← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 90

Sashe 53

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duban ta takai kan khaltum wadda take ta aikin sharar bacci, murmushi Suhaima tayi saboda ta tuna maganar khaltum a daran jiya, data ce ita fa tana tunanin ko a aljannah iya dadin daza taji kenan, sannan tasan ko a gidan shugaban ƙasa baza a taɓa samun irin wannan katifar ba saidai mai girman ta badai laushi ba, ƙauyan ci khaltum tayi tayi har Allah yasa bacci ya ɗauke ta,
ita dai Suhaima idan ba dariya ba babu abun da take, duk da itama shiru kawai takeyi amma wasu abubuwan har mamaki suke bata da irin kuɗin da aka narka akayi wani abun da take ganin bashida wani amfani, Don ma Allah yasa suna da waye wa basa nuna ƙauyan ci a ko ina saidai suyi shiru,

Jin alamun kamar ana magana daga parlour ne, yakatsewa Suhaima tunanin da take, cikin sauri tazuro ƙafar ta saman lallausan carpet wanda saboda laushi har lumshe idanuwan ta tayi,

Tare da gara zaman hijab É—in ta nufi parlourn,

wata dattijuwar mata tagani tsaye ita da wata matashiyar budurwa hannun budurwar ruƙe da tire da alama kayan breakfast ne aka kawo musu, wanda da kagansu su biyun duka zaka shaida ƴan aiki ne saboda yanayin shigar su duk da komai nasu tsaf tsaf yake, rigar jikin su iri ɗaya an rubuta, _ARAB KITCHENS_ abayan rigunan nasu wanda suke har gwaiwa,

Murmushi dattijuwar tayi wa Suhaima tare da FaÉ—in Yarin Ya kuntashi lafiya,"

Alhamdulillah abunda Suhaima tace kenan,

Kallon matashiyar budurwar matar tayi tare da FaÉ—in" K.C jeki jera kayan abincin idan kingama kitafi ganinan zuwa,

Da " To ta amsa tare da wucewa dinning wanda ke daga gefe acikin area parlourn,

K.C Kuma wannan wane irin sunane? Suhaima tayi tambayar cikin ranta, Ba mamaki Cristan ce zuciyar ta tabbata amsa da haka,

Ganin matar tasamu guri ƙasa ta zauna ga kuma kujeru, hakan yasa Suhaima ƙarasawa cikin Parlourn tare da kallon matar tace,

BaBa yaki kazauna a ƙasa bayan ga kujera kikoma sama mana, cewar Suhaima dai dai tana zama saman kujera mai cin mutun biyu,

A'a Yarin Ya Bakomai nan ma ya isa, dattijuwar tafaÉ—a fuskantar da yalwataccan murmushi, kafin Suhaima tace wani abu matar ta É—ora da FaÉ—in dama anci nazo ne mutafi tare, idan kungama karin kumallon,

Kamar Suhaima za tace injiwa? Sai kuma tace to bari na taso Æ´ar uwata sai muyi sauri mu kammala,

To badamuwa kuyi komai a nitse zanjira ku,

Batare da Suhaima tace komai ba ta tashi tanufi bedroom ɗin da ta fito daga cikin, cikin ƙanƙanin lokaci suka fito tare da Khaltum wanda ta turo baki gaba tare da turɓune fuska, wai ita a dole Suhaima ta tasheta tana baccin ta mai daɗi wanda bata taɓa irin saba Tunda aka haife ta a cewar ta,

Dariya Suhaima kawai tayi wadda idan ba akusa da ita kake ba baza kagane tayi dariyar ba,

Dinning ɗin suka nufa kai tsaye, suna zama khaltum ta shiga washe haƙura cike da murna tace, amma wlh Suhaima kin kyautamin yanzu da biki tasheniba shikenan nayi asara ko? Tayi tambayar tare da tura wainar kwai abakin ta wanda ta haɗo da plantain (Agada),

