← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 61

Sashe 15

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin ya qarasa maganar shi 'Yar Gwale da qawar ta suka tashi tsaye suka kama hannun Alhazan nasu dan kai su d'akunan da suka saba sheqe ayar su tinda sun ji buqatar su za ta biya, kuma Alhazan ba su yin alqawarin karya.

Tin a hanya suka fara romancing din su, ina ganin haka na yi baya na koma gidan Suwaiba naga wainar da take toyawa.

Hango suwaiba na yi tana zaune ta baza kaji a gaba da fresh milk tana darje baki, hankalin ta kwance ba ta da wata damuwa da ta wuce ta faranta ran ta da dukiyar da mijin ta ya ke da ita,hannun ta ɗaya riqe da waya tana dannawa, bayan ta gama cin naman ta ne ta shiga band'aki ta yi wanka ta yi brush, ta saka kayan bacci dan ta yi bacci, amma sam bacci ya qi ɗaukar ta,komawa ta yi palour ta kunna kallo, ta na kallo tana duba lokaci, wannan rayuwa anya za ta yuwu a haka kuwa? ace miji ba zai dawo da wuri ba sai dare ya raba? Tashi ta yi ta dakko fruit salad data hada ta saka a fridge, ta zauna tana kallo tana shan abunta, bayan ya qare ne, ta ajiye bowl din a gefe, sai hamma take tana miqa, duk ta gaji da zaman shirun, wayar ta ta ji tana ringing, miqa hannu ta yi ta dauka, Sunan Saudat ta gani na yawo a screen ɗin wayar ta ta,

"Saudat love"

Shine sunan da ta yi saving No Saudat da shi.

" Hey sis"

"Hi"

"Ya ki ke, da yayan nawa?"

" Muna lafiya, Ya Alhjn ki?"

"Muna lafiya"

"Dama kiran ki na yi na ji ko Baby na gidan ku, tsoro nake ji, gidannan ya min girma ni kaɗai masu aiki na bangaren su, duk dare sai na dinga ji kamar kirana ake,"

Ta faɗa cike da tsoro,shiru Suwaiba ta yi kafin daga baya ta ce,

" Sis kiyi hakuri baya nan, nima zaman jiran mine nake yi yanzu haka, duk yanda akai suna tare, ki kwantar da hankalin ki ki mori abinda ya kawo ki, tin kan lokaci ya qure maki"

Saudat amsawa tai da

"To"

Sallama suka yi suka kashe wayar Suwaiba ta tashi ta yi d'aki, bata jima da kwanciya ba, lokacin qarfe 2:45am ya shigo bakin shi duk warin giya, tsabar kwarewa da suka yi dan shan barasa ko layi na marisa  ba sa yi,sai dai a gane ta idanun su da ke yin jawur, da kuma saurin fushin su,Suwaiba ce ta miqe ta nufe shi a zafafe ta ce,

"Wai wannan wanne irin wulaqanci ne Sweethert, tinda nazo gidan nan i can't remember the last time we had xxx, amma da na yi maka magana sai kace lokacin ban da lafiya a bari na wanke to yanzu da na ji sauqi ka kasa sauke nauyin dake kan ka, amma kai da dikkan alamu har yanzu kayi auren ma wasu kake bi a waje baka dena ba,ga wani sabon hali da na ga kana yi na shaye shaye wai ashe  har da giya ka ke sha wadda ni ban san kai din dan giya bane kuma d'an maye,wannan ai iskanci ne da wulaqanci"

Suwaiba ta qarasa maganar cikin d'aga murya da masifa, a karkace Alhaj Salihu ya kalle ta ya ce,

" Ni ki ke kira dan iska,ni ki ke kira dan iska ko, ba dai ni ki ka cewa dan iska ba suwaiba ? Yau Zaki ga iskanci ganin idon ki Suwaiba"

Miqewa ya yi ya janyo ta ya hau duka kamar an aiko shi, a haka ya cire mata kayan jikin ta ya wurgar duk ya yaga su saboda kiciniya da dambe, wurgara gado ya yi ya ta kanta, Suwaiba kuwa ba abinda take da ya wuce kuka da neman taimakon tare da ban haƙuri,

"Dan Allah Mine ka yi hakuri nice yar iskar ba kai ba, ba zan qara ba , ka taimaka min, ka duba auren soyayyar da muka yi da kai ka yi hakuri"

kwad'e bakin ta ya yi ya ci gaba da abinda yake yi sannan ya ce,

"Auren soyayya ki kai da wa? ko dai auren kwad'ayi auren kudi? Karki zaci ban san ke da uwar ki da qanwar ki kwad'ayayyu bane,  Ina sane da komai, ni ba qaramin mutum bane, kamar yanda ku ka yi auren kuɗi mu ma mun aure ku ne dan kyan ku da biyan buqatar kammu,kowa kin ga ya samu abinda yake so ko Suwaiba 'Yar Abuja? Ko ba haka qawayen ki suke Kiran ki ba?"

