← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 90

Sashe 34

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eye lallai to Shikenan inajira, Yanzu dai Nima nawa Sadaukin Na mota yana jirana, Kinga dare yana ƙara yi, da Wannan Estate ɗin naku da mutum sai ya ɓace acikin sa bai saniba, Amma Saleema karki manta da Shawarar dana baki Ki jarraba kigani, Maleeka takai ƙarshan Maganar Suka sa dariya A tare,

"Na gode da ziyara zanyi komai yadda kikace, ki gaida Khaleel É—in naki,"

Saida Saleema ta raka ta har Gurin Su mommy tayi musu Sallama kafin ta kai ta bakin ƙofar shigowa parlourn, ta tafi ita kuma ta juya ciki,
Saleema fa kai ya ƙara girma, Gani take gaba ɗaya Ta mallaki Sulaim hakan yasa Ko magana bata fiyaye sosai ba, Batare da tabi takan kowa dake Parlourn ba ta wuce Sama abunta, Gimbiya Sultana ce tafaɗo mata arai, Take taji bari takirata ta sanar mata,"

"Bugu É—aya gimbiya Sultan ta É—aga kamar mejira," Hello Wallahi Bello Arab bakida Kirki Ashe har zaki iya Tafiya bikimin sallama ba"

Saleema tace Ayya to kiyi haƙuri mana kiji Meye Uziri na, naji kamar kina cikin farin ciki,

To inaji dama yanzu fa zankira ki sai kuma ga kiranki, Ina so inyi miki Albishir kafin kiji Abakin wasu, Yarima Sultan yazama mallakin Gimbiya Sultana,

Saleema ta furta Wow Sultana really?
Ai duk abu É—aya ne abakin namu, Nima nazama Mallaki Ya Sulaim, daga nan zuwa 2 months Amma Gaskiya namiki Murna,"

Da gaske mana, Amma wane Sulaim ÆŠin? Badai Aminin Sultan ba,

Shi mana, kinsan ai Cousin Brother nane, Saleema tafaÉ—a cikin NishaÉ—i dajin daÉ—i,"

Ɗil Ɗil, Gimbiya Sultana ta katse kiran batare da tace komai ba, Da mamaki Saleema ta ɗauke wayar daga Kunnan ta Jin Sultana ta katse mata kira, kallon Screen ɗin wayar take cike da mamaki, Can kuma ta taɓe baki tare da ɗaga kafaɗa irin na _I don't care_ ɗin nan,"

*Suhaima*
Har ƙara juyawa take, Tana kallon Uncle Shaddad, Wanda take mamakin Meye yake a zaune shi kaɗai Acikin dare, Gashi babu kowa a kusa dashi ko waya babu A hannun sa bare tace wani abun yake,
Tabbas ta gane shi tasha ganinshi shi kaɗai a zaune gashi baya magana, Bata taɓa kawo komai a rantaba sai yau, ko dai yanada damuwa ne? Tayiwa kanta Tambayar, Take taji tana son Jin wani abu akan shi,

Kallon House É—in Alhaji Hameed take wanda shigowar ta kenan, Babu a'lamar mutum ko É—aya, kowa na cikin Part É—in sa, Motoci ne gasunan barkatai Anyi parking É—in su, sai kuma kukan tsintsaye dake tashi, da yanayin dare dakuma Sanyin Gari da yake kaÉ—awa da iska kaÉ—an kaÉ—an,

Part ɗin daya tsaya mata a cikin Zuciya shi ta nufa gadan gadan, Part ɗin Sulaim dake cikin House ɗin Abiiy, Wanda tun ranar da tazo Ɗaukar, Akwati bata ƙara zuwa ba, Amma ya tsaya mata arai Saboda mawuyacin halin data shiga ranar da ta shiga wannan bedroom ɗin,

Kamar yadda tayi tsammani, tana tsayawa a bakin ƙofar shiga parlourn, take glass door ɗin tashiga zuge kanta A hankali,

Sannu a hankali ta tura kai ciki bakin ta É—auke da Sallama, Kallon parlourn tashiga yi, ko ina tsaf a gyare kamar Ana rayuwa aciki,"

