← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 90

Sashe 1

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _
WhatsApp group👇

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALIN MU ÆŠAYA_*

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

*_Fatima Y zakariyya👌_*
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _
WhatsApp group👇

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALIN MU ÆŠAYA_*

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

*_Fatima Y zakariyya👌_*
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

*_Ina mai farin cikin sake haɗuwa daku a cikin Littafin AHALIN MU ƊAYA. Kashi na biyu, ina roƙon Allah ya amfanar da mu abin da ke cikin sa, akasin haka kuma da kuskure na ku watsar dashi gefe, saboda nima mutum ce kamar kowa zanyi dai dai zanyi kuskure, domin ɗan Adam ajizi ne, Allah ya shiga dukkan lamuran mu yayi mana jagoran ci_*

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿�1️⃣�2️⃣📖

"Gimbiya Sultana sosai take jin zafi a ƙasan ranta, jitayi tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu dan baƙin ciki,

Mamaki yahana Galadima motsawa daga inda yake zaune, ganin abun yake tamkar amajigi, Mamakin ganin Yarima Sultan yayi hawa kuma ya sauka lafiya, Ba tare da wani abu ya same shi ba, kenan aikin damukai ya tashi abanza kenan?
Cikin Ransa Yayi wa kansa tambayar,

Duk da sanyin da ake a gari hakan bai hana Jakadiya jiƙewa sharkaf da gumi ba, Saboda tsabar tsoro da fargabar abunda zata tarar daga gurin Hajiya mai soro, Ya a kai Yarima ya tsallake wa tarkwan su, ina Bazai Yiwuba,
Tabbas akwai abun da ya faru amma nidai nasan nayi komai kamar yadda aka bani umarni, Tafaɗa cikin ranta tana ƙara rarraba ido,

Cikin isa, izza, da taƙama Yarima Sultan ke tafiya shida princess Salma, zuwa inda aka tanada don zaman shi Fadawa biye dasu Suna kirari,
Suna isa gurin da aka Ta nada Don zaman su, Yarima ya nufi gurin da Aminin sa Sulaim ke zaune, rungume Sulaim É—in Yarima yayi cikin kunnuwan Sulaim ya Furta "Allah yasa Amini na yana lafiya kasan cewar aminin sultan cikin farin ciki shi zai faran Zuciyar Yarima ina fatan kasan cewar ka haka"

ÆŠan É—aga kai Sulaim yayi tare da FaÉ—in komai dai dai Sultan ina fatan babu damuwa a tare da kai"

Shima ÆŠaga kai kawai Yarima Sultan yayi tare da janye jikin shi batare dayace komai ba ya nufi gurin zaman sa,
Ya haye kan Kujerar sa mai kama da karagar mulki,

Ita kuma princess aka bata kujerar Da aka tanada Ga tauraruwar da tayi nasara a Hawan da Yarima Yayi, wanda Gaba É—aya mutanan Gurin suka sa ran Gimbiya Sultana ce zata hau Saman Kujerar,

Cike da alfahari da murna princess ta ɗane gujerar wadda ke kusa da Ta Yarima kaɗan, taɓan garan hannun daman shi amma har a lokacin bata dawo hayyaci taba, saboda ta tsorata sosai, Har lokacin Ji take tamkar ana mata lugude a ƙirjin ta,
Ba mutanan gurin ba hatta Sarki yaji daÉ—in hawan da yarima yayi tare da princess, wadda duk wajan babu wanda ya iya gane wace ce,
Banyan hayaniya taragu sai tashin ƙananun maganganu ƙasa-ƙasa, a lokacin Maga Takar da ya sanar, da za'a fara Gabatar da kyaututtuka ga Yarima Sultan, ɗaya bayan ɗaya aka fara gudanar da shagalin kyauta, abun ban sha'awa cikin irin, al'adun su, sai da aka fara gabatar da kyaututtuka, da ɓakin masarautar suka bayar, ga Yarima sultan tare da yi masa barka da dawowa,

