← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 90

Sashe 71

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Turai tace, Daughter Bawasa Nake ba Keda Sai yau kika taɓaji, Aikowa yasan Bashi kaɗai bane, Shiru Sabrina tayi Kamar mai Nazari wani abu,
Sosai hajiya Turai taji daÉ—i ganin tafara shawo kan Æ´ar tata,

Yauwa Mammy naji Shikenan, na yadda amma da sharaÉ—i É—aya,

Cikin hanzari Hajiya Turai tace, Ina jinki komeye za'ayi,

Murmushi Sabrina tayi akaron farko Tunda Suka fara maganar da mahaifiyarta ta, Mammy zan Auri Barrister Sulaiman, zanzauna dashi na 2 years ko Shekara É—aya da rabi, Sannan Yaya Sulaim yasamu lafiya Tunda kince bashida lafiya zuwa lokacin sai murabashi da waccan Banzar Saleema Nikuma na'Aure shi,"

Kallon ta kawai hajiya Turai take ta marasa abunda za tace, tsabar takaici da baƙin ciki,
"Cikin ranta tace, Wato yarinyar nan, baza ta taɓa gane abunda Muke so ta gane ba, Mtsss taja dogon tsaki, Afili kuwa Murmushin Saman laɓɓatayi Tace Ta shikenan Daughter zanyi magana da Da DADAN naki za'ayi duk yadda kike so,"

Tashi Sabrina tayi ta nufi Parlour wani ɓangaran na zuciyar ta Bai karɓi amincewar tayi ba, Saijin ɓacin rai take cikin Ranta,

Bayan Fitar Sabrina waya Hajiya Turai ta É—auka tare da dannawa He Excellency Sambo kira,

Dama yanzu zankira ki, Saboda yanzu zamu shiga Meeting Room É—in, inaso inji ta Amince kafin mushiga,

Saida hajiya Turai ta nisa kafin tace, Eh ta amince amma, da sharaÉ—i Kasan yarinyar nan taurin kaine da ita, har maganin nan saida nabata amma duk a banza kamar bata shaba,"

Oky Tunda ta amince da kyau Sharaɗin kuma kunameye idan nadawo kyafaɗa min lokaci ya ƙure, yana kai wanan yayi rejecting call ɗin,"

Gaba ɗaya Sun haɗu a babban Parlourn Baffa manyan ƴaƴan gidan kawai ake jira, Alhaji Hameed, sai Mai Girma Hasheem, Alhaji Hameed yabada uzirin Meeting ɗin office ne ya tsaida shi amma gashinan zuwa, Mai Girma Hasheem kuwa babu wani Dalili, Zuba'idon ganin sa kawai ake baffa har sawa yayi aka kira wayar shi amma ba'a picking, shikuma baffa aƙa idar shi ba'a meeting idan babu ɗaya daga cikin su saidai idan mutum baya ƙasar,"

Ganin ba agama haɗuwa ba hakan yasa, Uncle Mansur ƙara tashi a karo na biyu, kai tsaye ya nufi kujerar da Baffa yake zaune, Russunawa yayi a gaban Baffa cikin girmamawa,
Baffa inason abani izinin Fita Uziri ne yataso amin Afuwa na minti 10,

Batare da Baffa ya kalle inda yake ba, Yace zaka'iya tafiya nabaka minti 15 ma,"

"Ina godiya ya faÉ—a tare da nufar waje cikin hanzari,

Uncle wai Meye ya faru kabani tsoro da Allah yasa lafiya dai, Barrister Sulaiman yafaɗa tare da zuƙar hayaƙin Sigarin dake hannun sa, Ita kanta Sigarin ta musamman ce ba irin gama garin nan ba,"

Uncle Mansur yace Bari kawai A lokacin nan da kaji ne a razane Gamo nayi,

Murmushin Barrister Sulaiman yayi Yana Fitar za hayaƙin dayazuƙa cikin wani irin salo na kwararru acikin harkar, Haba Uncle Gamo fa kace, To gamo dame?

