Sashe 16
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafawa suka yi suka koma palour suka debo dambun nama da juice suka zauna tare da kunna kallo, sunayi suna hira qarshe waya suka dauka, suka hau kiran Goggo Sarai, suna waya, a lokacin suna tsakar gida dikkan su, Mama Bilki, Abban su Juwairah da ta kai masu ziyara sai Ammar dake zaune a cinyar Juwairiyyah, da ita kanta Goggon, wanki Mama Bilki keyi na kayan Abban su da na Ammar, ita kuma Goggon su na duba girkin ta wanda ta dad'e da dena cin abincin gidan sai dai ta yi nata, su kuma suci nasu, hakan da ta yi yaba Abban damar su samu sauqi daga dawainiya, shiyasa ma wataran suke samun abinda suke aikawa Juwairah dan Mama ta kula da rayuwar da take ciki a zuwan da ta yi sau ɗaya, amma da ta tambaye ta ya zaman nata yake a gidan ta sai ta qeqasa qasa tace ita lafiya lau komai yake tafiya masu, ganin ba zata buɗe baki ta yi bayani bane ya sa Mama yi masu addu'a kawai ta kyale ta, amma tabbas tasan akwai wata a qasa, cikin firgici ta daga kai daga tinanin ta sakamakon wata qara da Goggo Sarai ta saki......[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*SANARWA ! SANARWA !*
*Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?*
*Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA*
*Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each*
*Please share*❤️
Page 11:
Mama na juya wa sai ta ga wai ashe Goggo Sarai dariya take a hakan dan kawai ta ja hankulan su Mama Balki su ji ta na waya da 'Yan Abujan yaran ta da take alfaharin sun haye a rayuwar zaman duniya dai ba ta qiyama ba.
"Hahhhhaaaaaiiiiii kaiiii amma na ji daɗin haduwar ku gaba ɗaya waje guda, ikon Allah ana can ana cin amarci sai yau aka samu haɗuwa kenan, to ya masu gidan? Ya rayuwar hutu da jin daɗi kuma?"
Suwaiba ce ta ce,
"Lafiya qalaou Goggo, ina Baba?"
" Hmmmm ga shi can wajen waccan sallamammiyar matar tashi da ta shanye shi"
" Bashi mu gaisa kar yace bamu neme shi ba"
" Aiko bada wayata ba ehe ku kira shi a yar rakani kashin shi kawai"
Tana fada tana hura hanci tana turo dankwali gaba irin na fitsararrun matan nan? Kad'a kai kawai Baba Baballiya ya yi sannan yace,
" Allah ya kyauta"
Murgud'a baki Goggo Sarai tayi kamar wata qaramar yarinya, irin na rashin kunyar nan da raini ita a dole sai ta nuna ta fi ƙarfin mijin ta kuma ba ta jin maganar shi balle girmama shi.
Makaranta kunsan fa shi murguda bakin ma kala2 ne, akwai sexy murguda baki mai daukan hankalin oga, ya ji dole sai ya kai nashi bakin a naki sabida yanayin yanda ki ka yi shi da salon jan hankali, sannan akwai na rashin kunya kamar na Goggo sarai kenan.
Ganin yanda take masa rashin kunya gaban matar shi da yara shi ne ya sanya shi tashi dan ya je waje ya sha iska sai wayar shi ta hau ringing, d'agawa ya yi da sallama muryar su Suwaiba ya ji a tare su na gaida shi kamar ba sa son gaishe shi,ya kula sarai amma sai ya danne ya amsa tare da tambayar su gidajen su tare da Mazan sannan ya qara da fad'in,
"Ku na nan dai lafiya ba wata matsala ko?"
Cike da rashin kunya suka buga shewa tare da fad'in
'Hhhhh Baba do u really have to ask ? To muna lafiya qalou alhamdulillah, komai normal kamar dai yanda ka sani Baba mazajen mu masu kuɗi ne, so ina ganin ai bamu da wata matsala mu a rayuwa, sannan gida da mazajen namu duk suna lafiya da Fatan mun amsa tambayar ka"
Cikin qunar rai Baba ke magana,
" Suwaiba ni mahaifin ku ne dan haka ba zan gaji da yi maku nasiha akan ku bi duniya a sannu ba, yau in kaine gobe ba kai bane, dukiya da abinda ke cikin duniyar nan ba komai bane face rudin shaid'an ga wanda ya mai da su abin bauta, kuji tsoron Allah a lamarin ku, Hello ! Hello..... "
Shiru ya ji ashe sun dad'e ma da kashe wayar tin da ya fara wa'azi suna ta fad'in yanzu zai takura masu, mamaki ne cike da zuciyar shi Baba ya ce,
" Yaran nan ni suka kashewa waya?"
" Baban su ka yi hakuri komai zai daidai ta da qarfin addu'ar da zaka dinga wa iyalan ka, Allah zai shirya maka su inshaa Allahu, adduar iyaye amsasshiya ce a wajen Allah, Allah ya shirya mana zuria"
"Hmmmmm Ameen Gimbiya ta Allah ya albarkace ki da zuriar mu duka"
Daɗi ne ya kama Mama mara musaltuwa kwatankwacin daɗin da take ji a duk sanda ya yi mata irin wannan adduar,
" Ameen a bin sona"
Murmushi suka yi wa junan su wanda ya sanya shi ya ji baqin cikin shi ya tafi gaba ɗaya ,ruwan wankan da ta saka masa ya ɗauka ya tafi ya shiga wanka abin shi ya fito tsaf,ita kuma Mama sai ta fara qoqarin dora masu abincin dare.
