← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 90

Sashe 61

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
*_(THE QUEEN👑)_*

________Dedicated to anty salma💎

*_Part 2_*
(Littafi na biyu📘)

_Godiya ta musamman gareku ɗaukacin masoya na ina matuƙar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.🤗😘😘_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

➡️🅿� 2️⃣1️⃣�2�2️⃣📖

"Yarima Sultan harya kai bakin ƙofar parlourn yajiyo a fusace cikin matsanancin ɓacin rai ya fara magana tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya,
"Na rantse da sarkin da raina yake hannun sa, idan wani abu yasamu aminina, babu wanda zai tsira acikin ku sai na hukunta ta kowa hukunci mai tsanani zansa azabtar daku daidai da abunda kuka aikata,"

"Magana yake cikin ƙaraji da kaushin murya kamar bashiba, yama manta da Ummeetha na gurin dasu mommy da gwaggo,

"yana kai ƙarshan maganar yafice a fusace fadawa suka rufamasa baya, ya shiga mota kai tsaye suka wuce asibitin masarautar wanda aka tafi da Sulaim, can suka nufa,"

Saleem dama dashi aka É—auki Sulaim zuwa asibitin, Allah sarki bawan Allah ya rasa ina zai saka ranshi yaji daÉ—i gaba É—aya, faÉ—ur Sulaim ta tayar musu da hankali,

Cikin ƙanƙanin lokaci Yarima Sultan ya isa hospital ɗin, take akabashi hanya ya shiga adai dai ƙofar shiga ya dakatar da fadawan dake biye dashi ta hanyar ɗaga musu hannu, ya shiga shi kaɗai,"

Bayan farfaÉ—owar Saleema, dasunan Sulaim tafara, cikin kuka take FaÉ—in ina yaya Sulaim É—ina please Mommy kudawomin dashi Dan Allah kukaine gurin sa, ganin mommy bata da niyar magana sai sharar hawaye take babu mai lallashin wani acikin su, da sauri Saleema ta tashi daga jiki Mommy ta nufi, Inda Ummeetha ke zaune ta rabka uban tagumi hannu bibiyu,
"Dan Allah Ummeetha ina yaya Sulaim kufaÉ—a min mana idan ma baza ku kainiba kufaÉ—amin naje da kaina,"

"Janyo ta ummeetha tayi jikin ta tare da Shafa kanta, lallashin ta ta shiga yi cikin shigar kwantar da hankali tace, ya'isa haka Daughter, kukan ya isa kada ya saki ciwon kai, jikin Sulaim da sauƙi, za a dawo dashi yanzu insha Allah"

"Ƙara kwantar dakanta tayi sosai saman cinyar Ummeetha cikin muryar kuka, tace Ummeetha Meye yasami Yaya Sulaim dan Allah kufaɗamin bazan iya jurewa Ina..... Sai kuma ta kasa ƙarasawa,"

It's okay Rashin lafiyar sane ya tashi,"
Ta bata amsa a gajarce,

"Kafin Saleema ta ƙara magana, Rafiq ya shigo da sauri babu ko sallama, gaba ɗaya sukai kanshi, suna tambayar Ya jikin Sulaim ya farfaɗo kuwa,"

"Aɗan harzuƙe ya furta, yanzu naji labarin rashin lafiyar tashi, aiku nazo tambaya yana ina?"

"Jiki babu kwari kowa Yakoma inda ya taso, antafi dashi hospital, suhailat tafaɗa da dakusashshiyar muryar ta wadda dagaji kasan tasha kuka, ba yau suka saba ganin ciwon Sulaim ɗin yatashiba amma kullum ciwon ya tashi sai sunyi kuka sosai, duk da ba wata shaƙuwace tsakanin su ba amma dai suna san ɗan uwan nasu,"

"Kallon inda gwaggo murja take zaune a raƙuɓe damuwa ƙarara asaman fuskar ta, Rafiq yayi ƙasa ƙasa ya watsa mata harara, ciki ciki ya furta ai duk kece sula saboda bakinki baya shiru, saunawa za a faɗa muku cewar baya son hayaniya,"

"kai" tsawa ummeetha ta daka masa, fita kabawa mutane guri, kamanta ita wacece a gurina, to bari na tuna maka ita ɗin uwa tace ita tahaifeni, nikuma na haifeku daga ku har Sulaim ɗin dake kwance ba lafiya, koda ba tayi magana ba dole ciwon sa zai tashi Tunda Allah ya ƙaddara hakan, _in fact_ ma ai ba ita kaɗai tayi magana ba, saboda haka tayi ɗin,"

