← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 90

Sashe 47

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eh shine abunda nake faÉ—a miki idan muka sameshi to tabbas mungama samun komai a duniya,
To babban abun tashin hankalin bansan a ina zamu samoshiba, saboda shi ɗin mallakin wannan Masarautar ne tun kakannen iyayen mu, dalilin barin sa Masarautar nan shine wani yaƙi da akai tsakanin Masarautar ABZIN Dake yankin ƙasar NIGER Cikin garin AGADAS zamanin sarki Shareef zaki, a lokacin aka nemeshi aka rasa,

Kallon shi Hajiya mai soro take tamkar zata fashe da kuka jin, sunga samu sunga rashi,

Ɗorawa Galadima yayi da cewa amma yanzu Sarkin Bokaye yake sanar min da cewa tabbas HATIMIN mallaka yana nan kuma Akusa damu idan har muka yi nasarar samoshi to matsalar tazo ƙarshe,

Cikin sauri Hajiya mai soro tace to abazama neman shi mana idan ma mutane baza su iyaba atura Aljanu susa moshi mana,!

Shiru Galadima murtala yayi kafin yamiƙe kamar wanda aka tsikara yace inazuwa cikin sauri yayi waje,

Yana fita aka sanar wa da Hajiya mai soro isowar, Matar ɗan ta Mudassir Wato Sa'adatu wadda ake kiran ta da Kilishi, saboda itace babbar Ƴa ga sarki Yusuf shareef, wadda Mahaifiyar ta yafara aure kafin Ummul Bait, tun tana ƙarama Mahaifiyar tata ta rasu, tata so a gurin Kakar su Mahaifiyar su sarki Yusuf, sai suka haɗa auran zumin tsakanin, ɗan gidan Galadima Wato Mudassir da ita Sa'da Kilishi,

Bayan ta fashe da Hajiya mai soro cikin isa da ƙasaita, tace waini Hajiya naji wata magana shin da gaske ne akwai tabbacin maganar kuwa?

Kallon ta mai soro tayi wace magana kuma?

Mai martaba sarki mahaifina, shin ya sadaukar da rabin Masarautar nan ga Sultan,!

Hararar ƙasan ido mai soro tayi mata aranta tace wai mai martaba mahaifin ta, to ina ruwan mu da mahaifinki, mahaifin naki mara adalci kamar wata tsiyar yake tsinanawa,
Afili kuma tace eh muma haka muka samu labari, tafaɗa ataƙai ce,

Miƙewa Kilishi tayi tare da gyara zaman Alkabbar jikin ta cikin jin wani irin zafi a zuciyar ta ta furta nabarki lafiya, tafita zuwa sa shan su saboda tasamu amsar abunda takeson ji saboda bata samu zuwa wajan hawan da Yarima Sultan yayiba shiyasa bataji komai daya wakana ba saida mijin ta ya dawo a hautsine yabata labari,

Tana tafe cikin ranta tana tunanin wlh bazai yiyuba kullum burin ta shine mijin ta Mudassir ya gaji kujerar mahaifin ta, amma shine za ayi kyauta da Rabin Masarauta, cikin sauri ta ƙarasa shiga cikin sa shan tare da kuyangi biyu a bayan ta, a zahiri tace ai dole na je Fada yau gurin Mai martaba sarki,

_________________________
____________________
_____________

Idan ka raunata kanka aikin banza kayi gara Ka tsaya ka fuskance ni mu samu hanyar bullewa,

Haba Fulani taya za ayi ace sarki ya bada wani ɓan gare acikin masarautar mu, kuma ga ɗan uwana, sai kace niba ɗanshi bane, yarima Safwan ne ke magana hannun sa ɗaya na zubar da jini sakamakon wata kwalbar turare da ya fasa, saboda tsabar baƙin cikin abun da ya faru,

