← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 61

Sashe 8

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zahiri kuwa wani irin lelen ta yake kamar kwai, a cikin sati dayan nan ya nuna mata gata sosai, wanda ta dinga hango gidan su tana ayyanawa a ranta

'Dama haka rayuwar Abuja take da daɗi, ga miji gangariya na samu, ga kayan alatu na ci na sha na kwanta miji namin hidima, tab amma an bar Juwairiyyah a baya ina tausaya ma rayuwar ta, dan kuwa haka zata qare ta cikin talauci da babu'

Shafa gefen  fuskar ta Alhajin nata ya yi tare da fad'in,

"Tinanin me kike yi haka ?"

Cike da shagwab'a ta kwanta a jikin shi ta ce,

"Ba komai, ina tinanin ka ne kawai"

Ta qarasa  maganar ta tana wani karairaya tare da qarasa haye cinyar shi,

" karki damu ai gani kome kk so naki ne, nema kawai zaki a baki baby"

Dariya ta yi tana shafa jikin shi tana limshe ido, sannan ta kashe murya ta furta,

"Da gaske Alhaji na?"

Da gaske mana tambayi ki ga aiki da cikawa"

"Hmmm ni dama dubu dari biyu kawai nake so zan je na dan siyo kayan sawa na gida, dan na ga ba a kawon kayana nan ba, kace a bari inna zo gidan ka akwai amma ka hana ni shiga dakuna ukun can, sannan kuma in da nake ba wasu kayan kirki na saka wa"

' Yarinya wannan lokacin nake jira da zaki nemi wani abu a wajena'

A zahiri Kuma sai ya ce,

"Sorry my love ki yi haƙuri,maza  shirya muje na kaiki ki siyo kayan da duk ki ke buqata, menene wani dubu ɗari biyu kuma? Ai ba abinda ba zan kashe maki ba in dai ina da shi"

Da sauri ta sauka tana murna ta saka kaya ta dauki jakar da tazo da ita ta fito ta na jiran su tafi shopping,tsaf ta ganshi a tsaye Shima ya fito yana mata wani irin shegen murmushi,  fita suka yi suka dauki hanya, suna ta tafiya, sai ta ga suna barin gari suna ta wuce shaguna da super markets, kasa jurewa ta yi cikin kissa ta ce,

"Ina zamu ne haka sweety?"

Idanun sa na saman hanya ya furta,

"Wani waje zan kai ki na musamman in kk ga wajen zaki ji daɗi sosai"

"Wooow  Sweety u ar so romantic , i love u"

"I love u more dear"

kiss ya yi wa hannun ta, a haka yana tuqi ta yi bacci, bata bude ido ba sai a wani qauyen da bata san ina bane, wani gidan qasa ne mai girman gaske, ko ta ina mata da yara qauyawa ne a ciki sai wasu dattijai a gefen wata bishiya, sina cin wani tuwo baqi miyar koriya sharrr da ita, da sauri ta miqe ta fara murza ido, a zaton ta mafarki take yi,cikin tsananin razana ta furta,

"Babe ina ne nan? Me muke yi anan? Ko mafarki nake yi ne?"

" Hhhhhhhh ba mafarki ki ke yi ba Salame, nan shine ya dace da ke, kuma nan ne gidan ki, na asali, can gidan gidan oga na ne daya karban auren ki, anyway sun yi tafiya shine na kai ku mu ci amarcin mu, karki damu bangaren ki yafi na dika gidan kyau, da taimakon ogana, harda TV an sa maki, tin da ko gidan uwale da ubale ai babu su ko?"

Ya faɗa yana wani shu'umin murmushi, ita ko ta dad'e da fara kuka harda majina, kuka take tana bashi hakuri ya maida ita wa Goggon ta ita ta fasa auren nashi in dai a nan zai ajiye ta, wanka mata mari ya yi mai lafiya sannan cikin fushi ya ce,

" Dan uwar ki mai kwadayin nan an gaya maki wawa ne ni? Na kashe maki yan kudaden nawa kice na maida ki gida, ai ke da gida sai kin haifi biyar a qalla, sai dangin ki sun manta dake , ba dai Abuja kk so ba, to ai nan ma Abuja ce, dan haka baki da damuwa,inna fita ki tabbatar kin biyo ni in ba haka ba a gaban su zan fara ballaki, danni ba sabon abu bane wajena dukan mace"

D'aga kai ta yi ta na kallon shi cike da tsoro da mamaki,dan yanzu wani irin tsoron shi take ji ba kadan ba, hankailin ta kuwa idan ya yi dubu to ya tafi yawo, musamman da ta shiga ta ga daki daya ne dakin nata da wata yar TV da kayan kallo, sai gado qarami da kujeru biyu, da yan kwanika da ledar tsakar d'aki, kai abun dai kamar wata mara gata, haka ta shiga tana kuka kamar ta suma take ji dan baqin cikin da ke ran ta, biyo ta ya yi yace ta biyo shi d'aki mai kallon nata, amsawa ta yi ta bishi kamar raquma, wani d'aki ta shiga mai cike da tarkace da tsohon gado, sai wata uwar datti da aka tara a gefe na kayan wanki, ga poo din kashin yaro ba a zubar ba qazanta dai ta qarshen qarni kawai, wasu yammata ne a gefe an ci mai an yi fari ta fuska an d'ashe har fuskar ta yi wani kampala kampala, ba kyaun gani, sun sha bra ta dame su anyi daurin qirji da yan wayoyi a hannun su, manyan 'ya'yan Alhaji Talle ne, a qauyen nasu duk da Talle aka san shi, ko kuma a ce masa Tallen marka wato matar shi uwar 'ya'yan shi manyan kenan.

