← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 90

Sashe 51

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyin murya Hajiya umma tace to shikenan alhaji insha Allah yadda kace haka za'ayi, saboda nasan duk abunda kayi, bazai cutar damuba don cigaban mu ne, Allah yasa tazama alkhairi acikin mu, amma ita Æ´ar uwar tata fa naji ita kaÉ—ai kake magana akai,

Har cikin ransa baffa yaji daɗin abunda yafito daga bakin Hajiya umma, dama yasan baza tataɓayimasa gaddama ba, kafin yace wani abu, suka tsinci Mama bilki akan su ta shigo babu ko sallama,

Wani irin mugun kallo ta jefawa Hajiya umma tare da jan guntun tsaki, batare da Hajiya umma tace komai ba ta tashi taraɓa mama bilki ta wuce, saboda dama yau girkin mama bilkin ne, badon kiran da baffa yayi mata ba daba tazo a irin wannan lokacin ba,

Ko zama batayiba bare gaisuwa mama bilki tace, alhaji Meye kuke tattaunawa da wannan matar, tayi tambayar cikin ƙuncin zuciya,

Ko kallon ta alhaji imran baiyi ba saima ya janyo, jaridar dake saman table tare da sai ta zaman medical glass É—in dake Idon sa,

Taɓe baki mama bilki tayi tare da zama ciki ciki ta furta barka da dare alhaji,

Ko kallon ta baiyi ba bare tasa ran zai amsa,

A fusace mama bilki ta tashi ta nufi bedroom É—in baffa,
Bayan ta yabi da kallo tare da girgiza kai, yamaida dubansa kan jaridar dayake karantawa,

Suhaima tafiya take cikin wani guri da yayi nesa da gida jan cikin estate, babu wada taccan haske a gurin tamkar daji, babu motsin wani mahaluƙi agurin sai kukan tsintsaye, ga iska tana busawa, da sanyi cikin nutsuwa Suhaima ke tura kai cikin ɗan dajin, bubu alamun tsoro ko kaɗan atare da ita tafiya take cike da kwarin gwaiwa,
Tana ƙara shiga ciki haske na ƙara gushewa,
Saida ta tabbata tayi nesa sosai da acikin gurin sannan ta tsaya cak, sai kuma ta tsugunna, tafa tsintar, ƙirare wanda suka faɗo daga saman bishiyun dake gurin acinkushe, rass rass rass gabanta yafaɗin jin takun mutum abayan ta, cikin ranta ta furta waye a wannan gurin cikin wannan duhun daran ga sanyi.!!!!

_F pen's_
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _Typing📲_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALIN MU ÆŠAYA_*

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿�9⃣➖1�0⃣�

Sai data tabbata tayi nisa sosai a cikin gurin sannan ta tsaya cak, tare da kasa kunne tamkar mai sauraron wani abu, shiru babu sautin komai illa na tsintsaye, sai ta tsugunna tafara tsintar ƙiraran bishiya wanda suka faɗo daga saman bishiyun gurin,
"Rass Rass Rass, gaban ta yafaÉ—i jin takun mutum abayan ta"
Cikin ranta ta furta waye a wannan gurin cikin wannan duhun daran ga sanyi, jin takun naƙara kusanto tane, yasa ta saurin miƙewa tsaye, a hankali ta juya don ganin waye, kallon kallo aka shiga yi tsakanin Suhaima da mutumin dake tsaye cikin shigar baƙaƙen kaya ƙugunsa ɗaure da jan ƙalle, yayi kwalliyar Jan fanti arabin fuskar shi, ba'a iya gane asalin kamanin sa, hannun sa ruƙe da wata ƴar madai dai ciyar ƙwarya, ƙafar sa ko ta kalmi babu, yaja ya tsaya cak daga ɗan nesa da Suhaima,

Wanda duk a tunanin sa, ko waye a gaban sa baya iya ganin sa saboda duhun dake gurin, batare da sanin Suhaima tagama kallon sa ba tun daga sama har ƙasa, shima kuma anashin ɓangaran yana kallon ta, amma bakamar yadda ita ke ganin saba,

