← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 90

Sashe 58

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shu'umin murmushi Galadima yayi wanda shikaÉ—ai yasan fassarar kayan sa, Ina Nagode da lokacin da nasamu daga mai martaba, sai munhaÉ—u a Fada Na barka lafiya,
"Galadima na kawa nan ya miƙe mai maƙon ya nufi waje sai ya nufi wasu hotuna manya manya guda uku wanda suke maƙale a jikin bangon babban parlourn Sarki,". Na Farko Yarima Sultan ne sanyi da kayan saraki tun yana yaro, Na biyu tsohon sarki Adam Shareef sanye da Jallabiya sai alkyabba da yaɗora akai, sai hoto na uku hoton wannan Yarin yar ne dake parlourn Ummul Bait, anan ma shine da alama duk rana ɗaya aka yiwa jariryar hoton saboda komai irin ɗaya da wancan hoton na parlourn Ummul Bait, tsarƙar wuyan Yarin yar sai ƙalli take ga tambarin zaki nan a jikin sarƙar, wanda Idan ba magajin Masarautar gabas ba babu me irin wannan sarƙar, acikin Masarautar ake ƙirata, bayan sarƙar kuma abun mamaki Zanan HATIMIN MALLAKA Ne a jiki, jariryar masha Allah kamar kasa hannu ka ɗakko ta saboda yadda ta fito sosai acikin hoton duk da jaririya ce hakan bai hana gaba ɗaya dinfull ɗin ta lotsawa,"

Hannu Galadima Murtala yasa ya shafi fuskar Yarin yar, cikin ransa ya furta shigeya da kinanan da tuni masifar da muke ciki tafi ta yanzu, mun kawar dake saura uwarki da É—an uwanki tare da mahifinki,
A zahiri kuwa kwallace ta gangaro saman kuncin sa cikin sanyin murya ya furta Allah sarki Jarumarmu munyi babban rashi a zuri'ar mu, Allah yasaka mana akan duk wanda yaraba mu dake, yakai ƙarshe tare da matsar kwalla,

"Da sauri Mai martaba sarki Yusuf ya kauda kanshi, saboda Galadima ya sosa masa inda yake yi masa ƙaiƙayi, ƴa mafi soyuwa a gareshi kenan, Ahalin yanzu babu ita, son ta yake fiye da komai a rayuwar sa, gashi anraba su tun tana jaririya, amma haryanzu jinta yake acikin ransa fiye da duka ƴaƴan sa,"

"Ƙalla ido Galadima yayi ya kalli sarki Yusuf ganin ya kauda kai gefe hakan yasa shi nufar ƙofa da sauri yana share hawaye, buɗa masa hanya Dakaran dake tsaron ƙofar sukayi Fadawa biyu suka rufa masa baya, wanda suka kasance nasa ne dama dasu yazo,
"wata irin ma haukaciyar dariya ya saki bayan fitar sa a fili ya furta zaka gane kuranka Yusuf dole mulkin nan da kake taƙama dashi sai ya dawo hannu na bazan taɓa barin kaba," saida yafita daga sashen mai martaba sannan yayi shiru,

Saleema ce zaune a parlourn Su gimbiya Sultana kan ta a ƙasa sai faman kallon hoton Sulaim take,
"Oh ƙawata ashe dama muna guri ɗaya tare har natsawan kwana uku amma Bamu saniba" kuma fa ko _last day_ nakira wayar ki amma bata zuwa, Gimbiya Sultana takai ƙarshan maganar dai dai lokacin tana zama kusa da Saleema,

"Aje wayar Saleema tayi tajuya sosai ta fuskanci gimbiya Sultana tare da rungume ta baki ɗaya suka sa darita, janye jikin ta, ta sakar mata murmushi" Friendy ashe zamu sake haɗu, a zahiri, Tunda ki kabaro ƙasar mu shikenan kika manta da muta ne saidai a chat,"

"Haba Bello Arab wlh kinsan ina neman ku, nifa Tunda nabaro Canada itama antyn nawa tadawo Nigeria shiyasa banƙara zuwa ba Tunda wadda zanje gurin nata itama aiki ne yakai mijin ta can yanzu kuma sun dawo nan,
" Ai idan da me laifi acikin mu ma kece saboda _at any moment_ Kuna Zuwa Nigeria amma biki taɓa ne mana ba" wai duk bawa wannan ba abun mamakin shine meya kawo ki masarautar mu?" na tambayeki tu a waya kince sai kinzo za kibani labari inajin ki,"