"Amma Ummeetha,

"Rafiq _I say get out_ tunkafin nasaɓa maka _I don't hear anything from you about it_ Tafaɗa tare da nuna masa ƙofar fita da ɗan ya tsanta idanuwan ta duka a rufe,"

"Allah ya huci zuciyar ku, yana Faɗin haka yafita fuuuuu, da sauri Taufiq yaja baya ganin suna ƙoƙarin yin karo shida ɗan uwan nasa, shi yana shirin fitowa shikuma yana shirin shiga,
"Ganin Rafiq a wannan yanayin ne yasa Taufiq fasa shiga yabi bayan sa da sauri wanda tuni yayi nisa yama kusa fita daga Sashen Baba wazirin,"

Sanarwa Akashiga cewar mai martaba yafito zuwa duba Aminin Yarima Sultan a asibiti, sosai Ummeetha taji daÉ—i ko Bakomai ankarrama É—anta,"

"Gwaggo Murja cikin tane ya ƙara ɗurar ruwa jin, Zuwan mai martaba Asibiti tasan dole zai tambaye dalilin faɗuwar Sulaim ɗin, tasan kuma sunan tane a farko, Duk da tayi jika da sarki amma tasan hukunci bai barkan kowa ba gashi dama Yarima Sultan yayi alwashin sai ya hukunta kowa, haɓar zaninta takai zuwa fuskar ta tashare gumin daya tsatstsafo mata saman goshi goshi, "

Princess na lura da ita ganin duk ta furgicene tsoro yakamata gashi hadda gumi hakan yaso bawa princess dariya sai kuma ta maze,"

"To aiko nayi murna Tunda ta amince ai haka muke so, Fulani tafaɗa fuskar ta ɗauke sa yalwataccen murmushi, kallon ta ta mayar zuwa ga ɗan ta Safwan, Yarima ainaji daɗi sosai kasan fa Yarin yar nan Gimbiya Shaheedah baƙaramin dukiya ne da itaba, Saboda gaba ɗaya gadon ta da mahaifin su yabari, Galadima Abdullahi, kasan suna hannun Galadima Murtala, yanzu kuwa da ka aure ta gaba ɗaya za a tattara abaka kaizaka cigaba da yadda kasu da gadon ta ga kuma mulki kakarɓa kaga batun kyautar rabin Masarutar ta ga wancan shashashan yaron Sultan ai babu shi yaron dabe san komai akan mulki ba daga yau yana waccan ƙasa gobe yana waccan ƙasa"

"Nifa Fulani badon dukiya nake son taba, idan kuÉ—ine na fita saboda karfa kimanta mahaifa na shine sarkin wannan Masarutar, nikuma magajin sa, to ai babu wani É—a ko jika acikin Masarutar nan dazai nuna min kuÉ—i ko mulki,"

"Au Au ashe kai sakarai ne waya biya maka wannan karatun ai shi kogi baiƙi daɗi ba, idan akabaka gadon ta saikaƙara ka cigaba da bushashar ka,

"Shiiiiiii" Yarima Safwan yaɗora ɗan yatsan sa ɗaya a saman laɓɓan sa yayiwa Mahaifiyar tasa alamun tayi shiru tare da kasa kunnan sa kamar mai sauraron wani abu,"

Ƙasa ƙasa da murya tace Meye ya faru,"

"Bikiji Alamar kamar ana Sanarwa ba, tabbas wani abun ake Sanarwa kuma wannan mai shelar Fada ne, duk yadda akai akwai wani abu da sarki zai gabatar ko ya gabatar,"

"Take kunnuwan Fulani yajiyo mata Sanarwar sarki ya ziyarci asibiti don duba Aminin ÆŠan sa Yarima Sultan,"
"Mtssssss taja wani irin dogon tsaki cikin jin haushi da baƙin ciki tafara magana, kaji wani abun ban haushin ko wai mai martaba, ne yaje duba wannan yaron Aminin Sultan har asibiti dakan shi ba saƙo ba, amma kai nan kaji ciwo a hannu nake ga ko saƙon sannu da jiki bai aiko makaba, ga ciwon nan haryanzu bai warkeba tafaɗa tare da cunu baki ta nuna hannun ciwon da bakinta,"

To Meye yasa me shi?" Yarima Safwan ya tambaya cikin halin ko in kula,

"Em nikam ina zansani, Tunda ni dakai muna nan zaune,"