Qara wurgata gadon ya yi da take qoqarin guduwa ya kwanta a jikin ta, kamar wani wanda aka yi wa allurar bacci nan da nan bacci ya dauke shi, kuka ci gaba da yi sosai jikin ta na yi mata ciwo, haka ta tashi ta ja jiki da kyar, ta tafi toilet, ruwan zafi ta haɗa mai zafi sosai ta shiga, tana shiga ta yi wata muguwar qara saboda azaba, a haka ta gasa jikin ta sai da ta ji ta daina jin ciwon wajen sannan ta saki jiki ta kwanta a ruwan da ta sake sanya wa nan da nan bacci ya fara diban ta a zaune a ruwan, buɗe ido ta yi ta fita ta je ta saka wasu kayan ta koma ɗaya dakin ta kwanta, ta rufa, nan da nan baccin wuya ya yi awon gaba da ita.

Da asubar fari Saudat ta kira ta a waya tana kuka, ta sanar da ita irin cin mutuncin da Alhj Kalla ya mata itama, sata ya yi ta yi ta masa tausa, har wayewar gari shi kuma ya na shaqar bacci, data fara gyangyadi ya zabga mata mari dole ta farka ta ɗora daga inda ta tsaya, kuka suka yi ta yi a tare ba mai lallashin wani, itama Suwaiba labarin nata bala'in da ta qunsa tayi sannan suka ce gobe zasu haɗu in mazajen sun fita.

Shigowa dakin suwaiba ta ji za a yi cikin sauri  ta danne wayar ta kwanta ta yi lamo kamar me yin bacci, qarasa shiga Alhj Salihu ya yi ya zauna kusa da ita ya ce,

" Haba my Suwai hakuri zaki yi, ke ma kin san in rai na ya ɓaci bana son a cika tambaya ta musamman maganganu na rainin wayo, auren kuɗi ki ka yi kuma ga kud'in nan, to meye na damuna sai na maki wani abun?"

Kuka take a zuci hawaye na zuba ta gefen idon ta bata ce masa komai ba, janta ya yi jikin shi yana shafata, take ta fara sauke ajiyar zuciya tana hamma, don bacci take ji sosai, kiss ya mata ya maida ta ya kwantar yace shi zai fita, d'aga masa kai kawai ta yi ta koma ta lumshe ido, bayan ya fita ne ta yi baccin awa uku ta tashi ta yi wanka , ta haɗa abin karyawa mai rai da motsi da tea mai kauri ta ma manta jibgar da ta sha, taci tai nak abinta, Wayar ta ce ta yi ringing ta amsa da ,

" ku barta ta shigo qanwa ta ce"

Sannan ta kashe, Wajen kamar minti 5 Saudat ta shiga cikin gidan cikin shiga ta alfarma, ga wata arniyar mota da ta zo da ita driver na tuqata, ta ci gold ko ta ina hannu da qafa da kunne, dan harda sarqar qafa suke daurawa saboda wadata ba dan wani abu na,har parlourn sama mai aikin Suwaiba ta yi mata jagora ta na  isa ta zauna kusa da sister din ta akan dinning table ta ja plate ta zuba chips da kwai da farfesun naman kan rago, sai tea da ta haɗa itama mai kauri ta hau sha, ba wadda ta ce wa 'yar uwar ta sannu,sai da ta gama sannan ta yada kai baya ta zame kaɗan daga kujerar tace,

" Sis ina cikin tashin hankali wanda da dikkan alama kema hakan take a wajen ki, dan ga jikin ki nan ya nuna, dubi fuskata nima ki gani"

Ta fada tana mai nunawa Suwaiba fuskar ta da ta yi jawur ta kumbura, sai rufewa ta yi da mayafi da ta shigo gidan kar a gani, sannan ta ci gaba da magana,

"Ga kuma zaman yunwa da na yi dan jiya kwata2 kasa cin komai na yi har safiyar nan, sai da na ga wannan abincin ne na ji yunwa ta motsa min"

Suwaiba ce ta yi murmushin takaici sannan ta ce,

"'Yar uwa bari ki ji, ki cire komai a ranki shawarar da zan bamu shine mu cire rai a son sai sun zama mutanen kirki, tin da dai ba halin su bane, mu zauna mu mori dukiyar da muka zo Abuja domin ta, mu zama manyan hajiyoyi,mu bawa maqiyan mu kunya, dan ni kam kin ganni nan, in ba jiya dana sha jibga ba, bana wasa da abin ci ko wani nau'i na jin daɗi, sannan kuma da kk ganni nan haqqina na aure in daga yau ya ce ya daina ban ba zan damu ba ba zan sake tambayar shi ba, domin kuwa akwai hanyoyi da dama da zan iya maganin matsala ta, wanda na san kema kin san su ba sai na tsaya bayani ba, i hope ba zasu yi gangancin turamu wannan stage din ba, zasu na daure wa ko once in a while ne suna biya mana buqatun mu, to kinga ba mu da matsala da bin matan su ko kuma wani abu mai kama da shan giya, sun dad'e ba suyi ba, dan ba zan qara yarda a taba lafiya ta ba, an gama daga jiya"

" kaiiiii yar uwa wannan shawara tayi sosai"
Chapter 15 · 0% Book details