya bashi lafiya, Ina neman Alfarmar Idan Abiiy ya Amince inason ganin Sulaim,"

Me zakiyi Idan kinje, Yanzu kina fita hankalin su zai dawo kanki,

Ganin sa kawai zanyi Nayi masa Addu'a, Sannan nayi maka Alƙawarin babu wanda za faɗawa, sannan Taƙofar baya zan fita yadda babu wanda zai lura da hakan, Idan bangan shiba bazan taɓa samun nutsuwa ba,"

To shikenan ki kula,

Tun jiya da daddare take jin Babu daɗi a ranta, Har zuwa safiyar nan, Sulaim ne kawai ke faɗo mata A rai, Shiyasa Tasa aranta ba lafiya ba, Gashi tunanin ta yazama gaskiya, Amma Taji daɗin Jin Abul ƙasim a ka kira saboda ita ta daɗe dagane Rashin lafiyar ɗan ta bana Asibiti bane, Hijabi kawai ta zura ajikin ta, jin Abiiy yace Baffa yana gurin, Duguwar hijab har ƙasa, Tunkafin tafita Ta sanarwa Driver yafito da mota zasuje, Babban House,

A dai dai ƙofar shiga Part ɗin Sulaim drivan yayi parking, Kai tsaye Ummeetha ta shiga ƙirjin ta na dukan tara tara, Shattima ne kita faman Safa da marwa a tsakiyar parlourn ya goya Hanbayen sa Duka biyun A baya, faɗuwar Sulaim ta bashi tsoro Abunda bai taɓa gani bane shiyasa Har wannan lokacin bai dawo hayyacin saba,

Sallama Ummeetha tayi a karo Na uku sannan yayi Firgigit, Yana kallon ta idanuwan sa gaba ɗaya Sun rune sunyi jajir, Saboda tsabar tashin hankali da kuma rashin bacci, ƙarasawa yayi ta gaida ummeetha, ta amsa ba yabo ba fallasa, Sannan yayi mata Jagora suka Wuce Upstairs har ɗakin Sulaim wanda bata taɓa taka Part ɗin sa dake House ɗin baffa ba Sai yau gashi har cikin Bedroom, wanda A wancan Part ɗin nashi dake House ɗin su Kusan kullun sai taje, Amma nan saboda da kunya yana tare da sirikan ta bata taɓa zuwa ba,"

Gaba ɗaya saida sukai mamakin ganin ta, tashi baffa yayi Yakoma Saman kujera ya zauna, Itako har ƙasa ta Russuna ta gaida baffa kanta a ƙasa Tare da yi masa ya mejiki,

Amsawa baffa yayi Ɗauke da murmushin yaƙe wanda Yafi kuka ciwo, Maryama yakira Sunan Ummeetha Saboda shi ba ruwan sa Sirikan sa Tamƙar ƴaƴan cikin sa haka yake kallon su,
Jim yakira Sunan ta yasa ta Amsawa batare da ta É—ago ba

Sulaim na buƙatar addu'ar ki A matsayin ki na Mahaifiya,

To Baffa Insha Allah, Allah ya bashi lafiya,"

Ameen tashi ke duba shi,

Ba musu ta tashi, Yarima Sultan, Dr. Jabir wanda yama rasa abunda zaiyi, gaba É—aya suka matso suka gaida Ummeetha, cikin kulawa ta Amsa,

Jikin gadon taje saitin Kansa ta zauna tare da ɗora hannun ta ɗaya A saman Kwantacciyar Sumar kan shi, Wadda ta ƙara yin lif lif idon shi a rufe kamar mai bacci, Amma idan ka taɓa jikin sa baza kaso ka ƙara taɓa wa ba, saboda tamkar garwashi haka ya ɗau zafi, jin zafin dake jikin Sulaim yasa ummeetha bata san Lokacin da wasu Siraran hawaye masu ɗumi Suka Gangaro daga idon ta zuwa kuncin taba,"
Tausayin É—an nata yakama ta sosai fiye da na da,

Ganin Ummeetha a zaune yasa Uncle uncle Tsayawa hannun sa ruƙe da wani tsafta taccen bucket ɗan ma dai dai ci, Ruwa ne aciki wanda ko rabin bucket ɗin bai kaiba, Sai Towel fari Tass da Alama Shafa masa za'ayi ajikin nasa don samun sauƙin zafin,

Ƙasa ummeetha tayi da kanta zuwa saitin kunnen Sulaim Addu'a tashiga yi masa Tamkar baza ta daina ba, Tayi da Hausa tayi da larabci saida taɗau lokaci kafin ta janye bakin ta daga saitin kunnan nasa,"

Ganin Kamar ita uncle Yusuf yake jira, hakan yasa ta Tashi Daniyar komawa, Kamar A mafarki taji An ruƙe mata Hannu, tsayawa tayi cak, A sukwane ta juya, Sulaim ne Hannun ta takalla ya ruƙe shi gam, Amma babu alamar motsi A tattare da shi, Yana nan yadda yake kwance,

