← Book details Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 90

Sashe 43

Ahalinmu Daya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aɓangaran Mama Bilki kuwa, Ta rasa Ina zata Tsoma Ranta taji daɗi Gaba ɗaya Tunanin ta Ya tafi Wajan, Ta yadda Zasu samu Suhaima, Gashi Ta Kira Boka Zarshima Yaƙi ɗaga Wayar ta,
Gashi Baffa yakira ta Bata je ba Har angama walimar, Komai ya dagule mata, Kiran Sara ne ya katse mata Tunani, kamar baza ta É—aga ba sai kuma ta É—aga, "Ina jinki"
"Hello Mama Barka da dare Fatan kuna Lafiya"
"Lafiya Yanzu ina wani abu zankira anjima, Mama Bilki tafaɗa tana ƙoƙarin Katse kiran, Jin alamar hakan yasa Sara Saurin faɗi, Mama Lafiya dai Kiyi haƙuri in faɗi abunda zan faɗa mana,
"Wani Dogon Tsaki Mama Bilki taja Kafin Tace To Uwata Ina jinki,
"Mama Dan Allah Ki rinƙa kwantar da Hankalin ki, kina kauda ido akan Wasu abubuwan, Kada wani ciwon Yaka maki,
"A ƙufule Mama Bilki tace Zaki faɗi abunda zaki faɗa ko sai kingama yimin faɗan,
"Allah ya huci zuciyar ki, Ashe Sulaim Bashida lpy Babu wanda YafaÉ—a min Yanzu Nasamu labari"
"To tinda kinji yanzu ai shikenan, karki dameni,
"Shikenan Mama ina nan Tafe Next week Har biki Idan muka zo Saboda Ayi komai damu sai Induba jikin nashi idan nazo,
"Ke kika sani, Tana FaÉ—in haka ta kashe Wayar ta ta ajiye,
Zuru Sara tayi tana kallon Screen ɗin wayar, duk da tasan maman nasu, Akwai faɗa Amma Yau taji abun ba sauƙi, wai (Ciwon Ar ne,) Sara Itace Ƙarama A Ƴaƴan mama Bilki Yanzu haka tana Aure a ƙasar Senegal 🇸🇳 Wanda aiki ne yakai mijin ta can Allah Bai bata haihuwa ba ita kadai daga ita sai mijin ta, Tana son Ƴan uwan ta Fiye da yadda su suke son ta,
Amma Mama Bilki da Anty Jamila Basa ta acikin Al'amuran su, Saboda ita babu ruwan ta Batasan komai akan Abubuwan da suke ƙullawa ba, Ko yaushe cikin basu shawar warin gaskiya take, Amma a banza (Man kare) ita halin ta ɗaya da Uncle Yusuf shiyasa tasu tafi zuwa ɗaya, Shine abokin shawarar ta,

A Daran Ranar Sajad ya Sauka, kai tsaye part ɗin Sulaim Acan yayi landing Gaba ɗayan su suna zaune a parlour, Bayan baƙi Sun tafi Kowa na huta,
Kallon Idan Sulaim Ke Zaune yana ta faman Typing A Computer É—in shi Gefan shi Cup É—in Coffee ne sai Tiriri Yake, "Aminina wai Meye kakeyi?
ÆŠagowa Sulaim yayi Tare da FaÉ—in, Zan koma Aiki ne Ina shigar da Sabbin Decumenents ne,

"What Aiki ina? Sajad Ya tambaya yana kallon Sulaim,

"Abuja Sulaim ya bashi amsa a taƙaice,

"Wow Really? Sulaim Yau da kanka, cikin mamaki Sajad yayi Maganar

"Sulaim yace "Em ko akwai matsala,

" No no Nayi farin ciki ne matuƙa

"Aminina wai da gaske kake ko wasa? Yarima Sultan ya tambaya, wanda Tunda Sulaim yayi magana Shock NA mamaki yaka masa,

"I'm not joking, meye ma abun wasa aciki?

"Sultan yace Masha Allah, Amma Baffa ya sani kuwa?