Sai da aka gabatar da kyautar sarakuna kafin na "Æ´aÆ´an su, da haka aka kammala aka dawo cikin Masarautar Gabas,
Akafara gabatar da kyautar Mai martaba sarki zuwa ga ɗan sa Yarima Sultan, wanda mai martaba yace a sanar ya sadaukar da Rabin Masarautar Gabas ga Yarima Sultan, tare da bashi damar zaɓar duk wani abun daya keso bayan haka,
Wani irin zabura Galadima murtala yayi wanda har sai da rawanin kansa ya kusa faÉ—uwa yayi Saurin tarosa, batare da kowa ya kula da hakan ba, illa baba Waziri wanda Yaga komai Murmushi yayi haÉ—i da girgiza kai don yasan akwai matsala,

Kasa jurewa Fulani tayi, tsabar baƙin ciki batasan lokacin da ta tashi ta nufi sa shan taba, kuyangin ta suka rufa mata baya,
Yama za ayi inaji ina gani ga ɗana amma ace sarki yayi kyau ta da rabin masarauta, cikin ƙunar rai, ta furta wlh bazai yiyuba Da sake An ɗaura zanin Mahaukaciya,

A Ɓangaran Sultana kuwa Cikin sanyin jiki Da suyar Zuci, Wanda gaba ɗaya kunya ta hana ta Ɗaga kai ta dubi mutanan gurin, A haka tagabatar da kyautar ta zuwa ga Yarima,
Wasu kyawawan alkyabba ne guda 5 launi daban daban masu kwalliyar Azurfa a jikin su, sai tagwayen Dokuna Majiya ƙarfi da gudun gaske, farare tass Masu Baƙin Bindi guda biyu, haɗi da sandar girma launin ruwan zinare,
Sai da kowa yayi mamakin Kyautar Sultana ga yarima,
Da'alama shi hakan Sam bai dameshi ba ko a fuska bai nuna komai ba,

Bayan Gimbiya Sultana, Ta kammala Aka gabatar da Saƙon gimbiya Shaheedah wadda ita tsabar mulki Ko tashi batayi ba yayin gabatar war daga zaune tafaɗi komai, tabada manya manyan kyaututtukan Girma ga Sultan wanda sunshafe Na gimbiya Sultana, Nesa ba kusa ba,
Tashi Siyama Tayi cikin shigar ta takaran miskin, tayi kyau sosai ita da zara suga gabatar da kyautar su zuwa ga Yarima Sultan Yarima,
Fadawa ne suka amsa da Cewa Yarima ya amsa kuma yana godiya ga "Æ´aÆ´an Fulanin Sarki Mahaifiya ga Yarima Safwan,
Nan fa kallo ya koma sama Hankalin kowa Yakoma zuwa ga Princess ana jiran ganin Meye kyautar ta kowa abunda yake jiran gani kenan,
Kamar princess tasan Abun dake cikin zuciyoyin su, cikin nutsuwar ta tashi ta ɗan juya ta kalli Yarima, Cikin sa'a shima ita yake kallo mamakin ganin ta tashi, cikin Ransa yake Tunanin Meye zatayi, sannu ahankali tafara gangara wa zuwa ƙasa gurin maga takarda, hannu tamiƙa masa alamun yabata abun magana,
Babu musu yamiƙa mata Cikin Rawar jiki, bayan tayi sallama ta gabatar da gaisuwa zuwa ga mai martaba sarki da manya manyan ɓakin, sannan ta ɗora dafaɗin,
"A matsayi na na baƙuwa a wannan masarauta mai albarka da cikakken iko da adalci ga al'ummar da suke ƙasan ta, ina matuƙar godiya da karramawa,
Na duba kaf cikin Abunda na mallaka a rayuwa, Kuɗi, Dukiya, Matsayi, Babu abunda yadace Ga Yayana kuma Sarkin mu na gobe Yarima Sultan, amma zan sadaukar da duk wani abu da yake, mafi girma daga sashen rayuta, kyauta ce mafi girma a gurina, Amma mafi ƙanƙanta a zahiri, kyauta ce ƙarama amma kuma mafi girma a zuciya," Tana kaiwa nan ta juya tare da nufar gurin da Yarima yake zaune,
Gaba ɗaya akabi ta da kallo hatta Yarima Sultan ita yake kallo har ta isa zuwa gareshi, Kowa na gurin yazuba ido yaga abunda zata yi, take tazare zoban hannun ta guda biyu, duka zobinan na ɗutse mai daraja ne sai ƙalli suke,
Ɗaya zoban azurfa ne mai kwalliyar Jan Dutse, ɗayan kuma zinare ne mai haske da ɗaukar ido wanda akayi masa ado da Farin Dutse, cikin wani irin salo princess ta russuna agaban Yarima Sultan Tare da miƙa masa Zobinan da hannu biyu cike da girmamawa, ba musu Yarima Sultan ya buɗe hannun sa mai ɗauke da kyawawan yatsu dogaye, take ta ɗora masa zoban a tsakiyar tafin hannun sa,
Wani irin murmushin girma Ummul Bait, daga inda take zaune, lamarin Yarin yar duk ya É—aure mata kai ta rasa daga ina Yarin yar tazo, har cikin ranta take jin daÉ—in Yadda ta gabatar da komai,