Fulanin sarki wato (ummu Safwan) wadda idanuwan ta suka kaÉ—a sukai ja abunka da farin mutum hatta jijiyoyin ta ana gani sunyi data dara fuskar Nan babu annuri,
Kar kabari fushin ka yarinjayi hankalin ka yanzu Meye amfanin wannan abunda kayi, idan har ka yadda da abunda nake faɗa maka to ka kwantar da hankalin ka komai ya kusa zuwa ƙarshe, a yau ba ƙar amin mamaki nayi ba ganin Yaron nan yayi hawa lafiya duk abunda muka shirya akansa ya warware, bansan Meye dalilin hakan ba saboda gabaɗaya filin hawan saida nasa akayi aiki a gurin amma duk abanza,
Nasan abunda zanyi yanzu ga likita yazo katashi muje ya duba ka,

To wai Fulani ita wannan Yarin yar da tayi zamiya da sultan yayin gabatar da hawan sa wacece ita?

izuwa yanzu banda wata masaniya dangane da ita ba musan daga wace masarautar tazo ba, amma nasa ayi bincike akanta saboda naga haske atattare da Yarin yar dole mu kawar da ita gudun matsala, sannan babu fashi matar yarima Tafar ko itace Siyama,
Naji labarin Yarin yar ta gudu daga taron batare da sanin kowa ba amma dole za asamota,!

Batare da Yarima Safwan yace komai ba yatashi zuwa parlour don ayi masa treatment a hannun sa da yajiwa rauni saboda fushi..!!

*_F pen's✍️_*
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _Typing📲_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALIN MU ÆŠAYA_*

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

*_Fatima Y zakariyya👌_*
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

*_Ina mai farin cikin sake haɗuwa daku a cikin Littafin AHALIN MU ƊAYA. Kashi na biyu, ina roƙon Allah ya amfanar da mu abin da ke cikin sa, akasin haka kuma da kuskure na ku watsar dashi gefe, saboda nima mutum ce kamar kowa zanyi dai dai zanyi kuskure, domin ɗan Adam ajizi ne, Allah ya shiga dukkan lamuran mu yayi mana jagoran ci_*

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 3️⃣�4️⃣📖

Batare da yarima safwan yace komai ba yata shi zuwa parlour, saboda an sanar masa zuwan DR. Zaiyi masa treatment a hannun sa da yaji ciwo, duk a ƙoƙarin kawar da fushin sa,

A ɓangaran Ummul bait, sosai tasa aka shiga neman princess Salma, wadda ta gudu kafin atashi taga gurin taron, ko ina anduba acikin Masarautar amma babu ita ba alamar ta,
Sai da tayi aike zuwa Sarkin ƙofa take yashai da musu babu wani baƙo da yafita daga masarautar,
Mamaki ummul bait tayi tare da Faɗin to tabbas Yarin yar tana cikin masarautar, to amma ina ta shiga?, a ina za asamota? Shin wa ce ce ita? Meye alaƙar ta da ɗana Yarima Sultan har take kiranshi da yayan ta?,
Waɗan nan tambayoyin sune suka yiwa ummul bait tsaye cikin ƙokwan rai, alƙawari ta ɗaukar wa kanta kowa ce ce wannan sai ta gano ta,

Ya shugaba ta, Allah ya ƙara miki lafiya, gani na amsa kiran gimbiya, cewar wata kuyanga dake zaune daga gefan Gimbiya shaheedah wadda ke zaune ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sai wani siririn glass dake Idon ta jikin ta sanye da riga da wando jikin su yanayin Kayan sanyi, amma kanta ko hula babu ta ɗaure gashin ta a tsakiyar kai ƙafar ta ɗaya sanye da tsarƙa ta zinare,
Saida tagama danna wayar ta kafin taÉ—ago dakanta kamar wadda akayi wa dole, ta kalli kuyangar dake zaune gaban ta ko kwakwkwaran motsi batayi saboda tsabar girmama wa,
Magana tafara ahankali tamkar mai ciwon baki,
Barira inason ki sanar min menene labarin da kika samo game da Yarin yar nan da tayi wa Yarima Sultan zamiya a filin Hawa, ina son jin komai dangane da ita,
Kuyangar nan da aka kira da Bariri cikin girmamawa ta ƙara russunawa sosai kafin tace, " Allah ya temaki uwar ɗakina, babu wani tabbataccan labari game da ita saboda tayi ɓatan dabo acikin masarautar nan, hatta uwar gidan sarki (Ummul bait) tasa ane momata ita,"

