← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 90

Sashe 22

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Suhaima*
Ganin babu komai a dajin tagama zagayen ta aciki tana shirin tafiya, Turus Taja ta tsaya jin ƙafar ta tayi karo da wani abu, da sauri takai duban ta ƙasa, a nutse ta tsugunna ganin, ƙaton kwaɗo an kulle wani abun dashi, koda ta tsugunna babu komai a gurin sai iya kwaɗon, gashi yayi ƙura sosai jikin sa anyi wasu ƙannan rubutu da wani jan abu kamar painti, kamar jini, hannu tasa daniyar Ɗaukar shi, Gam Gam taji shi acikin ƙasa ƙomotsawa ba yayi, da ƙarfin ta ta ƙara jijjigashi, Still ko motsawa baiyi ba, ko alamar gajiya babu a tare da ita, tasa aranta dole saita cire shi taga Meye a gurin, ƙarfin ta tasa ta ƙara kai hannu ko zata iya, ko taɓa shi ba tayi ba taji kamar anyi wulgi da ita sai gata, a gefe yashe a ƙasa kwance, yun ƙurawa tayi bakin ta ɗauke da sunan Allah ta tashi tare da karkaɗe jikin ta, ta ƙara nufar inda ƙwaɗon yake, Tunkafin ta ƙarasa wata guguwa ta taso zata yi sama da ita,
"kwayar cikin Idon Suhaima wadda dama Tuni ta koma Rainbow Colour wani Irin farin haske ne yafito daga cikin idon nata, tune wannan guguwar ta ɓace ɓat,

"Mai Girma Hasheem dake can gefe tsaye ya goya hannayen sa saman ƙirji, mamaki ya bayyana akan fuskar shi duk da ba'a iya gane asalin kamannin sa saboda kwalliyar da yayiwa Fuskar ta shi," Kafin ya gama dogon Tunanin nasa Kamar Saukar a radu haka Suhaima ta tsaya A gaban Sa, babu alamar tsoro ko razani a tare dashi, magana yafara cikin wata irin ƙatuwar murya kamar bata shi ba,
"Idan kika gaggauta barin Estate ɗin nan wataƙila zaki iya tsira da Ranki da na waɗan da suka aiko ki, bazan tambaye ki wacece keba saboda nasan turo ki akai, ina sane dake tun sanda kika shigo cikin mu kum......

*Suhaima*
Ta katse shi cikin ƙara ji, Sauraron barazana da kashedin wani wannan baHali na bane, Banason doguwar magana, idan na tashi ai watar wa kawai nakeyi, Niba Shashasha bace dazan kashe muciji ban sare kanshi ba kamar yadda kukai, Fansa ce takawoni ba sauraron ɗayan kuba, Kashirya iya shirin ka domin yaƙi yana tunkaro ku, A tunanin ka Za ka kashe nine to kacanza tunani, tarihi bazai mai mai ta kanshi a nan ba, alƙawari nane ka sanar wa duk wanda kake jin yakai shege yayi shirin tun karata, har lokacin da na shigo Nan tunani na shene kashe ku, bayan dogon tunani nagane tonuwar Asirin ku kafin mutuwar ku yafi komai mahimmanci, da kisan zanyi da bawannan maganar ake ba,
"Ɗan ya tsanta takai saitin Fuskar sa tace, kasani Banzo ba saida nashirya, Sannan ba gudu ba ja da baya, kowa ye kai ko dame kake taƙama, idan har kana cikin Fansata to bazan taɓa sassautawa ba, saina shafe tarihin ku, akwai kisa mai armashi,
Tana kaiwa nan ta gyara zaman mayafin dake Fuskar ta kai tsaye ta nufi hanyar da zata sa data da House ɗin Baffa don aikin ta na yau yaƙare,"

*Mai Girma Hasheem*
"Kasa Tsaiwa yayi da ƙafafuwan sa suka kasa Ɗaukar sa da sauri yanemi guri ƙasa ya baje cikin ƙunar rai, Damamakin kwarin gwaiwa Irin na Yarin yar nan, sannan da alama tana da taurin kai, Yaro Yaro ne idan da kinsan masifar da kika tarowa kanki haƙiƙa da kinyi gaggawar guduwa a daran nan, zan nuna miki asalin Hasheem, ba ayi mutumin dazai tonamin asiri ina kallon shi nabar shiba,"

