← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 90

Sashe 5

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wani ƙungurmin daji mai haɗe da mugun baƙin duhu da manya manyan tsaunika, matar Abdullahi tanufi wajan bokan ta, take tasanar masa da abunda takeso, duk yadda za ayi mijin ta takeso yazama wanda zai hau karagar sarki a ranar naɗin da za ayi, ba musu boka yabata asiri tare da gindaya mata manya manyan sharuɗa da kuma sanar mata idan har tayi kuskure to tabbas mijin asirin zai koma kan mijin ta zai haukace daga ƙarshe kuma zai mutu,
Batare da wani dogon tunani ba ta amsa da eh taji ta amince,

Anyi shagali sosai na tariyar Bahijjah a sashan mijin ta, wanda Tunda Yusuf yakawo ta cikin masarautar bata taɓa koda taka bakin ƙofar fita daga sashen gimbiya Aziza ba sai ranar koda ya sanar mata da rasuwar Mahaifiyar sa taso yabar ta zuwa cikin masarautar danyin gaisuwa amma yahana ta,
Anyi mata komai irin na al'adin su ƙarƙashin umarnin sarki Adam, wanda gimbiya Aziza itace akan komai na hidimar, sosai Bahijjah taji daɗi saboda, Yusuf tasanar mata akwai ɓangaran Mahaifiyar ta acikin sashen sannan akwai masu kula da ita da lafiyar, hakan yasa taji ya shiga ranta lokaci ɗaya tare da soyayyar shi mai tsanani,

Abinda Allah ya hukunta dole sai ya faru Bahijjah ta tare a É—akin ta a matsayin matar Yusuf bayan babu ran hajiya Baitu, Yusuf Adam shareef yazama sarki mai cikakkyan iko a masarautar Gabas,
Wanda yayi dai dai da mafarin haukan Galadima Abdullahi, Giwar sarki saboda tsabar tashin hankali ɗan ta bai zama sarki ba kuma ya haukace batare da sanin dalili ba take tunanin ta yabata asiri Yusuf yayi masa, hakan yasa ta yanke jiki tafaɗin tasamu shanyewar ɓarin jiki,

Magani sosai aka shiga nema wa Galadima Abdullahi na addini saboda an tabbatar sihiri ne ya koma masa, amma ina abun kullum cigaba yake hauka tuburan duka yake ga duk wanda yaje kusa dashi hatta masu gadin sa sai sunyi da gaske suke kuɓuta,

Babu wanda yasan abunda ya faru sai matar shi wanda itace silar faruwar komai, a ranar da boka yace ta aiwatar da aikin sai Allah bai bata dama ba, cikin daran matsananciyar naƙuda ta kama ta, hakan yasa aka nufi asibiti da ita, saboda tsabar azaba tama manta da batun boka da shara ɗin da yabata,
Ranar ta haifi É—a namiji wadda yaci suna Mu'azzam,

_BAYAN SHEKARA UKU DA RABI_

Lokacin sosai Sultan yayi wayu kyakkyawan yaro mai kama da Mahaifiyar sa wato bahijjah wadda suke kira da ummul bait (uwar gida) a gurin sarki Yusuf, saidai sultan ɗin Tunda aka haife shi bashida wata cikakkiyar lafiya, kamar irin yaran nan dasuka sha ruwan mahaifa kullum cikin dalalar da yawu ga hannu da ƙafa a shanye suke,

Ƙarshan haukan Galadima Abdullahi yazo ƙarshe, ya mutu yabar yara biyu a duniya, Mu'azzam da shaheedah sai matar shi wadda taza silar komai amma duk da haka zuciyar ta nakan kwaɗayin mulki kuma ta ɗau aniyar dole sai ɗan ta Mu'azzam yayi sarki Tunda Mahaifinsa bai yiba,

Sosai Galadima murtala ya ƙara tsanar ɗan uwan masa Yusuf amma dai baya nunawa a fili kullum ƙarashiga jikin sa yake domin son samun ma Kasar sa, amma ya kasa bashida burin da yawuce ganin babu ɗan uwan nasa a doron duniya gaba ɗaya,
Shikuma sai ya maye gurbin sa idan bai samu dama ba dole yaÉ—ora É—an sa wato mudassir yaya ga sultana.!!!