"Ɗan taɓe baki Saleema tayi, Emm babu wani dalili mai ƙarfi fa, matar uncle ɗin muce,Mahaifinta shine wazirin masarautar nan, to duk lokacin da muka zo ƙasar nan su mommy na zuwa su gaishesu, ni ban taɓa zuwa ba sai wannan karon shima saboda wani dalili ne,"

_Oky You mean_ Anty Maryam Nasan dai itace ke aure a Kano kuma itace babba cikin Æ´aÆ´an Waziri, kuma family É—in datake aure _something_ Arab ne kinga kema ai Saleema Bello Arab ne So ita cema,

"Yeah ba mamaki namanta Meye sunan ta na asali amma ummeetha muke kiran ta dashi,

"Of course itace tana tana da wani ɗa mai kama da aljanu saboda tsabar kyansa kamar ba mutumba ina yawan ganin shi aminin Yarima Sultan ne, Baya ko fara'a amma yana matuƙar burgeni da ace babu Yarima Sultan to tabbas shi zan aura"

"Da sauri Saleema ta kalle ta jin abunda ta faɗa sarai ta gane akan wa Sultana ke magana, Yaya Sulaim ɗin ta, take annurin fuskar ta a ragu don ita bata haɗa soyayyar Sulaim da komai ba, ji take zata iya ɓatawa da kowa akan Sulaim"

"jin tayi shiru hakan yabawa gimbiya sultana damar cigaba da magana saboda ita bata ma lura da chanzawar ƙawar tata ba, amma Bello Arab ina ganin ai na taɓa gaya miki ni ƴar cikin masarauta ce kuma a garin Barno amma shine ko kiyi tunanin ne mana"

Sorry mana friendy yanzu dai Tunda mun haÉ—u ai komai ya wuce, ko sai nafaÉ—i É—ayan sunan ne, Murtala Shareef Zaki,"

Gaba É—aya suka sa dariya haÉ—i da tafawa,
"Wannan ai sunan school ne yanzu anan da Gimbiya Sultana zaki kirani"

Heeyyy Sannu Gimbiya Saleema ta faÉ—a cikin wasa,

Yauwa Bello Arab kuma kinsan me?

A'a cewar Saleema tare da tattara hankalin ta akan Sultana,

"sosai kuna yanayi da wannan kyakkyawan ɗan Anty Maryam ɗin, yauwa Natuna sunan sa Sulaim yeah Sulaim ta ƙara faɗa tare da ɗaga kai alamar dai dai tafaɗa,
Wlh friendy bashida kirki ko dariya ba yayiwa mutane bare kasa ranyin magana dashi,"

Sallamar da akayine yasa gaba ɗaya suka maida hankalin su zuwa ƙofa, wasu kuyangi ne su biyu hannu ɗaya ruƙe da tiri anjira kayan abinci, ita kuma ɗayar anjira abunsha da kayan marmari kala kala,

Sosai Gimbiya Sultana ta ɗaure fuska tare da maida ƙafar ta ɗaya ƙan ɗaya kamar ba itace keta faman surutu yanzu ba, cikin isa da izza ta kalli kuyangun, zaku iya ajeye wa, tace batare da ta ƙara wata maganar bisa haka ba,"

Da sauri suka ƙarasa shiga suka aje kayan hannun su a tare a gaban Gimbiya Sultana da Saleema wadda gaba ɗaya Haushin ƙawar tata ya kamata jin tana yaɓon kyan Sulaim a gaban ta, jitayi baza ta iya zama ba, kuyangin na fita itama ta miƙe,

Ruƙo hannun ta Sultana tayi, Ina zakije badai tafiya zakiba,

Tafiya zanyi mana Anjima nadawo,

"A'a gaskiya ga abinci ankawo miki idan kikaci sai ki tafi Meye na damuwa Tunda duk muna guri É—aya gashi mun daÉ—e Bamu haÉ—uba ko hira bamuyi sosai ba",