*Barrister Sulaiman*
Daya tuna ta sai yaji murmushi ya suɓoce masa Shin ina zan ganta yanzu? Ya tambaye kansa, siffar ta dataja hankalin sa yake ƙara tunawa, Yarin yar ta tafi dani _She is so beautiful_ ya faɗa a fili, amma ai bata kama ƙafar Sabrina kyau ba, Take yabawa Zuciyar Shi amsa, Ko wacce da irin kyan ta,
"A yau basai gobe ba Zanne mo Yarin yar nan, Bazan iya runtsawa idan bangan taba, shi kaɗai yake maganar sa har yafice daga parlourn nasa hannun sa ruƙe da muƙullin mota,"

*Suhaima*
Harta kusa shiga Part É—in Hajiya Umma sai ta tuna da Girkin da tayi É—azu a part É—in Sulaim, da hanzari ta juya ta nufi Part É—in nasa saboda tayi ne don taci abincin ta, Ace kawai Kiga An cinye Zuciyar tace ta raya mata hakan,
Tab tashin hankali aiko da sai anbiya ni Tunda Bawani ƙato nayiwa ba, a fili take maganar har ta ƙarasa ƙofar shiga Parlourn..!!
[01/04, 3:10 pm] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing📲_

*_AHALINMU ÆŠAYA_*
💗💗💗
*_Fatima Y zakariyya👌_*
_Tymer's henna_💅

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS ......✨�*
*_T.M.W_✍️*

_Sarauniyar👸 Taurarin Marubuta writer's✍️✨_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 2️⃣9️⃣�3️⃣0️⃣📖

*Suhaima*
Har takusa shiga Part É—in Hajiya Umma sai ta tuna da Girkin da tayi É—azun A part É—in Sulaim, Da hanzari ta juya ta nufi Part É—in nasa cikin ZumuÉ—in zataci Girkin ta gashi dama yaji nama ita kuma akwai Amana Tsakanin ta da Nama,
"Ace kawai kiga Anciye Zuciyar ta taraya mata Hakan,"
Tab Tashin hankali aiko da sai anbiya ni Tunda Bawani ƙato nayiwa ba, Emm yadda mutanan gidan Nan suke kamar Turawa tayama zasu iyacin irin wannan Abincin, A fili take ta magana ita kaɗai har ta ƙarasa ƙofar shiga Parlourn Sannan tayi shiru,
Da sallama ɗauke a bakinta tatura kai zuwa ciki, kallon Parlourn tashigayi cikin tsanaki, Ko ba'a faɗa mata ba ta tabbata an shigo Parlourn, ga daddaɗan ƙamshin turare daya kaura ye mata Hanci,
Ya dawo kenan? Ta tambaye kanta tare da wucewa Dinning Area kai tsaye, Turus taja ta tsaya ganin plates Anci Abinci da alama abincin ta ne akaci, Gashi kusan 4 plates, Da sauri taƙarasa kamar zata yi kuka ta furta, Wayyo Allah Sun cinye wlh Sun cinye, ta shiga buɗe Food flakes ɗin data zuba DASHISHIN Aciki, hannu tasa tatattara saura gaba ɗaya acikin tafin hannun ta, juice ɗin ma Ko rabin ƙaramin kofi bai kaiba, flakes ɗin Chicken and Salad tabuɗe, Shi kaɗaine taga tamkar ba'a taɓa ba, amma komai antashi dashi, kallon kwanikan take ɗaya bayan ɗaya, wani irin suya zuciyar ta keyi mata,
Wato hadda wasu ƙattin ya ɗakko suka cinye mun Abincin ko saboda ga baiwar shi, to wallahi basuci banza ba Sai sun biya ni gaba ɗayan su, kuma Na rantse bazanci ragowar ƙatti ba, Tana masifa Tana Tattara kwanikan kamar wadda aka yiwa dole gara ma in wanke kwani kan kona rage zafi gobe ma na huta da aikin safe, saida ta kwashe komai, takai kitchen ta wanke kafin tamaida komai mahallin sa, sannan ta fito daga cikin Kitchen ɗin Dinning ta koma shima ta gyara Tsaf,
Allah kabimin haƙƙina Tafaɗa tare da fice daga Parlourn,"

*_In The Morning_*

*Barrister Sulaiman*
Kamar a mafarki yake kallon khaltum dake ta faman zazzare ido,

Wayyo Allah munƙara haɗuwa, Khaltum tafaɗa cikin ranta,
Ganin ya tsare ta da ido ne yasa ta FaÉ—in Barka da Safiya,

"ke waye yabaki izinin shigo min part?

