← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 90

Sashe 16

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" yoo ni ina ruwa na koma Meye ake kiranku dashi Tunda iyayen ku suka zaɓa muku sunan tsuntsaye, Yarima kaga saika shirya aurar da ƙannan ka, Sasseleem da Sassleema kai kuma ɗan kuma sai ka shirya auran da Tauheed da Raufa kunga kuna zaune sai su haifa muku ƴaƴa, Tunda ku kunrasa mashan shana,

Yarima Sultan hankalin sa nakan princess Wadda take dariya sosai cikin nutsuwa, sai hakan yaja hankalin sa,

"Gwaggo kiyi hakuri Tunda biki iya faÉ—a ba, Rafiq da Taufiq ne suka Tasleem da Tasleema haka sunayen suke," Suhailat tafaÉ—a tana dariya, Saleem na gefan ta shima dariyar yake,

Tuni Rafiq ya tashi yabar parlourn ganin hakan ne yasa Shima Taufiq ɗin bin bayan shi, amma yaso ace dashi aka ƙarasa chapter ɗin nan,😂

Mommy kuwa hadda dafe ciki, Saleema batasan anayi ba saboda tana bedroom ɓata fitoba,

"Ummeetha da murmushi a fuskar ta tace wai ina ruwan ku kada ku takurawa uwata yadda ta iya haka zata faÉ—a duk mai son tafaÉ—i sunan sa dai dai to yaje yayi aure,"

"Allah yayi miki albarka Æ´an nan cewar gwaggo,"

Gumi ne yafara tsatssafowa Sulaim take jikin sa ya hau rawa jijiyoyin kansa suka tashi gaba ɗaya hannun sa biyu duk yasa yadafe kansa jin yana barazanar fashewa, kafin kowa ya ankara tuni ya sulale ƙasa babu Numfashi,"

"cikin kaɗuwa da tsantsar tashin hankali Yarima Sultan ya rungumo Sulaim ajikin sa wanda tuni yakai ƙasa daga zaune,"

" Ina lillahi wa'inna ilaihi raji'un Ummeetha tafaÉ—a cikin maÉ—aukakin tashin hankali, gaba É—aya hankalin kowa ya dawo kansu, Kamar aljani haka Saleem ya iso gaban Sulaim wanda ke kwance jikin Yarima Sultan,

Hospital ɗin dake cikin Masarautar Yarima Sultan yakira Waya, cikin ƙanƙanin lokaci Akazo da Ambulance mai tambarin zaki, Harcikin parlourn suka shigo aka tafi da Sulaim, sosai Su mommy Suke kuka,"
Laifin mune wlh bayason haya niya Suhailat tafaÉ—a cikin kuka, gashi yanzu ciwon sa ya tashi,

Gadon da aka ɗorashi princess Salma tabi da gudun gaske, please yaya katashi wlh baza mu ƙara ba, _wake up please_,"
Da sauri mommy ta ruƙota ajikin ta tana lallashi, jin haya niya ne yasa Saleema fitowa da sauri kanta ko ɗan kwali babu,

"Mommy Meye yake faru? Kinyi shiru mommy please wani ya faÉ—a min kukan Meye kuke take itama tafara hawaye,

Wayyo Allah Yaya Sulaim Princess tafaÉ—a hadda shiÉ—ewa,

" Yaya Sulaim kuma Saleema tafaɗa tare da sulale wa ƙasa asume,

"GAba É—aya sukayi kanta cikin tashin hankali"

Yarima sultan har yakai bakin ƙofar parlourn yajiyo a fusace yafara magana tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya,"
"Na rantse da sarkin da raina yake hannun sa Idan wani abu yasamu Aminina, Babu wanda Zai tsira acikin ku, Saina hukunta kowa hukunci msi tsanani," Yakai ƙarshan maganar tare da ficewa da sauri fadawa suka rufa masa baya, yama manta akwai su Ummeetha a gurin, wanda idon shi yakaɗa yayi ja gaba ɗaya ya fita hayyacin sa",

"Gaba É—aya shi suke kallo kowa yayi tsuru tsuru idanuwan fal hawaye..!!