Bari naje nagani,
A a fa babu inda zakaje kaje awane dalilin, kana nan zaune jakadiya zata kawo labarin,"

"Dafe kan Sulaim Ummul Bait tayi fuskar ta na gaf da tashi da'alama addu'a takeyi masa tadaɗe sosai tana yi masa, wanda yana kwance ko motsi ba yayi an ɗaura masa Drive, idanuwan Sa a rufe, fuskar tashi har taɗan faɗa, hakan sai yaƙaramasa kyau sosai,"

"Ahaka mai martaba ya iso yasamesu, ga Yarima Sultan tsaye, sai Saleem dake zaune daga jikin bango yana fuskantar gadon, gaba É—aya fuskokin su É—auke da Matsananci damuwa,"

Har ƙasa suka russuna suka gaida mai martaba, bai iya ko amsa musu ba hannu kawai ya ɗaga musu,

"Shiru sarki yayi yana kallon Ummul Bait nazarin ta yashigayi, Sosai yake ji daɗin yadda yasamesu tanayi wa Sulaim addu'a, tunani ya farayi cikin ransa ashe bashi kaɗai ke ƙaunar Sulaim ba yana son Yaron Tamkar Ɗan sa Sultan haka yake jin sa a rai,"

Ɗagowa tayi bayan ta kammala yi masa addu'ar, Fuskar ta babu yabo ba fallasa, ta dai dai ta zaman alkyabbar dake jikin ta launin ɓaki mai fararan duwatsu,
"kallon mai martaba tayi, Barka da zuwa Ranka tadaɗe Allah ya ƙara maka yawan Nasara,"

"Barka dai ya jikin nasa fatan Da sauƙi,"

"Alhamdulillah, tafaÉ—a tare da matsawa daga jikin gadon saboda mai martaba yasamu damar duba shi,"

"Sunan Allah É—auke abakin sa ya fara motsawa ahankali, ya ware manyan idanuwan sa gaba É—aya, tare da cire hannu ya dafe kansa alamar ciwo yake masa,"

Gaba ɗaya suka nufo gadon Yarima Sultan da Saleem, ganin mai martaba ya isa jikin gadon hakan yasa su dakata wa gaɓa ɗaya,"

Ɗakyar Sulaim yakai Dubansa zuwa gurin Sarki, Yinƙurawa yayi zai tashi, Sarki ya dakatar dashi tare da kama kafaɗun sa duka biyun Yamai dashi kwance, Allah yabaka lafiya Sannu da jiki, Allah yasa ka kasan ce cikin aminci da samun sauƙi, ka huta sosai,"

"Baffa inaso naga Baffa yanzu, Sulaim ya faɗa muryar shi tayi ƙasa sosai har lokacin bai cire hannun sa daga goshin saba,

Kasan cewar gaba É—aya sunyi shiru hakan ya basu damar jin abunda yace,
"Matsawa Yarima Sultan yayi kusa dashi, Alhamdulillah Sannu yakakejin jikin naka?

"Kallon sa Sulaim yayi, Tare da ruƙo hannun Yarima Sultan ɗaya, Aminina yaushe Baffa yazo nan Ina Baffa inason ganinshi yanzu,"

Baffa bai zo ba kamanta yanzu dare ne kayi haƙuri zuwa gobe zamuje zakaga Baffa, Emm

A'a Baffa yazo nan shine yayimin addu'a yanzun nan, naji hakan acikin raina, please ku kaine,"

"AÉ—an raunane Yarima Sultan yakai Dubansa kan iyayen nasa, yana nuna musu alamar suna jin Abunda Sulaim yake faÉ—a,"

Tasowa Saleem yayi ya nufi gadon Dai dai lokacin wayar Sulaim dake hannun sa ta É—auki ruri, kallon screen É—in wayar yayi, Ras Ras, gaban sa yafaÉ—i ganin, _Lovely Grandad_ a rubuce, ganin Saleem yayi shiru yana kallon screen É—in wayar ne gashi kiran ya katse wani ya sake shigowa,"

Saleem Lafiya dai? Yarima Sultan ya Tambaya,

Baffa ne yake kira,"
Tabbas ansanar masa Rashin lafiyar Sulaim yanzu ya za ayi,?

"Iska Yarima Sultan ya furzar, huuuuu, batare da yace komai ba,"

"Shi ko Sulaim ya ƙara rufe idon sa kamar mai bacci amma duk yana jin su baya son Magana ne kawai"
Chapter 61 · 0% Book details