← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 90

Sashe 77

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barrister Sulaiman ke zaune shida khaltum hannun ta ruƙe da Chocolate Shikuma yana shan coffee, Dakagan su kasan suna cikin nishaɗi da farin ciki, Khaltum har ta canza shiga yanzu Riga da wando ne a jikin ta rigar har gwaiwa T-Bubu amma ƴar kanti, shikuma wanda ya buɗe sosai daga ƙasa, Hulace a kanta dagani ta kayan ce,"

Yallaɓai nagode sosai, da Alkhairin ka a gareni, Kullum baka gajiya kayan nan da kake ta siyamin ai sunyi yawa,

Dariya yayi wanda har haƙoransa saida suka bayyana, _My Beautiful_ nace kidaina cemin Yallaɓai bana so, kisamu wani sunan mai daɗi ki ringa faɗa min, kuma Duk abunda na siya na baki ai banfaɗi ba ko kinma sonki nake sannan auranki zanyi,
Nanda wata biyu za'a É—auramin aure da Sabrina, anayi ba jimawa tsakani kema zan aure ki, Fatan dai kinshirya zama da Kishiya ya tambaye yana kallon idon ta cikin sigar wasa,"

Ƙasa tayi dakai yana wasa da ya tsunta, Kafin tace, Ni gaskiya bana son kishiya ban tsara rayuwata da haɗa miji da wataba ko wace, Amma Indai akan kane na yadda inzamu nice ta huɗu 4 ma,
Amma inajin tsoro fa, Naga Sabrinan kamar tanada faÉ—a sannan kuma ita Æ´ar uwar kace gata kamar balarabiya tafini kyau..!!

Hhm kwaÉ—ayi mabuÉ—in Wahala khaltum sai a kula.

*_Wannan kenan daga alƙalamin_*
_F pen_✍️.
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS ......✨�*
*_T.M.W_✍️*

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

*_TEAM FIVE STARS💫_*

*TAURARI BIYAR*✨✨✨✨�

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 4�1⃣➖4�2⃣�

*Khaltum*

"Ni fa ina jin tsoro, Na ga Sabrina kamar tana da faÉ—a, kuma ka ga ita É—in Æ´ar uwar kace, gata da kyau kamar balarabiya, Tafini kyau, wai ku gaba É—ayan ku haka kuke? TafaÉ—a Tare da kai kallon ta Kan Barrister Sulaiman, sai akayi sa'a Shima ita yake kallon,"

Ƙara Matsawa yayi sosai Jikin khaltum Hartanajin ƙamshin turaran sa tamkar ita tasa, Abunka da wadda bata saba ba, gaba ɗaya ta takure jikin ta guri ɗaya, jin yakama hannun ta yasa ta saurin Runtse ido,

Murmushi Yayi, kafin yace wai Meyasa baza ki waye ba, wannan duk nameye? Emm, hakan ya nuna bakya sona kenan ko?

"A'a Nifa bahaka nake nufi ba, Kawai dai Ni bansaba irin wannan abun ba, Babu wanda ya taɓa zuwa kusa dani irin haka, Saboda Mother tace Babu kyau matuƙar ba aure kukai ba, A Film kawai nake ganin irin haka"

Ɗaure Fuska Barrister Sulaiman yayi, Yace To Nima ai auran naki zanyi ko kin manta, Sannan duk wanda yafaɗa miki Haka Ƙarya ne....

Zunbur Khaltum ta miƙe tsaye kamar wadda aka tsikarawa allura har saida Barrister ya ɗan tsorata yayi tsammanin wani abune ya cijeta,
" Khaltum tace, Mother Bata ƙarya, Bakasan wace ita A guri naba, ita ɗin uwa ce da babu kamar ta,

Ganin ya kafeta da ido hakan yasa tayin shiru, Tare da Sunkuyar dakai, Da'alama ta manta dawa take magana,
Yallabai kayi haƙuri na manta kaine,"

Shi dariya ma ta bashi, Saboda har ga Allah yake Son ta, ya rasa Dalili,
"Bakomai Zo ki zauna, Saida ta zauna sannan ya cigaba da magana,
Beauty, Nifa bawasa nakeba da gaske ina sonki, Yakama ki saki jikinki, Idan kika saki jiki zakiji daɗin rayuwa dani komai zan miki babu abunda zaki nema ki rasa matuƙar ina raye, Sannan aure na da Sabrina ba wata matsala bane, Akwai dalilin yinshi, zan iya auran ki kuma in aure Sabrina Duka a rana ɗaya, babu wanda ya isa ya hana, Sannan nifa a gurina kinfi kowace mace kyau a duniya kema daina haɗa kanki da wata,"