*_F pen's_*
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _Typing📲_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALIN MU ÆŠAYA_*

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

*_Fatima Y zakariyya👌_*
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 7️⃣�8️⃣📖

Sosai Galadima Murtala ya ƙara tsanar ɗan uwan nasa Sarki Yusuf, amma saboda tsabar makirci baya taɓa nunawa a fili, kullum ƙarashiga jikin sa yake domin yasamu ma Kasar sa, amma Allah bai bashi dama ba har zuwa wannan lokacin, bashida burin da yawuce, yaga babu ɗan uwan nasa a doran duniya gaba ɗaya,
Daga nan kuma sai ya maye gurbinsa na sarki, idan hakan bai samu ba, yaɗaukar wa kansa alwashin dole yaɗora ɗan sa mudassir, duk da a lokacin mudassir ɗin ƙaramine,

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Sosai bahijjah (Ummul Bait) tasamu karɓuwa daga wani ɓangare na mutanan masarautar saboda batashiga harkar kowa tsakanin ta da mutane kyautata wace sai girmama juna, shiyasa wasu keson ta bata da wulaƙanci Sam duk da irin matsayin da take dashi acikin masarautar gabas,
Duk da tana fuskantar ƙalubale dayawa daga ɓangaran Facalolin ta da kuma kishiyar uwar mijin ta wato Giwar sarki Adam me murabis, amma bata taɓa kulawa ba ita basune agaban taba batada wani buri daya wuce ganin ɗan ta Sultan yasamu lafiya yazama cikakkyan yaro mai lafiya da kuzari kamar kowane ɗa duk da wasu abubuwan dayake tamkar shafar aljanu ko asiri, kullum cikin addu'a take,

Lokacin tsohon sarki wato sarki adam yaɗaurawa ɗansa, sarki Yusuf aure da ƴar abokin sa wazirin Gombe, mai suna Fa'iza ba don sarki Yusuf ya so ba haka ya karɓi umarnin mahaifin nasa saboda bazai iya jayayya dashiba sannan yana ganin auran sa nafari yayi shine batare da sanin iyayen saba, kuma suka yi hak'uri ya zauna da matar,
Don haka dole shima ya karɓi nasu umarnin, amma tabbas aranshi yafison rayuwa da matar shi wato bahijjah,

Fa'iza ƴar gidan sarauta ce Tunda ta shiga masarautar gabas tasamu labarin, uwar gidan mijin ta, ƴan gudun hijirane ita da Mahaifiyar ta, shikenan tasamu damar rainata da wulaƙanci kala kala, Tunda sarki Yusuf yasamu labari sosai aranshi yaɓaci saboda bahijjah bata taɓa gaya masa abunda ke faruwa ba,
Da babbar murya yajawa Fa'iza wani kyakkyan kashedi tare da jamata layi, yafaÉ—a mata ta tsaya iya matsayin ta, idan ba haka ba zai iyarabuwa da ita don shi bai haÉ—a matar shi bahijjah da komai ba,

Ta razana kwarai dajin abunda sarki Yusuf yafaɗa, take taƙarajin tsanar Bahijjah aranta, tare da ɗaukar mummunan al'washi akan ta,
Lokacin da Fa'iza ta cika shekara É—aya a masarautar hakan yayi dai dai da haihuwar É—an ta na fari, wanda yaci suna Safwan, hakan yasa ake kiran ta da (ummu Safwan) bayan Fulanin sarki da ake kiran ta dashi,

A lokacin ne matar sarki Abdullahi mai rasuwa, tasa wasu ƴan fashi shiga cikin masarautar don yin gagarumar sata ta manya manya dukiya hadda hatimin Zaki na masarautar kasancewar na ƙarfe mai darajane zinare, tare da samun haɗun bakin wasu manya manyan mutane acikin masarautar da fadawa,
Cikin rashin sa'a aka kamasu, sanda labari ya risketa cewar ankamasu take ta haÉ—a kayan ta tsaf daniyar guduwa ita da É—an ta mu'azzam, sai shaheedah wadda bata haura wata takwas ba a duniya,