_F pen_
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 2️⃣1️⃣�2�2️⃣📖

"Yarima Sultan harya kai bakin ƙofar parlourn yajiyo a fusace cikin matsanancin ɓacin rai ya fara magana tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya,
"Na rantse da sarkin da raina yake hannun sa, idan wani abu yasamu aminina, babu wanda zai tsira acikin ku sai na hukunta ta kowa hukunci mai tsanani zansa azabtar daku daidai da abunda kuka aikata,"

"Magana yake cikin ƙaraji da kaushin murya kamar bashiba, yama manta da Ummeetha na gurin dasu mommy da gwaggo,

"yana kai ƙarshan maganar yafice a fusace fadawa suka rufamasa baya, ya shiga mota kai tsaye suka wuce asibitin masarautar wanda aka tafi da Sulaim, can suka nufa,"

Saleem dama dashi aka É—auki Sulaim zuwa asibitin, Allah sarki bawan Allah ya rasa ina zai saka ranshi yaji daÉ—i gaba É—aya, faÉ—ur Sulaim ta tayar musu da hankali,

Cikin ƙanƙanin lokaci Yarima Sultan ya isa hospital ɗin, take akabashi hanya ya shiga adai dai ƙofar shiga ya dakatar da fadawan dake biye dashi ta hanyar ɗaga musu hannu, ya shiga shi kaɗai,"

Bayan farfaÉ—owar Saleema, dasunan Sulaim tafara, cikin kuka take FaÉ—in ina yaya Sulaim É—ina please Mommy kudawomin dashi Dan Allah kukaine gurin sa, ganin mommy bata da niyar magana sai sharar hawaye take babu mai lallashin wani acikin su, da sauri Saleema ta tashi daga jiki Mommy ta nufi, Inda Ummeetha ke zaune ta rabka uban tagumi hannu bibiyu,
"Dan Allah Ummeetha ina yaya Sulaim kufaÉ—a min mana idan ma baza ku kainiba kufaÉ—amin naje da kaina,"

"Janyo ta ummeetha tayi jikin ta tare da Shafa kanta, lallashin ta ta shiga yi cikin shigar kwantar da hankali tace, ya'isa haka Daughter, kukan ya isa kada ya saki ciwon kai, jikin Sulaim da sauƙi, za a dawo dashi yanzu insha Allah"

"Ƙara kwantar dakanta tayi sosai saman cinyar Ummeetha cikin muryar kuka, tace Ummeetha Meye yasami Yaya Sulaim dan Allah kufaɗamin bazan iya jurewa Ina..... Sai kuma ta kasa ƙarasawa,"

It's okay Rashin lafiyar sane ya tashi,"
Ta bata amsa a gajarce,

"Kafin Saleema ta ƙara magana, Rafiq ya shigo da sauri babu ko sallama, gaba ɗaya sukai kanshi, suna tambayar Ya jikin Sulaim ya farfaɗo kuwa,"

"Aɗan harzuƙe ya furta, yanzu naji labarin rashin lafiyar tashi, aiku nazo tambaya yana ina?"

"Jiki babu kwari kowa Yakoma inda ya taso, antafi dashi hospital, suhailat tafaɗa da dakusashshiyar muryar ta wadda dagaji kasan tasha kuka, ba yau suka saba ganin ciwon Sulaim ɗin yatashiba amma kullum ciwon ya tashi sai sunyi kuka sosai, duk da ba wata shaƙuwace tsakanin su ba amma dai suna san ɗan uwan nasu,"

"Kallon inda gwaggo murja take zaune a raƙuɓe damuwa ƙarara asaman fuskar ta, Rafiq yayi ƙasa ƙasa ya watsa mata harara, ciki ciki ya furta ai duk kece sula saboda bakinki baya shiru, saunawa za a faɗa muku cewar baya son hayaniya,"

"kai" tsawa ummeetha ta daka masa, fita kabawa mutane guri, kamanta ita wacece a gurina, to bari na tuna maka ita ɗin uwa tace ita tahaifeni, nikuma na haifeku daga ku har Sulaim ɗin dake kwance ba lafiya, koda ba tayi magana ba dole ciwon sa zai tashi Tunda Allah ya ƙaddara hakan, _in fact_ ma ai ba ita kaɗai tayi magana ba, saboda haka tayi ɗin,"

"Amma Ummeetha,

"Rafiq _I say get out_ tunkafin nasaɓa maka _I don't hear anything from you about it_ Tafaɗa tare da nuna masa ƙofar fita da ɗan ya tsanta idanuwan ta duka a rufe,"