Sulaim yace Babu wanda yasani amma zan sanar musu,

Hakan yayi kyau gaskiya kowa zaiyi farin ciki, bayan tsawon lokaci Gashi yau Aminina yana maganar aiki da kanshi,

Murmushi kawai Sulaim yayi don shima kanshi ji yake tamkar an sauke masa wani abu da yayi masa nauyi a ka da kuma zuciya wanda yake jin tamkar shi yake hana shi ai watar da abunda ya dace a cikin rayuwar sa, ya rasa dalilin can za warsa,

Wayar Hannun Samrat Sajad ya faki idon sa ya waf ce, kallon sa Samrat yayi da sauri,

"Ana ta magana kazo nan sai wani danna waya kake,

"Omg Give me my phone please," abunda Nake me mahimmanci ne, Samrat yayi magana yana miƙawa Sajad hannu alamar yabashi,

"Meye mai mahimmancin Ai da sai kabar cikin mu, Sultan ya faÉ—a yana harar sa,

Murmushi Shattima yayi, "Na faÉ—a muku ita É—in ta musamman ce, dole Duk wanda ya ganta zuciyar sa sai ta karye a kanta Yarin yar kyakkyawa ce,

Kallo ya koma sama, Shiru sukai duka suna kallon shi,
Sajad ne yace"Wow Cigaba muna sauraron ka wacece wannan mai sa'ar?
Samrat Murmushin sa ya faÉ—aÉ—a, cikin jin daÉ—i Sajad ya goyi bayan sa yace,
"Har yau ban ganta a zahiri ba bansan inda take ba, Amma ina mutuwar son ta, itama tana sona, Sun kasa Bani goyan baya saboda Su Sunkama nasu matan a hannu,

"To Siffan ta mana ita yaya kamannin ta suke?
Sajad ya ƙara magana yana Matsawa kusa da Shattima,

Dama Sajad akwai son labari,

"Siffar Hmm ta Ita É—in abar so ce ga kowa, Mai Haske, Hasken ta tamkar Tauraruwa acikin Hasken Farin wata,
Kyakkyawar Fuskar ta, Fuskar mutanan kirki.
Dai dai tattun haƙura.
Idanuwa masu ÆŠaukar hankalin mai kallo.
Murmushin zinare.
Tabbas akwai hasken makaranta atare da ita, ilimin ta Tamkar kogi.

"Samrat
Sulaim yakira Sunan sa,

Da Sauri Shattima yabuɗe idanuwan sa Wanda tunda ya rufe su yana ta karantu Baitikan yabo ga ɓoyayyar masoyiyar sa,

ÆŠaga wasa Sulaim gira yayi alamar, lafiya inajin ka,

"Oh shatt Gaskiya Bro ka ɓatamana yanayi Yanzu gashi ka katse shi bai gama ba, Sajad ne yayi maganar yana kallon Sulaim,

Tsaki Sulaim yaja Tare da Sun kutar, Computer É—in shi Yanufi Dinning Area,

Gaba É—aya suka dariya,

Yarima Sultan yace Wallahi, ku ƴan iska ne, Amma zanyi maganin ku Soon, yafaɗa shima yamiƙe yabar musu gurin, Yanufi Upstairs Don yagaji sosai,

Sajad yace Amma ai da kun tsaya yafaÉ—a mana sunan ta, kafin kutafi cikin É—aga murya yayi maganar Amma ko juyawa Sultan baiyi ba bare yayi magana,

Suma tashi Sukai a tare, Samrat yace Ina son Zuwa MALL Ko zamuje?
"OK muje Sajad yabashi amsa a taƙaice,
"Samrat yace Oh sorry, Naman ta baka jima da zuwa ba Akwai gajiya a tare da kai, Ka huta kawai,
"No Muje kawai Ba wani gajiya fa,
Key É—in mota Samrat ya É—auka sama table suka fice abun su, Suna sa kai Suhanna itama na sako nata kan, Da sauri taja baya tana basu hanya,

"Tace Kuyi haƙuri ban kula ba"

Ba tare da Sun kalle taba Suka wuce itama dama basu take kallo ba Waya ce a hannun ta, kuma hankalin ta nakan wayar, Suna wuce wa tasa kai,

Suna shiga mota Samrat ya kalli Sajad yace, "Man Allah kamar nasan Voice na Wannan data wuce,
Cikin halin ko in kula Sajad yace, To a ina kuma?
"Shiru yayi tare da FaÉ—in, Nakasa tunawa amma tana min kama da muryar Masoyiya ta, SOHANA,
"Dariya Sajad yayi Sosai, "Kace Har Gezo take maka Kana Jin Voice É—in wasu like her, Easy Man Mutafi Kawai,
"ÆŠan É—aga kafaÉ—a Samrat yayi, Batare da yace komai ba ya tada mota,