Ƴan fashin da akakamasu da fari sunyi gaddama wajan faɗan gaskiya amma da sukaji azaba mai radaɗi, babu shiri suka bayyana wadda ta sasu tare da magoya bayan ta,
Cikin sauri sarki yabada umarnin azo masa damar É—an uwan sa Abdullahi, bata samu nasarar guduwa ba aka caff ke ta, kuda aka zauna zaman shari'ar sirri saboda duk cikin gida ne sarki yabada umarnin kada a fitar da maganar,
Koda aka tambaye ta Meye dalilin ta na aikata hakan, babu wata kwakkwarar hujja, bata bayyana musu gaskiya ba, hakan yasa alƙalan fada yanke mata hukunci, nabarin cikin masarauta gabas na har'abada babu ita ba masarautar, tare da barin garin Barno gaba ɗaya, cikin tsananin tashin hankali da danasani mara amfani ta kwanta ta shiga kuka da ban hak'uri amma ina, babu wanda ya saurare ta,

Mai martaba sarki Yusuf yaroƙi alfarmar alƙalan fada kan cewar, Tunda ita kaɗai tayi laifi ayi wa yaran afuwa abarsu a cikin masarautar su rayuwa ƙarƙashin kulawar sa,
Nanfa aka sake sabon zama, saidai sarki bai samu yadda yake so ba, saboda ƙin amincewa da sukai tare da Faɗin saidai akarɓi jariryar wato shaheedah, itakuma ta tafi da mu'azzam, babu yadda sarki Yusuf ya iya haka ya hak'uri yakarɓi shaheedah tare da damƙa amanar ta a hannun matar shi ummul bait, cikin farin ciki da jin daɗi ta karɓi shaheedah,
Cikin adalci irin nasa yasa aka kai ta har airport tare da mallaka mata hamshaƙin gida acikin garin Kano, ya buɗe mata account wanda za a rinƙa sama ta kuɗe koda yaushe, tare da damƙa mata gadon ɗan ta mu'azzam baki ɗaya wanda mahaifin sa ya bari sai yabar na shaheedah a hannun Ƙanin sa Galadima Murtala,

Cikin kuka tabar masarautar gabas, wanda son zuciyar ta ya janyo mata, nasa Æ´an fashi suyi gagarumar sata saboda tana ganin, sarautar da take kwaÉ—ayin mijin ta yayi to babu shi a duniya, tanaganin bata da wani mahimmanci acikin masarautar, babu abunda zata samu sai abunda mijin ta yabar musu, shiyasa ta aikata hakan,

Wannan shine dalilin barin Mahaifiyar Gimbiya shaheedah daga cikin masarautar gabas tare da ɗan ta mu'azzam wanda hakan yasa ta tsani kowa dake cikin masarautar tare da mummunan al'washi aranta sannan tayi alƙawarin koba daɗi ko bajima sai ta dawo masarautar gabas tare da ɗan ta kuma sai ya mulki masarautar sannan ta ɗauke ƴar ta da aka karɓa, da wannan tunani takoma garin Kano cikin baƙin cikin karɓar mata ƴar ta shaheedah da akayi,

ƙarshan taƙai taccan tarihin Sarki Yusuf Adam shareef kenan,

"Mukoma asalin labari"

*_GARIN KANO_*

Railway Quarters Arab Estate.....

Night 10:04pm
Alhaji imran tun ranar dayayi ar'ba da fuskar Suhaima wani abu wanda ya rasa Meye shi, ya tsaya masa acikin kai, tunani kala kala acikin kwakwalwar sa, mutanan da suka kasan ce wani jigo na rayuwar sa, wanda azahiri sun daÉ—e da shuÉ—ewa, sune suka dawu cikin tunanin sa,
Cikin ransa yafara tunanin Tabbas ita ɗin wani ɓangare ne na rayuwa ta, tabbas fuskar ƴar uwata nake gani atare da yarinyar nan, shin su waye iyayen ta? Zanso ƙara ganin fuskar ta, duk da taroƙeni batason wani bayan ni yaƙara ganin fuskar ta acikin gidan nan,
Chapter 5 · 0% Book details