Ganin Suhaima na tun karar sane hakan yasa shi fara ja dabaya kaɗan kaɗan, ganin haka ne Suhaima tafara sauri don cimma sa, amma ina tamkar isaka haka ya ɓace ɓat, waige waige ta shiga yi, cike da mamakin al'amarin da ya faru, ta tsaya shiru alamun nazari, kafin can tajuya abunta,

Ƙiraran da ta tattara su ta koma ta kwashe babu alamun tsoro a tattare da ita, kafin ta nufi hanyar da tabiyu sanda tashigo daniyar komawa, masaukin da aka basu kafin akai su inda zasu zauna,

Khaltum wadda tabaje saman carpet sai ciye ciye take, babu alamun damuwa, sannan babu alamun tashin hankali atare da ita, duk abunda take hankali kwance,
Da sallama Suhaima ta shiga parlourn ganin khaltum ta baje a ƙasa tare da kayan abinci, hakan ne yasa ta jan ɗan gudun tun tsaki, ta wuce khaltum ɗin batare da tace mata komai ba aranta tana mamakin hali irin na khaltum, da rashin lissafi irin nata duk da itace babba,

Tunda khaltum taga Suhaima ta wuce batare da tayi magana ba, sai ta taɓe baki ta cigaba da ciye ciyan ta,

Cikin minti nan da basu wuce goma ba Suhaima ta fito bayan ta adana ƙiraran da ta ɗebo a wannan ɗan ƙaramin dajin,
Guri tasamu saman kujera ta zauna, sosai, take kallon khaltum wadda bata masa tanayi ba,

Khaltum wai kinsan inane nan kuwa? Suhaima ta tambaye ta,

Au ashe kinfito, a a bansani ba, cewar khaltum,

Amma shine kawai kika zauna saicin abinci kike batare da sanin inda muka zo ba sannan baza ki tambaya ba, hankalinki kwance,

Sai a lokacin khaltum ta ajiye tsokar naman kazar dake hannun ta tare da É—aukar, fresh milk, Mai sanyin takora, sannan ta fuskanci Suhaima, tare da FaÉ—in,
Akan me za tambaye ki bayan duk tambayoyin danayi miki abaya nakasa samun amsar su, tun muna asibiti nake tambayar ki game da wasu abubuwan danakasa gane kansu a tattare dake, amma sai ki nuna bakida lokacina, kinga kuwa ai tambayar batada amfani, sannan kuma idan banci abinci ba Me zanyi, Tunda na fahimci ashe dama tsawon kwanakin nan da bakya zama ashe nan kike zuwa kina kwasar daɗi, shine nima nake fanshewa yanzu kafin ki kuma jana mubar nan ɗin, sai abu naƙar she, nibanga dalilin dazai sa na tashi hankalina ba Tunda nasan baza kikaine inda za'a cutar dani ba, takai ƙarshan maganar tare da kai lomar fish roll ɗin dake wani tire na kayan snacks,

Idan ran Suhaima yakai dubu to yagama ɓaci dama gata da saurin fushi, ganin duk ƙoƙarin da take saboda sune, sannan tana tausawa khaltum ɗin shiyasa take duk wata fafutuka ita kaɗai, amma shine ta rasa abunda zata gaya mata sai waɗan nan maganganun,
Batare da nuna komai ba, tace shikenan duka laifi nane, amma inaso insanar dake komai yanzu, zansanar dake kalma É—aya wadda ta isa tazama amsar tambayoyin ki gaba É—aya,

Kallon ta khaltum tayi cikin son jin abunda zata faÉ—a,

Ɗorawa Suhaima tayi da Faɗin, yanzu haka dani dake muna cikin inda muka daɗe muna nema, cikin gidan maƙiyan mu, ARAB ESTATE,

Zabura khaltum tayi tare da zaro ido cikin mamaki ta furta ARAB ESTATE?