Babu alamar tsoro ko wani tashin hankali, zuciyar ta a dake, ta nufi ƙofar bedroom ɗin nan, Bayan tagama karanta Addu'o'i Sannan ta murɗa Handle ɗin ƙofar bedroom ɗin ta tura kai ciki, ɗakin tashiga zagaye wa Kamar mai neman wani abu, Gashi babu haske sosai Amma da yake Ita babu ruwanta da Akwai haske ko babu, haka ta cigaba da dube duben ta, A yau lafiya lau Ba abunda ya faru da ita, ba kamar ranar Farko ba da tazo taji ana juyata, Hatta zanin gado saida ta yaye ta ɗaɗɗaga pillows da'alama akwai abunda take nema"
"Kamar Ance ta Tsugunna, Haka ta Sunkuya tare da leƙawa ƙasan bed ɗin, ta Zura kanta cikin ƙarƙashin Gadon Sulaim ɗin, Wanda babu komai Har ta fito da kanta sai kuma ta ƙara mayarwa, Hannun ta ta ta zura don son kamu abunda take hangowa, Amma ina hannun bai kai ba kasancewar Abunda take hangowar yana can daga ƙarshe,

Jikin ta ta zura sannan taƙara sa hannun ta, take ta kamu Wata ƙaramar Tukunyar ƙasa, janyo tukunyar tayi, Tafito da ita ganin, ta A rufe yasa Suhaima tabbatar wa kanta Akwai wani abu aciki, Babu ko ɗar Aranta Haka tasa hannun tabuɗe Tukunyar,

Da maÉ—aukakin mamaki Suhaima ke kallon Cikin Tukunyar Jini tagani Fal aciki, Gashi kamar Ansaka wani abun aciki,

Hannu ta zura cikin Aljihun rigar ta, tafara laluɓe sai gashi ta zaro, Hand gloves guda biyu, ɗaya ta saka a hannun ta nadama, sannan ta maida Ɗayar Aljihu,

Wannan abun dabs tasan Meye ba tashiga zarowa Acikin jinin dake cikin Tukunyar ƙasar, Sannu a hankali take za ruwa yana Fitowa saidai tagama Zaruwa gaba ɗaya, Sannan ta gane Ashe riga ce akasa aciki,
"Ta yunƙura daniyar miƙewa, taji anbuga mata wani abu a tsakiyar kanta tabaya, kamar guduma, Take ta sulale ƙasa A sume,
Wanda yayi dai dai da Fasa gigitacciyar ƙarar Sulaim shima ya faɗi Ƙasa A sume, Cikin Tsantsar tashin Hankali Yarima Sultan da Shattima sukaiyi kansa..!!!

_F pen_✍️
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS ......✨�*
*_T.M.W_✍️*

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

*_TEAM FIVE STARS💫_*

*TAURARI BIYAR*✨✨✨✨�

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 4�3⃣➖4�4⃣�

"Cikin Rashin sanin Abunyi Dakuma Matsanancin Ta shin hankali Yarima Sultan Ya kira Dr. Jabir, Cikin ƙanƙanin lokaci Yazo,
Dr. Jabir sai da yakai Kusan Awa Uku Akan Sulaim Amma Babu Abunda ya canza Dan ko Farcan sa Bai Motsaba bare Asaran Zai farfaÉ—o,"

"A daran wannan Rana Wadda ta kasan ce, Alhamis, Yarima Sultan, Dr.Jabir, Samrat, Sunga tashin Hankali Yadda Suka ga Rana Haka suka ga dare, Sultan ne ya hana Asanar wa kowa, A cewar sa kada a tashi hankalin Su, Amma ina Ganin Amininsa Kwance Ba'alamar Numfashi A tare dashi Hakan yasa Shi Kiran Abiiy Asubar Fari Tunkafin A shiga Masjid,"

"A na fitowa Daga Sallah Abiiy, Daddyn Canada, Uncle Yusuf, Ga ba É—aya Suka Nufi house É—in Baffa kai tsaye suka Wuce Part É—in Sulaim, Uncle Bello da Uncle Yusuf, Suka Wuce Upstairs Har cikin Bedroom É—in Sulaim Wanda Aciki Yake Kwance A lokacin DR. Jabir ya koma kan Sulaim ÆŠin Don ganin ko zai farfaÉ—o, Abiiy na Zaune A Downstairs Shi kaÉ—ai Amma zuciyar sa da gaba É—aya Tunanin sa na gurin É—ansa Sulaim,