Markan ce ta fito daga kicin kamar wata baqar mahaukaciya, futu2 da ita tana goge hanci da bakin zanin ta, ido ya yi mata jawur, da dukkan alamu girki take yi dan kuwa jikin ta sai qauri hayaqi da warin hammata ke tashi, cikin d'aga murya Talle ya ce,

"Dalla malama ki yi sauri yau zan koma ni"

Shiga d'akin ta yi tana bin salma da wani irin mugun kallo,cikin neman qarin bayani ta ce wa Talle,

"Wannan fa Talle?"

"Qanwar ki ce, dama na zo ne na kawo ta zan koma, ki kula da ita in ta bar gidannan kashe ku zan da ke da asararrun yaran ki, kun dai san hali na ai"

Ya na gama maganar shi ya liqe ya sa kai zai fita, Marka ta kama qugu cikin masifa ta ce,

"To ina zaka rabon ka fa da nan wata uku kenan, sannan yau kazo ko kwana ba zaka yi ba zaka wuce" 

"Jarababbiya muje na maki ko sau daya ne ba dai jarabar ki in ta motsa har a gaban 'ya'yan ki sai kin nema ba"

Cikin rashin kunya ta furta,

"Eh ɗin na ji muje"

A gaba ta sa shi suka koma d'akin yaran na dariya suna tafawa, ita ko salma qafafun ta ta ja ta yi d'akin da yake nata a yanzu,gado ta faɗa tana kuka mai ban tausayi, ga mijin da take so can da wata qazama yana mu'amalar aure da ita duk suna jiyo wa, ga talaucin da ta hango tsabar shi a gidannan, yau ina zata saka kant ? Kuka take sosai ta ji an banko qofar d'akin nata da ta saya , cikin masifa ta ga wata matashiyar yarinya ta tsaya a kan ta tana fad'in,

" Malama ki je ki qarasa mana abincin tin da baba ya qule daka da marka, yunwa muke ji , dan yanzu kan su fito sai an gan su"

sShewa yaran suka yi suka tafa tare da fad'in ,

"Hahaiiiiiiiiiiii casssssssss "

Miqewa Salma ta yi ido ya yi mata jawur saboda kuka tace,

"Ni na saka uwar taku shigewa d'aki da uban naku da zaku nuna min ku fitsarraru ne?"

"Ni ki ke mayar wa da magana? Yau zamu daga maki qafa ko dan darajar Baba na gari, amma ki kiyaye mu, mu nan da ki ka ganmu zane matan baba muke yi, ki tambaya kiji, sakarai kawai, kema ba zai wuce tarkon baba kika faɗa ba ai kwadayi mabudin wahala ne dama ai,"

Dariya suka saka suka sake tafawa, wata ce a cikin su da bazata wuce shekara 14 ba ta shigo ɗauke da bokiti akan ta na markaden koko, kallon su ta yi ta kauda kai ,

" ke jummala je ki qarasa abinci marka  bata kusa,"

" ku me kuke yi tin dazu baku je ba? Ba in da zani sakarkaru kawai"

wucewa zata yi Huwaila ta janyo ta ta kwada mata mari, kuka ta saka tana fad'in,

" Allah ba zan ba mugaye kawai sai dai ku kashe ni, baku da aiki sai dai kuci ku yi wanka in su yaya Baban gida sun zo su yi ta lalibe ku da sunan wasan abokan wasa kuke yi, ko ji kuke ban sani ba ne?"

Shiru suka yi suka sake ta suka kama hanyar shiga madafin nasu, kuka taci gaba da yi, daga baya kuma a hankali ta yi shiru ta daga kai tana kallon Salma, cikin washe baki ta ce,

" laaaaa kece amaryar Baba da za a kawo dama?"

Daga mata kai Salma ta yi ta shige d'akin ta, shigar ta ke da wuya Talle ya fito daga dakin Marka.............
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼     ' YAN ABUJA  💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

Page 6:

Talle ne ya qarasa fitowa Yana gyara wandon shi, rigar shi kuwa na yafe a kafadar shi, d'aurin qirjin gado ne a jikin Marka lokacin da ta fito daga d'akin nata ta na wata miqa , bakinnan na ta na ta fidda wani wari kamar an bude shaddar gidan haya, hammatar ta har wani kore2 brown2 take, qafar nan fururu da ita kan ya danqare, ba a qanin tsagar kitson ma, kuma gashi ita mace ce mai cika da tsahon gashi amma ba gyara ,yawu ne cike a bakin Talle na kyankyamin Marka ya je ya zubar yana masifa.
Chapter 8 · 0% Book details