"Dama' Dama nice sabuwar mai aikin dazan rinƙa kulawa da wannan sashe, Jiya nafara aiki anan ɗin bansan Waye mamallakin nan ɗin ba"

"Tunda tafara magana yake kallon bakin ta, har saida Khaltum taji shiru, tayi zaton ya tafi, tana É—agowa suka ido huÉ—u da juna,"

"Itace Wallahi itace na kwana tunanin ta Ashe tana kusa dani, Thank god, Takawa ya farayi zuwa inda khaltum ke tsaye cikin shigar doguwar rigar Material launin ɗorawa, ta lulluɓa mayafin Material ɗin akanta dayake babba ne ya rufe mata har bayan ta,
Saida yaje daf da ita sannan ya tsaya tare da goya hannuwan sa ya baya, take jikin ta ya hau ɓari, Allah ka tseratar dani daga hannun Mutanan Gidan nan, Cikin Tsoro khaltum ta faɗi hakan a ranta, Tayi Tsammanin Wani Abu zaiyi mata, "
"Nine mamallakin wannan ɓangaran Zaki kula dashi Sosai, Sannan inaso ki kula da mamallakin Part ɗin ma,"

"Eh zanyi Insha Allah, Hadda Mamallakin nashi Zaki kula dashi? Yaje fa mata wata Tambayar, Da sauri ta kalle shi Har lokacin batawani gane abunda yake nufi ba"

Murmushi Yasaki ganin Alamar bata gane abunda yake nufiba,
Kiyi aiki mai kyau kinji _Black Beauty_ see u later yana kaiwa nan ya haura Sama don shirin Office zuciyar sa fal Farin ciki ya rasa na Meye, Tunjiya nake son ganin ta gashi babu dalili,"

Dafe ƙirji Khaltum tayi tare da sauke wata nannauyar ajiyar Heart, aikin banza yasa zuciya ta tana barazanar barin ƙirjina, Ashe Nan ɓangaran shine, Nashiga Uku ni Khaltum, yanzu haka zancigaba da haƙuri da wannan mai jarabar kallon, wallahi dama a maidani wani sashan, Emm koda yake gyara nan ɗin akan da a kaini cikin masu kisan kai, su tsotsemin jini don gaba ɗaya mutanan gidan nan abun tsoro ne, Suhaima tajamin bala'i Dana san fargaba da tashin hankali zan tarar da banbiyo taba,
Munzo dan ÆŠaukar fansa amma kullum cikin Zullumi nake da'alama sai munyi taran mu nanan gidan, idan naji bazan Iyaba Allah guduwa zanyi, Jin alamar kamar Motsin mutum hakan yasa Khaltum saurin kame bakin, tafara aiki Gadan Gadan,
Sabrina ce ta turo kai Parlourn ko sallama babu, jikin ta sanye da Egypt Gown red colour Mai kwalliyar duwatsu cin kushe guri ɗaya sai ƙalli suke kanta sanye da p-cap tasaki gashin ta tabaya, ƙaton glass ɗin Idon ta daya rufe rabin Fuskar ta, ta ɗan zameshi kaɗan, kallon khaltum tayi Sheƙeƙe,
"You ina Yaya Sulaiman?
Ganin ita take kallo yasa khaltum saurin FaÉ—in, Yana sama tare da nuna mata da É—an ya tsantsa Batare da Sanin Waye Sulaiman É—in da ta tambaya ba Kawai tayi amfani da Mutumin dayace shine mamallakin Part É—in shiyasa ta ce mata yana sama,
Chapter 22 · 0% Book details