Kallon ta gimbiya shaheedah tayi sosai tana nazarin wani abu, aranta can kuma tasa hannu ta É—au wayar ta,
Kinsan waye wannan? Yaya girman alaƙar su yake shida Yarima Sultan,

Kallon fuskar wayar Kuyanga Barira tayi take kyakkyawar fuskar Sulaim ta bayyana cikin faffaɗan screen ɗin wayar saida taɗan kalla sosai kafin tace, Allah ya ƙara salama acikin zuciyar shugaba ta, wannan ai aminin Yarima ne, akwai tsananin So da shaƙuwa a tsakanin su,

Kafin ta ƙara gimbiya shaheedah amma ai bansan shiba, sannan Meye Sunan sa?

Ranki ya daɗe Shidin babaƙo bane a masarautar nan kowa yasan shi, ina tunanin kema don bakya ƙasar shiyasa biki sanan shiba, idan kika ganshi anan to tabbas Yarima na nan, sannan banida masani ya akan Sunan sa nafi jin kowa nakiran sa da Aminin Sultan,

Jinjina kai Gimbiya shaheedah tayi cikin ƙasan maƙoshin ta tace zaki iya tafiya idan da buƙatar wani abu zanne meki,

Angama, nabarki cikin aminci Gimbiya ƴar sarki jikar sarki, Allah yajiƙan Mahaifin gimbiya, Galadima Abdullahi Allah ya kyauta ta makwancin sa, takai ƙarshan maganar tare da miƙewa ta fice,

Lumshe ido Shaheedah tayi tare da ɗan jingina bayan ta da jikin kujerar, da alama ba bacci take ba, ta nutsa cikin tunanin da take wayar ta ta ɗauki ruri, ko motsawa batayi ba bare asaran zata ɗaga wayar, akaro na biyu wayar ta ta ƙara ɗaukar ruri, saida takusa tsinkewa sannan ta kai hannu ta ɗauki wayar batare da ta buɗe idonuwan taba,
Cikin sanyin murya wanda hakan kamar ajinin ta yake, "tace hello Mom barka da warhaka" tare da sa wayar a hansakowa, yadda da dawani akusa zai iya jin abunda tacikin wayar ke faÉ—a,
" barka dai shaheedah fatan kin isa lafiya, shiru Gimbiya shaheedah tayi batare da za tace wani abu ba,

Jin shirun yayi yawa ne Tace mom inajin kifa idan babu wani abu zan iya ajiye waya,

Magana akacigaba dayi ta ɗayan ɓangaran wadda aka kira da mom tace, " shaheedah ina son sanar miki dole zaki haƙura da Auran Yarima Sultan, ki auri yarima Safwan ɗan gidan Fulanin sarki,

Sai a lokacin gimbiya Shaheeda tabuɗe idanuwan ta ahankali, kafin tace komai Mom taci gaba da Faɗin," saboda munsamu tabbacin, Yarima Safwan ne zai gaji karagar mahaifin sa nan kusa, to kinga dole shizaki aura, domin lokacin cikar wasiyyar mahaifin ki yayi, kinsan dai haryana kan gaɓar mutuwa abu ɗaya yake faɗa, Mulki! Mulki!! Mulki!!!
Kada mubari mulki yabar hannun mu tun dashi mafarkin sa nason hawa karagar sarki mai cikaba, har Allah yayi masa rasuwa to dole ne É—ansa ya gada,
Shaheedah inaso kisani kece zaki iyadawo da martabar mu, amma hakan bazai samuba idan har ba auran Safwan kikai ba, Tunda sarki Yusuf yasa aka yimana korar kare acikin Masarautar nan nida ɗan uwa ki banƙara Bacci mai daɗi ba kema kinsani, sannan yakwace ki daga hannu na to nayi kuka kamar raina zai fita, amma gashi yanzu Rainon da yayi miki zai amfane mu, kice makasar su tabbas nasan zaki iya,
Chapter 47 · 0% Book details