"Allah ya huci zuciyar ku, yana Faɗin haka yafita fuuuuu, da sauri Taufiq yaja baya ganin suna ƙoƙarin yin karo shida ɗan uwan nasa, shi yana shirin fitowa shikuma yana shirin shiga,
"Ganin Rafiq a wannan yanayin ne yasa Taufiq fasa shiga yabi bayan sa da sauri wanda tuni yayi nisa yama kusa fita daga Sashen Baba wazirin,"

Sanarwa Akashiga cewar mai martaba yafito zuwa duba Aminin Yarima Sultan a asibiti, sosai Ummeetha taji daÉ—i ko Bakomai ankarrama É—anta,"

"Gwaggo Murja cikin tane ya ƙara ɗurar ruwa jin, Zuwan mai martaba Asibiti tasan dole zai tambaye dalilin faɗuwar Sulaim ɗin, tasan kuma sunan tane a farko, Duk da tayi jika da sarki amma tasan hukunci bai barkan kowa ba gashi dama Yarima Sultan yayi alwashin sai ya hukunta kowa, haɓar zaninta takai zuwa fuskar ta tashare gumin daya tsatstsafo mata saman goshi goshi, "

Princess na lura da ita ganin duk ta furgicene tsoro yakamata gashi hadda gumi hakan yaso bawa princess dariya sai kuma ta maze,"

"To aiko nayi murna Tunda ta amince ai haka muke so, Fulani tafaɗa fuskar ta ɗauke sa yalwataccen murmushi, kallon ta ta mayar zuwa ga ɗan ta Safwan, Yarima ainaji daɗi sosai kasan fa Yarin yar nan Gimbiya Shaheedah baƙaramin dukiya ne da itaba, Saboda gaba ɗaya gadon ta da mahaifin su yabari, Galadima Abdullahi, kasan suna hannun Galadima Murtala, yanzu kuwa da ka aure ta gaba ɗaya za a tattara abaka kaizaka cigaba da yadda kasu da gadon ta ga kuma mulki kakarɓa kaga batun kyautar rabin Masarutar ta ga wancan shashashan yaron Sultan ai babu shi yaron dabe san komai akan mulki ba daga yau yana waccan ƙasa gobe yana waccan ƙasa"

"Nifa Fulani badon dukiya nake son taba, idan kuÉ—ine na fita saboda karfa kimanta mahaifa na shine sarkin wannan Masarutar, nikuma magajin sa, to ai babu wani É—a ko jika acikin Masarutar nan dazai nuna min kuÉ—i ko mulki,"

"Au Au ashe kai sakarai ne waya biya maka wannan karatun ai shi kogi baiƙi daɗi ba, idan akabaka gadon ta saikaƙara ka cigaba da bushashar ka,

"Shiiiiiii" Yarima Safwan yaɗora ɗan yatsan sa ɗaya a saman laɓɓan sa yayiwa Mahaifiyar tasa alamun tayi shiru tare da kasa kunnan sa kamar mai sauraron wani abu,"

Ƙasa ƙasa da murya tace Meye ya faru,"

"Bikiji Alamar kamar ana Sanarwa ba, tabbas wani abun ake Sanarwa kuma wannan mai shelar Fada ne, duk yadda akai akwai wani abu da sarki zai gabatar ko ya gabatar,"

"Take kunnuwan Fulani yajiyo mata Sanarwar sarki ya ziyarci asibiti don duba Aminin ÆŠan sa Yarima Sultan,"
"Mtssssss taja wani irin dogon tsaki cikin jin haushi da baƙin ciki tafara magana, kaji wani abun ban haushin ko wai mai martaba, ne yaje duba wannan yaron Aminin Sultan har asibiti dakan shi ba saƙo ba, amma kai nan kaji ciwo a hannu nake ga ko saƙon sannu da jiki bai aiko makaba, ga ciwon nan haryanzu bai warkeba tafaɗa tare da cunu baki ta nuna hannun ciwon da bakinta,"

To Meye yasa me shi?" Yarima Safwan ya tambaya cikin halin ko in kula,

"Em nikam ina zansani, Tunda ni dakai muna nan zaune,"

Bari naje nagani,
A a fa babu inda zakaje kaje awane dalilin, kana nan zaune jakadiya zata kawo labarin,"
Chapter 16 · 0% Book details