Murmushi Khaltum kaye Wanda dagani kasan tun daga ƙasan zuciyar ta yake, Ashema Nafita kyau hasken fata kawai zata gwadamin, kuma shima idan na cigaba dacin kayan daɗi sai nazo Nafita, Tunanin ta zancen zuci take wanda batasan yafito fili ba,"

Ganin Barrister na dariya Sosai hakan yasa ta saure dafe bakin ta,
Hannu yakai yaɗan ja kumatun ta kaɗan, Kinganki ko bakyaji Ashe kayan daɗi ne suke sa Hasken fata, Idan Sune kuwa to Saikin fi kowa ce mace haske a duniya, Wannan alƙawari ne,

Kin san me kuwa?

Da sauri Khaltum tace A'a,

Zanyi miki, Wata babbar bazata Amma sai gobe, yanzu dai tashi mu tafi,"

"Cikin nishaɗi dajin daɗi ta miƙe, Hannun ta cikin nashi Suka nufi Sashen sa",

*Dr Jabir*
Kwance yake Saman kujera, Mai mazaunin mutum Uku 3 siter, gaba ɗaya ya tattara hankalin shi, Akan Screen ɗin wayar shi, Daka ganshi basai anfaɗa maka yana cikin Annushiwa, yanayin sa kaɗai Ya Isa kagane, video Call Suke shida Dr.Anisha Wanda itama Anata ɓangaran Tana cikin Farin ciki,
" My Dr. Kasan me?

Girgiza kai Dr. Jabir yayi, Kafin Yace, A'a Rayuwata saikin faÉ—a"

Em, Dama, Am Yama tafaÉ—a tana kallon Shi ta screen É—in,

Murmushi yayi kafin yace, Hayatiy Ai bansan Meye za kifaÉ—a ba, Dan Allah kifaÉ—a min inajin ki,

To shikenan kashirya infaɗa maka,? Dr. Aisha ta ƙara tambayar sa akaro na biyu,
Shima ƙara ɗaga mata kai yayi kamar ƙaramin yaro,

Saida Dr. Anisha tagama jamasa rai, tagama sa masa tunanin wani babban Abun zata faÉ—a kawai tace,
"Yauwa My Dr. Kanaji ba

Em Rayuwar Jabir, Ina jinki Inajiran ki Bazan gajiba, duk abunda kikai girman kine,

Awwwn😍
To rufe idon ka, ba musu ya rufe Idon sa kamar yadda ta buƙata,

Cikin Nutsuwa, Dalla Dalla, Ta Furta,
Ina Son Ka, _I love you More than My Self_,"

Jin daÉ—in kalamanta ne ya hana Dr. Jabir buÉ—e ido har'na tsawon wani lokaci, Murmushi kawai yake famanyi, jiyayi kanshi yana Masa yawo a sararin Samaniya,

KabuÉ—e idon ka mana,

A hankali ya ware idon sa akan Fuskar ta Tana Murmushi, Hannu yasa yashafi gefan Fuskar ta tasaman Screen É—in Wayar tashi Sannan yace,
"Lillahi Ya faranta miki Hayatiy, ina ƙaunar ki fiye da rayuwa ta, Komai ya kusa zuwa ƙarshe, nan da 2 months zakiza ma mallakin Jabir gaba ɗaya,
Anisha," cikin Sanyi murya yakira Sunan ta,

Na'am, Ta amsa tare da maida hankalin ta gurin shi baki É—aya,

Zanyi miki wata tambaya, Ina fatan zaki amsamin,

Insha Allah, taba shi amsa,

Kinga jiya, Aka Samana Ranar aure, Nayi matuƙar farin ciki, jin abun nake tamkar a mafarki, Sannan nayi mamakin karɓar soyayya ta da kikayi da Sauri haka, wanda banyi tsammani ba, keɗin ta musamman ce acikin rayuwa ta,
Ina son kifaÉ—amin, har yanzu kina son Dr. Sulaim?.