Hhmm Suhaima tace tare da Faɗin amma da kintashi sai masifa kike na tashi ki, wai nikam jiya bacewa kikai baza ki ƙara cikin abin cin gidan nan ba Tunda kingano inda muke, cikin wasa takai ƙatshan maganar,

Wata irin harara khaltum ta kaiwa Suhaima, kafin tace wani abu da sauri ta furzar da abunda tasa abakin ta, kwai da plantain, kan Uban can Suhaima kinji wata ƙazan ta kuwa, kinga an haɗa gishiri da Suger, tana maganar tare da ka karin amai tana ƙara tofar da abun da ke bakin nata,

Me Suhaima zata ba dariya ba, sosai tadara, khaltum hadda Æ´ar kwallar ta,

Suhaima tace kewai khaltum dole saikin sa mutanan gidan nan Sun raina mu ko, da kika ci, kikaji haka saiki daure ki haɗeyi, ai kwaɗayin kine yaja miki, kika haɗa abu biyu lokaci guda, kuma fa baƙazan ta bane idan biki manta ba a cikin film ɗin nan da muka taɓa kallo ai munga ana soya ayaba kuma anaci da abinci,

Ita dai khaltum Tunda ta janyo plask ɗin chickens and chips, tafara dannawa ɓata ƙarabi takan Suhaima ba don bama sauraran ta takeyi ba,

Dahaka su kammala saida khaltum taji kamar cikin ta zai ɓillata bayan ta sannan ta hakura,

Suhaima baiwar Allah hankalin ta duk ba yakan wannan kayan alatu babban burin ta shine taga tafara aiwatar da aikin da yakawo su,

Sosai alhaji Imran yasakar musu fuska hadda ɗanjan su da hira, khaltum ce mai ƙoƙarin amsawa, ita dai Suhaima daga eh sai A'a, Hajiya umma wadda ke gefe, itama taɗan sakar musu fuska babu yabo ba fallasa, Tunda taga Suhaima fuskar ta a rufe ta gane itace wadda Baffa ke nufi, wanda ita ko kwayar idon Suhaiman baya samu nasarar gani ba, saboda Tunda suka shiga parlourn kanta na ƙasa,

Anan Baffa ya sanar da Suhaima zata zauna a gurin hajiya umma zata rinƙa kulawa da sashen, jikan sa Sulaim wanda yake a cikin house ɗin nan,

Sulaim! Sulaim!! Sulaim!!!

Saida Suhaima ta mai maita sunan sau uku a zuciyar ta, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne taji su lulluɓe ta, jin ance zata kula da ɓangaran DR Sulaim, wanda a duniya tanajin babu wanda ta tsana irin sa, idan aka cire wanda ya tarwatsa musu rayuwa to tabbas Sulaim ne na biyu, sau ɗaya ta taɓa ganin sa, amma suffar shi da kamanin sa sunan zane cikin ƙoƙon zuciyar ta, wulaƙancin dayayi mata nanan ajiye cikin ranta wanda kullum jin shi take tamkar sabo, shiyasa ta ƙudir ce a ranta matuƙar yana cikin mutanan da zata ɗau fansa akan su to tabbas sai azabar shi tafi ta kowa tsanani, idan kuma baya ciki to sai ta rama fiye da wulaƙancin dayayi mata, duk da shine silar ta zuwa ARAB ESTATE, take kuma sai taji tabar jin baƙin cikin saboda tasamu damar rama abun da yayi mata ɗin,

Khaltum ce ta taɓo ta tare da Faɗin Suhaima sai magana akeyi kinyi shiru,

Kafin tace komai, baffa ya É—ora da FaÉ—in Æ´ar ta tunanin Meye kikeyi Allah yasa lafiya?