Gaba É—aya mamaki ya kama su, Baffa yadda tasowa daga inda yake zaune, Yarima Sultan ya matso,

baima san lokacin da yace "Aminina Sulaim dan Allah katashi na ruƙeka"

A hankali ummeetha ta ta koma ta zauna Kamar mai tsoron Kada Sulaim É—in ya saketa,

Cikin Taushin Murya da daÉ—in Sauraro Sulaim ya fara magana, idon sa a rufe, kamar yadda yake,
" _May Thoughts Are telling me that Something might be happening to me. I don't feel well, But I always love you Ummeetha, when I see you, Nothing can happen to me_"

Badon Bakin sa dake motsiba baza ka taɓa cewa shi ke maganar ba, Banda bakin sa babu abunda ke motsawa, Jin yayi shiru ne yasa Ummeetha daina kallon bakin sa, Cikin raunin murya tace Sulaim Sulaim, katashi mana Dan Allah nima ina son ka, Nima idan ina ganin ka nasan babu abunda zai da meni, Sulaim Ummeetha ta ƙara faɗa tana girgiza Sulaim wanda Tunda yayi shiru, bai ƙara motsawa ba, Bare asa Ran zan buɗe ido,

Karo na farko da hawaye suka fito daga cikin idon Yarima Sultan na tausayin Uwa da É—an, Samrat kasa tsayawa yayi da sauri ya fita daga cikin bedroom É—in...!!

*Suhaima*

_F Pen_✍️
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS...✨�*

*_T.M.W_*✍️

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

*_TEAM FIVE STARS💫_*

*TAURARI BIYAR*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 4️⃣5️⃣�4️⃣6️⃣📖

Ummeetha Sosai idon ta yaka ɗa yayi ja kamar wadda tasha kuka, ƙallon Sulaim take kamar baza ta daina ba, Lokaci ɗaya taji jikin shi yayi sanyi sosai sa ɓanin zafi, Kallon Ta ta maida Kan DR.Jabir wanda gaba ɗaya Tunanin sa ya tsaya cak,
"Dr. Dubamin kodai Sulaim mutuwa yayi, cikin rawar murya tayi maganar idon ta na zubar da kwalla"

Rige-rige aka shiga yi tsakanin DR. Jabir, Daddy Canada, uncle Yusuf, ganin haka yasa Ummeetha tashi ta koma gefe ta tsaya,

Sai tin zuciyar Sulaim Dr. Jabir yasa Kunnan sa, jin bugun zuciyar Sulaim É—in na tafi yadda akeso hakan yasa Dr. Jabir É—agowa Ya sauke wata gajiyayyar Ajiyar zuciya, ganin Ummeetha ta kafe shi da ido, A'alamar Amsa take jira,
"Alhamdulillah Zuciyar sa na Aiki yadda ake so"

Baffa
Ganin Ummeetha ba tada Niyar tafiya taja ta tsaya gashi lokacin Azahar ta ga bato, Hakan yasa Baffa FaÉ—in, "Maryama zaki iya tafiya"

Jiki babu kwari, Ummeetha tace to, Tare da sa kai ta fice ba don taso ba, jin zuciyar ta na mata ciwo hakan yasa ta saurin Dafe Saitin zuciyar tare da Ambaton Allah har tasamu ta fita daga Parlourn, Tana sa kai Ƙasim na sako nashi Da niyar shiga ciki, Da sauri ya ja baya Yabata hanya, sannan suka gaisa yayi mata ya me jiki, Kana ya wuce,

Kamar yadda tabawa Driver Umarnin Tsayawa ya jira ta, Haka Tazo ta Sa meshi yadda ta barshi, Cikin ƙanƙanin Lokaci ya tashi mota Suka wuce, Hameed Arab House,

Wayar Yarima Sultan ce taɗau ruri, kamar bazai ɗa ga ba sai kuma ya kalli Screen ɗin wayar, Ganin ƙasim ne mai kiran Ya sashi ɗaga wa,
"Ranka ya daɗe Na ƙara su,
"Ciki ciki Yarima Sultan Yace,"Oky Samrat ya ƙara so da kai, Yana Faɗin haka ya katse kiran,

Takawa Yarima Sultan yayi Zuwa Gaban Baffa, Cikin Girmamawa Ya shaida masa Zuwan Ƙasim,
"Baffa yace to Bismillah yashigo mana"

Baki ɗauke da Sallama Ƙasim ya tura kai cikin Bedroom ɗin hannun sa ruƙe da Wata ƴar ma dai dai ciyar Box, wadda Aka rubuta (Ashshifa Islamic medicine) Bayan Ƙasim ya Gaisa da kowa, Ba tare da ɓata lokaci ba yashiga aikin sa, cikin Nutsuwa Ya shiga fito da komai da yake da buƙata, daga cikin wannan Box ɗin,
Chapter 36 · 0% Book details