Meƙewa princess tayi daga gaban yarima tafara tafiya tare da zagayawa bayan Sultan ta tsaya, guri yayi shiru kowa na kallon iKon Allah saboda yadda princess takeyi ko ɗan da ya tashi ya tsufa acikin masarauta bazai iya abunda princess salma take ba komai irin na masu mulki,
Hannun tasa ta dai dai ta zaman Hular da aka É—ora mata Alkyabbar jikin ta wadda akayi Hular da azurfa mara nauyi, akayi mata ado da dutsan mundurwar zinare, idan kaga hular sai kayi tunanin ta Sarauniyar matan Larabawa ce gashi sai É—aukar ido take, shiyasa mutane kitunane Princess daga wata babbar masarauta ta fito,
Tsayawa tayi a bayan Yarima takai hannu akaro na biyu ta cire Hular, Ƙara matsawa tayi Sosai bayan Yarima Sultan Hakan yasa fadawan Saurin Matsawa daga Gurin, Bisa mamakin kowa Princess ta ɗora hular saman rawanin Yarima,
Wannan itace kyautata ga Ga sarkin mu Nagobe insha Allah, inayiwa Yaya Yarima Sultan barka da dawowa Gida Nigeria Allah ya tsare mana shi daga sharrin dukkan magauta, Tana kaiwa nan ta koma mazaunin ta, tare da miƙa abun maganar ga maga takarda,
Babu wanda bata burgeshi a gurin ba, sai É—ai É—ai kun mutanan dasukeji tamkar su tashi su kashe ta a gurin TafaÉ—i ta mutu,
Suhailat ce ta matsa kusa da inda ummeetha ke zaune cikin kunnan ta tace, Ummeetha wlh ji nake muryar wannan Gimbiyar Kamar Autar ki,
Kallon Suhailat ummeetha tayi kafin tace, ashe bani kaÉ—ai naji hakan ba, komai nasu iri É—aya amma wannan Æ´ar gidan sarauta ce, ai auta bata ji tana can tana yawo ko yanzu nakira wayar ta tana shiga amma bata É—agawa,
Gaskiya wannan auta ce nidai nakasa yadda ace ba iya bace, mommy ce tayi maganar tana daga kan kujerar da ke gefan ta ummeetha,
Murmushi kawai ummeetha tayi batare da tace komai ba,

Kyautar da Sulaim yabawa Yarima Sultan saida kowa ya girgiza agurin saboda babu wanda yabada makaman ciyar ta idan aka cire mai martaba sarki,

Dakan sa Sultan ya gabatar da godiya zuwa ga aminin sa Sulaim,
Bayan kammala gabatar da kyauta masu kiÉ—e kiÉ—e da busa suka cigaba da yi haÉ—i da kirari ga Yarima Sultan Yusuf Shareef Zaki,
A lokacin kasanar da tafiyar mai martaba sarki, saboda babu abunda ya rage sai cin abinci, hakan yasa Shima Sultan tashi Zuwa ciki Fadawan sa suka rufa masa baya yadda yaje gurin a doki haka Yakoma a saman doki,

Sulaim dama tunkafin tafiyar sarki shiya fara barin gurin saboda dama kawai daurewa yake yi amma kansa har ciwo yake yi masa saboda hayaniya ga kiÉ—e kiÉ—e,
Chapter 1 · 0% Book details