~ Suhanna ~
Zama tayi Saman kujera ta ciga ba da Shafa wayar ta, Tana jiran Sulaim kamar yadda yabata Umarnin ta jirashi,
Tayi Tsammanin yana Upstairs kawai tagan shi daga Dinning Area yafito Hannayen Sa zube cikin Aljihu,
Murmushi ta sakar masa, ta ajiye wayar tace, "Ya Sulaim barka da dare, Fatan anfito Lafiya ya ƙarfin jiki?
ÆŠan É—aure Fuska Sulaim É—in yayi, "I don't know,it's not what I ask you,
Nace kizo tun É—azun sai yanzu ko, Suhanna yaushe nafara wasa dake?
"Dan Allah Yayana kayi haƙuri, Naje aiki nadawo, Nasamu ana walima Na zauna, bayan an gama na koma House, Sannan na cimma saƙon ka, A Time ɗin nagaji sosai, Kuma inayin.....
"Na Tambaye kine?"Just answer my questions, Sulaim yafaɗa yana Kallon ta ƙasa ƙasa,
"A'a Please ya Sulaim nayi Laifi amin Afuwa, gani na amsa kira,
"Better, Gashi wanda ki kaiwa laifin Har Ya fita Kidawo gobe ki bashi haƙuri,
"Ya Sulaim laifi kuma ni? TafaÉ—a tana nuna kan ta Tamkar zata fashe da kuka,
"No Maybe Ni,
"Sorry Amma bansan laifin dana aika ta ba, Please kafaÉ—a min,
"Zaki iya Tafiya dare yayi, Idan kika dawo Gobe Zakiji laifin da kikai Tunda, U don't Know oky"
ÆŠaga kai tayi alamar Eh, Tashi tayi jiki ba kwari ta gyara, Maya finta Wanda yake Siriri ko gashin kanta bai Rufe ba, Amma jikin ta sanye da wata jib gegiyar Rigar Sanyi wanda ta É—ora Saman Kayan jikin ta takai mata har gwaiwa,
Bin bayan ta Sulaim yayi da kallo Yana sakin Murmushi dan yasan da'alama ta shaƙa,
Bayan ta fita Da har yayi hanyar Sama Sai kuma ya dawo yabi bayan ta shima sai da yafita har waje, Akan idon sa tashiga motar da tazo da ita, Bai dana kallon motar, ba har saida yaga ta fita daga House É—in gaba É—aya,
Bai koma ciki ba Sai ya nufi Coffee Garden Aran Sa yaji ya daɗe bai jeba, yana son gurin kodan Shuke shuken dake cikin Garden ɗin masu Dadda ɗan ƙamshi,
Ƙarasawa yayi cikin gurin, Haske Tamkar da rana Ko ina gwanin ban sha'awa ga Dadda ɗan isakar dake ƙadawa A hankali Cikin yanayin sanyin garin,
Mutum ya gani zaune An juya baya da'alama Wanda ke zaune ya shagala da tunanin wani abu ko kallon wani abun, Saboda daga yadda Wanda ke zaune Ko alamar yaji motsi ya juyo bai yi ba,
Mace ce, Sulaim ya Furta hakan a ranshi, Kasan cewar Daya ƙara matsawa yagan ta sanye da Hijab, Sosai ya ƙara matsawa Kanta, don ganin wace, Kamar wanda aka ɗaure haka yaja ya tsaya cak ya kasa Matsawa gaba ya kasa matsawa baya,

"Kama ta yayi kamin Sallama baka tsaya min a kaba, Suhaima ce tayi maganar ko motsawa ba taiba daga yadda take,

"who are you and what are you doing here? Sulaim yayi maganar babu ƙoɗar a ranshi,

"Baka ganewa ne, Ko bakajin Hausa, Nace Sallama ce fari,

Zagayawa Sulaim yayi,
Ga mamakin Suhaima Sai taga ya zauna kusa da ita Kujera ɗaya, bata ko motsa daga yadda take ba, Kallon ƙasa ido tayi masa batare da ce komai ba,
Chapter 43 · 0% Book details