"Aljani mana kamar yadda mahaifinka yayi gamo da Aljana kwanakin nan har yazo yana tambayar mu ko ankawo sabbin masu aiki, Cewar Uncle Mansur, Wallahi ina gaya maka wani irin wawan karo mukayi har saida kawunan mu suka gwaru, maganar sa kawai naji amma ban iya ganin komai a tattare dashiba, ai wlh nayi Dana sanin cewar ka kashe gaba ɗaya wutar estate ɗin nan, Kuma lokacin da ka kunna bangan shiba ko alamar sa babu, wani ƙarin abun mamakin har haƙuri Yabani tare da tattaro min kayana da suka zube Yabani,"

Hhh, Uncle Kennan wlh ni kabani tsoro a time É—in nan nayi tunanin wata matsalar ce ta faru, to wai a ina makayi gamon?

"A cikin House É—in Baffa gab da zanshiga Part É—in sa, Kwatsam naji munyi karo, abun Yabani tsoro kuma kamar part É—in Sulaim yanufa,"

Uncle Bafa komai, Tunda Duhu ne bazaka iya gane komai ba, Maybe Abokin Sulaim É—in ne yazo, Amma babu wani Gamo da kayi, But saboda kauda kokwanto zamu iya duba, Cameras É—in dake house É—in mugani,"

Uncle Mansur yace, Yauwa hakan ma yayi,

Uncle duk ba wannan ba, Kasamu ka kai File É—in kuwa sunayen kuwa?

"Nakai komai Lafiya yanzu babu wani sauran Fargaba, Yanzu Komai zai tafi normal, ka dai tabbata Sunayen Kasa su dai dai ko? Uncle Mansur yafaÉ—a yana kallon Barrister Sulaiman,

Barrister Sulaim yace Komai bisa tsari nayi,

_Good Job_ yaro na, Yanzu ai Tunda Suka shiga hannun baffa, duk wani fargaba taƙare, ko Hameed ya gano daga baya ne babu abunda ya isa yayi sunaye sun shiga record kuma baffa bazai yadda dashiba laifin komai zuwa kansa zai koma, nikuma zannuna babu ruwana shiya bani na kawo, "

Dariya Suka sa, Uncle Mansur yakai hannu ya karɓi, tsinken karan Tabar Wiwin dake hannun Barrister Sulaiman yazuƙa,
Yanzu nifa tashin hankalina É—aya ne, wannan meeting É—in daza ayi bansan akan Meye ba, Allah yasa dai Bawani sabon Binciken bane,

"Karka damu Uncle nasan akan Meye za a zauna ba wata matsala, muje kawai kada a jira mu,"

*Suhaima*
Ta canza shigar jikin ta zuwa riga da sket da alama wanka tayi, Wayar Da Baffa ya aiko mata da ita take ta faman dubawa, wani irin daɗi take ji har cikin ranta, sabuwa ce fil, acikin kwalin ta ta fito da ita, ƙirar Infinix, har ta danna madannin da niyar kunnawa, sai kuma ta dakata kamar mai nazari wani abu,
Tashi tayi daga saman É—an madaidaicin gadon da take zaune tayi, filla filla da kayan dake cikin kwalin wayar, Charji tajona wayar sannan ta koma tafara tattara komai ta mayar dashi ma hallin sa,

"Idan khaltum taga wayar na aisai takusa suma saboda murna, Hhm idan ma tanuna tana so sai inbar mata a gurin ta idan zankira mother sai inkar ɓa,"
Ita kaÉ—ai take magana tana Murmushi, Wanda sautin sa kawai kake ji saboda fuskar ta a rufe take da mayafi kamar kullum,"
Kayan ta tanufa da niyar ɗakko sim ɗin da ta taho dashi Tunda ga garin su Bichi, Mother ce ta bata, saboda Su rinƙa waya, Gashi Tunda suka baru garin Basu taɓa waya da'ita ba, A yau basai gobe ba zankira ki uwata komai dare,"
Jin ana knocking ne yasa ta saurin yin shiru, tana mamakin waye haka,

Batare da tace komai ba ta nufi Ƙofar tabuɗe, ganin Hajiya Umma tayi tsaye, Cikin shigar Doguwar rigar Atamfa A'Sharp wadda tabuɗe sosai daga sama har ƙasa anyi mata adon net daga ƙasan anbishi da duwatsu masu haske,

Ƙasa Suhaima tayi da kanta ta rasa Meye dalilin tana jin nauyin matar, Barka da dare,"

Barka dai Suhaima, zanje Part ɗin baffa idan nadawo zamuyi magana, ko da abunda kike buƙata?