Magidan ta ku dinga qoqarin yi wa matan ku godiya da addu'a musamman ta nema masu albarka a wajen Allah, in albarkar nan ta samu a garesu zata shafe ku kuma da zuri'ar ku kenan,ku kuma mata ku dinga yawan yin abinda ku ka san zai faranta wa Mazajen ku rai su yi maku addu'a, soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa.
Juwairiyyah bata bar gidan nasu ba sai yamma liss cike da tunanin halin da rayuwar gidan su take ciki.
****************************
Bayan kwana biyar da zuwan Juwairiyyah gidan iyayen ta suna hira da Nafee da safe suka shirya yanda suke so Watarana su kai wa Shamsiyyah qawar su ziyara,nan take Nafee ta ce me zai hana su kai mata ziyarar a yau? Juwairiyyah sai ta nisa sannan ta ce,
"To bari mu gani Allah ya sa aiki be sha min kai ba lokacin"
Cikin ran ta kuwa ta na tunanin yawan fitar da take yi a 'yan kwanakin gashi ita ɗin ba ma'abociyar yawan fita bace.
Da yamma kuwa sai ga Nafeesa ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atampa, tayi kyau sosai ta taho bangaren su Juwairah, ganin Juwairiyyah ta yi na harkokin gaban ta ba ma ta da niyyar fita,cikin jimamta lamarin ta ce,
"Matar Yayah ya na ga baki shirya ba kin saka dan guntun wando da vest an faka gashi gefe?"
" Nafeesa kenan da dikkan alama kin manta yau Yaya da wuri zai dawo gida ko? sannan yau ranar dana ware ce domin gyaran lambu na ko duk kin manta qafar yawo? Sannan ga girki da zan yi da wasu aikace2n, kuma sanin kan ki ne ni fa yawon shiga nan shiga can dinnan ba son shi nake yi ba, shike kawo mace ta daina kula da iyalan ta da gida tana qarewa a titi"
Cikin mutuwar jiki Nafee ta ce,
"Hakane kuma gaskiya ki ka faɗa,amma gaskiya ni dai zan tafi gidan Shamsiyya na gaida ta dan na riga na yi niyya kuma na yi mata alkawarin zani yau din, na zaci zamu tare ne tinda na ga ke kin dad'e baki je ba, sai na dawo to"
" To ki dawo lafiya, ina gaida ta da yaran"
Fita Nafee ta yi ta tafi gidan Shamsiyya, ko da ta isa gidan Shamsiyya sai ta tarar da ita a gida tare da yaran ta biyu mace da namiji, Farha da farhan, goyo take yi na 'ya macen , gaba daya gidannan sai a hankali, komai da kan shi yake zaune a inda bai kamata ba,cike da kyankyamin halin da ta samu gidan qawar tasu ta shiga parlour ta zauna a kujera ta na qarewa parlourn kallo,da sauri ta miqe tana duba skirt din ta daya jiqe, hannu ta sa ya tab'o skirt ɗin sannan ta kai hancin ta,wani irin mugun zarnin fitsari ta shaqa, da sauri ta kauda kanta ta fita tsakar gidan ta ɗauki buta ta sa ta ruwa ta wanke hannnun ta sannan ta saka a skirt d'in ta tana masifa ba tare da ta amsa lale maraban da Shamsiyya ke yi mata ba,
"Ni gaskiya shiyasa bana son zuwa wajen ku shamsiyya, ga gida har gida Allah ya hore maki amma sai uwar qazanta, duba dan Allah daga zuwa na na zauna akan fitsari , ko da Juwairah bata haihu ba na san abin da ba za a taba samun ta da shi ba kenan a duk lokacin da ta haihun, yanzu haka saboda gyaran gidan ta da kula da haqqin mijin ta yasa taqi biyo ni, Juwairah na da lokutan yin komai na kula da iyalin ta da gidan ta, tinda ba za a hadu ace kullum zaka haɗa kowanne aiki kayi ba zaka gajiya watarana, sai wanda suka zama aikin yau da gobe, dan Allah ki gyara, dan yana ɗaya daga abinda yasa Baban Farhan yake neman aure duk.da ya faɗa maki amma kin qi gyarawa haba Shamsiyya"
"kaiiii Hajiya bala'i daga zuwa.sai wannan dogon karatu? To dan Allah ya kuke so nayi? Ga aikin gida gana miji gana 'ya'ya, ni dai gaskiya abun ya min yawa ya kuke so na yi ne wai"
Kawai sai ta fara hawaye wai ita a dole komai ya mata yawa, kama hannun ta Nafeesa ta yi suka koma palour ta zaunar da ita a kujera, sai da ta laluba wata kujerar ta ji ba jiqa sannan ta zauna ta fiskanci Shamsiyya ta ce,
"Qawata ki yi haƙuri ki daina kuka ni ba wai ina maki faɗa dan ranki ya baci bane"