Kyakkyawar Fuskar ta da ta ɓace daga Saman Screen ɗin wayar sa hakan ya tabbatar masa data Kashe Kiran, cikin Sauri ya ƙara kiran ta amma ina Bata ɗaga ba Da'alama tama sauka daga Layi,
Oh Allah Jabir ka kwafsa, YafaÉ—a tare da dafe goshin sa, Shikenan najawa kaina,ya faÉ—a dai dai yana tashi zaune daga kwanciyar da yake,"

*Princess*
Kallon Ya tsunta hannun ta take tana tafaman sakin murmushi Da'alama Jan lallan da akayi mata a ya tsun nata, Ya burgeta gashi Sunyi Ja sosai, zoben hannun ta É—aya ta dai dai tawa zama saboda yaÉ—an kar kace,
Take zuciyar ta ta tuna mata da wanda yabata, zoben nanYarima Sultan ne, Murmushi ta ƙara saki a karo na biyu,
Da sauri ta miƙe tayi hanyar Bedroom ɗin ta tunawa da tayi akwai Ɗayar Kyautar da Yarima Yabata wadda tama manta da ita bata duba taga Meye ba, hakan yasa ta tashi cikin Sassarfa,

"Diamond ina zuwa haka Cikin sauri?
Juyawa princess tayi ta kalle Mommy wadda suke zaune ita da Ummeetha suna Tattaunawa game da Yadda hidimar biki zata kasan ce,"

"Mommy yanzu zandawo, Wani abu zan É—akko a bedroom É—ina,

Afito Lafiya mommy tafaÉ—a, tare da maida hankalin ta gurin Ummeetha,

Bayan Princess tashiga, Bedroom ɗin Har key saida tayi masa taciki, Kafin tayi tsalle ta faɗa saman makeken Bed ɗin nata, Box ɗin ta ta janyo wadda Tunda suka dawo daga, Masarautar Gabas, bata ƙara koda taɓa taba, kayan ciki tashiga fito dasu ɗaya bayan ɗaya, saiga wannan kyautar da Yarima Sultan yabata wadda, Aranar bata kai ga buɗewa ba Ummeetha ta tazo,

BuÉ—ewa tashiga cikin zumuÉ—in ganin Meye aciki, saida tagama buÉ—e gaba É—aya ledar dake jiki kafin tazo kan kwalin waya,
"Waya, Princess tafaɗa a hankali kafin ta cigaba da ƙoƙarin buɗe kwalin,
Wow, ta furta tare da zaro wayar daga cikin kwalin ta, Wayar ta haɗu sosai ƴar madai dai ciya, ƙirar IPhone tafi waccan wayar tata girma wadda ta bari a part ɗin Yarima Sultan ɗin, Amma komai iri ɗaya, hatta colour ɗin, Murna tahana ta magana, iya kacin ta murmushi kawai,
Batare da wani dogon tunani ba, ta kunna wayar, Abunda ya É—aure mata kai ganin komai tayi akan tsari ansaita komai nakan wayar irin tsarin waccan tatan, gashi sim É—in tane aciki, hatta Hoton waccan wayar dake kan Wallpaper É—in ta, shine A saman wannan, Ga Full Charge,

Acan ɓangaran Yarima Sultan kuwa, Har wannan lokacin yana Cikin mota Ya rasa Abunda keyi masa daɗi yama rasa ta ina Zai fara,
Wannan "A gogon hannun nasa mai sanar masa da saƙone yayi ƙara tare da kawo haske, a hankali Yarima Sultan yakai duban sa, Kan Agogon,
Cikin ransa ya Furta, Sai yau taga damar kunna wayar kenan,"

Gani tayi Hatta Contact ɗin ta suna nan Babban abunda ya ƙara ɗaure mata kai hadda videos ɗin ta da pictures duka aciki, har lokacin mamaki Princess take badon wannan wayar tafi tata tsayi da faɗi ba, aida cewa zatayi tatace aka dawo mata da ita, Dayake Numbers ɗin dake cikin Contact ɗin nata basu da yawa, saida tagama dubawa su tsaf, Idon ta ne ya tsaya akan wata _Special Number_ amma babu Suna Ajiki, gashi Tazo cikin jeren contact ɗin ta wanda ita bata masan da'ita ba,
To wannan Number É—in waye? Ta tambayi kanta, ki kira kiji mana, kamar yadda zuciyar ta tabata Umarni haka tabi, kiran Number É—in ta shiga yi, sai kuma taji zuciyar ta na bugawa, Dum Dum"
Chapter 77 · 0% Book details