"Suhaima tace A'a adawo lafiya,

To Allah yasa hajiya Ummu tafaÉ—a tare da juyawa, cikin ranta tana mamakin Suhaima kullum fuska A rufe ko damunta mayafin bayayi,"

*Sulaim*
zaune yake a Parlourn ƙasa ya meƙe ƙafafuwan sa saman Table ɗin gaban sa, Computer ce saman Ƙafafuwan nashi,

Hallo Sultan kana ina,

_in oder Hand_ Yarima Sultan Yace Aminina Ina Part ɗin baffa ne Meeting akeyi, Baffa yahanani tahowa Yace Tunda kaƙi zuwa, Ni na zauna agama, ƙasa ƙasa Yarima Sultan ke maganar batare da wani yana jin saba Saboda Bluetooth ne a kunnan nasa,

Saraki please Ana kammalawa Kataho Banson Magana, cewar Sulaim,

Ina nan tafe, ka huta lpy kafin nadawo, Yarima bai jira cewar Sulaim ba yakatse kiran,"

"Ko Sallama Babu haka Suhaima ta turakai Cikin Parlourn Sulaim, kai Tsaye kasan cewar tasaba duk sanda tazo babu kowa shiyasa yasa kamar kullum ba tayi tunanin ganin kowa ba,

Kamar ance ta kalli tsakiyar Parlourn sai ga Sulaim zaune kamar yadda yake, Yakafeta da Manyan idanuwan sa masu kaifi da kwarjini, kwayar ciki launin GRAY, Mai haske sai walwale suke,

Itama shi take kallon, Shiru Babu wanda ya tan kawa É—an uwan sa, idon sa yamar Kan Computer É—in sa ya cigaba da abunda yake, Wani irin haushi ne yakama Suhaima lallai wannan yarainamin wayo,
Kuma aini yakamata nafara yi masa magana ko? Ta tambayi kanta,

Ciki ciki ta furta Barka da dare,

Sarai yaji amma ko ido bai É—ago ya kalle ta ba bare tasa ran zai amsa gaisuwar tata,

"Wani irin haushine ya turnuƙe Suhaima, Mtsss duk laifina ne dana gaida shi, kuma wlh ba hakan ne zai sa nafasa rama wulaƙancin da kayi min ba, cikin ranta tayi maganar,

Kallon ta Sulaim yayi, Kin tsayamin akai, idan Akwai Aikin da zakiyi, kiyi ki fita, Tamkar bashine yayi maganar ba, Saboda can ƙasan maƙoshin sa yayi maganar, itama don tana dajine kamar miciji shiyasa har ta iya jin abunda yafaɗa,

Takaici ne Yahana Suhaima Magana, Idan banfita ba Meye zaka iya, cikin ranta tayi maganar,

Kamar Sulaim yasan Abunda tace, A fili yace Sai insa a fitar dake, cikin harshen su na Larabawa Yayi Maganar Suhaima taji amma batasan Meye yace ba,
Tab zagina yayi da yaran su kenan, wallahi bazan haƙura ba sai yafaɗa min wa yake zagi, da wannan tunani tafara taka wa zuwa inda yake zaune ko motsawa bai yiba..!!
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS ......✨�*
*_T.M.W_✍️*

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 3️⃣5️⃣�3️⃣6️⃣📖

*Suhaima*
Saida takai har tsakiyar parlourn Gab da Kujerar da Sulaim yake Zaune, Cak taja ta tsaya, kollon ta tamaida gefe tana zare ido shiru tayi Cikin Ranta tana Tunanin ta'inama zata fara,
Cikin Nutsuwa Sulaim ya sauke ƙafafuwan sa daga saman Tablet ɗin daya miƙesu, tare da Rufe Laptop ɗin ya ajiye ta a gefe, ya miƙe ya nufi Upstairs hannayen sa zube cikin Aljihun dogon wanda jikin sa, Batare da ya kalli ko inda Suhaima Take tsaye ba,
Chapter 71 · 0% Book details