Firgigit tayi cikin inda inda tace a a babu komai inajin ku,

Koda Inda aka bakine biye miki ba? Baffa yaƙara tambayar ta,

A'a komai yayi nagode sosai,

Baffa yaÉ—ora da FaÉ—in to alhamdulillah,
Ita Æ´ar uwar take za akaita inda zata zauna, amma zaku iya ganin juna a duk lokacin da kuke so,

ÆŠaga kai Suhaima tayi cike da gamsuwar abunda yafaÉ—a,

Yanzu zaku iya yin magana ku kaÉ—ai idan kuna so saboda yanzu kowa zai wuce inda zai zauna, hajiya umma ce tayi maganar wadda gaba É—aya hankalin ta yana kan Suhaima,

Eh muna so cewar Suhaima da sauri,

Hajiya umma tace to shikenan, zaku iya komawa parlourn farko idan kuka gama sai kuyi magana,

Kama hannun khaltum Suhaima tayi bayan sunfita, tafara magana kamar haka,

khaltum kinji abunda nafaɗa miki daran jiya ko, basai na mai maitamiki komai ba, abu ɗaya zanfaɗa miki shine, kada kisaki jiki da kowa kada kiyi wani labarin komai da kowa kowane iri ne, sannan kada ki taɓa nunawa mu biyu ne ki nuna cewar ki kaɗai ce, nikuma zan sama mana inda zamu rinƙa haɗuwa, duk wani abu da biki yadda dashiba inaso kisanar min cikin gaggawa, tahakan ne kaɗai zamu cimma burin mu, kiyi hak'uri da duk abunda zakiji ko zaki gani hakan ma nasara ne,

Matsar kwalla khaltum tafara, cikin sauri Suhaima tace Haba khaltum nace miki kuka ba namu bane, kada kibari zuciyar ki ta karaya a kowane hali, ki jajirce akan komai shine muradi na, saboda haka kibar wannan kuna muna tare fa idan kinason ganina zakizo inda nake idan inason ganin ki nima zanzo,

Murmushi khaltum tayi tare da fadin babu komai nabari insha Allah,

*_BARNO STATE_*

_MASARAUTAR GABAS_

_F pen's_
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: _Typing📲_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 1�3⃣➖1�4⃣�

Murmushi khaltum tayi tare da FaÉ—in nabari insha Allah, amma bakya ganin zasu iya gane cewar mu biyu ne,

Eh to kafin su gane hakan, munyi nisa cikin aikin mu, cewar Suhaima,

ÆŠan rangwaÉ—ar da kai khaltum tayi gefe alamar ta yadda,

Kallon ta Suhaima tayi cikin lulluɓin fuskar ta ta saki murmushi mai sauti,

Da sauri khaltum ta kalle ta jin murmushin da tayi, lafiya kuwa,

Girgiza mata kai Suhaima tayi da sauri tace a'a Bakomai wani abu na tuna,
Sai ta kyau da maganar ta hanyar FaÉ—in, yanzu ke a matsayin ki na babba babu wani abun da za kifaÉ—a min kafin murabu?

ÆŠan Farr khaltum tayi da ido cikin jin daÉ—in ankira ta da babba, don khaltum badai son girma ba, ina dashi mana,
Ni abunda zanfaɗa miki Ba wata doguwar magana bace, inason duk abunda kikasamu kada kimanta dani, komai ƙanƙan tarshi kiraba biyu kikawomin nawa,

Ganin da gaske take babu ko alamar wasa, hakan yabawa Suhaima dariya sosai, aranta tace wato ita dai khaltum bata da burin daya wuce naci kullum ci,
"Kada kidamu khaltum Indai akan wannan ne bakida matsala, komai nasamu kinfi ƙarfin shi, insha Allah bazan taɓa mantawa dake ba saboda wani abun duniya, idan duka kika nuna kinaso zan iya baki, hakan Bakomai bane, saidai inaso inƙara tuna miki, munzo gidan nan, Dan Ɗaukar Fansa bawai don jin daɗi ba ko saba wa da mutanan gidan ba, kada mu bari kowa ya shiga jikin mu har yayi mana illa ta hanyar, zambo cikin aminci,"

Kafin khaltum ta ce wani abu, Hajiya umma ta shigo parlourn bakin ta É—auke da sallama,

Suhaima ce ta amsa, can ƙasan maƙoshin ta,

" Kallon su hajiya umma tayi, idan kungama zamu iya tafiya ko,
Chapter 53 · 0% Book details