_Look_ Sultana zandawo Yanzu inada uziri may be na kwanar miki anan ma, so please kibarni na tafi,

Jin hakan ne yasa Sultana FaÉ—in oky ina jiranki yau anan zaki kwana, _promise_

"Ɗaga kai Saleema kawai tayi, ta ɗauke wayar ta, gimbiya sultana ta taka mata har zuwa bakin ƙofar parlourn, friendy bazan iya fita ba alkyabba ba kiyi hakuri, ki sauka lafiya nagode da ziyara sai najiki,"

"Murmushin yaƙe kawai Saleema tayi _don't worry about that_ Haka ma Nagode nabarki lafiya" tana kaiwa nan ta fita,

"Saleema da Gimbiya Sultana ƙawayene sosai, Sun haɗu a school, *(UNIVERSITY OF TORONTO)* A ƙasar Canada, acan gimbiya Sultana tayi karatun ta na degree, a gurin ƙarwar Mahaifiyar ta hajiya mai soro, saboda babu kowa a wajan ƙanwar maman nata shine su roƙi alfarma taje ta zauna musu acan har Allah yasa ta kammala degreen ta na farko acan, ita kuma Saleema dama can ne ƙasar su acan aka haife su gaba ɗaya, sosai jinin su ya haɗu saboda kusan halin su yazo ɗaya, akwai wulaƙanci ka girman kai, ita Sultana mulki ke yawo acikin jikin ta, ita kuma Saleema dukiya da gayu ga kyau, duk da itama Sultana ba baya ba, wannan shine dalilin shaƙuwar su komai tare sukeyi, har suka kammala a lokacin ne Sultana ta dawo gida Nigeria, tare da begyan juna ita da Saleema saida ko wacce tayi kuka lokacin rabuwa kamar baza su ƙara ganin juna ba har Airport saida Saleema taraka Sultana, sannan suka yiwa juna alƙawarin ziyarar junanan su lokaci zuwa lokaci," wannan itace alaƙar dake tsakanin gimbiya Sultana da kuma Saleema a taƙaice,

"Na daɗe inajiran wannan rana, naji daɗi sosai Gimbiya ta, Yarima Safwan ya ƙara she maganar tare da sakarwa Gimbiya shaheedah murmushi,"

"Martanin murmushin itama tamai da masa, Bakomai nima ina sonka saboda banfiye zama anan É—in ba shiyasa bana nuna maka hakan _But I love you_ Yarima Na,"

Sosai maganar ta ratsashi hakan yasa shi kasa mayar mata da martani,

Jin yayi shiru ne yasa tace Yaya Safwan kana lafiya dai ko?"

"Murmushi yayi sosai tare da dai dai ta nutsuwar shi, _ Nothing is wrong with me_ farin ciki ne ya hanani magana, _So I really appreciate you, and I love you so very much beautiful angel my world_"

Murmushin gefan baki ta sakar masa, cikin ranta kuma wani irin haushin sa take ji, ina ma Yarima Sultan ne ya agabana kamar haka yana faÉ—a min waÉ—an nan kalaman,

"Daga lokacin dana zama sarki a masarautar gabas za kizama uwar gida a gurin na, lokacin da naji ance wancan Sultan É—in kikeso, zuciya ta kasa jurewa tayi nashi matsanancin tashin hankali, saboda haka a yau basai gobe ba zan sanar wa da mahaifin mu mai martaba, kowa ya shaida gimbiya shaheedah ta zama ta Yarima Safwan sarkin gobe,"

Naji daɗin hakan tafaɗa tare da miƙewa, Nabar ka lafiya"

"ki huta lafiya yabata amsa a gajarce"

Tana shiga bedroom É—in ta ko zama ba tayi ba tayi dialing No. BaÉ—in Mahaifiyar ta, bugu É—aya aka É—auka,"

"Mom barka da yamma kuna lafiya ya yah Mu'azzam?"

"lafiya muke Allah yasa kema haka,

"eh Mom wlh kinsan banason wannan Safwan É—in ko? Amma yanzu saboda ke har lokaci na na bashi sai wani faÉ—amin magan ganun banza yake Mtss" taja wani dogon tsaki,
Chapter 58 · 0% Book details