ÆŠaga mata kai Suhaima tayi alamar eh,

Kasa zama khaltum tayi kamar wadda aka tsira da allora, haka ta tashi ta koma kusa da Suhaima ta zauna, tace amma taya ya kika samu nan ɗin har suka karɓe ki suka Bamu wannan kyakkyawan muhallin tare da kayan alatu na more rayuwa da daddaɗan abinci, tayaya???

Lokacin da muka taho a mota kina bacci har muka zo nan ɗin amma da Tunda ga bakin babban gate ɗin shigowa zaki ga sunan a rubuce don ko makaho yashafa zai iya karantawa, yanzu inaso kamar yadda hankalin ki yake a kwance kafin na sanar dake, yanzun ma ki kwantar da hankalin ki, saboda nasamu karɓuwa sosai a gurin mamallakin wannan Estate ɗin sannan da alama shi ɗin mutumin kirki ne duk da baza mu'iya gane hakan ba a yanzu, nidai ina roƙon ki da kibani haɗin kai sosai muyi abunda yakawomu mubar garin nan, sannan nidake ba guri ɗaya zamu zauna ba kowa da inda za'akaishe, naji daɗin hakan saboda zamu rinƙa samun bayanai ta kowane ɓangare, sannan zan samu mana waya wadda zamu rinƙa sanar da mother komai kinga Tunda muka baro Bichi mu bamuyi waya da ita ba, Suhaima takai ƙarshan maganar Indon ta tab da kwalla saboda ta tuna da mother,

Sosai khaltum ke kuka saboda jin maganganun Suhaima, a hankali ta rungume Suhaiman tare da FaÉ—in dan Allah Æ´ar uwata ki yafemin, nayi miki mummunar fahimta har nafaÉ—a miki maganganu marasa daÉ—i abisa rashin sani dan Allah kiyi hak'uri,

Da sauri Suhaima ta goge kwallar dake idon saboda bata son zuciyar ta takaryi, tare da sakin murmushi mai sauti, saitin kunnan khaltum ta furta,
" Laaaa laaa wai kuka kikeye lallai waya gaya miki jarumai suna kuka, bai kamata ba, nafiso ki adana hawayanki har zuwa lokacin da zamuyi nasarar É—aukar fansar mu, kinga lokacin hawaye zasu yi amfani, saboda zamuyi kukan farin ciki babu mai hana mu,

Dariya khaltum tayi tare da Faɗin inason ki sosai Allah yarayamu tare da juna cikin aminci da ƙauna, Suhaima na daɗe ina faɗa miki ke ɗin ta musamman ce a cikin mutane samun kamar ke sai antona duk wanda yake da ƴar uwa irinki to tabbas bazai taɓa kukan rashi a rayuwa ba, insha Allah zamuyi nasara ɗari bisa ɗari,
Sai dai abu É—aya ina jin tsoro"

Hannun Suhaima tasa tare da share hawayen da suka wankewa khaltum fuska, cikin tausasawa Suhaima tace, kada kiji tsoron komai, Allah yana tare da mai gaskiya, nasara tana tare da jajirtattun mutane, idan kikaji tsoro to tabbas zamuyi rashin nasara, wanda bazan bari hakan ya faruba, da yaddar Allah, sannan duk ɓangaran da aka kai ki acikin estate ɗin nan ina tare dake koda yaushe, kikasan ce cikin farin ciki da nutsuwa, idan kika zama mai gaskiya to komai naki zaizo cikin nasara yadda kike so,
Tana kaiwa nan tazare jikin ta daga na khaltum, ta nufi inda kayan abincin nan suke,

Kallon ta khaltum tayi tama kasa magana saboda jikin ta duk yayi sanyi,

Duk da fuskar Suhaima a rufe take amma alamu sun nuna murmushi take yiwa khaltum tare da FaÉ—in malama sakko ki cigaba dacin abincin ki saboda ni rabona da abinci irin haka tun muna asibitin nan tsawan kwana 3,
Chapter 51 · 0% Book details