*WASHE GARI*

Lillimin Hadari Mai haɗe da Sassanyar iska, Tamkar lokacin tsakiyar Damina, Garin yayi duhu Sosai Kasan cewar Hazon Da Aka tashi dashi, Wanda ya lulluɓe Sararin Samaniya, Lokacin Sanyi ne Amma Tamkar Za'a tsuge da ruwan sama Hakan ba ƙaramin kyau ya ƙarawa Cikin Estate ɗin ba, Karka so kaga Yadda Shuke-Shuken dake Harabar Cikin Estate ɗin Suka buɗe, Ganyayyaken Sukai kore shar, suna bada ƙamshin Firanni da Bishiyu Kala kala, A yayin da Iska ke kaɗa wannan Doguwar Bishiyar Kwakwar Dake Tsakiyar Roundabout, Ɗin nan Sannu a hankali,
"A zahiri Wannan yana yin, Nishaɗi ne da Farin ciki, Amma A Ɓangaran mutanan cikin Estate ɗin Yanayin, Baƙin ciki ne da Damuwa A gurin Su Wanda Kusan Gaba ɗaya acikin Alhini Suke,"

*Baffa*

Zaune yake cikin ɗakinsa ya Fuskanci Alƙibila Addu'a Kawai yake Akan Zaman lafiya da haɗin kai Ahalin sa, Tunda ya dawo daga Masallaci Yake jin babu daɗi A jikin sa, hakan yasa ko zaman Parlour baiyi ba, kamar yadda ya saba kullum yanayi, kasan cewar Ƴaƴan sa na zuwa Gaidashi,
"Haya niyar Da yake ji na tashi daga Cikin parlourn sa, yasa shi Saurarawa, Yanayin yadda yake jin Suna magana A jujjuye Cikin Tashin Hankali, Yasa Baffa Ya miƙewa, Tare da ɗaura jaffar shi Irin ta malamai Saman kayan jikin sa, Cikin Nutsuwa Ya fito Parlourn Kallon su ya shiga yi ɗaya bayan ɗaya, Yanayin Fuskokin su dakuma Tsantsar Tashin Hankalin Dayagani Cikin Idanuwan su, Ya tabbatar masa Ba Lafiya ba, Dattakun sa Da cikar Fuskar sa da Kamala, Hakan yasa gaba ɗaya sukai shiru, Ba tare da yace komai ba illa kallo,"

Ganin kowa Yayi Shiru Yasa
Baffa FaÉ—in Ina Sulaim??

Ƙirjin Wasu daga cikin Mutanan Parlourn saida ya buga, Ciki Hadda Daddyn Canada,

A karo na biyu Baffa ya ƙara cewa, Meye yasami Sulaim, Kuma yana Ina?

Kallon Kallo Aka shigayi, kusan Tunani É—aya Suke A zuciyoyin su, Shin ko dai An faÉ—awa Baffa rashin lafiyar Sulaim ne,

Wani Guntun Tsaki Mai Girma Hasheem yaja, Ƙasa Ƙasa yadda babu wanda Yaji shi,
Tsabar Son zuciya mutane nawa ne Basa nan Amma Ba'a Tambaye Suna ina ba Sai Wannan Shegen Yaron, Wanda Dashi da babu duk É—aya ne Zaku gane kuranku Basai ya tashi ba Sannan za a cigaba da maganar sa, Cikin Zuciyar sa Yayi maganar, A fili kuma
"Ganin babu Wanda yake daniyar Bawa Baffa Amsa Hakan yasa shi yin magana, Ai Baffa Yana can Kwana ya ƙare Don yanzuma munzo sanar maka ne Domin Ayi Jana'iza da wuri kafin gare yayi haske sosai, kowa yasan idan yanuf......

ÆŠaga Masa Hannun da Baffa Yayi ne, Yasa shi HaÉ—eye Sauran Maganar sa,

Hasheem Tashi Kafita Daga yau Har zuwa Lokacin da Sulaim zai Farfaɗo Bana Son ƙara ganin ka Anan Har sai na nemeka, Daganin Yadda Baffa Yayi Maganar kasan Ranshi Yagama ɓaci,

Mama Bilki Ji tayi Kamar an da ɓa mata wuƙa aciki, Saboda Kurar da Baffa Yayiwa Mai Girma Hasheem, Ta ƙara cika Tayi Fomm, Dama gashi tana ganin An Sata Ta fito da Sassafe ba tare da tayi niya ba, Akan wani Banza Acewar ta,

Amma Baffa Ai Gaskiya nafaÉ—a,

Cikin Fushi Baffa Yace, Hasheem idan ka ƙara Minti Guda Anan, Tabbas Zakabar Jahar Kano Baki ɗaya,

Fuuuu Mai Girma Hasheem ya tashi ya fita, zuciyar sa cike Fal da ƙunci da baƙin ciki,

Baffa Dubansa ya mayar Kan Uncle Yusuf, "Yusuf Akaini Inda Sulaim yake,"

Ba Musu Uncle Yusuf Yace to, Tare da miƙewa yashiga Gaba,
Chapter 34 · 0% Book details